Ɗanɗano
*KIRAN RABO.*
#FitattuBiyar
#Ɗanɗano
#Nana Haleema
#September2025
***
*Ko wacce ƙaddara tana da mafari, dukkan abinda zai faru da bawa yana da sila...*💔
…Ɗan daba ne lamba ɗaya, ɗan daba ne mai lasisi wanda ya samu goyan baya daga iyayen ƙasar wato ƴan siyasa. Duk da dabancin ta sa mai tsari yake yi amma yana daga cikin ƴan dabar da ake matuƙar tsoron su a faɗin Kano. Kaf yankin ƙofar nasarawa shine shugaba, babu wani ɗan daba da zai aikata ba daidai ba a wannan area sai Damisa ya sani. Kuma saboda shine kawai ake jin tsoron yin faɗa a arear saboda in ya tashi ɗaukar fansa bai iya ba, shiyasa ba a cika koda sace-sace a unguwar ba saboda ya zama kamar kura da nama ya shigo zai kama.
OMAR kenan! wanda ake yiwa laƙabi da DAMISA wasu kuma su ce MADUGU, wasu kuma ce JAN WUYA.
Aisha da take zaune ganin Muktar ya firgita da ganin ƙanin nata cikin bada umarni ta ce, "Omar ka tashi ka shiga gida babu ruwan ka." Jin abinda Yayar ta sa ta ce sai ya miƙe tsaye yana kallon ta, shigowa ciki yayi sosai yayi kamar zai wuce ta kawai ya ɗuka ya damƙi wuyan Muktar ya miƙar dashi tsaye.
Nan take jikin sa ya soma, yana kallom Omar yana karkarwa dan daman an faɗa masa Omar indai akan Yayarsa ne babu abinda bazai yi ba. Tiger ya kalli cikin idon sa cikin dakakkiyar muryar sa irin ta jarumai mazajen gaske ya ce, "maimaita abinda ka faɗ mata naji." Jikin Muktar rawa yake yi sosai, ji yake kamar ya yi fitsari saboda tsoro ya kasa furta komai saboda tashin hankali.
Aisha da take tsaye itama t ce, "Omar meye haka ne? Ka sake shi!?" Ta faɗa cikin ɗaga murya. A fusace ya kalle ta ya ce, "DIDI ki matsa baya, babu abinda zai hana ban farka bakin wannan mutumin ba. Nan gaba na ga da wanne bakin zai furta irin abinda ya ce yanzu" ya dawo da kallon sa ga Muktar shi ya ce, "Tunda ya tako har cikin gidan mu babu abinda zai hana ban ɗauki mataki a kansa ba. Ko na datse masa harshe, ko na farka cikin sa."
"Wayyo Allah na shiga uku!. Aisha don girman Allah ki taimake ni, ki ce ya ƙyale ni, ki taimaka min kar......" maganar da ta maƙale saboda wuƙar da ya kawo kusa da wuyan sa ya ce, "kana cigaba da magana wallahi sai dai uwar ka ta haifo wani."
Ɗif ya yi ya kulle bakin sa da jikin sa yana karkarwa sosai nan da nan hawaye suka fara ambaliyya daga idanun sa saboda tsoro. Didi ta ƙaraso wajan ta riƙe hannun sa ta ce, "Omar ka ƙyale shi ya tafi na ce ko?."
"Bazan ƙyale shi ba. Ba shi yana da zarrar zuwa har gidan nan yake cewa ya fasa auren ki ba?. Inda iya wannn kalmar ya faɗa da sauƙi, amma har magana mara daɗi ya fada a kan ki. Didi ko duniya ce zata taru yau babu abinda zai hana ban farka cikin mutumin nan ba."
"To ba ni aka faɗawa magnar ba ina ruwan ka...? Malam ka cika shi ya tafi bana son wannan ɗabi'ar" Ta faɗa da ƙarfi tana son cire hannun Omar daga wuyan Muktar amma ta kasa.
Kallon Muktar din ya yi da yake hawaye kamar ƙaramin yaro jikin sa na rawa sosai ya ce, "ka ci albarkacin ta a yau ka sha, amma kar ka sake idanuna ya sake ganin fuskar ka. In kayi wannan gangancin zaka yi dana sanin zuwan ka duniya." Kai yake ɗaga kamar ƙadangare saboda tsoro Omar ya ce, "baka da baki!?." Yadda yayi maganar cikin tsawa ya ake firgita shi ya ce, "na....ji....ka yi....ha...ku....ri."
Omar ya cika masa wuya ya kalle shi ya ce, "durƙusa ka bata haƙuri." Babu ɓata Lokaci ya zube a ƙasa ya ce, "Ki yi haƙuri Aisha, na tuba ki yafe min." A fusace Omar ya ce, "sunan ta ka ke faɗa kai tsaye babu girmamwa? Sa'ar ka ce?." Jiki na karkarwa Muktar ya ce, "ki yi haƙuri Mama, Allah ya wuci zuciyar ki."
"Haifar ka tayi da zaka ce mata Mama!?" Ya sake faɗa yana cakumar rigar sa. Muktar ya fashe da kuka ya ce, "Ki yi haƙuri Anty, ki yi haƙuri don Allah." Omar ya sake shi ya nuna masa ƙofa ya ce, "bar nan." Ai bai sake magana ba ya fita a guje ko takalman sa bai ɗauka ba saboda tsoro.
Yana shiga tsakar gidan Didi ta tare shi ta ce, "Omar me yasa ka ke min haka ne? Omar me yasa ka ke son saka min ciwo ne wai?." Zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta ce, "kar ka ce komai sai na baka dama. Ya ka ke so nayi ne? Me ka ke so ka zama ne Omar?. Yau gabaɗaya satin ka biyu da fitowa daga prison bayan ka shafe kwana goma a ciki, so ka ke ka kuma komawa ne?."
"Didi...." Ta katse shi ta ce, "ba wani didi, babu wani didi kar ka ƙarasa. Omar me ka ke son zama ne don girman Allah? Ɗan ta'adda ka ke so ka zama ko me?. A gaban idona ka dinga zancen zaka farkawa wani ciki?."
"Duk abinda ya faɗa miki naji, in ya fasa auren ki ya faɗa cikin magana mai daɗi mana sai ya faɗa da wulaƙanci?. Na rantse da mamallakin ka'aba na dan ke ba sai na yiwa bakin sa illa."
