JADEEDA

Page 32

by @cwtsumiey19988

Part 32

Kai tsaye Jadeeda bayan sun yi landing Eko Hotels and Suites da ke located at Plot 1415 Adetokunbo Ademola Street, PMB 12724, Victoria Island, Lagos, ta nufa hotel ɗin da yake ɗaya daga cikin hotel ɗin da su kai Shura a cikin Garin Lagos  ya na ɗauke da kimanin 825 rooms and suites across  four multistory buildings,tun kafin su isa ta ke trying ɗin wata number amma cikin rashin sa'ah har yanzu ba ai picking ba,sai faman tsaki ta ke saki time to time ta na ƙara gwada kiran,can kiran na gab da sake katsewa ba tare da an daga ba akai picking,tare da cewa,,"I'm so sorry friendy ,bcos I'm in a noisy environment, that's why I'm not picking your call."shiru Jadeeda ta yi ba tare da ta ce da ita komi ba,hakan ya sa ita kuma ta kasa iya jurewa har sai ta ce da ita,"Ki yi min magana mana kin san tun muna yara bana iya jure shirun ki",cewar Ruth  cikin son shawo kan Jadeeda,daga nan Jadeeda na jiyo sautin kiɗan dake tashi a wurin da ta ke,sai a lokacin ta ce da ita,"Ban san sai yaushe za ki sauya ba Ruth yau kina wancan Partyn gobe kina wancan,anya kuwa?"...."No...no..no sis ba haka ba ne ba,na tuba fa na bar duk waɗannan halayen yanzu haka muna Birthday Party Fredrick ne shiyasa ","Oh really?,yanzu fa haka ina cikin Lagos,na so in yi surprise ɗin ki shiyasa ban gaya maki ba har sai da na iso",wata ƙara Ruth ta saki tana mai tsalle kafin ta ce,"Tell me kina ina,gayamin  I'm eager to see you,yanzu zan bar duk abinda na ke in taho", murmushi Jadeeda ta saki kafin ta sanar da ita inda suke,"To ai a cikin Hotel ɗin muke gudanar da Birthday Partyn ɗin ganinan maza ƙaraso in yi welcoming ɗin ki,wanne Room ɗin ki ke ne ","Room 263 ",ta Bata amsa a taƙaice,tamkar waɗanda su ka kwashe tsawon wasu shekaru ba su haɗu ba haka suka  rinƙa murnar ganin juna,"Na yi murnar ganin ki,ba na jin kin taɓa burge ni irin yau,ban san da wacce murya ko hanya zan iya nuna maki jin daɗi na ba","Kin ga ni kaina I'm so happy,kin san bikin Ester da za ai shine Church ɗin (SCOAN),,   Suka gaiyace ni a Matsayin zaɓaɓɓiyar mawaƙiyar su","wata ƙara Ruth ta saki mai ƙarfi kafin ta dakata da cewa,"Kai abun alfari na ji daɗin jin haka,tafi-tafi sai ƙara samun ɗauka ka ki ke yi","Ke dai bari duk hakan ya na faruwa da Encouragin ɗin a da ku ke min tun muna school","Haka ne yanzu abinda ya kamata  Sister ta shi ki fresh up mu tafi Partynnan tare da ke,ba ƙaramin murna Fedrick zai yi ba idan ya gan ki a wurin,saƙon isowar ki shine zai zama Birthday gift ɗina a gare sa ","Ah I'm tried I can't go anywhere,na gaji sosai ko kin manta gobe ne z mu fara shagulgulan bikin Ester,don haka ina buƙatar hutu kafinnan","Kema kin san ba zan bar ki ba,kin ji my dear, please just thirty minutes ya isa","Amma dai  kin san hakan ba zai yiwu ba ko,oyah mu je tashi ki shirya",da haka ta tursasa ta har sai da ta sa ta shirya suka fita tare.
"Ku saura! Kussurara!'',Ruth ta shelanta bayan ta amshi mike a hannun Dj ɗin,"Ko kunsan wannan hall ɗin yana ɗauke da baƙuntar fasihiya kuma sananniya a cikin sa,Look who we have here,the one and the only Lucifer,ita da kanta tana jealous ɗin zaƙin muryar ta,Afrika wake up, waiting to listen her song,the nation rise and shine, her voice is in the anthem of the country,A.k.A Jadeeda Anderson",ta kai zancen ta na mai nuna saitin inda ta ke a tsaye,nan fa gabaɗaya hall ɗin suka fara ihu gami da taɓi da ambaton  sunanta,wasu sun santa a fuska wasu kuma muryarta kawai su ka sani.
    Fedrick ka sa motsin kirki ya yi,bai yi zaton zai sake ji ko ganin ta a sauran rayuwarsa da tai ma shi ragowa ba,yaso ta so mai tsanani,so mai tsayawa a cikin rai da zuciya,so irin mai yankan shakkunnan,ganin da gaske itace ɗin ya sa ya zubar da duk kyaututtukan da su ke a hannunsa ya ƙarasa inda take cike da sassarfa dakuma shauƙin ganinta,yana zuwa bai jira komi ba ya haɗe jikinta da na shi.
