πŸ’žπŸ’žπŸ’žLAILAHπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

page 11

by @gimbiyaayshu

πŸ’žπŸ’žπŸ’žLAILAHπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

STORY AND WRITTEN BY

AISHA MA'ARUF

GIMBIYA AUSHUπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

ELEGANT ONLINE WRITER'SπŸ“š

PAGE 21-22

_________________Direct daki ya shiga bai tsaya parlor ba ya shiga bedroom,jakan shi ya ajiye ya zauna saman gado ya rike kan shi,shi dai changes din da yake ji this days na damun shi,bai san mai yasa yake jin changes in yaga yarinyar ko kuma suna tare ba,tashi ya yi ya cire kayan jikin shi ya shiga wanka,bayan minti goma ya fito daure da towel,gashin kirjin shi da ruwa ya jika su sun kwanta luf-luf gwanin ban sha'awa,share ruwan kan shi ya yi ya busar sannan ya shafa mai,ya yi kyau sosai Kaman balarabe,kujera ya ja ya zauna sannan ya fara shafa lotion din shi a lallausar fatar shi mai kama dana mace,bayan ya gama ya nufi drawer yana takawa daddaya Kaman bai so,wani hadaddan jeans ya ciro kalan blue,farin boxers da singlet sannan ya dauko farin T-shirt an rubuta Handsome a jikin shi,ajewa ya yi saman gado ya nufi dressing mirror ya fesa turare sossai,sai kamshi ke tashi Kaman anyi barin turare a dakin,shiryawa ya yi cikin kayan daya ciro,zo kuga yanda ya fito a kayan nan,a raina na ce"amman Mummy ta iya haihuwa,he look's handsome,ya hadu 100%",turare ya Kara fesawa sannan ya dau wayan shi da car key,parlor ya nufa ya shiga da sallama.

Mummy dake ta jiran dawowar shi ne ta ce"haba son,daga cewa za kaje ka dawo shi ne sai yanzu,wannan wankar fahh! sai ina,ko dai ko dai",ta karasa maganar ta tana dage mai gira.

Hade rai ya yi ya ce"kai mummy! wurin Hydar fa zani".

"Fada gaskiya dai",ta fada tana rike dariyar dake kokarin kufce mata.

"Haba mummy  kema dai kin san halina,ni dai na tafi sai na dawo",ya fada yana hade rai.

"Toh a dawo lfy Allah ya tsare,idan kaje kace Ina gaishe ta,ta fada tare da fashewa da dariya ganin yanda yake ta cika yana batsewa".

Turo baki kawai ya yi tare da kankance ido daya ya ce"Ameen mummy na love you,ni dai Mummy wurin Hydar zani,banda budurwa fahhh".ya fada tare da ficewa.

"Mummy na dariya ta ce"love u too my son".

Bai zarce ko ina ba sai gidan su Hydar,yana isa yayi horn a bakin gate,lekowa mai gadi ya yi yaga shi ne,da sauri ya bude kofar ganin babban abokin dan gidan ne,parking ya yi ya kira Hydar din a waya,bayan ya daga ya ce"hello man ina kake?".

"Ina gida".

"Okh gani a compound".

"Wani compound",ya fada fuskar shi dauke da mamaki.

Hade rai Sa'ad ya yi ya ce" ban san raini,ka fito kar ka bata min lokaci",ya fada tare da katse wayar.

Hydar na fitowa ya hango motar sa'ad,da sauri ya nufe shi ya ce "shege man,ashe dai da gaske ka ke,shi yasa naga gari da hadari,ashe duk dan kai ne,ya fada yana dariya.

Kokarin rufe murfin motar shi yake,da sauri Hydar ya rike kofar ya ce"daga wasa,dan Allah ka bari,kai na bisa wiya,a yi hakuri shalelen Mummy,yan zun dai mu shiga ciki ya fada yana jan hannun shi.

"Toh tsaya ni kam kar ka tuge min hannu na shiga uku".

"Dariya Hydar ya yi har da rike ciki",daukan wayoyin shi ya yi ya fito ya kulle motar.

Jerawa suka yi,suna tafiya Hydar ya ce"man mai ke damun ka ne?",ya fada tare da kure shi da ido.

Cikin dakiya Sa'ad ya ce"mai ka gani".

"A,a ba komi".

"No is not true,gaya min".

"Na ce ba komi",dai-dai nan suka isa kofar parlor,Hydar ne ya fara shiga da sallama sannan Sa'ad yabi bayan shi,Hajiya dake zaune a parlor ta ce"wa nake gani haka",ta fada hannun ta rike da habar ta.

Dariya Hydar ya yi ya ce"taya ni gani Ummi".

"Duba min waje ko da hadari".

Dariya Hydar ya yi harda rike ciki ya ce"nima sai da nace haka wlh Ummi".

"Atoh ba dole ba,rabon ka da gidan nan fah an fi wata uku"

Murmushi ya yi ya ce"ba laifi na  bane Ummi,wlh aiki ne yamin yawa".

