KIRAN RABO

004

by @nanahaleema11

 *KIRAN RABO.*

#Fitattubiyar2025


             ©️ *Nana Haleema.*


Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11.


*Book 1*

*P 04*




Nayla da Abiy tafiya suke a mota a hankali kafin ya kalle ta ya ce, "Ummina." Ta kalle shi ta ce, "Na'am Abiyna." 

"In kin je Kano ban da yawo kin ji?." Ta ɗaga kai sannan ta ce, "in sha Allah Abiy." 

"Kin ga abinda ya taɓa faruwa dake a shekarun baya shiyasa na tsani zuwan ki kano, ki kula ba ko yaushe zaki gida fita ba."


Nayla ta ce, "zan kiyaye in sha Allah Abiy." 

"Yauwa. Allah ya yi miki albarka ya jiƙan Ummanki." Ta amsa da amin kafin ya kalle ta ya ce, "zan saka miki kuɗi a account ɗinki duk abinda ki ke so sai ki siya." Tayi murmushi ta ce, "Thank you Abiy." Shima murmushin ya yi kana ya ce, "Ya batun Sadiq ne? Ban ji kin ce komai ba." Ta turo baki tace, "Abiy ya cika takura, kuma shi wai in na aure shi bazan yi aiki ba ni kuma gaskiya a'a" ta faɗa da shagwaɓa tana juyar da fuska gefe tana ƙifta idanu.


Murmushi ya yi cikin ƙaunar ɗiyar ta sa ya ce, "Gaskiya bazai yu ba, ya kamata ki turo min shi mu tattauna." Ta sake ƙifta idanu wanda hakan ya zama ɗabi’arta tace, "A'a Abiy, ka ƙyale shi kawai." 

"To na ƙyale shi. Sai waye kuma?." Tayi dariya ta rufe fuskar ta alamun kunya ya sake yin murmushi suka cigaba da tafiya.


Awa biyu da mintina ne suka kawo su Kano, har ƙofar gidan Hajja ya faka motar ya kalli Nayla bayan ya tsaya ya ce, "Ki shiga ki sanar da Hajja zan shigo mu gaisa." Nayla ta amsa ta fito ta ɗauki jaka ta shiga gidan dan ta sanar da Hajja zuwan Abiy ɗin. 


Da sallama ta shiga cikin muryar ta mai zaƙin gaske, Hajja da take alwalar sallar azahar ta amsa yana kallon wacce ta shigo. Nan da nan fuskar Hajja ta washe Nayla ta tafi a guje ta faɗa jikinta ta ce, "Hajja ta."


Hajja tayi dariya tace, "Hauwa'u ke ce da ranar nan? Sannu da zuwa mutanen zazzau. To ɗaga ni kar ki karya ni." Nayla tayi dariya ta ce, "Abiy yana waje zai shigo ku gaisa." Hajja ta tashi daga inda take ta ce, "maza jeki ki ce ya shigo, ai ban san shi ya kawo ki ba." Nayla ta juya ta fita ba jimawa suka shigo tare da Abiy.


A falo suka same ta Abiy ya zube a kan carpet ya gaishe ta. Hajja ta amsa da fara'a suka ta ce, "ya yara?."

"Lafiya lau Hajja."

"To ma sha Allah, Allah ya taimaka ya tsare." Ya amsa da amin kafin Hajja ta kalli Nayla ta tace, "Hauwa'u maza kawo masa ruwa a fridge, Yau Salma bata nan ta shiga kasuwa sai zuwa anjima zata dawo." Nayla ta ce, "Hajja ni fa shiyasa bana son zuwa wani lokacin, Na faɗa miki ki daina ƙara u ɗin nan a gaban sunana bana so." Hajja bata kula ta ba saboda sirikinta da yake wajan.


Abiy ne ya yi murmushi ita kuma ta tashi ta ƙarasa wajan fridge ta kawowa Abiy ruwan roba harda lemo. Ya ɗauki ruwan ya riƙe a hannun sa. Hajja ta ce, "Na gode fa Abdullahi da ka kawo min ƴar rigimata." Abiy yayi murmushi cikin girmamawa ya ce, "Babu komai Hajja, Allah ya ƙara lafiya."