    Sai da ya gaji dan kan shi sannan ya raba jikinsa da nata,"Na yi kewa ki Angelenah,Son ki na ƙoƙarin durƙusar da ni ya hana ni zuwa ko ina ,ya dakatar da ni da ga samun ko wanne cigaba na rayuwa,ina son ki da dukkan raina Jadeeda Anderson",wani ihu gabaɗaya Hall ɗin ya sake ɗauka,"Ki ce da ni wani abu mana ba zan iya samun natsuwa ba in har ban ji wani abu daga gare ki a yanzu ba",ya kai zancen yana mai sake haɗe jikin su a karo na biyu,duka ta kai masa da hannu tana mai sakin murmushin yaƙe a kan fuskarta,sai da ta kai bakinta saitin kunnensa kafin ta fara cewa da shi,"Za ka fara ko,ko kamanta a inda ka ke ne,nan ba University College of London (U.C.L) ba ne ba,don haka ka ɗan riƙe kan ka kaɗan zuwa a tashi",ta kai zance tana mai fuskantar shi gami da jujjuya masa idanunta bai san sanda komi na shi ya daskare ba,wanda ita kuma tai amfani da wannan damar ta sa Dj sakar ma su sautin waƙar Dr Sid and DJ Sose Mai taken Over the Moon,da wannan damar ta samu hankalin mutane ya kauce akan su,sai dai me duk inda za ta sa ƙafarta Fedrick na biye da ita,haka har su ka tashi daga Partyn,a hankali ta ke tafiya ta na yi tana waigen baya duk tana haka ne don ƙoƙarin  gujema sake haɗuwa da shi take amma ina haƙan ta bai cima ruwa ba,domin sai ganin shi kawai ta yi ba tare da ta yi zato da tsanmani ba,da alama ya sha ya bugu sosai,bayanda ta iya dole sai kama shi tai ta nufi Room ɗin tada shi,da kyar ta samu ta iya kai shi cikin Parlonta  shima sai da taimakon Waiter na hotel ɗin.
   Kamar wacce tai tsere haka ta ke sakin numfashi da huttai,wayarta ta laluba tana mai fara kiran number Ruth,a ɗan zafafe ta fara yi mata magana da cewa,"Ruth wai ina ki ka shiga ne,tun ɗazu sai neman ki na ke ban gan ki ba,kina ina",cikin rashin gaskiya Ruth ta fara yi mata magana cikin inda-inda,ba tare da ta faɗa mata inda take ba"Koma ina ki ke,ke ki sa ni,amma ki gaggawar zuwa ki fidda min Fedrick daga cikin Room ɗina","....Fedrick Kuma garin ya akai ya san Room number ɗin ki da har zai zo wurin","Ya sha wine ne ya fita daga cikin hankalinsa,Ni kuma ba wani sanin friends ɗin sa na yi ba,balle in samu wani ya tafi da shi,don haka ki ma za ki zo ki san yanda za ki yi ,ki fitar min da shi","Okay okay I'm on my way ganinan tafe".
  Cikin yanayin wanda ya sha ya bugu Fedrick ya matso kusa da ita tare da cewa,",Ba wai ....sai kin....kin.kin... kira wani ba kawai ki bar ni,mu kwana a tare ko kin manta mu ɗin masoya ne,kuma wata rana Aure za mu yi,don haka kar ki wani damu...",ya kai zance ya na mai yunƙurin faɗowa kan ta da sauri ta janye daga wurin ya faɗa kan three seater da ke kusa da su.
   "Kar ki bari a tafi da ni don ko an tafi dani sai na dawo,domin zuciyata tana liƙe da ta ki ne,ba zan samu natsuwa a cikin barci na ba har sai na jiki a kusa da ni,sai na ji numfashi da kuma bugun zuciyar ki a saman ƙirjina"......irin wannan maganganun ya rinƙa faɗa har barcin Giyar ya kwashe shi,sanda Ruth ta zo bai ma sani ba,ita da taimakon saurayin da Ruth ɗin ta zo da shi da kuma security guda ɗaya suka sanya shi a motar su ka nufi kai shi gidan sa.
   Wata kyakkyawar ajiyar Zuciya Jadeeda ta saki ta na mai dafe gefen kanta da yai mata nauyi,wuri ta samu ta zauna gami da rafka tagumi da hannu bibbiyu, abubuwan da suka faru tsakaninta da Fedrick ne suka fara dawo mata a cikin kwakwalwar a lokacin baya ta da sauri ta runtse idanunta gami da miƙewa ta nufi bedroom ɗin ta bakin ta ɗauke da addu'ar Allah ya sa ta gama abinda ta zo yi lafiya ta koma Gida lafiya ba tare da wani abu makamancin na baya ya sake faruwa da ita tsakanin da Fedrick ba,sosai ta dage da addu'ar Allah ya sa su rabu lafiya ba tare da hayaniya ko hargitse ba,ko isasshen barci kasa samu ta yi ,saboda ta sa shi a cikin ranta,har dana sanin kawo shi cikin ɗalinta ta rinƙa yi da ma ta sani a can waje ta yasar da shi ba tare da ta kula dashi ba,balle har ta kawo shi Room ɗin ta.