"Ba wani aiki,baka yi niyya bane kawai".

Shiru kawai ya yi yana sosa kai fuskar shi dauke da murmushi,dukawa ya yi har kasa ya gaishe ta ta amsa ta ce"ya kake son?,ya aikin da kake cemin yana hanaka zuwa guna?".

Yana murmushi ya ce"lafiya lau Ummi ya gida da rigimar wannan abokin nawa".

"Ahhh rigima kam kullum sai kara karuwa yake,i wannan abokin naka sai addu'a".

Turo baki Hydar ya yi ya ce"kai Ummiiiiii!,mai nayi,ya fada tare da zama kusa da ita ya kwantar da kan shi a kafadar ta".

"Kaga irin ta kohhh!,ban gama magana ba,har yanzu bai san ya girma ba,shekara 28 fahh!".

"Dariya Sa'ad ya yi ya ce"kina barin shi ne Ummi shi yasa,marin shi za ki yi".

"Toh gulma hada fada,karshen abin dai ko aure na yi bazan bari ba a heee,ni da Ummi na kuma a hanani shanawa".

"A'a ni kam babu ruwana,in ka yi aure diyar ce tawa,kai kuma za ka koma gefe".

Dafe kirji Hydar ya yi ya ce"ni din Ummiiiiii!,nine auta fahhh!",ya fada yana turo baki.

"Gwalo Sa'ad ya yi mai yana dariya".

Dama abinda kake so kennan,toh bazan yarda ba,mai kwace min Ummi na sai ya shirya.

Ka bi ka cika shi da surutu baka kawo mai kayan motsa baki ba.

"A koshe nake Ummi".

"I kuma inda ka yi karya kenan,sai ka ci".

Kitchen ta nufa da kanta ta hada mai kayan ciye-ciye a tray kaman su shawarma,doughnut,fishroll da holandia,tana juyowa ta gan shi a bayan ta.

"Kawo na Kai Ummi",a'a barshi,nacewa  ya yi har sai data ba shi tana sa mai Albarka,a nan kam ka fi wannan abokin naka hankali,murmushi Sa'ad ya yi yana kannewa Hydar ido.

"Wa ya fi hankali Ummi?".

"Waye toh idan ba kai ba".

"ohhhhh! Ummi,mai yasa kike min haka yau,dan kin gan shi kohhhh!",ya fada tare da turo Baki irin na shagwababun yaran nan.

"Zo muci sarkin surutu,matsowa ya yi ya dau shawarma,suna ci suna hira har suka cinye tas,dama Sa'ad bai ci komi ba ya bar gida,hamdala ya yi ya kwashe kwanonin ya kai kitchen,bayan ya dawo ya zauna suka cigaba da hira,suna cikin hira aka kira sallar magrib,fita su ka yi zuwa masallaci bayan sun yi alwala,bayan an idar suka shigo gidan,direct part din Hydar suka nufa,bude kofar ya yi suka shiga,a parlor suka yada zango.

Yauwa dazu na ce"mai problem dinka".

Kai tsaye Sa'ad ya ce"mai ka gani,I have no problem".

Ohhhh! haka za ka ce,toh shikenan,kokarin tashi yake ya rike shi ya ce"haba aboki zauna zan gayama,I don't know was wrong with me too sai in ta tunaninta".

Ido Hydar ya zaro yana kallan shi da alamun mamaki,am worried in ban gan ta ba,inna gan ta kuma I feel some how,and I like her voice with her mode of dressing,tagumi Hydar yayi yana kallan shi baki bude,juyowa ya yi ya taba Hydar ya ce"kana jina kuwa".

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce"anya ba gamo ka yi ba".

Hararan shi Sa'ad ya yi ya ce"u see,daz y I don't want to tell you".

"Wait wait! are u serious,ban taba jin ka yi maganar mace ba".

Tsaki Sa'ad ya ja zai mike Hydar ya yi tsaurin mai da shi zaune ya ce"wait dan Allah am serious,wai dagaske ka ke".

"Kaga na yi kama da mai wasa da kai ne".

"Ikon Allah,toh ina yarinyar take,yarinyar nan na da sa'a,gaya min sunan ta and ina kuka hadu",ya karasa maganar shi cikin zakuwa.

Shiru ya yi daga baya kuma ya ce"she's my student".

Bige kafadar shi Hydar ya yi ya ce"shege,kace NIDA DALIBATA ce",ya fada tare da fashewa da dariya.

Ka gani kohhh!,matsala ta da kai kenan"mtswwww".

Kokarin tsayar da dariyar shi ya yi ya ce"sorry friend,ya sunan ta?".

Banza ya yi da shi,sai daya gama shan kamshi sannan ya ce"khadijat".

Wow sunan Ummina,ya fada tare da rungumar shi..................................

COMMEMT

AND

SHARE

BY GIMBIYA AYSHUπŸ’žπŸ’žπŸ’ž.