005
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 05*
Didi da ta bar wajansa wajan Nayla ta koma ta zauna kusa da ita ta ce, "na bar ki ke kaɗai ko?." Ganin Nayla a tsorace har lokacin sai ta tausasa murya ta ce, "har yanzu a tsorace ke ki ke? Ki nutsu mana." Nayla ita dai gaban ta faɗuwa yake saboda duk abinda suke faɗa tana ji, tana ji Didi tana ce masa kar ya yi mata komai duk shine ta sake firgita. Dana sanin shigowa gidan ta mamaye mata zuciya, ji take ina ma bata shigo ba ta haƙura da chajin wayar.
Didi ta kalli Nayla ganin har lokacin tsorace ta ke sai tayi dariya ta ce, "Wallahi dariya ki ke bani, yadda ki ka firgita haka kamar kin ga wani abin tsoro, In kina nuna kina tsoronsa har haka sai ya fi cewa zai latsa ki. Omar fa yana da sauƙin kai, kawai shi bashi da saurin sabo ne, amma na tabbatar miki kafin ki bar Kano zaku saba, Zaki yi mamakin yadda yake da hira da kuma yawan murmushi." Murmushin yaƙe kawai Nayla tayi dan kawai tana jin ta ne, amma ta yaya zasu saba da dashi bayan abinda ya faru.
Didi ganin tayi shiru ta dinga jan ta da hira kaɗan-kaɗan tana amsawa duk da har lokacin a tsorace take matuƙa. Agogo ta kalla sai ta kalli Didi ta ce, "Didi bara na ɗauki wayata na tafi saboda zan kira Abiy na ji ya koma gida lafiya." Didi ta kalle ta tace, "Ko dai kina so ki gudu saboda Omar?."
"A'a Didi, Abiy zan kira na tabbatar yana jiran kira na."
"To Shikenan. Ina jiranki da daddare ki zo ki taya ni hira." Nayla ta ɗaga kai kawai ta tashi ta ɗauki wayarta da charger tayi hanyar fita Didi na bayanta.
Tana fitowa daga falon yana shigowa gidan idanunsa ya faɗa cikin na ta. Nayla bata san lokacin da wayar charger sun suɓuce a hannunta ba, wayar ta faɗi ta ɗan yi ƙara amma bata duba ba jikinta ya cigaba da rawa. Hannunta Didi ta riƙe ta bayanta, Nayla ta sunkuyar da kai cikin tsoro. Didi ta kalle shi bata ce masa komai ta kalli Nayla ta ce, "Nayla don Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga kin yar da wayarki" ta faɗa tana sunkuya ta ɗauki waya da charger ta riƙe mata hannunta har suka bar cikin gidan.
Ai Nayla bata iya cewa Didi komai ba, tana bata wayar ta kwasa a guje ta yi hanyar gidan Hajja. Didi tayi dariya ta dawo cikin gidan tana dariya suka sake haɗuwa da shi cikin dariya ta ce, "Kaji tsoron Allah ka daina tsorara yaran mutane don Allah, haba wannan bala'i daga haɗa ido da kai duk ta ruɗe?. Ni ban ga meye abin tsoron a nan ba." Bai ce komai ba ya sake shiga cikin gidan tayi dariya ta bi bayansa tana jinjina ƙarfin tsoron da Nayla take masa.
Nayla a haka ta faɗa cikin gida a firgice Hajja da Salma da suke zaune a falo suka ganta kamar an cillo ta Hajja ta ce, "ke lafiya?." Nayla ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Hajja har abada bazan sake shiga gidan Didi ba, na gama shiga gidan ko me za a bani." Salma ta wara ido ta ce, "shiyasa daman da Hajja ta ce min kina can nace wallahi bazan je ba, in yaga ka shiga gidansu kamar zai yanka naman ka haka yake ji. Sam baya so ya ga an shiga gidan, ba ya ƙaunar kowa ya shiga gidan su daga shi sai Didi."