"Amin ya Allah, Allah ya gafartawa Bilkisu." 


Da Abiy da Nayla suka amsa da amin kafin Abiy ya ce, "To Hajja zan wuce, ina so na shiga Kaduna kafin duhu ya yi." Hajja ta ce, "Da wuri haka? Na ɗauka sai anjima har zan yi waya a kawo maka gurasar Kano ka kaiwa yara." Yayi murmushi ya ce, "Babu komai Hajja, a kan hanya nake daman ita kawai na sauke zan koma." Hajja ta ce, "ikon Allah, daga zuwa har zaka koma kamar ba waje mai nisa zaka koma ba? Baza ka zauna ka ci abinci ba?." Murmushi ya sake yi ya ce, "Hajja kamar wani baƙo? Babu komai wallahi" ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya ajjiyewa Hajja kuɗi sannan ya fita Nayla ta bi bayan sa.


Yana jin godiyar da Hajja take yi yana murmushi har ya fita. Nayla da take bayansa ta tsaya kusa da shi ta ce, "Abiy Allah ya kiyaye hanya, Allah ya sauke ka Lafiya."

"Amin Mamana, ki kula kin ji? Banda yawo. Kin ga yadda gari yake babu tsoro ƙwacen waya yayi yawa, duk inda zaki je kar ki yi dare kuma ki sanar dani. Ki kuma tabbatar driver Hajja ne ya kai ki ban yarda da hawa keke ba kin ji?."

"İn sha Allah Abiy, Kuma daman Hajja bata barin fita da daddare."

"Yauwa."

"Allah ya kiyaye a gaishe da Mama" ya amsa yana shiga mota ya tafi.


        Wajan Hajja ta koma tana cewa, "Hajja me ki ke dashi a gidan nan? yunwa nake ji wallahi." Hajja ta ce, "Sarkin ci, shiyasa ki ke ƙiba ai. Duba Salma tayi abinci kafin ta shiga kasuwa." Falon Hajjan ta shiga dan a ciki kitchen yake dan gidan Hajja gidan ƴan gayu ne. Hajja ta biyo bayanta sai ta same ta ta shiga da kayan ta ɗakin da take sauka in tazo sannan ta fito.


Hajja ta kalle ta tace, "Baki zuba abincin ba?."

"Sallah zan fara yi tukunna, wai Hajja ya gidan yau babu wuta ne?."

"Wata waya ce ta solar ta katse har yanzu dai ba a zo an gyara ba." Nayla ta wara idanu ta ce, "wai kina nufin babu wuta a gidan nan?."


         "Eh yanzu dai kam babu, Wataƙila sai gobe ko jibi." Nayla ta ce, "Innalillahi! Wallahi da na sani bazan zo ba sai an gyara, Ga wayata babu chaji ina zan saka?." Ta faɗa ido na cikowa da hawaye cikin shagwaɓa. Hajja ta harare ta tace, "Sarkin shagwaɓar tsiya, gabaɗaya Abiy ya shagwaɓaki. Ki yi sallah tukkuna sai a san abinda za a yi." Nayla ta ce, "wallahi Hajja gabaɗaya raina ya ɓaci, bana son zama babu chaji" ta faɗa tana komawa cikin ɗakin tana mita ta yi alwala ta fito tayi sallar azahar sannan ta ci abinci.


       Kallon Hajja tayi da take kallon ta itama ta ce,"babu masu chaji a unguwar nan na kai?." Hajja ta ce, "a sace miki wayar ai." Nayla ta ce, "ni fa shiyasa ban cika son zuwa Kano ba wallahi, da na san babu wuta ai da na taho da power bank ɗina. Yanzu tsakani da Allah ta ya zan iya rayuwa babu chaji?."


