The Gobir's: forbidden hearts

chapter eleven

by @rularnt

Graduation

Yayin da lokaci ke tafiya, Hameed ya kammala secondary school.
Yin murna sai kuka—saboda zai tafi Amurka don karantar aviation.

Safeenah da Abdullah sun yi murna da alfahari, amma Hannah? – Hannah ba ta iya ɓoye hawaye ba.
“You’re leaving me,” ta ce da murya mai rauni.
“No, I’m just flying a little far. But I’m not going away,” ya amsa.

Yana durƙusawa a gabanta, yana share hawayenta kamar ya share nata da tasa.
“Na yi miki alkawura, ko kin tuna?”
“Wanne?”
“Zan kira kowace rana. Zan turo pictures. Zan gaya miki komaibthat happens around me.Kuma zan dawo duk lokacin da kike buƙata.”

Yana rungumarta da ƙarfi – ba kamar yaro ba, amma kamar mutum da ya san nauyin ƙauna.
“Hannah, ba ni da wata sister sai ke. Ko da ina can, zuciyata za ta kasance a nan da ke.”

Yana sane cewa tafiyar zai ɗauke shi daga gida, amma ba zai bari nesa ya rushe abin da suka gina tare ba.
Zasu koma magana ta waya, hotuna, bidiyo, from time to time – har zu  dawowan shi.


****


Hameed ya sauka a New Jersey don karantar aviation, kuma ba a ɓata lokaci ba—ya faɗa ciki da zuciya ɗaya.
Books, simulations, night flights – duk sun zama rayuwarsa. Amma duk da haka, wani abu na rashi yana ci gaba da damunsa: Hannah.

Ko da suna waya kullum da dare, har su wuce ƙarfe goma sha biyu na dare – wayar ba ta cika gurbin da Hannah ke bari a zuciyarsa ba.
Ba dai sautin dariyarta, ba dumin rungumarta, ba hannunta a cikin nasa lokacin barci.

Kowane dare kafin barci, yana raira mata wakar lullubi da ta fi so – wata tsohuwar wakar da suka saba ji a lokacin suna yara.
Wakar da can tana zama bedtime ritual kawai, yanzu ta zama magani, sako, da siffar soyayya da baya faduwa.
Kamar yana kokarin dawo da hannunta cikin nasa.
A lokacin da daddare ya yi shiru, sai ka ga yana kallon ta screen – idonsa na cike da damuwa da sha’awa.
“Oh, I wish you were here, Hannah,” yana furta, “just for one hug.”


---

A Najeriya, Hannah Na Jin Rashinsa A Kowane Guri

A gida kuma, rayuwar Hannah ta sauya. Ba wata ƙara, ba dariyar dare, ba karatu tare da Yaya Hameed.
Da farko, tasirinsa ya bayyana sosai: Hannah ba ta iya mai da hankali a makaranta.
Kowane abu yana tunatar da ita da ɗan'uwanta.
Reading corner din su? Empty.
Breakfast table? Too quiet.
Homework time? Silent and lonely.

Ko da suna waya kullum da safe da dare, akwai wani abu da ke ɓacewa.
Wurin da Hameed ya bari a gida ba wani ke iya cikawa ba – ko maids, ko iyaye.
Safeenah da Abdullah suna yawan tafiya yanzu – aikinsu yana ɗaukar lokaci sosai.
Hannah kuwa? Ta koma zama da maids kawai, tana jin duniya tayi mata faɗi.

A lokacin da take jin haushi ko gajiya, babu wanda ta fi buƙata sai Hameed.
“I wish you were here,” ta furta wani yamma, tana kallo cikin tile.
“You always made things better.”