Nayla ta ce, "wallahi Salma fitsari ne kawai ban yi ba, yau ni naga bala'i ganin idona. Salma duba min wayar nan ki ga ko screen ɗinta ya samu damuwa, dan yadda ta faɗi a hannuna da na ganshi na tabbatar daƙyar bai fashe ba. Wannan halitta ta mutumin nan akwai ban tsoro, ga ido kamar na aljanu." Salma ta karɓi wayar da take miƙa mata dubawa kana ta ce, "Wallahi ya tsage. Wannan bala'i har ina? daga gidan su ya jawo miki asarar sama da naira dubu ɗari biyu. Dan screen ɗin wayar ki in bai yi haka ba ya kusa."
Nayla ta faɗi akan kujera ta dafe kai ta ce, "gabaɗaya ban shigo Kano da ƙafar dama ba, da fari gidan nan babu haske, ga tashin hankalin da na haɗu dashi sannan ga asara." Hajja da take jin ta take kallon ta tayi dariya ta ce, "wai duk tsoron Ummarun ne ya saka ki ka firgice haka?." Salma ya ce, "ba dole ba Hajja, wannan mutumin kallon sa ma tsoro yake bawa mutane balle kuma ya harare ka ko yayi magana. Ni na jima ban ga mutum bai baƙin hali kamar sa ba, sai kyaun fuska kamar shi ya tsara kansa, amma zuciya da hali baƙaƙe."
Hajja ta ce, "ai kam yana da kirki sosai, kaf unguwar nan ni kaɗai ce nake kiransa da Ummaru ya amsa har yayi min magana. Duk da nima ɗin kafin ya amsa sai ya ce bana son sunan amma sai na faɗa, kuma zai gaishe ni wani lokacin da fara'a sannan ya tafi. Kawai shi baya so a raɓi yayarsa ne saboda mutanen unguwar nan suna yi musu wata fassara mara daɗin ji. Shiyasa sa baya son kowa ya shiga gidan su dan baya ƙaunar munafurci da gulma."
Nayla ta ce, "to mu ina ruwan mu da wata fasaara da ake musu Hajja? Shima ya san in ba dan Didi ɗin ba waye zai shiga gidan nan? To Didi tana da kirki sosai, tun ɗazu naso fitowa amma ta hana ni ta ce sai yanzu zan fito, shima ƙaryar zan kira Abiy ne ma ya saka ta ƙyale ni. Har tana cewa na dawo da daddare, to in ba aljanna ake bayarwa ba me zai kai ni gidan nan na ta?."
Salma ta ce, "bashi da mutunci bai san mutunci ba, ai ko dan yayarsa ya kamata ya dinga ɗagawa mutane ƙafa. Ni fa shiyasa wallahi bana ma shiga gidan dan bana so na haɗu dashi kwata-kwata, In ta shigo gidan nan ta dinga yi min mitar bana shiga inda take, kin san ni babu ɓoye-ɓoye kai tsaye na ce mata Omar yana gidan bazan iya shiga ba.." Nayla ta ce, "ina yaga kirki? shi ai abin alfaharinsa ne ma a shiga gidan su. Nima ba dan chaji ba da sai dai ta shigo ta ganni, duk abinda zata ce bazan je ba."
Hajja tayi dariya ta ce, "ke dai kawai ya firgita ki ne Hauwa'u."
"Wallahi sosai Hajja, haka na saka Didi a gaba ina kuka tana rarrashi." Hajja tayi dariya sosai ta ce, "ke fa babu abinda zaki cewa Omar wallahi, ya taimake ki a lokacin da ake gab da tuntsurar miki da budurcinki. Ba dan shi ba da yanzu ana zancen an yi miki fyaɗe shekarun baya."
"Hmmm!" Shine abinda Nayla tace kawai tana sauke numfashi. Salma ta ce, "Kai Hajja! daman wai shine ya taimake ta?." Hajja ta ce, "Ke duk labarin da ake yi baki sani ba?."
"Ban taɓa tsayawa na fahimta ba ai."
"Shine wallahi. Haka ya ɗauko ta kamar jaririya saboda a tsorace take sosai sai kuka take yi daman ita sarkin shagwaɓa. Gashi babu riga a jikinta sun yaga rigar atamfar da take jikinta, hakan ya saka shi ya cire rigarsa ta sama ya saka mata sannan ya dawo da ita."