"To waye zai aure ni bayan kowa tsoron ka yake ji? Da irin wannan dabi'ar taka ka ke so na yi aure Omar?. Wanne iyaye ne zasu amince ɗan su ya aure ni bayan ina da ƙani irin ka?." Ganin idon Yayar tasa ya fara kuka da hawaye sai ya lumshe idanun sa ya buɗe ya kalle ta ya ce, "Didi don ina so ki yi aure ba haka yana nufin zan juri ko wacce kalma a kan ki ba, Wallahi ko waye yayi ƙoƙarin ɓata miki rai shima sai nasa da na dangin sa ya ɓaci."
Didi ta ce, "waye yace maka raina ya ɓaci? Gaskiya ya faɗa Omar kowa a unguwar nan kallon da suke min kenan. Ban taɓa aure ba muna zaune da kai a gida ɗaya gani suke kamar ni da kai wani abun mu ke aikatawa mara kyau shiyasa rashin auren baya damuna. Shekaran jiya matar Alhaji Yusuf ni da ita ta faɗa min ido cikin ido. Kaga na damu...? Ban damu ba saboda ni na san ba haka bane, suna yiwa abun kallon baibai ne, kuma babu wanda ya isa ya ce zamana da kai a gidan nan akwai haramci, sai dai su yi tunanin banza su daina. Aurena kuma lokaci ne kawai bai yi ba."
Bai yi magana ba kallon ta yake yana kuma hakaito kamannin matar da ta ambata a idanun sa yaji ta ce, "kowa tsoron zuwa ya ce zai aure ni yake yi saboda kai Omar, kaf ƙofar nasarawa da kewaye tsoron ka suke ji iya kallon idanun ka ma tsorota su yake yi balle ka yi musu magana. A haka ka ke cewa burin ka nayi aure?."
Ya sauke numfashi yana kallon ta kafin ya dafa kafaɗarta ya ce, "Didi lokaci ne kawai bai yi ba, in yayi zaki yi aure. Kawai bazan yarda ki auri ɗan kutmar uba bane, dan ko kina auren nasa ya raina miki hankali ni mai iya ganin bayan sa ne."
Ta cire hannun sa daga kafaɗar ta ta ce, "Omar ka daina furta wannan kalmar, ka daina cewa zaka ga bayan mutum don Allah ka daina."
Leɓen sa ya ciza ya kalle ta ya ce, "Didi kamar uwa ki ke a wajena, in na kira ki da uwata ban yi laifi ba. Ina so ki sani babu wani ƙato ɗan ƙatuwa da ya isa ya ɗaga miki yatsa ban karya shi ba, kuma shi wannan da ya fita na ƙyale shi ne yanzu saboda ke amma ai zamu haɗu ko da sanayya ko da ganganci. Itama matar Yusuf ɗin zamu gauraya" yana faɗa ya juya ya shiga wata ƙofa da take farko a cikin gidan.
İdanu ta wara waje jin abinda ya ce cikin ɗaga murya ta ce, "Omar kar ka yiwa matar nan komai fa, matar aure ce kar ka sake ka yi wannan gangancin!." Bata ji maganar sa ba daman ta san bazai ce komai ba.
••••••••••
"Ni ki ke yiwa korar shaiɗanu? Wacece ke! Waye ya turo ki gidan nan!?." Tsawar da ya yi ya sake firgita Nayla, ta runtse idanun ta cikin fargaba da tashin hankali. Numfashi ta ya kusa ɗaukewa saboda ƙaramar wuƙar da ya zaro daga ƙasan takalmin sa ya ɗora ta akan wuyan ta yana sake wara idanun sa waje ya ce, "Wacece ke!?."
Nayla bata taɓa shiga tashin hankali kamar yadda take a ciki yanzu, ƙafafun ta sai rawa suke yi saboda tashin hankali. "Omar!" Didi ta faɗa da hanzari tana zuwa ta janye Omar daga kusa da Nayla da take zubar da hawaye. Sharaf Nayla ta faɗi a numfashi ta na sama da kasa.
"Baka da hankali ne Omar? Kashe ta zaka yi?." A fusace ya kalle ta ya ce, "Wacece ita? Ban ce kar na sake ganin ta a gidan nan ba?."
"Gidan ka ne da sai wanda ka ke zo zai shigo? Na ce gidan ka ne?."
"Ba gidana bane, amma ina da ikon hana duk wanda bana so shigowa cikin sa. Ban son sake ganin wannan yarinyar a gidan nan, bana son sake ganin ta!" Ya fada da ƙarfi yana nuna Nayla da take zaune a baya kamar sumammiya.
Didi ta fusata sosai ta ce, "baka isa ba, baka isa ka hana ɓaƙina shigowa gidan nan ba Omar. Wai kai meye yake damun ka? Meye a cikin kan ka. Meyasa baka aiki da hankali ne kai?." Idanu ya sake warawa waje yana kallon Didi jin kalaman ta ta ce, "eh na faɗa, Meyasa baka aiki da hankali?. Meyasa ko yaushe zuciya ce take sarrafa tunanin ka?." Kai yake girgizawa Didi ta sake cewa, "wacce irin zuciya ka ke da ita ne kai? Meyasa baka mantuwa kuma baka yafiya?."
"Eh bana yafiya kuma bazan yafe ba. Iya yau kin cece shi ya sha, amma wata rana zamu haɗu a lokacin da babu ke ko?."
"Ƙanin mahaifin ka ne, ko ka ƙi ko ka so dole ka kira shi da Kawu." Ƙasa ya yi da muryar sa yana girgiza kai ya ce, "Har abada bani da dangin mahaifi, bani da dangin mahaifiya kamar yadda na rasa iyayena suma ki ɗauka sun mutu. Ke kaɗai na sani dangina, baya ke babu wata halitta a duniyar nan da ta rage sa zan kalle ta matsayin dangi!" Ya ƙarashe maganar da ƙarfin gaske.
"Ƙarya ka ke Omar, ƙarya ka ke. Kawu ƙanin mahaifin ka ne duk da abinda ya aikata maka ba a canjawa tuwo suna. Baba Adamu Yayan Mahaifiyar ka ne duk da abinda ya yi maka ba a canjawa tuwo suna. In dai har ka manta da dangin iyayen ka to zaka manta da wanda suka haife ka Omar!."
Hannu ya saka ya daki kansa ya juya ya sake juyowa ya kalle ta ya ce, "iyayena sun rasu dan haka bani da wani a duniyar nan in ba ke ba."
"Nima ɗin baka ɗauke ni komai ba Omar, tunda ba ka yin abinda nake so."
