27
🔥ZINARE🔥
NAFISA ALIYU SASAAL
Page 27
Bayan na katse wayar, rungume kaka na yi, kafin na sumbaci ƙuncinta ina dariya. Kai ta girgiza jikinta a sanyaye.
Kamar ban lura da sanyi jikinta ba na ɗauko waya ina kiran layin Yasar.
"Alhamdulillah!" ya furta da daukakkiyar sauti kafin ya ƙaracewa cikin tsokana "Finally yokel sis zata leƙa Babban Birnin Abyad, har na hango idanuwanki wallahi" Kaka da ke sauraronmu dariya tasa haɗe da sakin ajjiyar zuciya.
Da tsokana muka ƙare wayarmu da Yasar.
Da yammaci Kaka Mallam ta kira, ta yi tsammanin zai soki zuwanmu Babban Birnin Abyad amma sai taji ya furta "Alhamdulillah" ƙwarin gwiwa da addu'o'in tsari kala-kala ya ƙara bata domin acewarsa sanadin zuwan Naila Babban Birnin Abyad ya daɗe ya na jira.
Kafatanin kuɗin na nake tarawa A banki na turawa account ɗin mutanen Yankin Tudu.
Kafin dare kiraye-kirayen su sai shigowa yake yi, abun dariyar duk da wayan mutum biyu ake wayan, talauci ya hana da yawansu mallakar wayoyin hannu.
Kaka bakinta kamar zai yage, banda "Ameen Ya Allah! Ameen thumma Ameen!" Babu abinda take maimatawa. Ba su gajiya da kira ba har sai da chajin wayar ya ƙare.
A jiyar zuciya Kaka ta sauke, lokaci zuwa lokaci sai ta saki murmushin farin ciki. Kusa da ita na matso na zauna Sannan na ce
"ya ya zakiji idan akace mutanen Yankin mu, sun samu farin cikin da ya fi wannan?"
"Zan ji daɗi Naila sama da wanda na ji a yanzu" Kaka ta faɗa da murmushi kwance a saman fuskarta.
"To ki saki ranki mu shiga Babban Birnin Abyad, In Shaa Allah ba zamu dawo ba sai da nasarar da zai kawowa Yankinmu gagarumin sauyi." Murmushi muka sakarwa juna.
Surprise visit Yasar da ƴan gidansu suka kawomana.
Kaka baki ta saki kafin ta kwashe da dariya ta na cewa "wai ni kuyimin bayani wani irin arziƙi Naila zata samo a wannan Babban Birnin Abyad ɗin da kowa yake farin ciki, kar fa muje a siyar da mu" Dariya Yasar da Iyayensa suka kwashe da shi, ƙannensa da suka saba wasa da dariya na tsokanarta.
Cikin raha Yasar yake bawa Kaka labarin da zarar ta shiga Babban Birnin Abyad zatasan ko wanda ya yi wanke-wanken rana ɗaya dole ya fito da kuɗi mai tsoka.
Ana raha da wasa mukayi Dinner da su Yasar.
Sai dare sosai suka tafi Gida.
Washe gari muka fara kimtsa kayan da zamuyi tafiya da shi, amma har lokacin abinda yake bani mamaki shine tayaya za'ace zuwanmu na kwana biyu ne zai warware ƙullin shekaru aru-arun da ko Kakana ba haifa ba, ko dai ta Kaka kashemu za'ayi.
★tsaf na shirya cikin baƙin Abaya haka Kaka same Abaya muka sanya na Company ɗaya. Har Gida ƙaramin ƙanin Yasar ya zo ɗaukarmu domin tare zamu wuce da Yasar don haka sai mun fara biyawa Gidansu.
A dai-dai lokacin da Motarmu ta gifta na hangi Sufyan A cikin Motar da nake kyautata zaton Taxi ne. Mamakin abinda ya kawoshi na yi cikin daƙiƙu kafin na tattara lamarinsa na watsar ina duba wayata.
SUFYAN.