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Don Allah Hajja ki daina faɗar haka bana so wallahi" Nayla ta faɗa da ƙarfi tana runtse ido. Salma ta sake cewa, "Hajja wai kina nufin rigarsa ya sakawa Nayla?." Hajja ta ce, "ƙwarai kuwa."
"Tab! amma ya cuce ta wallahi."
"Meye na cuta shi da ya yi taimako? Kuma magana ake ta shekaru takwas ko tara baya."
"To Hajja shekara tara baya a ƙalla tana da shekara sha uku ko sha huɗu."
Hajja ta kalli Nayla da har lokacin idon ta yake a kulle ta ce, "Kuma da yake tana da girman jiki ƙirjinta a cike yake shiyasa ma suka so lalata ta." Nayla tashi tayi ta bar falon cikin takaici da baƙin cikin wannan labari, ta tsani ta ji ana bada labarin nan ko kusa.
Salma ta ce, "Gaskiya Hajja ki daina bada labarin nan, hakan yana nufin fa ya gama ganin halittarta tun shekarun baya. Yanzu kallon raini yake mata shiyasa ma yake tsoratata."
Hajja ta ce, "to sai me? Da ya gani ɗin wani abun yayi mata? Da ya barta a wajan su da ba lalata ta zasu yi ba?. Ni tun daga lokacin nake ƙaunarsa saboda abinda ya yi mata, daga ranar ya fara riƙe amfani da makami dan a kanta ya fara zubar da jini, akan taimakon ta ya fara saka makami a jikin mutum. Haka yazo gidan nan yana faɗa kamar ƙanwar sa aka ao cutarwa. Ni yayi min, kuma har gobe ina kallon sa da wannan ƙimar."
Salma tayi shiru bata ce komai ba Hajja ma tayi shiru dan da alama tana taya ƴar uwarta kishi dan ance ya ɗauko ta babu riga. Ita kuma bata ga abin fushi ba, taimako ne kuma ya wuce wataƙila ma shi ya manta.
Omar kuwa bayan Nayla ta fita shima fita ya yi bai dawo ba sai bayan an yi sallar magriba as usually shi da mutanen sa. A falon ta suka baje suka ci abinci kamar yadda ya saba ciyar da su kafin ya sake fita. Bai dawo ba sai tara na dare ya same ta a zaune da waya a hannunta tana dannnawa.
Kallon sa tayi bayan ya shigo ta ce, "baka faɗa min me ya faru a Abujaa ɗin ba." Zama yayi ya kalle ta ya ce, "wani ɗan aiki zan yi zuwa wani satin."
"Allah yasa ba harkar siyasa ba ce ba." Murmushi yayi kaɗan amma bai ce komai ba. Ta kalle shi ta ce, "ina so ka gane ƴan siyasar nan amfani suke yi da ku wajan lalata rayuwarku su kuma su inganta ta ƴaƴan su, ku ɗauki makami ku je ku yi musu yaƙi su kuma su gina yaran su da ilimi. Kuna nan kuna wahalar banza kuna haƙilo ƴaƴan su suna gida cikin ac da kwanciyar hankali, ku kuma sun mayar da ku ƴan wahala waɗanda ba su san darajar kan su ba. In da gaske yaƙin neman zaɓen su ke yi su fito a yi da ƴayan su mana. Baza su yi ba saboda rayuwar ƴaƴan su ba irin ta ku bace, aikin ku ku salwantar da rayuwarku a kan su, su kuma su gina na su." Kallon Didin yayi ya ce, "Didi kenan."
"Ko nayi ƙarya ne?."
"A'a" ya faɗa yana ɗauko wayar sa ƙirar iphone yana dannawa.
Didi ta kalle shi ta ce, "Ni wai ya aka yi ka ke iya operating ɗin waya? Gashi ko labarai ne da turanci sai na ji ka karanta ka faɗa min, ya abin ya ke?." Ya kalle ta da mamaki ya ce, "Oh dan bana so ana yi min magana da turanci shiyasa ki ke yi min kallon ban iya ko?." Ta yi ƴar dariya ta ce, "A'a ban ce ba. Kawai dai na san ko secondary school baka yi handling ba, duk da ka ce jarabawa ce baka yi ba."
