NI DA GIDANA BOOK 1

NI DA GIDANA page 1

by @zainab221

NI DA GIDANA

BY

Zainab ilyas mazawaje

Best brilliant intelligent writer

Baa yarda a juya wannan littafiba ta kowacce irin siga ba tare da izinin marubuciyar ba

🌹

🌹🌹🌹🌹

Page 1

Laila ta numfasa ta dubi sumayya tace "Allah yaja da ran gimbiyar mata, Allah ya k'aro twin's biyu bayan su Abalkhair. "

Murmushi Kawai tayi. Saboda sun jima suna yi mata nacin labarin rayuwar'ta saboda ta zamewa kowa kamar abar shaawa da kwatance.

Amma fa ga Wanda ya San'ta ko ya gan'ta ko labarin'ta da ya shahara ya riski Mutum.

Bayan Sati biyu kuwa Sumayya ta cika alk'awari ta basu rubutaccen labarin'ta.

_______________________

jigon al'amarin kaddara

Had'uwa ta da Fa'iz Bukar, daga nan k'addarar ta soma.

__ Ajin ya kaure da hayaniya saboda rashin malami,dama kuma al'adar 'yan a jin na mune surutun, koma da malamin, saboda sunci sunan mun gagara.

Ni da nake monita na tashi na duba time table, domin naga wani malamine da mu a lokacin,naga English teachear ne, wato malamin turanci.

Na nik'e na nufi taff room in da mu kaci karo da malam Abba class teacher d'in mu. Na rusuna nace.

"Sir, babu malami a ajin, Sai hayaniya kuma suke sunk'i yin shiru."

"Wani malami ne daku bai shigo ba?". Yace.

Nace "English teachear ne sir, kuma anyi masa transfer,sabon malamin da a kace yau zai soma zuwa kuma bai zo ba."

Da sauri yace.

"Ai kuwa yazo. Malam Fa'iz sunan sa, yana ma staff room suna ganawa da princepal na baro su.muje na nuna miki shi, ki fad'a masa period d'in sa ta Shiga, bai Sani ba ne."

Ban da shi malamai uku ne a staff room d'in biyu maza, Sai malama wasila dake aikin sa hannu a test a gefe guda.

Yana gefe d'aya shi kad'ai a zaune yana duba wani text book. Dole da ka Shiga, shi zai fara d'auke maka idanu, saboda farar fatar'sa irin haka ta shuwa a rab. Matashin saurayi ne da duk cikin malaman babu mai k'asa da shekarun sa, sai dai sama.

Ni dai Ina yin tozali da shi, na Shiga mamakin sake had'uwa ta da shi a karo na biyu a rayuwa ta, kuma zai zomin a matsayin malami. Ko da yake had'uwa ta da shi d'in ma ta farko, ba wani a bu ya Shiga tsakani na da shi ba, face wayata da na tab'a yarwa ya tsinta ya kawo min.

Tsawon Wata tara Kenan.

Amma a bin mamaki nunawa yayi kamar bai tab'a gane ni ba, da ya d'ago kai muka had'a idanu. Sai da ya wani ja a ji, cikin jin kai, Sannan yace da k'yar.

"Kece monita"Yace.

Na gyad'a kai.

"Yes, sir".

Har ya mik'e nayi ni kuma gaba, ya kirani yace.

"O K. Jeki, gani nan zuwa.'" Ya koma yayi Zaman'sa kuma bansan dalili ba.

Ban jima kuma da Shiga ba, Sai gashi ya shigo. Duk da an ga shigowar'sa ba'a saurara da hayaniya ba, kuma duk kuma da jarabar kallon da a ka bishi da shi, kamar bak'on halitta.

A haka ya soma gabatar da kan'sa cikin harshen turanci. Ya dakataYace

"Keep Quiet. I said keep Quiet. "Amma ba'a rage Surutu ba. Ai sai ya daka Mana Wata irin tsawa da dank'ara mana zagi, ya zarce da.

"Ku wad'an ne irin jakai ne ku, a na cewa Kuyi shiru baza Ku yi ba?"

Ai kuwa sai tsit ka ke ji , saboda dalilai biyu. Farko tsorata, na biyu babu wani malami da ya tab'a zagin mu, saboda ji da mu da malamai suke, koma me muka yi.

Amma shi wannan daga zuwa har ya fara yi Mana lugude? Saboda Surutu Kawai ma?.

Tabbas da a lamu zai fita zakka. Domin da jin kai da tsare gida ma ya shigo class d'in. Shiru yayi kuma yana ta harare harare da nufin yaga wata tayi ko uhum! yaci zarafin'ta, haka na karance shi. Babu Wacce kuwa ta kuma yin ko tari.

Yayi sanyi kad'an ya soma magana cikin harshen Hausa kuma.

"My name is fa'iz Bukar. Ba wasa ne ya kawo ni nan ba. Kuma bazan d'auki ko wani irin iskanci na d'aliba ba. Kuyi k'ok'arin Sani na kafin ku fad'a tarko na, shine maslaha a gareku. Bana son wasa, ko kusa cikin darasina.