Ƙwallane ya tararwa manyan idanuwansa da suka ƙara zama farare ƙal lokacin da mai gadi ya tabbatar masa da mun fita yanzunan Ni da Kakata. Yasan kuma ba Makaranta na je ba, domin can ya fara biyawa akace munyi hutu, a hankali ya nemi waje ya zauna ya zaro wayarsa. Bugu ɗaya Hindu ta ɗauka.
Ko sallamarsa Hindu bata amsa ba ta ce;
"Ka riski Naila?"
Jiki a sanyaye ya ce; " a'a"
Kuka ta saki na tsayin mintuna shida kafin ta ɗora da;
"Son zuciya shine mafarin halakata, Sufyan mafita ɗaya ya ragemaka, ka koma bakin aikinta ka riƙi aikinka da gaskiya da amana, amma a kowani yanayi ka ji tsoron Allah kuma kaji tsoron Malik, domin baya ganinka ba kuma ya tare dakai amma ka sani yana saurararka a duk inda kake a Babban Birnin Abyad, a yanzu amfaninka a wajen Ɗayyib shine ka bincikomai su wanene DHAHAB? banda wannan baka da wani amfani a gareshi, su kuma su Malik suna tare da kai ne domin ganin iya gudun ruwan Jalal, kamar taku ɗaya haka kake da mutuwarka Sufyan a tsakanin Ɗayyib da su Malik, amma abinda na faɗawa Ɗayyib ya hukuntani shine wanɗanda suka ƙirƙiri sabon Dhahab ba abokanan yaƙar su ba ne, saboda suna da damar shafe Yankin Tudu da mutanen cikinta, domin ko kai kanka da kake cikin Daular ba su san dakai ba, da tuni ka jima da ruɓe a cikin ƙarƙashin ƙasa. Ina gayamaka dukka wannan ne domin kayi takatsantsan kamar yadda malamin duba ya sanar da ni, ina nadama Sufyan, ka yafemin. Ba lallai mu sake magana makamanciyar wannan da kai ba, ba kuma lallai ka dawo ka riskeni a raye ba, amma Allah Ne shaida bani da masaniyar komai a kan kisan su Abduh da ahalinsa." Ɗif wayar Hindu ya katse kamar dai waccen ranar.
Wayar Sufyan ya bi da kallo yana zare idanuwansa da suka koma jajaye cikin ƙarajin da ya tashi dukka jijiyoyin wuyarsa da goshinsa ya ke furta "Ummee! Ummee!! Ummee!!!" A lokaci ɗaya yana ƙara kiran layinta da baya shiga kwata-kwata. Hankali a tashe Mai gadin gidansu Naila ya kiran layin agajin ƙasar. Kafin su iso Sufyan ya zube ƙasa idanuwansa a juye.
NAILA.
Wannan hanyar da nake bi da kallo tsayin shekaru yau gashi zan tunkareshi da ƙarfin ikon Allah.
Tsakanin Birnin Abyad da Babban Birnin Abyad tafiyane da bazai yiwu a ƙafa ba dole sai da mota ko jirgi gashi Customer iyakacin kuɗin jirgin Naila da Kaka ta biya ina masu son su san abinda zai faru a Babban Birnin Abyad?????
In Shaa Allah anan Free pages ɗin ZINARE ya tsaya. Ga waɗanda suka bibiya ba su da halin biya na gode da comments da addu'o'in ku, ga waɗanda suke da wadatar biya suma ina godiya mai tarin yawa Allah Ya bar zumunci.
Kuɗin motar zuwa Babban Birnin Abyad Naira 500 ne kacal ta wannan account ɗin
Nafisat Aliyu Muhammad First Bank 3207955182 tare da tura shaidar biya ta ***,***. Ga masu bibiya kuma ta Arewabooks sai su ɗora. In Shaa Allah zamu cigaba da Posting ranar Monday, 4, August, 2025 da misalin ƙarfe 8:00pm
Na gode🙏🏻