Sake kallon ta ya yi ya ce, "na rantse da Allah Didi, in na sake ganin ƙafar wani dangin Baba a gidan nan ranar bazai kwana lafiya ba. Zan iya ɗagawa dangin Mama ƙafa, amma bazan taɓa ɗagawa dangin mahaifina ƙafa ba. Ke kin san waye ni, kin kuma sana abinda zan yi da wanda bazan yi ba."
Didi sai ta kasa magana dan baza ta iya da taurin kan sa ba, tayi murmushin takaici kawai ta kalli Nayla da take zaune a wajan har lokacin kamar bata numfashi. Da sauri ta ƙarasa inda take ta ɗago ta jikin ta ta ce, "Nayla! Nayla buɗe idon ki don Allah." A hankali Nayla ta buɗe ido tana kallon Didi sai jikin ta ya cigaba da rawa ta ƙanƙame Didi tana kuka sosai.
Omar takaici kamar ya kashe shi haka yake ji, cikin tsananin ɓacin rai da takaici da matuƙar tsawa ya ce, "in na sake ganin yarinyar nan a gidan nan bazan ƙyaleta ba!." Cikin ɓacin rai da fusata didi ta ce, "Sai ta shigo! Omar sai ta shigo in ka dama ka kashe ta kaga in za a barka da rai. Na gaji da wannan shirmen na ka, kullum kana girma amma kana cin ƙasa, sam baka aiki da hankali balle ka san abinda zaka yi."
Zuba mata ido ya yi, duk wannan faɗan da take yi akan maƙiyan sa take masa da kuma wannan Nayla. To me zai saka ma ya bar Nayla lafiya bai illata ta ba....?
••••••
Abiy da Mama a zaune a falo Abiy yana cin abinci Mama na gefen sa ganin ya kammala cin abincin sai ta kalle shi ta ce, "ɗazu Nayla ta kira ni, na ce mutanen Kano ya Hajja." Abiy ya murmusa ya ce, "nima daga dawowa ta gidan nan zuwa yanzu sau biyar ta kira ni. Ai naga alama tana son zama wajan Hajja sosai."
Mama ta yi murmushi ta ce, "itama Hajjan tana matuƙar jin daɗin zama da Nayla ai, kasan Nayla ba dai hankali da iya magana ba." Abiy ya murmusa kawai bai ce komai ba kafin ta ce, "Kwana nawa ka bar ta yi ne?."
"Sati ɗaya."
"Haba Abiy, ina laifin ka barta tayi sati uku tunda dai ta kammala service ɗin ta kuma baka samar mata aiki ba. Tahzif ɗin da ta shiga ma ta kammala tana gida a zaune. Hajja na son zaman ta a can, ita take ɗauke mata kewar mahaifiyar ta da ta rasa take kallon Nayla tamkar Bilkisu."
Abiy ya kalle ta ya ce, "Bana son zaman ta a Kano ne gabaɗaya, kar ki manta abinda ya so faruwa da ita a shekarun baya, ba dan Allah ya kiyaye ba da an cutar da ita. Tun daga nan zaman ta a Kano ya gama fita daga raina, da ina da iko ma ko kwana ɗaya baza tayi a can ba, to ban isa na raba ta da dangin mahaifiyar ta da suke can ba. Kuma suna tsananin son Nayla da ƙaunar ganin ta, dole ne na barta ta je gare su."
"Na sani Abiy. Amma ai komai ya wuce kuma yanzu Nayla ai tana da hankali da wayon da abinda ya faru a baya bazai faru yanzu ba sai dai ƙaddara. Hajja tana sonta, tun farko ta nuna maka ka bar mata Nayla kawai dai ka ƙi ne. Kuma suma sun yi mana kara a kanta sosai."
Abiy ya ce, "har abada bazan iya barwa kowa Nayla ba, ke bama Nayla ba kaf ƴaƴana biyar har Nayla shida bana tunanin zan iya barin su su je wani wajan su zauna gaskiya. Sai dai aje ayi ziyara a dawo, ni ne na haife su haƙƙin riƙe su a hannuna yake."
"To ka ƙara mata lokaci kafin ta fara zuwa aiki ta zauna a Kano wajan Hajja."
Abiy ya sauke numfashi ya ce, "zan yi tunani a kan hakan na gani, amma a yanzu dai sati ɗaya na bari tayi, in naga zan ƙara mata sai na ƙara mata. In naga bazan iya ba ta dawo gidan mahaifin ta. Mama tayi murmushi ta ce, "Hakan yayi, Allah ya kaimu." Ya amsa da amin kafin ya tashi ya shiga ɗaki ya bar Mama a zaune a wajan.
"Nayla hmmm! Ai wallahi sai na raba ku, yadda ta bar gidan nan a bana tunanin zata sake dawowa cikin sa, in ma ta dawo na ɗan lokaci ne kawai amma sai nayi amfani da wayo da dabarar da na nisanta ka da Nayla. Sai na san yadda na yi Nayla ta je gidan mijin da zai ci uban ta, ya hanata walwala ya kuma hanata jin daɗi. Burina Nayla ta rayu a gidan auren da zata sha wahala kamar ydda uwarta ta wahalar dani. Zan fashe wahalar da na sha akan ta!." Girgiza kai Mama take yi tana hasaso lokacin da wannan buri na ta zai cika. Bata nufin Nayla da ko wanne irin sharri ko makirci, ta raini Nayla daidai da yadda ta raini ƴaƴanta, ta bata tarbiyya da rayuwa mai kyau. Ita babban burin ta Nayla ta yi aure a inda zata sha wahala kuma sai tabbatar da ta cika wannan buri na ta hankalin ta zai kwanta, ta yi ƙwafa ta miƙe zuwa daƙi.
••••••••
Minister ya kalli Sen bayan ya fita ya ce, "Amma wannan yaron sam bai yi kama da ƴan daba irin na mu ba, Anya kayi bincike akan sa sosai?. Ka duba fuskar sa fa, irin kyawawan mazan nan ne masu kwarjinin tsiya." Sen yayi dariya ya ce, "kai ka san bazan fara mu'amala dashi ba in ban san shi ba, na san shi tun da jimawa na kuma san komai akan sa. A kaf kano tsoron yaron nan ake ji in dai a ɓangaren daba ne, har ta kai ta kawo ƴan sanda su kan neme taimakon sa a ɓangaren kama wani ko wani abun. Duk yadda ka kai ga jin kai jan wuya ne da yazo waje ya kalle ka ya ce ta shi ka bi wannan ɗan sandan sai ya je. Dabar sa mai tsafta ce duk da a sanin da nayi masa a baya yafi haka jagaliyan ci. Jikin sa mai matuakr tsafta ne, baza ka taɗa ganin sa ka ce ɗan daba bane, amma kallo ɗaya zaka yi masa gaban ka ya faɗi."