Ya kalle ta ya ce, "Ai kin san jarabawar ce ban yi niya ba, kuma mutum nawa na rubutawa waec ana biyana?. Ko ke da ki ke taƙama da wani NCE ko diploma sai mu zuba, wallahi sai na kai ki ƙasa ko motsi baza ki iya ba. In kina mamaki a feɗe biki biri har wutsiya." Ta yi dariya sosai ta ce, "Wane mutum! Ku ai gifted ne, ku karatu yake bi kuna guduwa. Da ka tsaya ka yi karatu ko Omar, da ba ƙaramin amfana za a yi dakai a ƙasar ka ba."
"Babu niya, tunda sai wanda yake da ilimin boko ne yake zama wani a duniya zan ta zama a yadda ku ke kallona."
Didi ta ce, "Allah ya ke bawa kafirai arzuƙi a duniya balle musulmi mai bauta masa?. Allah yana bada duniya ga wanda yake da wanda baya so, lahira ce sai rabo. Ba sai mai karatun boko ne yake zama wani ba Omar, in dai Allah ya saka maka albarka zaka iya zarce wanda ya kai matakin professor. Ilimin yana da amfani ne saboda goyayya da mutane."
"Mutane haka suke ɗauka, wanda bai yi boko ba babu shi babu arzuƙi a duniya. Turanci ne kaɗai ilimi a nigeria, duk ilimin ka in baka iya shi ba a banza ake kallon ka. Mu baza mu yi karatun ba, kuma baza mu yi turancin ba, in Allah ya ce yes sai na ga ɗan shegiyar da zai ce no. Ko yanzu in niya zan je a bani takardar da ku ke taƙama da ita, kawai babu niya ne."
Didi ta yi dariya cikin tsokana ta ce, "Ni dai ina so naji ya akayi ka ke iya karanta turanci? Ko duk zaman social media ɗin ne ya kawo haka?. Yadda ka ke zama ko yaushe cikin danna waya da kuɗi ka ke samu da ita da ka ji daɗi." Murmushi ya yi kaɗan bai ce komai ba.
Ta ce, "tsokanarka nake, ko a shekarun baya kana cikin wanda makaranta take ji da ku." Bai bata amsa ba sai girgiza ƙafa da yake yi, ta kalli ƙafar ta sa ta ce, "wai ni meye benefit ɗin wannan baƙin abun da ka saka a ƙafarka? Gashi dai yana yi maka kyau sosai, amma adon mata ne."
Taɓe baki ya yi bai ce komai ba ta ce, "ko da yake ko mace aka gani da sarƙar ƙafa wata fassara ake mata daban."
"Ni kam yana burge ni."
"Sai matarka ta saka." Bai ce komai ba cikin tsokana ta ce, "Wai kuwa ka san me aure yake nufi?." Wani kallo ya ɗago ido yake mata na kin raina min hankali, Didi ta sheƙe da dariya ta ce, "to kai ba abokai ne da kai ba, ba wani waje ka ke zuwa ba ta ya zaka fahimta daidai?." Murmushi ya yi bai kula ta ba dan bazai kulata ba.
Kira ne ya shigo wayar Didi ganin sabuwar number sai ta ɗauka masu siyan abincin ta ne, ta saka a speaker daga can ɓangaren aka yi sallama jin muryar namiji sai ta amsa a sanyaye kafin ya ce, "don Allah da Aisha nake magana?." Didi ta ce, "eh itace. Wake magana?."
"Sunana Abdulhamid."
"Allah sarki!."
"Aisha ina so ki bani lokaci ina so zan yi magana dake." Didi ta kalli Omar da ya kafa mata idanu ta ce, "Magana da ni? Akan me?."
"Alkhairi. Magana a waya baza ta yu ba ikon ganin ki nake so ki bani." Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "To san sanar da kai."
"Yauwa na gode, don Allah ki saka lokaci mafi kusa in hakan zai samu."
