KIRAN RABO

012

by @nanahaleema11

 *KIRAN RABO.*

#Fitattubiyar2025


             ©️ *Nana Haleema.*


Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11.


*Book 1*

*P 12.*


Yadda ya taka burki da ƙarfi sai da tayi gaba kamar zata kifa kafin ta koma daidai ta zauna, ya jiyo ya kalle ta suka haɗa ido bata ɗauke idonta shima bai ɗauke ba ya ce, “in kika sake yi min magana a motar nan wallahi sai kin sauka, ki aikata ki gani.” Mamaki yake bata da tsoro, ita da motar gidan su shine yake cewa in ta yi wani abun ba daidai ba sai ta sauka? Lallai wannan anyi ɗan rainin hankali, rainin hankali mana, in ba haka ba ita zai kalla ya ce in bata yi shiru ba sai ta sauka daga motar da babanta ya siya.


Sai kuma ta kasa magana tayi shiru ya cigaba da jan motar yana aiyana wallahi in ta sake masa magana sai ta fita daga motar sai dai ta hau abin hawa ta koma. (Omar akwai ƙarfin hali). 


A haka suka koma gida motar tsitt babu wanda yake magana a cikin su sai ƙhamshinta da ya cika motar gabaɗaya. Yana tsayawa a gidan ta buɗe motar ta fita, ta kalle shi bayan ta fita shima ya fito ta ce, “zan ga abinda ka ke taƙama a duniyar nan, zan ƙure maka gudu, zaka fahimci ni ba sa’ar wasan ka bace ba.” Tk ne ya zabura ya yi kanta Omar ya ɗaga masa hannu alamun ya ƙyale ta, ya juyo ya kalle ta ya ce, “cigaba.”


Wani irin baƙin ciki ya zo ya tokare mata a maƙogwaro, kenan ya mayar da ita shashasha mara hankali kenan ta cigaba da magana mahaukaciya. Juyawa tayi a fusace ta shiga cikin gidan ta cillar da mayafin jikin ta a haukace. Wayarta ce tayi take ƙara ganin sunan Ashraf ya saka bata ɗauka ba ta tashi ta hau sama a guje raina a ɓace matuƙa.


Da wannan ɓacin ran tayi sallah sannan ta yi wanka ta kwanta bacci zuciyarta nayi mata saƙa da kwancewa akan abinda zata yiwa Omar dan ta huce. Bata farka ba sai bayan la’asar, ta tashi ta sake sabon wanka ta sako riga da wando na shan isaka ta sakko ƙasa da niyar cin abinci. Kamar yadda ta zata mai dafa mata abinci ta dafa abinci ta ajjiye, ta a dining table zauna ta zuba abinda take so ta fara ci.


Wayar ta ce ta sake yin ƙara ganin mai kiran sai ta ɗaula ta ce, “ina ciki.” Abinda tace kenan aka yanke wayar ba jimawa aka shigo falon. 


Kyakykawan saurayi ne fari tass siriri mara jiki ya shigo yana kallon ta daga inda take zaune tna cin abinci. Kallon sa tayi sai ta miƙe ta ɗauko plate ɗin abincin ta shigo cikin falon tana cewa, “Welcome Baby.” Ƙare mata kallo yake yi dan shigar da tayi ta yi masa kyau a idanunsa sosai. Surar Narma tana daga cikin abinda yake ɗaukar hankalinsa a kan Narma, duk lokacin da zai yi arba da ita sai yaji shauƙin son kasancewa da ita cikin yanayi na soyayya. Ya so hakan ya kasance tsakanin su amma taƙi ba da haɗin kai, da ya yi magana sai ta ce ya jira sai bayan auren su, shi kuma gani yake kamar bazai iya jurewa ba.


Ɗan hugging ɗinsa tayi daga gefen kafaɗarsa kana ta zauna a akan kujera ta ɗora ƙafa kan ɗaya tana cigaba da cin abincinta. Zama Shima ya yi yana kallon ta cikin yanayin da ya ke kasancewa da duk lokacin da suke tare, yanayin sa na sake yin gaba in ta yi hugging ɗinsa ko ta yi masa kiss sai ya ji kamar zai zauce. Ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce, “What wrong? Naga fuskarki da alamun damuwa.” 


Yatsine fuska tayi ta ce, “Wani banzan driver Dad ya haɗa ni dashi yake raina min hankali, wai ni yake ɗagawa murya har yana cewa in na sake magana sai na fitar masa a mota.” Ashraf ya ce, “Like Seriouly? Ke ɗin yake faɗawa haka?.” Bata amsa ba sai murmushin takaici da tayi tana girgiza kai.


“Waye shi haka?.”