Minister ya ce, "Amazing! Ya burge ni sosai fa, especially yadda yake magana da izza kamar shi ne senator ɗin."
"Bai yarda da wulaƙanci ba, tun farkon haɗuwa ta da shi ya faɗa min wannan. Kai baka ganin akan kujera nake akan kujera yake baka yi mamaki ba?."
"Nayi mamaki sosai, na saba ganin thugs suna warin wiwi da sun ganka su zube a ƙasa suna magana mara kan gado. But he's different gaskiya."
"That's why I choose him. Kar ka yi mamaki in nace maka bai jima da fitowa daga prison ba."
Minster ya ce, "a yadda ka ke bani labarin sa prison a wajan irin su ai is just normal, kamar a shiga gida ne a fito."
"Ya yi hidima a lokacin zaɓe, yana daga cikin wanda suka bani kujerar da nake kai. Sannan ka san shi baya kisa a lamarin sa, in ya zauna a ake zaɓen ma ganin sa zawo yake saka maza balle ya ɗauko wuƙa. In kaga ya zubarwa da mutum jini shi ya so. Minister, totally Tiger is different"
Minister ya yi murmushi ya ce, "I see. But yana da karatu?."
"Bashi da ilimi, bana tunanin yana yi SSCE."
"Ya aka yi ka ke mu'amala dashi kai da baka zama inuwa ɗaya da wanda bashi da karatu?."
Sen ya yi dariya ya ce, "shi ai daban da sauran mutane. Shi rayuwar sa ya ke sadaukar min, dan in aka kashe shi akan aikin da yake yi min an kashe banza da wofi. Kuma ina amfani dashi ne daga lokacin ya wuce shikenan. In ba dan haka ba shi da ganina sai dai in a waya." Dariya suka yi gabaɗaya minister ya ce, "Yaran ba su da hankali, muna gina rayuwar mu suna ɓata ta su."
"Rashin ilimin kenan."
"Kaga in ka haɗa Narma dashi babu sauran damuwa."
••••••••
Mum ta ce, "Tiger! Kana so kace da ɗan daba zaka haɗa min yarinya?." Sen ya ce, "Nafi yarda dashi akan police, zai kula da ita bazai bari wani abu ya same ta ba." Mum ta ce, "this is bad idea Sen, Ta ya zaka haɗa ɗan daba da daughter suna shaƙar numfashi ɗaya? Matsayin su ai ba ɗaya bane. Ta ya zai shiga motar da Narma take ciki? Hakan ai babban abin kunya ne kuma is so disgusting" ta faɗa tana yatsina.
"Na sani, na kuma sam abinda nake yi. Kuma daman su aikin su su yi a biya su, in ba dan zai kula da ita ba ai ko kusa da ita bai isa yazo ba balle har ya samu damar yi mata magana. To na yarda da aikin sa hundrent percent, in nace kar ya bari wani ya kalle ta ma zai iya shiyasa na zaɓe shi. Kar ki damu wannan ba komai bane aiki ne kawai."
Narma ta ce, "Dad ni tsoron sa ma nake ji, kuma ta ya za ka haɗa ni dashi bayan bana tunanin ya taɓa zuwa school?." Dad yayi dariya ya ce, "Daman ai ya kamata ki ji tsoron sa, yadda ki ke jin tsoron sa haka ake jin tsoron sa a duk inda ya je. Ganin sa kawai a kusa dake babu wanda zai iya yi miki magana. Kuma ba maganar school, dan bana tunanin ya yi secondry school."
Mum ta wara idanu ta ce, "da jahili zaka haɗa min yarinya? Gaskiya ban amince ba."
Dad ya ce, "haba dear, ki yarda dani mana na san abinda nake yi fa." Narma ta ce, "amma Dad sai ayi min dariya in aka gan mu tare."
"Kar ki damu kowa ya san aiki yake miki a ƙasan ki yake." Narma ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "well, a wanne Guest house ɗin zan zauna? Kasan akwai friends ɗina da zamu zauna tare."
Sen ya ce, "bana tunanin zan bar ki ki zauna a guests house, Ina tunanin ki tafi hotel kawai."
Narma ta ce, "okay Dad, yadda ka ce" ta tashi tana hawa sana dan ta ɗauko jaka ta tafi aiki.
Mum ta kalli Sen ta ce, "amma my dear meyasa zaka haɗa ta da wani ɗan daba for god sake? Meye haɗin ta dashi? Iya wannan bad smell ɗin ma da suka yi ai sai ya saka tayi ciwo, gaskiya hakan bai yi min ba."
Sen ya ce, "wannan ɗan daban ba irim wanda ki ka sani yake ba, kuma aiki ne na lokaci kaɗan da ya ƙare shikenan ba sake ganin ta zai yi ba. Ni nasan matsayin sa bai kai ace yana jan Narma a mota ba, kawai zamu jure ne saboda lafiyar ta. Zai iya bada ransa akan kula da Narma, ko da kashe shi aka yi a maimakon Narma an fa kashe banza."
Mum ta ce, "in ba dan aikin ba ina shi ina haɗuwa da Narma? Ai sai dai a tv." Sen to yayi dariya ya ce, "na san abinda nake yi kar ki damu." Ya faɗa yana tashi ya hau sama bayan ya saka waya a kunnen sa.
•••••••••
A can Abuja kuwa Dad yana yanke wayar Mum ta kalle shi a fusace ta ce, "ni fa tun asali ban so ka haɗa riƙaƙƙen ɗan daba da ƴata ba, ta ya ya za a ce kaf jami'an tsaron da suke Kano ka rasa da wanda zaka haɗa ta sai da ɗan daba?. Waye shi da zai mata tsawa har yake ganin yafi ƙarfin ta aike shi? Ba a a ƙarƙashin ka yake ba?."
