πππLAILAHπππ
page 14
πππLAILAHπππ
STORY AND WRITTEN BY
AISHA MA'ARUF
GIMBIYA AUSHUπππ
ELEGANT ONLINE WRITER'Sπ
PAGE 27-28
________________________karfe bakwai ya shiga gida,direct main parlor gidan ya nufa,a parlor ya tadda mai aikin su tana mopping,kai tsaye ya ce"Hajiya bata sauko ba?".
Ta sauko dazu amman yanzu tana sama.
Kada kai kawai ya yi ba tare daya ce komi ba ya nufi upstairs,knocking ya yi ya shiga da sallama bayan Mummy ta bashi izinin shiga.
Zama ya yi gefen drawer yana langwabe kai ya ce"Mummyna gud morning,kin tashi lafiya?".
Mummy na murmushi ta shafa fuskar shi ta ce"lafiya Lau my son,ya ka tashi,fatan babu wata matsala dai koh?".
"Alhamdulillah Mummy komi lafiya".
"Daddyn kama zai shigo yau insha Allahu".
Allah ya kawo shi lafiya Ameeen,nayi waya da shima dazu.
"Okh,baza kaje aikin bane yau?".
"Zani fa Mummy,yanzu ma zanje na fara shiri".
"Okh je ka shirya,is already pass seven".
Mikewa ya yi yana gyara zaman hular kan shi ya ce"ba ni da lectures da wuri shiyasa".
Okh toh,yi maza kazo ka yi break kafin ka fita.
************************************
Washe gari tunda suka tashi da asuba basu koma barci ba,kitchen suka nufa gabadayan su,lafiyayyan break suka hada kaman egg and yam,soyayyan Irish,yam bons,ruwan bunu,da pepper soup,Karfe 7:30 dai-dai suka Kammala Ramlat da Husna suka jera kulolin a dining suka wanke kwanonin da aka bata tare da tsaftace wurin.
Fita Lailah ta yi daga kitchen din bayan ta gama girki,wani irin zafi take ji,ji take kaman a saka ta cikin oven,ko kayan jikin ta bata cire ba ta fada toilet hannun ta rike da towel,bayan minti 15 ta fito daure da towel a kirjinta,shiga Ramlat ta yi bayan Lailah ta fito.
Mai ta shafa sannan ta yi light make-up,bude jakar kayan su ta yi ta ciro wani riga da skirt na lace kalan maroon da black da inner wear,cikin minti biyu ta gama shiri sannan ta yi daurin ture kaga tsiya,ta yi kyau sosai kaman ka sace ta ka gudu,hada baki Raihan da Husna suka yi wurin fadin"wow Aunty Lailah kinyi kyau sosai,u look so muahh"suka fada tare da huro mata kiss.
Wannan wankan haka gaskiya yau Akwai outing mun kashe islamiyya,suna cikin magana Ramlat ta fito,tana ganin Lailah ta ce"kai Antyna irin wannan kyaun hakaaaa!,gaskiya idan yaya ya gan ki bazai gane ki ba,wlh kin hadu over matar yaya",ta fada tare da fashewa da dariya.
"Galla mata harara Lailah ta yi tana hada fuska".
Dariya duk suka yi har da faduwa kasa,bayi Raihan ta shiga tana dariya ta ce",sai kin yi matar yaya ko ba poster".
Ficewa ta yi daga dakin fuskar ta hade,dakin Mum ta nufa ta shiga da sallama,gaishe da Mum ta yi fuskar ta dauke da murmushi.
Amsawa Mum ta yi ta ce"kinyi kyau sosai daughter,zaku fita ne,?".
Murmushi kawai Lailah ta yi ta sunkuyar da kanta kasa ta ce"ban dai sani ba,na dai ji Raihan ta ce"zamu fita".
"Toh shikenan ba matsala,sannun Ku da aiki daughter,kun yi kokari sossai".
Murmushi kawai Lailah ta yi ta ce"Mum the food is ready let go and eat".
A tare suka fita,dakin su Lailah ta nufa ta kira sauran.
Kujera taja zata zauna Mum ta ce"dan Allah daughter kira yayan ku kafin ki zauna".
"Toh mum",ta fada tare da ficewa daga dakin.
Part din yaya Abba ta nufa tana tafiya kaman kwai ya fashe mata a ciki,kwankwasa kofar ta yi gaban ta na faduwa,sai da ta yi knocking kusan sau biyar kafin ya bude kofar,yana bude kofar ya yi ido hudu da Lailah,bai san lokacin da murmushi ya subuce mishi ba.