Hajja ta ce, "In kin huta zuwa la'asar sai ki shiga wajan Aisha ki saka chaji." Nayla ta ce, "wace haka?." Hajja ta kalle ta tace, "Didi." Nayla ta wara ido ta ce, "wannan mutumin yana nan zan shiga gidan? A'a rufa min asiri kar ya naushe ni, Itama Didin in ta shigo gaiahe ki ma gaisa." Hajja tayi dariya ta ce, "babu abinda zai yi miki, ki huta sai ki shiga."


Nayla ta ce, "ni tsoronsa nake ji Hajja, Zuwana na ƙarshe harara ta ya dinga yi dan kawai ina hira da Didi. Didin ta fishi kirki shi bashi da mutunci, daman gashi da zubin abin tsoro." Hajja ta ce, "ke dai baza ki ce bashi da kirki ba, dan ya taimake ki taimakon da babu wanda ya taɓa yi miki shi a rayuwa." Ta turo baki ta ce, "ni wallahi ban so kuna tuna min wannan maganar" ta faɗa tana tashi ta shiga ɗaki. Hajja tayi dariya zuciyarta cike da farin cikin ganin jikarta ta.


          Didi kuwa cikin lokaci kaɗan ta kammala sana'ar abincin da mutane suka saka order, mai delivery ya tafi kaiwa kowa tayi wanka ta gyara gidan kamar ba ita ce tai aikin ba. Sana'arta karɓe ta, tun tana yi da kaɗan-kaɗan har ta kai ta kawo wata ran sai ta yi abinci pack ɗari da hamsin ko ɗari biyu. Sosai ta ke samun alkhairi tana kashe matsalolin gabanta, babu abinda zata cewa Allah sai godiya. Shiyasa kullum in ka ganta fes da ita, daman ga ta ƴar gayu in ta yi kwalliyya sai ka kalle ta ka sake kallo saboda babu abinda ya fi ƙarfinta.


Tana zaune bayan ta idar da sallar la'asar tana ta zullumin rashin kiranta da Omar bai yi ba tunda ya tafi Abuja, ta kuma san hakan ba halin sa bane ba. Sallama aka yi ta amsa tana jiran a shigo. Nayla ta shiga falon bayan ta sake yin sallama Didi ta amsa tana murmushi kafin ta ce, "kaii Nayla! Saukar yaushe?." 


Nayla tayi murmushi ta ƙarasa ta zauna ta ce, "ɗazu da azahar nazo Didi, Ina yini."

"Lafiya lau Nayla, ya hanya?."

"Alhamdu lillah."

"Ma sha Allah, sannu da zuwa. Tunda kika koma Wancan lokacin baki sake dawowa ba, na cewa Hajja Nayla tayi mana yaji kenan."


Nayla tayi murmushi ta ce, "Wallahi Abiy ne sam baya son zama na a Kano, kuma ga makaranta shiyasa dole ina can. A cikin kwanakin nan na kammala tahfiz ɗin da na shiga shiyasa." Didi tayi dariya ta ce, "baya so ki yi nisa dashi ne." Nayla murmushi ta yi kafin ta ce, "Didi don Allah zan saka chaji." Didi ta ce, "Kamar wata baƙuwa Nayla? Jeki ki saka mana." Nayla ta tashi ta saka chaji ta dawo ta zauna.


Didi ta kalle ta ganin sai murmushi ta yi sai tayi murmushi itama ta ce, "kwanaki na ga kun sha biki sai rawa ki ke, na ce Nayla akwai son rawa." Nayla ta kulle fuskar ta tana dariya ta ce, "Didi ashe kin ga status ɗin."

"Na gani tunda gashi na faɗa miki." Nayla ta sake yin dariya amma bata ce komai ba.


Didi ta ce, "yanzu kuma na gama aikin abincin order bara na duba miki abinci." Nayla ta ce, "Na ƙoshi Didi, ina zuwa gidan Hajja na ci abinci." Didi ta ce, "Daman ke ai bakya cin abincina, baki taɓa ci ba, kullum kin ƙoshi ki ke cewa."

"Ba haka bane ba wallahi, ina zuwa na ci abinci bana jin yunwa."

"Amma dai zaki mana shekara ko?." Nayla ta wara ido ta ce, "taɓ! Ai ko sati biyu bana tunanin zan yi a nan." Didi tayi dariya ta ce, "Abiy yafi so ya dinga ganin ki kullum, da gaskiyarsa."


