The Gobir's: forbidden hearts

chapter nine

by @rularnt

The Bond 
Ranar ta soma da hasken safe, rana na haskaka dakin cin abinci cikin laushi da annuri. Amma ba kamar kullum ba, Hameed, wanda kullum yana cikin farin ciki da kuzari, yau ya zauna, idonsa cike da hawaye. Bai ci komai ba, kuma ya kama bakinsa kamar zai yi kuka.

Dalilin? Yana jin zafi sosai cewa zai tafi makaranta, amma Little Ammi za a bar ta gida tare da masu aikin gida. Wannan rana ce da mum za ta koma aiki a CBN bayan hutun haihuwa, kuma wannan tunanin ya dameshi sosai.

"Sweetheart," ta ce a hankali, tana shafa gashinsa da taushi,
"Na san ba sauki ba ne ka bar Little Ammi, amma dole ne ka je makaranta. Kai yanzu babban yaro ne. You’ve got important things to learn."

Hameed ya girgiza kai, yana share hawayensa da bayan hannunsa,
“But idan ta yi kuka fa? Idan ta buƙace ni fa?”
“Su nannies ba za su gane abin da take so ba kamar ni!”

Safeenah ta nisa, tana ƙoƙarin kwantar masa da hankali.
"The nannies suna da ƙwarewa sosai. Sun iya kula da jarirai. Kuma ba za su bar ta haka kawai ba. Zata sami kulawa da ƙauna sosai."

Dole sai da aka ɗauki lokaci, aka yi masa alkawarin zai samu extra playtime da sweets a weekend, kafin ya amince a haka. Ya share hawayensa, ya ɗan ci abinci da sauri, amma kafin su gama, lokaci ya kusa ƙurewa. Safeenah ta ɗauke shi cikin gaggawa zuwa makaranta—har sun makara.

Unfortunately, Bayan wasu sa'o’i, malamarsa ta kira mum.
"Hameed is not himself today. He came with a slight fever, refused snacks, didn’t play or answer questions... he’s been quietly crying."

mum ta firgita—Hameed ba ya yin rashin lafiya haka. Ta kira driver ɗinsu da gaggawa, ta ce ya je ya ɗauko shi.

Zuwan Gida – The Healing Touch

Da suka iso gida, Hameed yana fita daga mota, ya ruga ciki, kai tsaye zuwa dakin Hannah. Kamar sihiri, da ya gan ta, murmushi ya bayyana a fuskarsa. Hawaye suka tsaya. Jikinsa ya ɗan huce.

mum ta rungume shi, tana lallaɓashi kamar ƙaramin yaro.
"Sweetheart," ta ce a hankali,
"Na san kana jin kewar Little Ammi sosai. Kuma hakan ba laifi bane. Amma kai jarumi ne. Kana kokari a makaranta."

Ta yi masa alƙawari mai taushi:
"Da zarar Little Ammi ta girma kadan, za mu sa ta a makaranta daya da kai. Za ku koma tare."

Daddynsu, Abdullah, ya kira da yamma ta video call.
Ya maimaita alƙawarin da Mum ta yi—“In sha Allah, za ku kasance tare a makaranta, son.” Wannan magana ta sa Hameed ya ji dadi. Ya amince zai koma makaranta, ba don yana so ba, amma saboda ya fahimci cewa akwai makoma inda zai koma ya kasance tare da ƙanwarsa.



Weekend Rituals – Ƙaunar Yaya da Kanwa

Yayin da makonni suka shige, weekend ɗinsu ya koma wani salo na ƙauna.
Hameed yana farkawa da sassafe—kafin iyayensa ma—zai fara ne da ziyartar dakin Hannah.

Hannah, yanzu tana da shekara guda, tana cike da fara’a da kuzari. Kyakkyawar baby ce, mai fara’a da dariya mai ɗaukar hankali.

Hameed zai wanke mata baki da kyau, ya yi mata wanka da dariya, yana sheƙa ruwa da wasa, yana sa ta dariya sosai.
Sannan zai saka mata kaya masu kyau, ya shafa mata man jiki, ya gyara gashinta da tsantsar kulawa.
Zai ba ta abincinta da kansa. Kafin ko ya ci nashi.

Yayinda ya zama cikakken mai kulawa—cike da ƙauna da hakuri.
Mum da Dad suna kallonsa a rufe, suna mamakin irin ƙaunar da Allah ya zubo a tsakanin ‘ya’yansu biyu.

A karshe, Safeenah ta ce da murmushi wata rana:
"Kai fa Hameed, da ka tsaya gida, sai ace kai ne nanny."
“No, Mummy,” ya amsa yana murmushi,
“I’m not a nanny. I’m her big brother. Na fi nanny.”

Ƙaunar Da Ba Ta da Iri / A Bond Like No Other
Hannah, a nata ɓangaren, ta zama kamar tana rayuwa ne bisa kulawar Hameed. Duk lokacin da yake wanke ta ko yana wasa da ita, sai ta fara yin happy baby babbles, tana ƙoƙarin taba fuskarsa da ƙananan hannayenta, idonta cike da ƙauna da aminci.

“Dama irin wannan ƙauna tana wanzuwa tsakanin ‘yan uwa?” Safeenah ta taɓa tambaya wata rana, tana kallon su daga ƙofa, murmushi a fuskarta.
A’a, wannan ba kawai brother-sister relationship ba ce. Wannan wata dangantaka ce mai zurfi—bond ɗin da ya zarce tunanin yara.

Hannah ba za ta iya bacci lafiya ba idan ba Hameed yana a kusa da ita ba. Idan ba ya cikin dakin, tana yawan farkawa da kuka, har sai an dawo da shi kusa da gadonta. Haka rayuwar su ta koma: cike da dariya, cike da ƙauna. Gidansu yana karfi da nishadi saboda zumunci da ƙaunar da suka raba.

---