"Shikenan, zan maka text."
"Na gode sosai, ki kwana lafiya" Didi ta amsa shi kuma ya kashe wayar.
"A ina ya samu number ki?" Omar ya tambaya yana kallonta.
"Omar ta ya zan sani? Ni dai kawai ya kira ni ne."
"Me ya ke nema?."
"Omar ta ya zan sani? A gaban ka fa ya kira ni."
Omar ya ce, "wanne lokaci zaki ba shi?."
"Bana ce ba." Ya kalli Didi cikin bada umarni ya ce, "ki faɗa masa yazo jibi, jibi juma'a kenan, ina gida nan zan so na zauna a tatauna dani. In da tsiya ya zo gidan ya tarar, in arzuƙi ne ya kawo shi ana yi masa maraba." Tayi murmushi ta ce, "to babban Yaya." Jin abinda tace sai yayi murmushi amma bai ce komai ba.
"Kai yaushe zaka yi auren ne?." Ya ɗan juya idanunsa ya ce, "kwana biyu meyasa ki ke yi min zancen aure ne?." Tana murmushi ta ce, "ai ka kai ka yi ɗin ne Omar, santalelen saurayi kamar ka ga kyau ga kwarjini ai dole ayi maka zancen aure."
"Ni wallahi bana kawo zancen aure a raina ko kaɗan."
"Ko me yasa?."
"Sai na fara aurar da ke" ya faɗa yana miƙewa tsaye.
Ƴar dariya tayi ta ce, "Ko kuma ni na fara aurar da kai ba." Bai yi magana ba ta miƙe tsaye tana kallon sa duk da ya kere mata a tsayi sosai ta ce, "burina naga kayi aure ka haifa mana mai sunan Mama Omar, duk macen da ta same ka zata yi sa'a, a haka ne ake kallon ka a baibai amma ni da na san ka, na san sa a tana tare da wacce zaka aura, musamman in ka ɗauki nasihar da nake yi maka a kullum."
Fuska sake yake kallon ta ya ce, "Yanzu in aka aure ni ba a yi sa a ba kenan?."
"Eh to, kusan hakan zan ce." Yayi murmushi mai sauti ya kalle ta ya ce, "ina zuwa." Fita yayi daga gidan gabaɗaya. Kasancewar unguwar akwai duhu da ya fito ƙofar gidan daga wajan gidan su ne kawai mai haske sauran wajan babu haske.
A hankali yake takawa yana jiyo magana na tashi ana daga inda yake nufa, muryar maza ya ji suna cewa, "hmm to Omar da Aisha meye basa aikatawa, kai a banza ta kai yanzu bata yi aure ba?. Wannan ingarmar namijin da take kwana dashi waje ɗaya ta tashi ba dole mugun abu ya faru ba."
Ɗaya daga cikin su ya ce, "wai don Allah da gaske ku ke?." Na ukun ya ce, "to kai gani ka ke wasa ne? Baka ganin yaron ko kula mutane baya yi saboda ya san iskancin da yake yi?. In da ma ace iya dabancin ya tsaya da sauƙi, to har da lalata da ƴar uwarsa. Ai ba a banza ta kai wannan shekaru babu aure ba, tana samun duk abinda ƴa mace take samu a gidan mijinta a wajansa. Kai baka ganin da an zo neman aurenta sai a gudu ba? Wannan mugun abun da suka binne ake tonowa."
“Kuma fa ashe gado ya yi, ubansu tantirin ɗan iska ne tsohon ɗan giya. Ai barewa baza tayi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, nan gaba zaman unguwar nan sai Omar ya hana mu.”
Omar yana jinsu ya runtse idanu cikin ɓacin rai da ƙunar zuciya, ya koma da baya ya hangi yaransa a gefe yayi musu alamun da su yi shiru kar su yi magana su zo inda yake. Nuni ya yi musu da kowa ya kama mutum ɗaya a cikin ƴan majalisar da suke gulmarsu. Cikin sanɗa suka ƙarasa inda suke sai caraf ko wanne ya riƙe mutum ɗaya.