    Yau Ester Sunday ta ɗau wankanta cikin expensive dress nata cikin jerin wanda Uncle Miey ɗin ta ya saya mata,ta nufi Synagogue, Church of All Nations (SCOAN),taro yayi taro a wurin haka suka cigaba da gaggaisawa da mutane,sai da manyan Reversed, Pastors da masu faɗa a ji a cikin Church ɗin su ka zo kafin a bata damar zuwa ta buɗe taron da daɗaɗan waƙoƙin ta kamar yadda aka tsara,Revered Anderson na can zaune a high table cikin manyan Reversed fuskar shi ɗauke da farinciki da zallar alfahari game da samun ƴa irin Jadeeda da ya yi.
   Cikin zazzaƙa kuma maɗaukakiyar muryarta ta fara cewa,"When every knee shall bow and every tongue weather you like it or not it's mandatory that you confese and acknowledge that Jesus Christ is lord,A day is coming when the arrogance people will come to a halt where the pride of people the plignative of men ,the brilliant of people and the intellectual capabilities of people/men  will mean nothing and on that day ever knee will bow,and the lamb shall make war revenquish the power of the enemy among us,we mute the voice of the adversery.we discredit the voice of the accuser of your people in the name of Jesus,we command salvation for All",ta ɗan tsagaita kafin ta fara kai kawo a harabar gurin da ta ke.
  "Now let God arise in the name of he,seated on the right of the father to ever make intercess,our soon coming king, Jesus Christ the son of God ,the lord of the all time and age,you are on the throne, you are the Lord".
   "We are a chosen generation,we have been called forth to show his excellent, hey all I required for life".
   Sai da ta kawo nan a zancen ta sannan duk taron mutanen da ke cikin Church ɗin suka zauna kafin daganan ta yi ma gan ɗin ta da suka iso yau alamar  da su sakar mata sauti ,cikin tautaysan lafuzanta ta da tsara waƙararta mai taken New soul,"Pass me not
          O gentle saviour
         Hear my humble cry.
                 Oh! and while on others.
                Thou art calling
                 Do not pass me by
          He he he
         Pass me not
          O gentle saviour....
Haka ta cigaba da raira waƙarta hatta kai ƙarshe  kafin su cigaba da gudanar da event ɗin su ,kamar yanda su ka saba,sosai ta samu yabo gun manyan mutane da Pastors da ma Revered.
     A gajiye ta dawo hotel ɗin,bayan ta rabu da su Papa sun tafi na su masauki su.jin knocking ɗin door ɗin ta yasa ta miƙa a ɗan kiɗime tana mai tambayar waye,"Who is on the door",ta tambaya cikin rarrababbiyar  murya,"Am ki buɗe ƙofar,Ni ne ba wani abu zai faru ba,i just come to see you","Oh Blood of  Jesus Christ Fedrick kai ne wai ,to ka sani I'll not open ba zan buɗe ba,ka koma inda ka fito"...."Ni.no don't say that,Bai kamata ki aikata haka ba,na yi ta bin ki tun  a Church Amma ki ka ƙi ssurarana kin ga bai kamata in zo nan ba ki sake watsamin ƙasa a ido ba".
   "Okay ka cigaba da tsayuwar a wurin in ka gaji ka tafi",ta na kaiwa nan ta kwashi abubuwan da za ta buƙata ta nufi bedroom ɗin ta haka ya cigaba da bugawa ya na magiya har daga ƙarshe ya haƙura ya tafi ,bayan ya tabbatar ba za ta buɗe ba duk da haka a cikin ransa bani wani abu da ya sauya game da ita ba,don haka ma ya ƙudurce a cikin ransa gobe ma zai dawo.
Washegari Ester Monday haka suka cigaba da gudanar da event ɗin su kala-kala,kafin daga bisa ni su tashi,taron ya koma gidajensu,irin taron family, friends da sauran su.
    Ita kanta Jadeeda hankalinta ya yi Gida ta ƙosa ta tafi cikin family ɗin ta su yi Shagali kamar yanda su ka saba,haka ta nufi Room ɗin ta ta fara haɗa luggage ɗin ta domin jirgin safe ta ke son ta bi.
   "Blood of Jesus!", shine  abinda ta faɗa cikin firgici da tashin hankali bayan ta ci karo da Fedrick zaune akan ɗaya daga cikin kujerun da suke a Parlonta.....