Nayla ta murmusa tana jin daɗin zama da Didi, saboda mace ce mai fara'a da wasa ga saurin sabo. Ta zama tamkar jikar Hajja itama, tana matuƙar girmama Hajja sosai, ko me yake damunta Hajja take iya faɗawa ta bata shawara. Shiyasa duk wani mai zuwa gidan Hajja ya san Didi saboda gidan zuwan ta ne, ko biki ake a ɓangaren Hajja Didi na zuwa kuma an santa sosai. Didi ta miƙe ta shiga ɗaki tunawa akwai abinda zata yi tabar Nayla a zaune tana ƙarewa falon kallo.


               “Wacece ke!?.”


Abinda taji an faɗa kenan cikin kakkausar murya. A hankali ta juyo a firgice suka haɗa ido nan take gabanta ya yanke ya faɗi. Kafin ta tattaro abinda zata ce ya ware murya cikin tsawa ya ce, "Nace Wacece ke!? Me kika yi a zaune a na wajan?." Nayla tsabar tsoro bata san ta miƙe tsaye ba, jikinta na rawa nan da nan ido ya cika da hawaye abin ka da ƴar shagwaɓa.


"Goje!, Tk!, Bash! kuna Ina!" Ya faɗa da ƙarfi yana kallon ƙofa, sai gasu sun shigo falon da hanzari. Nayla ya nuna musu ya ce, "ya akayi wannan ta shigo gidan nan? Wacece ita? Kenan in bana nan barin kowa ku ke yi ya shigo!?." Goje ya kalli Nayla da har lokacin jikinta yake rawa cikin tsawa ya ce, "Ke daga ina ki ke!? Waye ya baki izinin shigowa gidan nan?." 


Numfashi take ja daƙyar hawaye na sakkowa daga idonta, ta saka magana balle ta iya cewa wani abun. "Ba magana ake miki!?."

"Cha....ji....na....ka...wo..." a fusace Omar ya ce, "Nan gidan kawo chaji ne? Ku fitar min da yarinyar nan yanzu."


Didi da take banɗaki take jiyo amon maganarsa da hanzari ta fito dan da tasan zai shigo baza ta bar Nayla ita kaɗai ba, ta san sai an yi haka. Tana fitowa falon ta ce, "Kar wanda ya taɓa ta." 


Cak suka tsaya da ƙarasowa inda Nayla take ta jawo hannunta zuwa kusa da ita sai kawai ta fashe da kuka ta kwanta a jikin Didi. Didi ta shafa kanta ta ce, "yi haƙuri Nayla, da na san zai dawo yanzu da ban barki ke kaɗai ba, Zauna" ta faɗa tana zaunar da ita akan kujera.


Omar ta kalla fuska babu walwala ta ce, "kai wai meyasa ka ke haka ne? kenan bazan yi baƙi ba sai wanda ka sani?. Haka kawai daga dawowarka kazo ka fara yiwa ƴar mutane ihu ba tare da ka santa ba? Kenan bazan yi baƙuwa ba lallai sai ka santa? Meye haka ne?." 


Kallon Didi yayi amma bai ce komai ba ta kalli su Goje ta ce, "kenan ku ne masu yi masa gadina, sai baƙin da ku ka ga dama sannan zasu zo su ganni ko?." Zasu yi magana ciki tsawa ta ce, "ku fice ku bani waje!." Dole suka cika umarninta suka fita. Didi ta dawo da kallonta gare shi ta ce, "kar ka sake ganin baƙuwata ka sake yi mata ihu, in kai baka buƙatar baƙi ni ina buƙatarsu, wajena tazo ba wajanka ba dan haka babu ruwanka da ita."