Nabil da yake zaune shima rai a ɓace ya ce, "abinda zan ce kenan Mum. Ta ya zai mata tsawa har kuma Dad ka biye masa ka ce wai in zata yi aike ta aiki Yahya? Kenan shi ya fi ƙarfin ta aike shi ko me?. Gaskiya Dad wannan ba wanda za a zauna dashi bane, ina bayan Mum ka salleme shi kawai a tura mata wani ya dinga kaita duk inda yake so. Wani ƙazami dashi har yana da bakin da zai ce wai baza ta aike shi ba? Waye shi?."
Mum ta kuma ɗora da cewa, "ba kowa bane face ɗan iska gari na banza da wofi, matsayin numfashi su ma ba ɗaya bane amma Dear ya saka tana shaƙar gurɓataccen numfashin sa a mota ɗaya. Tsakanin ta dashi shine mahaifin ta ya biya shi ya ne ya tayar da hayaniya a wajan zaɓe da sauran su, amma matsayin ya haɗa mota ɗaya da Narma sam-sam bai tashi ba."
Dad yayi murmushi yana kallon su ya ce, "na fi ku tsanar kusancin da ya samu da Narma saboda bashi da wannan matsayin kuma bazai taɓa samun sa ba har abada. Tsakanin Narma dashi kamar tazarar sama da ƙasa, turaren da Narma take sakawa sai ya siyi dangin sa kaf balle kuma agogon da take ɗaurawa a hannun ta. Ban haɗa shi da Narma dan ya yiwa Narma wani abun ba, na haɗa ta dashi ne na ɗan lokaci saboda lafiyar ta da zaman ta lafiya a Kano. Ke kin san wancan lokacin abinda ya faru da ita, tare musu hanya aka yi ana ƙokƙarin sace ta in ba dan Allah ya tsare ba da yanzu wataƙila bata gidan nan. Shi kuwa kaf kano an san shi, in baka san shi ba ka san sunan shi, ana faɗar sunan sa shikenan duk iskancin da ka ke ki dashi ka ajjiye. Saboda haka kawai na bashi Narma ya dinga kai ta duk inda zata je, in ba dan haka ba haɗa ido ma bai kai matsayin da Narma zata yi dashi ba."
Nabil ya ce, "Amma Dad akwai police a Kano da zaka ɗauka a haɗa ta dasu ta je duk inda take so, suna da bindiga shi kuwa bashi da ita, sun san aikin su shi kuwa me ya sani ban da wasa da wuƙa?. Gaskiya Dad ban ji daɗi ba, wani ƙazamin bagidaje dashi har yana da zarra da kana yi masa magana yana cewa wai zai ajjiye aikin saboda baya son raini. Just Imagine, wani banza shashasha talaka ne yake faɗawa yar senator haka."
Dad ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "kar ka damu Nabil na san abinda nake yi, kar ka samu damuwa, wani lokacin yawo da irin su Tiger yafi amfani akan yawo da police. Na san abinda nake yi fa kar ka samu damuwa." Mum dai kawar da kai tayi zuciyar ta cike da haushin wannan hukunci na senator, gashi wani banza talaka yana wulaƙanta mata yarinya.
••••••••
Sen ya rasa abinda zai yi ya kalli Omar da yake tsaye ya ce, "kai kuma ka san ƴata ce ka amince har ka ke sonta?."
"Ga zahiri kana gani" Omar ya faɗa yana kallon sa kamar yadda yake kallon sa. Kasa magana Sen ya yi na wani lokaci kafin ya ce, "ƴar tawa ka zo nan da ka ce min kana so, ƴar tawa ka yiwa asiri saboda na haɗa ka da ita a Kano?."
Omar ya ce, "ƴarka zaka tambaya in asiri nayi mata ma ta sani."
"Shut up! Ina magana kana magana dan ka raina ni?."
"Kaine ka haife ni?" Omar ya bashi amsa kai tsaye yana kallon sa babu alamun tsoro a tare dashi.
"Ko a matsayin diver Narma baka isa ka zo ba, haɗa numfashin ka da na ta babban zunubi ne saboda tazarar ku kamar sama da ƙasa ne. Na baka ita ne saboda wani buri nawa har ka dinga yawo da ita a mota na wani lokaci, amma ba dan haka ba ko a mai aikin gidan nan baka isa kazo ba. Bana ɗauka mutum aiki sai yana da matakin diploma a karatu, kai kuwa fa?." Omar ya kalle shi ya ɗora yatsun sa biyu akan goshin sa kamar ko yaushe ya ce, "ban zo a mai aiki ka ba, amma nazo a sirikin ka."
Ai Sen ji ya yi kamar ya zuba masa ruwan zafi, jikin sa har rawa ya ke yi, ya zare ido ya ce, "me ka ke dashi? Waye kai a duniya?. Ko matsayin mai gadin gidan nan baka dashi, mai aikin gidan nan dukkan su graduates ne, meye matakin karatun ka? Faɗa min me ka ke dashi a duniya?.." Omar ya ɗan yi murmushi kalle shi ya ce, "abinda nake dashi ka ke so ka ji?" Ya kalli Narma da take wajen tana kuka ya ce, "zuciyar ƴarka, ita nake dashi."
Fusata Sen matuƙa ya yi ya kai hannu kamar zai mare shi amma sai ya fasa yana jin zuciyar sa kamar ana zuba masa ruwan zafi saboda ɓacin rai. Minster ne ya ƙaraso yana kallon Omar ya ce, "Dan kaji last time na yabe ka sai aka ce maka ka kai matsayin da zaka zo gidan nan neman aure?. Kana da hankali kuwa?." Omar shima shi ya ke kallo ido cikin ido ya ce, "babu tabbacin kowa yana da hankali tunda ba ganin hankali sa ake yi ba." Sen ya zabura ya yi kan Omar Minster ya riƙe shi Sen yana cewa, "ka barni nayi maganin wannan mahaukacin, bar ni na kashe shi kuma na kashe banza wallahi. Ni zai dinga yiwa hauka a cikin gida?. Kalle shi fa?." Minister ya ce, "ba class ɗin ka bane."
Ya kalli Omar cikin ƙunar rai ya ce, "baka da maraba da dabba a idona, amfanin ka a gare ni na biya ka kaje ka sadaukar da rayuwar ka domin cigabana da na ƴaƴana. Saboda wannan kawai nake nuna maka so a baki dan bai kai zuciyata ba, in ba dan haka ba baka ka kai ka ce kana son mai aikin cikin gidan nan ba. Jahili ne kai baka da ilimin komai, babu inda zaka je a rayuwa a haka zaka ƙare rayuwar ka a gagari akan titi. Ko riƙe gidan ku baka iya yi, Yayar ka itace take ciyar da kai ba kaine ka ke citar da ita ba. A haka ka samu zarar ratso cikin gidan nan ka ce kana son Narma!?. Ka san wacece Narma?."