“Wani ɗan iskan mutum ne dan daba wai shi tiger, ni yake yiwa tsawa saboda Dad yana son ya dinga kai ni ko ina nake so.”

“Kuma Dad ɗin ya san da haka?.”

“Yes he knew, but today i won’t inform him, i want to take action independently and how him my capabilities.” Ashraf ya ce, “That’s good my Love, you should teach him a lesson so he understands you deserve respect and won’t tolerate any nonsense.”


Kallon sa tayi taga yana kallonta ba, iya fuskarta yake kallo ba duka jikinta yake kallo sai tayi murmushi ta ce, “zan koya masa hankali.”

“Nima zan taya ki.” Murmushi tayi tana kallonsa  tace, “yaushe ka zo Kano?.”

Ɗazu.” Kai ta girgiza ya ce, “yaushe zaki fara event ɗin Samra?.”

“Lahh ka tuna min, gobe ne fa, ko makeup artist ban nema. 


He looks into her eyes yana wani lumshe ido then he say, “My Narma event without makeup you looks magnificent.” Tayi murmushi ta ce, “Duk da haka dai zan yi kwalliya.” Ya bita da kallo ta ɗauki waya ta kira tana magana da turanci nan da nan ta yi booking makeup artist za a zo har gida ayi mata home service.


Ashraf ya jima suna hira kafin ya tafi dan shima a gajiye yake ya tafi ya huta da niyar in anjima zai dawo. Narma bayan ya tafi sama ta hau ta buɗe balcony gidan tana kallon ma’aikatan gidan ɗaya bayan ɗaya tana mamakin rashin ganin Omar, wato ko ya taimaye ta ya ji babu inda zata je shine yayi tafiyar sa kamar itace take aiki a ƙarƙashin sa. Wayarta duba taga number sa Dad ya turo mata kawai ta dubawa number ido kafin ta girgiza kai tare da yin tsaki ta koma cikin falon.


      Omar kuwa ko da suka bar wajan shi da Tk ba gida suka koma ba sai da suka je wani wajan bai koma gida ba sai bayan la’asar. Yana shiga kai tsaye wajan Didi ya shiga, ya same ta a zaune tana shan magani ya ƙarasa ya zauna ya ce, “Ya jikin?.” Ta kalle shi ta ce, “Jiki da sauƙi sosai, na sha magani.” Ya girgiza kai ya ce, “kin tabbatar babu abinda yake damın ki?.” Ta ɗaga kaii alamun eh.


“AbdulHamid zai zo in anjima, ka zauna ku gaisa.” Da to ya amsa mata a taƙaice kafin ya tashi ya fita daga falon. Ba jimawa AbdulHamid ya ce masa gashi ya zo ta ce ya shigo ya shigo da sallama ya samu ta ajjiye kujeru gıda biyu kamar wancan lokacin.


Zama ya yi suka fara gaisawa cikin girmama juna ya faɗa mata duk yadda suka yi da Kawu da jiran sa da yake yi dan ya ce zai neme shi. Ta girgiza kai ta ce, “Kawu ya faɗa min komai, bayan ka bar wajansa ya kira ni a waya.”

“Haka nake so naji. Amma Aisha na tambaye ki.” Ta kalle shi ta ce, “ina ji.”

“In Kawu ya baki dama kina ganin zaki iya aurena?.” Murmushi ta yi ta ce, “Allah nake roƙa ko yaushe ya zaɓa min mafi alkhairi, sai gaka kazo, in dai har kai ba alkhairi bane Allah bazai bani ikon zaɓarka ba.” 


Ya yi murmushi ya ce, “Gaskiya ne, Allah ya tabbatar mana da alkhairi baki ɗaya.” Ta amsa da amin. Omar ne ya zo wajan ya ƙaraso yana kallon su ta kalli Omar ta kalli AbdulHamid da yake kallon sa ta ce, “AbdulHamid ga Omar ƙanina kuma Yayana.” AbdulHamid ya miƙawa Omar hannu suka gaisa ya ce, “Omar ya aiki?.”

“Alhamdu lillah” ya bashi amsa a taƙaice yana sake kallon sa dan haka kawai ya ji ya burge shi.


Didi ta ce, “Ina zuwa haka?.” Ya girgiza kai ya ce, “akwai inda zan je.” AbdulHamid cikin wasa ya ce, “ko wajan ƙanwarta mu zaka je?.” Kallon sa ya yi ya ɗan saki fuska amma bai ce komai ba kuma bai yi murmushi ba. 


Barin wajan Omar ya yi AbdulHamid ya kalli Didi ya ce, “ma sha Allah, babu wanda zai ce ƙanin ki ne, kallon farko in aka yi masa za a ace Yayan ki ne dan ya cancanci zama yayan naki. Yana da kwarjini sosai kana kallon sa kaga jarumi.”