Saukar da kanta kasa ta yi tana wasa da yatsun hannun ta ta ce"ina kwana Yaya Abba,Mum ta ce wai kazo muyi break",tana gama magana ta juya za ta bar wurin.
"Saurin meh kike?",ya fada tare da harde hannun shi a kirjin shi yana aika mata da wani sanyayyan kallo mai narkar da zuciya.
Girgiza kai ta yi ta ce"babu komi".
Murmushi kawai ya yi ya ce"jeki ina zuwa".
Kaman dama jira take,nan ta fara tafiya da sauri kaman zata kifa.
Murmushi ya yi tare da kullo kofar shi,wanka ya yi,bayan kaman minti ashirin ya fito tare da kullo kofar.
Main parlor gidan ya nufa kai tsaye,ko daya isa sun fara break.
Kujerar dake tsakanin Muhammad da Lailah yaja ya zauna.
Gaida shi duk suka yi ya amsa sannan ya gaida Mum.
Hararar shi Mum ta yi ta ce"da baka fito ba i".
Dariya ya yi ya ce"na tsaya wanka ne shi yasa".
Bayan sun gama break suka tattara kwanonin zuwa kitchen Husna da Ramlat suka wanke tare sa gyara wurin.
Bayan sun kammala Muhammad ya musu hotuna,sun yi kyau sosai masha Allah.
Yauwa Son ina san ka kaimin yaran nan shopping.
Murmushi ya yi ya ce"babu komi Mum",shi kam i wanan dama ce a gare shi,bai ki kullun a dinga aikan shi ba muddun princess din shi na nan.
Murna duk suka yi amman banda Lailah,daki su Husna suka nufa suka feshe jikin su da tulare.
"Baza ki bisu ba Lailah?".
Murmushi ta yi ta ce"a'a Mum nikam na gama shiri".
Fitowa duk suka yi a shirye.
"Miko min waya ta Ramlat",cewar Mum,ba jimawa ta dawo rike da wayar a hannun ta.
Yauwa ban account number ka na maka transfer.
Murmushi ya yi ya ce" ki barshi Mum".
"Okh tom shikenan Allah ya kiyaye ya dawo daku lafiya".
Sallama suka yiwa Mum sannan suka bi bayan shi.
Lailah bata so ba amman hakanan ta bi bayan su babu yanda ta iya.
Bin bayan shi suka yi,gaba daya suka shiga baya,fuskar shi ba yabo ba fallasa ya ce"wata ta dawo gaba,shiru duk suka yi babu wacce ta tanka har tsawon minti uku,rufe kofar bangaran shi ya yi yana mai umurtan Lailah data dawo gaba,hade rai tayi tana turo baki tare da kunkuni kasa-kasa,hakanan ta koma gaba babu yanda ta iya,bata gama gyara zaman ta ba yasawa motar lock tare da kunna ac ya dage glass din da aka saukar,tada motar ya yi ya nufi gate mai gadi ya bude yana mai a dawo lfy.
Wani babban supermarket suka nufa ya yi parking a inda ya kamata,fitowa duk suka yi suka shiga ciki,basket kowaccen su ta dauko,bayan sun gama suka nufi wurin biya aka yi lissafi kudin ya tashi 700.000, packaging komi aka yi a leather aka kai mota,daga supermarket basu zarce ko ina sai wurin shan ice cream,bayan sun gama suka nufi yawon bude ido,basu suka dawo gida ba sai uku da arba'in,a gajiye duk suka dawo barin ma Lailah duk ta yi laushi,Mum dake zaune parlor ta ce"sannun ku da zuwa yammatan Mum,an dawo lafiya?".
Hada baki suka yi wurin gaishe ta ko wacce na naiman wurin kwanciya,Lailah ko wurin Mum ta nufa ta zauna tare da kwantar da kanta a kafadar ta.
Dariya Mum ta yi ta ce"lallai kam na yarda kun gaji,ku tashi ku watsa ruwa,Lailah ta yi wanka a daki na,Husna shiga dakin yan biyu,ku kuma kusan yanda za ku yi da kanku",ta fada tare da tafa hannu.
Amsawa duk suka yi tare da mikewa tsaye,ko wacce ta nufi dakin da za ta yi wanka.
Zaune suke a parlor bayan sun kammala cin abincin dare suna shan kayan zaki a lokaci daya kuma suna hira,in kaga yanda Mum ke hira da su Lailah ba zaka taba cewa ba ita ta haife su ba sabida yanda suka shaku da ita sosai......................................................
COMMENT
AND
SHARE
FISABILILLAH.
BY GIMBIYA AYSHUπππ.