Omar ransa ya ɓaci sosai, tunda aka fara maganar sai yanzu ransa ya ɓaci hakan ya saka shi zubawa Sen ido bai ce komai ba. Ganin ya yi shiru Sen ya ce, "Ni Senator ne, Mahaifiyar Narma tsohuwar ƴar majalisa ce. Narma lawyer ce, ta kai matakin masters a karatu, tana kuma riƙe da company guda a ƙarƙashin ta. Tana juya biliyoyin kuɗaɗe wanda sai ta saka hannu kuɗin zasu fita. Tana aiki da babban kotun Nigeria, tana da ikon da zata yi ko wacce irin shari'a a faɗin ƙasar nan. Faɗa min kai waye?. Ɗan daba ne, mai garari akan titi, ɗan shaye-shaye, jahili, wanda bashi da ilimi balle a saka ran zai kai wani mataki a nan gaba?. Ko kana so kace ban san labarin uwar ka hiv ce ta kashe ta ba...." Ai bai ƙarasa ba Omar ya damƙi wuyam Sen jikin sa na rawa.
•••••••••
A zaune suka same ta a gaban Abiy da yake waya suma suka zauna saboda ya kammala. Kashe wayar ya yi ya kalli Nayla ya ce, "Mamana lafiya ki ke kuwa? Meye ya same ki haka fuskar ki tayi ja?." Nayla ta ce, "Abiy ai ka san Didi ko?." Abiy ya ce, "Wacece Didi kuma?."
"Maƙociyar Hajja Yayar...." Kafin ta ƙarasa ya ce, "Oh Yayar ɗan daban nan ko? Na gane ta, da Aisha na santa ni wani da Didi ba. Mutuwa tayi?."
Nayla gaban ta ya buga dum jin da sunan da Abiy ya kira Omar dashi, amma bata nuna ba ta ce, "da ranta." Abiy ya ce, "to lafiya ki ka shigo a firgice haka?." Jidda ta ce, "Haka ta dinga gudu damu a titi Abiy, gari ya cushe mutane an dawo daga masallacin juma'a amma bata daina ba, ƙiris ya rage bamu yi hatsari ba." Abiy ya kalli Jidda ya ce, "Wai daman ba Jawad ne ya shigo da mota a guje ba itace?."
"Wallahi itace" ta bashi amsa tana kallon Nayla.
Ya kalli Nayla ya ce, "Me ya faru haka?." Nayla ta ce, "Tausayin Didi nake ji Abiy, an kama mata ƙanin ta sai kuka take yi har da zazzaɓi. Don Allah Abiy ka taimaka a fito dashi don Allah." Abiy ya bita da kallo cikim mamaki ya ce, "akan wannan ne kika kusa kashe kanki da ƴan uwan ki?."
"Na kasa sarrafa kaina ne kawai Abiy, bana jin daɗi a zuciyata, Didi tana sona ina son abinda take so." Abiy ya kalle ta a nutse ya ce, "mun yi maganar da Hajja jiya sai dai ba a bani labari duka ba aka kira ni a waya. Waye ya saka aka kama shi ɗin sannan me ya yi?."
Shiru tayi bata amsa ba ya ce, "ke nake saurare, me ya yi aka kama shi har kike so na fito dashi?. Ko wani ya kashe?." Ta girgiza kai ya ce, "to faɗi." Nayla ta ce, "Dama ya je gidan Sen Sagir Sani ne, shine ya saka aka kama shi."
"Me ya je yi? Sata ko kuma kisan kai?." Salma ce ta bawa Abiy labarin abinda ya faru kaf har zuwan Didi wajan sa. Abiy ya girgiza kai ya ce, "Barr Narma ya je yace yana so? Kuma yana da hankali?." Salma ta ce, "gashi nan dai akwai Abiy."
Abiy ya ce, "gaskiya dai gashi nan dai kawai, dan in har yana da hankali to tabbas shaye-shayen su na ɓata gari ya taɓa masa ƙwaƙwalwa. In ba haka ba ya ɗauki ƙafa ya je ya ce yana son ƴar Sen Sagir? Ya san waye Sen Sagir kuwa?." Suka yi shiru Abiy ya ce, "To ai ko zaune gari banza wanda bashi da komai ya je ya ce masa yana son ƴarsa dole ya ɗauki mataki balle Sen. Kuma dole ya ce asiri ya yiwa mata take son sa. Meye abin so a tare dashi har da zata fita hankalin ta haka?." Nayla dai wani irin sanyi jikin ta ya yi da jin kalaman Abiy, zuciyar ta na bugawa, guiwar ta kamar ana dukan ta saboda sagewar da tayi.
Abiy ya ce, "well, ya taimaki Nayla a lokacin da take buƙatar taimako, ya kuɓutar da ita daga masu sharrin fyaɗe. Ya cancanci na taimaka masa a fito dashi tunda ba wani laifi ya aikata ba. Na san Sen Sagir sosai, abokina ne sosai tare muka yi ABU Zaria. Kuma ni ne class captain a lokacin, bara mu ga" ya faɗa yana ɗaukar waya yana dubawa.
A speaker Abiy ya saka kiran daga can ɓangaren Sen yana ɗauka ya ce, "Class Captain....!."
••••••••
"Didi ban san ki da ƙarya ba, dan kare ni kar ki faɗi abinda bazai faru ba. Babu asirin da na yi musu balle a karya shi. Ba ƴarsu ba, ko su ɗin ne da kansu basu isa nayi musu asiri ba wallahi, zuciyar Omar ta wuce wannan mataki. Babu wata halitta da zan iya yiwa asiri a duniya. Ƴarsu ɗin banza da wofi, wacce ita da har ni Omar zan yi mata asiri?."
Mum ta fusata sosai ta kalli Dad ta ce, "ka ga rainin da ka jawo mana, anya bouncers ɗin na suna akin su kuwa? Tunda har yake tsaye akan ƙafarsa wallahi bai sha wahala ba" ta juyo ta kalli Didi ta ce, "kince yana jin maganar ki gashi kema ya nuna mana jahilcin nasa bai bar ki ba. Ki ja masa kunne a tabbatar an karya asirin nan in ba haka ba wallahi zaku yi dana sani gabaɗayan ku."