Wani irin yake ji a jikinsa da zuciyarsa, ya zubawa Didi ido cikin abubuwan da suka tarar masa a ƙirji. Na farko kukan da Nayla take yi yana daga cikin abinda yake sake harzuƙa shi, a ganinsa dan shagwaɓa shi zata saka a gaba tana yiwa kuka, me aka yi mata?. Na biyu faɗan da Didi take masa a gaban baƙuwa yafi komai ɓata masa rai. Ta fi kowa sanin baya so ayi masa faɗa a gaban mutane balle kuma mace baƙuwa wacce bai santa ba, babban abin haushin ma ko gaisawa bata tsaya sun yi ba ta fara yi masa faɗa akan wata wacce bata da alaqa da ita.


Kallon Nayla ya yi a fusace ya ce, "dalla malama ki yiwa shiru ko na yanka bakin ki!." Wata irin firgita Nayla tayi sai gata ta dawo ƙasa daga kan kujera ta cure waje ɗaya jikinta na tsuma. Babu zato babu tsammani ta ji maganar shiyasa ta gigice. 


Didi ta sake fusata ta kalle shi ta ce, "Omar fita ka bar min falo." Ido ya waro waje jin mamakin abinda tace, a daidai lokacin da Nayla ta kalle shi sai ta sake gigicewa ganin idanunsa kamar za a saka hannu a cire saboda girma. Kafin ya yi magana ta sake cewa, "na ce ka fita ko!?." Bai ce komai ba ya juya ya fita a zuciyarsa yana tabbatar da dole ma ya hukunta Nayla duk da bai santa ba.


Didi ta koma kusa da Nayla ta riƙe ta ta ce, "yi haƙuri Nayla, taso ki zauna." Ta faɗa tana taso da ita ta zaunar da ita akan kujera ta kawo mata ruwa mai sanyi ta ce, "sha ruwa." Ba musu ta karɓa tasha tana sauke ajiyar zuciya. Didi ta kalli gaishe ta sai ta bata dariya ganin hawaye shaɓe-shaɓe fuskarta har tayi ja kamar wacce aka yiwa duka.


"Yi haƙuri kin ji, haka nan yake shi in yaga baƙo ko baƙuwa in bai san su ba shikenan sai faɗa. Ki nutsu ai ya tafi ki goge hawayen nan."


Nayla ta goge idanunta tana jan numfashi amma har lokacin a tsorace take. Sai da Didi taga ta nutsu sosai sannan ta sake cewa, "kar ki damu bazai sake yi miki haka ba." Nayla ta ce, "ai bazan sake zuwa ba ma Didi, bara na ɗauki waya 

ta na tafi." 


Didi tayi dariya ta ce, "Wallahi babu inda zaki je, kuma in baki shigo gidan nan ba shi zan saka ya ɗauko min ke a wajan Hajja." Nayla tayi gum bata ce komai ba amma zuciyarta cike take da tsoron sa, bata taɓa ganin halitta ta mutane wacce take tsoro kamar sa ba.


Ganin ta yi shiru sai Didi ta tashi ta shiga kitchen ta ɗauko abincin da ta dawo kusa da Nayla ta ce, "ko zaki kai masa abincin?." Yadda Nayla tayi da idanu cikin firgici ya bawa Didi dariya ta ce, "wasa nake kwantar da hankalinki" ta faɗa tana fita tana dariya dan wallahi yadda ta tsorata dariya ta bata.


Setroom ɗin da yake gidan wanda ya kasance ɗakinsa ta nufa, kafin ta ƙarasa ya fito har yayi wanka ya canja kaya zuwa na shan isa, dan rigar jikinsa ko hannu bata dashi sai wando wanda ya wuce guiwa da kaɗan. Kallon sa tayi ta ce, "sai mu koma ka ci abinci." Bai kula ta ba sai ma sake tamke fuska da yayi yana kallon ƙofar ɗakin da alama tana ciki tunda ga takalmin ta nan. 


Didi ta ce, "Magana nake maka Omar." Nan ma ya share ta dan tsakani da Allah in ba dan ita bace da yanzu ba wannan labarin ake yi ba, ta bashi haushi sosai. Itama sai ta ɗaure fuska ta ce, "ina yi maka magana kayi min banza."

"Me zan ce miki? Kin nuna waccan abar ta fi ni" ya faɗa cike da jin haushi.