Bana kuma shiri da dak'ik'ai da jakai da basu San me ya kawo su makaran ta ba. Dole ne ni a iya darasina in dai na karantar. Idan yarinya bata fahimta ba, to ta tambaya,bayan wannan bata da uzuri kuma na cewa bata iya ba.Duk wacce tayi sake ta fad'o tarko na, to ta Shiga uku,

ni bansan kalmar hakuri ba, ballantana tayi ceton ta. Ba wasa ne ya kawoni ba, na sake jaddadawa."

Ya nuna ni da pen.

"Ke monita lallai ki kula da hak'k'in aikin ki, ko kuma ki kwana a ciki. Duk mai Surutu Ina writing ki rubutamin sunan'ta. Kuma kiyi copy na time table ki kawo min anjima.

"Sit down" .

Yace, batare da ya kalleni ba, cikin jin isa.

Na zauna.

Note yayi mana muka kwafa. Yayi dogon bayani da turanci, yace duk wacce bata gane ba, tayi tambaya. Amma shiru kake ji. Iya tsiya da fad'in rai yasa wad'an da basu gane ba ma suka yi shiru.

Ko a jikin'sa. Yace Kowacce taje tayi bita kafin ya dawo.

Yana fita a ka rud'e da sowa. Yasha zagi, a d'abi'ar cin mutunci da ya soma da shi. Ya kuma Sha zuga da yabawa a b'angaren halitta. Ba'atab'a Samun malami mai kyau da a ji irin sa ba, bama iya cikin makaranta ba. Da ganin sa kaga half cast. Wato ruwa biyu.

Yabar a bin fad'a Kam da k'orafi. Saboda baki d'ayan makarantar, babu a jin da malamai ke tarairaya kuma a ke ji da su irin mu. Bawai ga k'ok'ari ba, Sai dalilai biyu. ''ya'yan masu kud'i su suka cike fiye da rabin a jin. Sannan babu a jin da ya kai shi tsula tsula kuma kyawawan 'yan mata gagara gasa, daga kan farare zuwa bak'ake. Idan Mutum ya zagaye a jujuwan d'alibai ko'ina

Mutum zai rantse tsince kyawawan 'yan mata a kayi na makarantar a ka zube a a jin mu.

Shi yasa yawancin malamai suna da wad'anda suke so cikin class d'in mu, dalilin da yasa kenan saisuyi ta tsiya ba'a yin komai na hukunci.

Amma duk da haka a Kwai d'alibai tsirari a cikin a jin 'ya'yan talakawa, kuma wad'an da baza'a ce musu kyawawa ba, kuma baza'a kushe ba. Wato irin mu, har dani.

Ni kad'aice ban tofa komai ba, a kan sabon teachear d'in namu. Wato Fa'izu Bukar.

Takun'sa ni ya burgeni sosai, saboda ta hakan na tabbatar zai yi maganin tsagerun d'alibai masu kuma nuna isar sunfi k'arfin komai. Kuma dole Zai kawo gyara da zakkarar da shagalallun d'alibai da dak'ik'ai. Saboda babu Wata alama ma da ya nuna na wata yarinya ta isheshi kallo ballantana a ce ya k'yasa da har zata samu damar kawo masa lalata.

Fari ne sosai, da ganin Sama kasan cikin iyayen'sa a Kwai sirki.

Bayan farin fatar sa a goge take, irin gogewar da ba'a cika samu ba cikin Hausa Fulani.

A gefunan fuskar sa a Kwai k'asumba da ta d'an feso, dake nunin yana da baiwarta askewa yake.

Idanuwan'sa madaidaita ne, masu launin shud'i, irin idanun nan da idan haske yayi haske yake dan ba da launin shudi.

Yana da dogon hanci sosai, da madaidaiciyar hab'a da k'asumbar sa ta zagayo ta kewaye ta, tayi masa wani irin kyau da ta dace da tsari da ita kanta siffar halittar tasa.

Babu a binda yafi komai yi masa kyau, irin turuwar girar sa bak'a da gashin kan'sa da suka d'ai sun isa bada shaidar irin jinsin da ya cakud'u da shi, ga Wanda yayi musu farin Sani. Wato (Shuwa).

Madaidai cine a tsawo. Yana da diri irin Wanda mata suka fiso.mai cikar b'araza da gab'b'ai ,da fad'in k'irji. Bashi da rama Sam. Kuma bashi da k'iba sosai. Idanuwa bazasu tab'a k'osawa ba da kallon'sa, musamman mace. Kome take nema ga namiji, na dai surar kyau, to dole ta taka burki, idan tazo kan Fa'izu Bukar. Sai dai fa idan tana k'yamatar namiji mara sakin fuska, mai jin kai da wulak'anci, tofa baza ta iya da shi ba Sai dai hak'uri.

Cinnaka ba Sani babu sabo, ko kuma mai kyawun dan maciji.

Kirarin da naji d'alibai ke yi masa kenan, wasu lokatan.

Amma Sai da ya d'an jima a makarantar yaci wadan nan kirarin sunayen.

domin lokacin ne kowace d'aliba tasan wanene Fa'izu Bukar, domin halayen sa sun bayyana a sarari sosai.

Alkalamin...... ✍️

Zainab mazawaje