Didi zata yi magana Omar ya rigata ya ce, "Jahili shine wanda bai san abinda yake yi ba, ni na san abinda nake yi kuma ban yi dana sanin zuwa gidan ku a matsayin mai neman auren ƴarku ba. Ina alfahari da hakan ko babu komai zan shiga cikin tarihin rayuwar ku, har abada baza ku manta da mai suna Omar yazo har falo ya ce yana son ƴarku ba. Jahilin da ku ka raina shine soyayyar sa ta hargitsa ƴarku har kuke tunanin an yi mata asiri. Ƙarfin tasirin Omar kenan ku ka gani, ƴar da kuke ji da ita zuciyarta ta gama narkewa a soyayyar wanda ku ka raina ku ke kallon sa ƙasƙantacce. Sai dai a yanzu ta makara, lokaci ya wuce Omar kuma in ya yi gaba baya juyawa baya. Ku bata haƙuri, ba wai na ƙita bane kawai akwai abinda ya fita mahimmaci a gabana yanzu. Ku yi mata addu'a Allah ya bata ikon jure rashina. Na san zaku sha matuƙar wahala kafin ta jure, dan nima tasha wahala kafin na fara koda ɗaukar kiran wayarta."
Sen ya fusata da jin kalaman Omar, ransa ya ɓaci sosai ya ce, "ƙarya ka ke yi, ƴata ta wuce ta fara soyayya da irin ka wallahi, sai dai aikin asiri. Kuma wallahi ka yi gaggawar sanar da ƴar uwarka inda ka ɓoye asirin, in ba haka ba kana gab da aikata aikin dana sani." Zai yi magana Didi ta riga shi ta ce, "Ku yi haƙuri don Allah, ku bani shi mu tafi zamu tattauna dashi zan yi iya ƙoƙarina wajan ganin an karya asirin."
Omar ya kalle ta da mamaki ya ce, "ki daina faɗar wannan maganar fa, babu abinda na aikata kin sani. Ita tazo har gaban ki ta zube a gaban ki tana roƙon ki ki saka na sota, na ji tausayinta saboda raunin da take tare dashi har naji a raina zan iya taimaka mata na sauraren ta..." ya faɗa yana kallon su Mum da suke kallon sa.
Ya sake kallon Didi ya ce, "Dan na taimaka mata na bata aron kaɗan daga cikin lokacina sai ya zama nayi mata asiri?.
•••••••••••
Jin kalaman take yi tamkar saukar aradu, ta zube a ƙasa ta riƙe hannun Abiy ta ce, "Abiy don Allah ka ce wasa ka ke yi min, Abiy dan na je Kano ka yanke min wannan hukuncin?. Mama...mama....tasan zan je kano..." ta juya tana kallon Mama ta ce, "Mama...baki sana zan je Kano ba? Ba ke kika ce min na je kano ba?. Meyasa ki baki faɗawa Abiy ba har ya yi fushi da ni?."
Mama ta ce, "ni na ce ki je Kano Nayla? Yaushe mu ka yi haka dake?. Ke kin san ban taɓa baki umarnin zuwa kano ba, Abiy ne yake yanke hukuncin lokacin da zaki je da lokacin da zaki dawo, ni na taɓa cewa tafi Kano ki dawo rana kaza Nayla?. Ban taɓa ba, kawai kin shiga ruɗani ne ki ke tunanin na ce miki ki je Kano, amma ba mu yi haka dake ba." Nayla sakin baki tayi tana kallon Mama jin kalaman da take faɗa ta ce, "Mama ta ya zan shiga ruɗani akan wannan? Wallahi...." Cikin tsawa Abiy ya ce, "Nayla ki tashi ki bar min ɗaki!, ki je can ki zauna da wanda kika zaɓa mu da zaki iya barin mu saboda shi ki bar mu, ke ki je ki yi zaman ki dashi tunda shine zaɓin ki. Ki tashi ki fita kafin na saɓa miki!."
Mama ta ce, "ka yi haƙuri ka sassauta wannan ɓacin ran da Allah. Nayla bata kyauta ba na sani, abinda ta yi sam bai kamata ba ta ci amanar ƙauna da soyayyar da ka nuna mata. Na tabbatar ko mahaifiyar ta da take kabari baza ta ji daɗin wannan abun da Nayla tayi ba. Da me aka rage ta dashi? Da ci ko sha ko suttura?. Amma ta rasa da abinda zata saka maka sai wannan abun?. Na san dole zaka ji babu daɗi a zuciyar ka, amma ka yi haƙuri ka kwantar da hankalin ka komai zai wuce in sha Allah."
Kalaman Mama sake hura wutar ɓacin rai suke yi a zuciyar Abiy, gasgata maganar ta yake yi dan tabbas Nayla bata yi masa halacci ba, tunda mahifiyar ta rasu bai taɓa bari tayi kukan rashin uwa ba amma da haka zata yi masa sakayya. Tabbas bata kyauta masa ba, ta cutar dashi ta kuma cutar da rayuwarta. Haka Mama ta dinga lallaɓa Abiy da kalaman masu kwantar da hankali wanda suke sake tunzura shi ya yi fushi da Nayla. A haka ta samu ya ɗan sauka ya ce ta bashi waje bacci zai yi ta fito daga ɗakin.
•••••••
"Ni kuma gani mai baƙin halin duniya wanda dashi kaɗai za a haɗa ta ya zama mummunan hukunci a rayuwar ta ko Didi?." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "mun gama maganar nan da Kai. Zaka riƙe auren ta babu saki koda mahaifinta ne ya ce ka sake ta kar ka sake ta, ka riƙe ta a hankali komai zai canja."
"Hmmm!" Shine abinda ya ce kenan yana kawar da kansa gefe cikin matuƙar takaici. Didi ta ce, "Yanzu ka ɗauko rigar ka, ka saka hula ka mu je gidan da zaku tare kai da amar....." kallon da ya yi mata shine ya hanata ƙarasawa. Ya ce, "ƙarasa mana Didi, Ina jin ki?."
"Omar Yayar ka ce ni fa, ka dinga sanin irin abinda zaka yi min."
"Ai ina gab da daina kallon ki matsayin yayar tawa, dan babu abinda zaki sake saka ni nayi kuma a yanzu."
Didi ta ce, "ni dai yanzu don girman Allah ka saka kayan ka mu je gidan da aka kai amaryar, don Allah ka zo mu je kar ka ce kin baza ka je ba."