"To haka kawai daga ganin yarinya sai ka fara yi mata ihu baka san ta ba baka san daga inda take ba? kai baza a yi baƙi a gidan nan ba kenan?."


Ya kalle ta ya ce, "duk wanda zai zo gidan nan munafuki ne, yana zuwa yaga ya muke rayuwa ni dake." Didi ta ce, "in ma hakan ne babu ruwan ka, kar wata baƙuwata ta sake zuwa kayi mata abinda ka yi yanzu, Wajena suka zo ba wajanka ba." Ya kalle ta ya taɓe baki ya nuna kansa da yatsa ya ce, "ni ki ka yiwa faɗa a gaban wata yarinya, ni kika yiwa tsawa har ki ka ce na bar miki falo kuma duk a gabanta. Ni ko Didi?."


Didi ta kalle shi dama ta san zai ji haushi ta ce, "kaine ka jawo, lokacin da ka shigo da kun gaisa ka shiga ɗaki inda nake ai da hakan bai faru ba." Ya girgiza kai cikin ƙunar rai, baƙin ciki yake ji zuciyarsa, kamar shi tiger Didi ta yi masa faɗa akan wata banzar yarinya wacce bai ma santa ba. Ya kalli Didin da take kallon sa cike da ɓacin rai ya ce, "ni wai kika kora a gaban wata, ni Omar hmm....." ta kalle shi ta ce, "meye hmmm? Kar ka cutar da ƴar mutane, kar ka saka a zubar mata da jini."


        "In ki ka ce kar ayi ɓata bakinki ke yi, zata san ta shigo gidan mu ta saka chaji har an yi min faɗa a gabanta. Nan gaba aka ce ta shigo baza ta yi wannan marmarin ba."


Ganin yadda yake cize baki yana maganar ya saka Didi ta ajjiye abincin da ta taho masa dashi ta riƙe hannunsa ta ce, "Omar kar ka saka ka cutar da ita, na faɗa maka kar ka yi mata komai." A fusace ya cire hannunsa daga nata ya ce, "to meyasa zaki yi min faɗa a gabanta? Meyasa?. daga wani gari na dawo ko tsayawa baki yi mun gaisa ba ki ka fara yi min faɗa." Didi ta ce, "shikenan nayi kuskure, amma kar ka yi mata komai na sake faɗa maka." 


Kai ya girgiza dan maganar bata wani shige shi ba ganin haka Didi ta ce, "wai baka gane ta ba ma?." Kallon ta yayi alamun na san ta ne daman, ta ɗaga kai dan tana fahimtar saƙon ido in ya yi mata tunda ya saba ta ce, "ka san ta mana, Nayla ce fa jikar Hajja. Yarinyar da aka taɓa ƙoƙarin yi mata fyaɗe ka cece ta ka dawo da ita wajan Hajja?. Ka tuna har ka dinga yiwa Hajja faɗa akan ne aka barta ta fita ita kaɗai bayan a san baƙuwa ce bata san gari ba, ka tuna?."


Kallon Didi yayi jin abinda take cewa dan ya tuna abinda ta ce ɗin tsaf a ransa, har hango lokacin yake yi a idanunsa da yadda komai ya faru. Amma bazai gane ta ba, dan a yanzu ma ba ganin fuskarta ya yi sosai ba, gwara ma a da ɗin ya san fuskarta saboda suna haɗuwa bayan abin ya faru tana yawan zuwa wajan Didi kafin ta bar garin. Bazai manta da ita ba dan ta silar ta ya fara yankewa wani ɗan yatsa a duniya, tabbas a kanta ya fara zubar da jini saboda ceto. Batu ake na shekara tara zuwa goma baya ta ya zai gane ta banda abin Didi?.


"Ni ban san ta ba, ina kallonta a matsayin wacce ki ka yi min faɗa a gabanta" Abinda ya ce kenan ya wuce ya barta a wajan tayi dariya tana jinjina son girma, da son mulki, da zafin kai irin na ƙanin nata, abincin ta shigar masa dashi ɗakim sannan ta koma wajan Nayla.