Omar ya tako ya bayyana a gabansu ransa a ɓace sosai duk suka kalle shi cikin firgici da tsoro. Alama yayi musu da su sake su, dukkan su suka sake su ya bisu da kallo dan dukkan su manya ne a haife zasu haife shi. Babu wanda yayi ƙoƙarin miƙewa a cikin su saboda duk sun tsorata matuƙa suna kallon Omar. Abin ka da wanda yake gulmar wani kuma ya kama shi, wanin ma kuma irin Omar."
Tsakiyar su ya shiga ya zauna tare da ɗauko ƙaramar wuƙa a ƙasan takalmin yana shafa ta a hankali ba tare da ya kalle su ba. Duk sun ruɗe, jikinsu ya fara ƙyarma cikin tsoro. Zaman da ya yi a cikin su yafi komai tsorata su, ga wuƙa kuma a hannunsa. Ajiyar zuciya Omar ya yi, ya daidaita kansa kana ya ce, "Ku maimaita hirar da naji kuma yi yanzu." Tsit suka yi kowa ya kasa cewa komai, Omar ya kalli ɗaya daga cikin su sai kawai ya zube a ƙasa saboda tsoro jikinsa na rawa sosai.
"Ku maimaita na ce" ya sake faɗa a kausashe yana kallon su. Nan ma suka yi shiru ya girgiza kai ya ce, "kenan kun san ba daidai ku ke faɗa ba ko? Shikenan, tunda baza ku yi magana ba bara na saka a saka ku magana."
Kallon na gefen sa ya yi nan take suka taho da wuƙa suka ƙaraso wajan. Omar ya sake kallon mutanen yaga duk sun tsorata gasu kuma manya dan suna cikin manyan unguwar.
Ɗaga musu hannu yayi alamun kar ya ƙarasa inda mutanen suke ya ce, "Maganar da ku ka faɗa a kaina da Didi naji kuma zan ɗauki mataki akan hakan, abinda ya saka bazan iya yi muku komai ba kun girma iyayen wasu ne ku. Ba dan ina jin tsoro ko kunya ba, sai dan haka na yi niya."
Bash ya ce, "Damisa ai in babba bai ji tsoron hawa jaki ba, jaki bazai ji kunyar kayar dashi ba."
"Allah ya baka haƙuri" ɗaya a cikin su ya faɗa yana kallon Omar. Omar zai yi magana wani matashin saurayi ya ƙaraso wajan ya ce, "Baba lafiya?."
Omar ya kalle shi ya kalli wanda ya kira da Baba bai ce komai ba yana jira ya ji ne zai ce. Murya na rawa Baba ya ce, "lafiya lau." Yaron ya ce, "lafiya naga wannan a tsakiyar ku da wuƙa a hannunsa?." Omar Bash ya kalla yayi masa alamun da a kawo yaron, ai kuwa suka damƙe shi aka ɗukar dashi a kusa da Omar.
Cikin takaicin da ya ke ji a zuciyarsa ya fara tsinke fuskarsa da mari cikin tsananin fusata. Ya jawo rigarsa ya kalle shi ya ce, "ku hana iyayen ku yin magana a kaina da rayuwata, in ba haka ba wallahi duk abinda nayi musu ku yi kuka da kan ku." Ya sauke numfashi cikin baƙin cikin da yake ji a zuciyar sa ya ce, "ina yiwa mutum alfarma sau ɗaya tak a rayuwarsa, to na yiwa iyayenka, na ga girman su duk da basu duba girman su ba suke faɗar ko wacce magana a kaina, ina gargaɗin ka da su kansu akan abin yazo ƙarshe daga yanzu, In hakan ya sake faruwa bazan ɗagawa kowa ƙafa ba" ya faɗa yana sakin yaron tare miƙewa zai bar wajan.
"Me ka ke taƙama dashi?." Yaron ya faɗa yana kallon sa." Juyowa kawai yayi bai ce komai ba ya juya ya bar wajan, inda zai je ɗin ma ya fasa dan in ya tsaya wallahi zai iya yiwa yaron kaca-kaca da fuska kawai ya bar wajan yafi alkhairi.