"Au ni ne ma zan bita wani gida ba ma ita zata zo ba ko?. To bara kiji, Na rantse da girman Allah baza ni ba, gwara na yi miki kankat ki ji, Wallahi babu inda zan je."
Ajiyar zuciya Didi tayi cikin damuwa, tunda har ya rantse ta san bazai je ba wallahi, ita gabaɗaya ta shiga damuwa. Ta kalle shi ta ce, "naji baza ka je yanzu ba, amma in anjima sai ka je zan zauna har lokacin mu je tare." Kallon banza ya yi mata dan bazai amsa ba ya share ta ya cigaba da abinda yake yi.
"Omar in Baka je yau ba babu daɗi, amarya ce fa Omar, amarya fa. Don Allah ka taimaka kazo mu je." Bar mata wajan ma ya yi har zai gota ya juyo yana kallon ta ya ce, "naji ana batun wani gwajin jini, Ina so ki sani babu wanda ya isa ya saka ayi min wani gwaji. Gwara ki faɗa musu kar azo ace za a ɗauki jinina na cakawa yaron da aka turo allurar" yana faɗa ya shige ɗaki ya barta a wajan a tsaye cikin rashin sanin abinda zata yi.
Kai ya girgiza yana taɓe baki ya ce, "bazan karɓa ba Didi, gwara na faɗa miki gaskiya bazan yaudare ki ba. Kin san bana ɓoye-ɓoye dan haka bazan ɓoye ba."
"Omar saboda ni zaka yi."
"Bazan yi saboda ke ɗin ba! Didi bazan yi ba. Bazan karɓi auren da bana so ba, bazan karɓi auren da ban san yarinyar ba, bazan karɓi auren da ban san ma anyi shi ba. Da me zan kira wannan auren in na karɓa? Na dole ko na sadaka!."
Jin yadda ya fara yi mata magana cikin muryar mai shegen amon tsiya ya saka ta sassuta murya ta ce, "ka saurare ni, duk wannan zai biyo baya amma a yanzu kar ka ce baza ka karɓi auren ta ba. Yarinyar nan bata da laifi, Allah kaɗai ya san dalilin mahaifin ta na aurawa maka ita. Ransa ne ya ɓaci a lokacin, da alama akwai abinda ya ɓata masa rai ya saka ya yi hakan."
Ya bita da wani kallo kafin ya ce, "Dan kawai ran mahaifin ta ya ɓaci sai ya ɗauko ƙafa daga wani gari yazo har garin nan, ya kuma rasa inda zai sauke ɓacin ransa sai a kaina?. Munin halayena ne ya saka ya yanke hukuncin bani auren ta ko kuma meye?." Didi ta ce, "ni dai koma meye kar ka ce baza ka karɓi auren nan ba, ka zo mu koma....." ya dakatar da ita ya ce, "ba fa zan karɓa ba, bana son auren ban ce ina buƙata ba. Su riƙe ƴar su, ban ce a ɗaura min aure da ko wacce yarinya ba."
Didi ta jiyo ta ce, "Omaar Didi ce fa take maka magana, roƙon ka nake yi akan ka amince don Allah."
"Sanin ke ɗin ce ma ya saka na ke sauraren ki, in ba dan ke bace da yanzu na sumar da ko wacece a wajan nan. Aure ne bazan karɓa ba!."
"Omar alfarma fa nake nema a gare ka, baza ka iya yi min ba?."
"Bazan iya ba! Bazan yi ba Didi!. Zan iya yi miki ko wacce alfarma amma ban da wannan, ki canja tunanin ki bazan karɓi auren nan ba. Dan ma an raina min hankali a rasa da wanda za a yi mata auren sadaka sai ni? Kawai dan ni aka raina kaf cikin garin nan, ko kuma dan ni ne kawai mutum mai munin halin da za a yi mata hukunci ta hanyar aura mata ni?."
Ganin yadda ya birkice lokaci ɗaya yana zazzaga mata masifa ya saka ta riƙe hannun sa ta girgiza shi ta wara ido akan idanun sa ta ce, "Omaar kamar uwa nake a wajan ka, yanzu baza ka yi abinda nake so ba?." Shima ya wara nasa idanun ya yi a cikin nata ya ce, "kamar uwa ki ka ce Didi, ai ba uwar ba ce. Bazan yi miki biyayya akan abinda bana so ba!."
Didi ta runtse ido ta buɗe ta kakkausa murya ta ce, "shikenan Omar ka yi abinda ka ke so, ka je ka aikata abinda zuciyar ka take faɗa maka. Amma Ina so ka san abu ɗaya, na rantse da Allah in ka sake ka furta kalmar saki akan yarinyar nan ka warware auren ka da yake kanta ka sani babu ni babu kai Omar!" Ta faɗa tana nuna shi da yatsa cikin fusata.......
••••••••
Narma ta kalle shi ta ce, "Dad do you want to me to be happy?."
"absolutely my Love! your happiness means everything to me. I want you to be happy and fulfilled in life."
"Please allow me to married Faruk, I'm still have strong feelings for him. Dad If you refuse it like you did previously, it will deeply affect my happiness."
Mum ta ce, "Tiger again! Narma what are you saying?."
"Gaskiya Mum, ina faɗar gaskiya ne kuma shine abinda yake zuciyata" tana faɗar haka ta bar falon ta hau sama da gudu. Mum ta ce, "har yanzu bata bar tunanin sa ba fa, wai wannan wanne irin bala'i ne haka? Wanne irin asiri ya yiwa yarinyar mu?." Dad da ya yi shiru ya kalle ta ya ce, "kar ki damu, da ta sake dawowa daidai zata dawo hankalin ta. Ki nutsu, kema kin san auren ta da shi ai ba abu ne da zai yu ba, itama faɗa take yi amma ta san ta fi ƙarfin sa, ba sa'ar auren ta ba ne."
Mum ta ce, "Narma da gaske take Sen, Narma da gaske take kana jin yadda take magana ka san daga zuciyar ta ne." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba ya hau sama shima, amma yana tunani a zuciyar sa ya zama dole ya samar mata da farin ciki ko ta wacce hanya ne. Kamar yadda ya ɓata mata yana so ya faranta mata ta hanyar yi mata abinda take so.
Labarin soyayya mai tsayawa a rai, taɓa zuciya, sadaukarwa, sanya zubar hawaye, ƙauna tsakanin ƴan uwa. KIRAN RARO!
*Release on 1st September 2025 in sha Allah!.*
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*Za a fara biyan kudi a yanzu*
***
***
Dm to subscribe yours.