Didi tayi murmushi ta ce, “Omar kenan.” Shima murmushin ya yi yana mamaki dan shi yadda ake bashi labarin Omar ɗin sam bai yi kama da haka ba, ba dan ya sani ba ma da bazai ce shine Omar tiger dake bashi labari ba.


AbdulHamid bayan sun yi sallama da Didi ya fito zai shiga mota sai ga wani babban mutum mai ƙaramin jiki ya ƙaraso inda yake, ya yiwa AbdulHamid sallama ya amsa da girmamawa. Mutumin ya kalle shi ya ce, “Bawan Allah don Allah wajan Aisha ka zo?.” AbdulHamid ya ce, “Eh, wajan ta nazo.”

“Neman aurenta ka ke yi kenan?.”

“Haka ne.” Ya girgiza kai ya ce, “kuma ka san duk abinda da suke faruwa a akan ta?.”


Abdulhamid ya ce, “a’a, sai ka faɗa min.” Sai kuwa ya gyara tsayuwa cikin son isar da gulma ya ce, “Ko da naji, da ganin ka yaro ne ɗan mutunci baza ka kawo kan ka gidan nan ba sai dai rashin sani. Wato Aisha da Omar da ka ke gani abinda suke aikatawa a gidan nan Allah ne kawai ya sani, ya hana kowa shiga gidan ko almajiri baya shiga ya yi bara, da shi sai ita kullum su kwana su tashi. Baligi mara aure da baligar mace a waje ɗaya ai dole a samu matsala, zan iya yi maka rantsuwa da Allah masha’ar su kawai suke aikatawa a cikin gidan. Shiyasa ba ya barin kowa ya shiga gidan, irin yaran nan ƴan mata na unguwa ko kallon ƙofar gidan basa yi saboda shi. Gashi tantirin ɗan iska ajin ƙarshe, kai da ka gashi ma ai ka ga zubin ƴan iska.”


AbdulHmaid kallon sa kawai yake yi cikin tsananin mamaki ya ce, “Baba ba ƙaninta ba ne? Aka ce uwa ɗaya uba ɗaya suke.”

“Hmm ƙaninta ne mana, amma zama suke yi kamar mata da miji. Kuma bayan shi ma ta kan kawo wasu cikin gidan shiyasa take samun kuɗi tana siyan abinda take so. To in ba mazan banza ne suke bata kuɗi ba wannan sana’arta ta ta siyar da abincin order wata riba ce da ita da zata dinga wannan kashe-kashe kuɗi? Ai kana gani ka san da walalin giro a miya, ba a haka kawai ta kai wannan shekarun bata yi aure ba. Akwai mai biya mata buƙatarta daga gefe.”


AbdulHamid ya sake kallon sa ya ce, “to Baba yanzu me ka nufi da labarin nan da ka bani?.”

“Ina nufin ka rabu da Aisha kaje ka samu yarinya ƴar mutunci ka aura, gabaɗaya unguwar nan babu wanda ya sana salin su, kwatsam suka tare a cikin ta kuma wayi gari dasu. Ba a ganin dangin uwar su dana uban su balle a saka ran suna da dangi. Kaga a haife na haife ka, kamar ɗana ka ke bazan ga abinda zai cutar da kai na bari ba, kayi gaggawar daina zuwa wajan Aisha kafin girman ka da mutuncin ka ya zube a idanun mutane.”


Yayi murmushi ya kalli gefensa kawai idanunsa ya faɗa cikin na Omar da alama duk yaji abinda suke tattaunawa. Sai kuwa ya ce, “Yauwa Omar ƙaraso ga Baba yana bani bayani akan ku.” Mutumin yana ji an ce Omar ya kalli wajan da sauri ya ganshi kuwa a tsaye yana kallon sa ya Kalli AbdulHamid murya na rawa ya ce, “Aisha ai mutuniyar kirki ce, ga sanin ya kamata, ga girmama na gaba da ita. Don Allah ba abinda nake faɗa maka kenan ba?.”


Ba AbdulHamid kaɗai ba Omar ɗin kansa sai da yayi murmushi jim abinda Baba ya ce, bai nuna ba haka ya tako cikin ƙasaita yana zuwa ya kalli mutumin ya ce, “Waye kai a layin nan?.” Jikinsa ya soma rawa kar kar kar saboda tsoro. Omar ya kalli gefe yana girgiza kansa kafin ya sake kallon sa fuska babu walwala ya ce, “nace maka waye kai a layin nan?.” Murya tana rawa ya ce, “Malam Salihu.”


“Mai kiran sallah?” Omar ya tambaya yana kallonsa. Jiki na rawa ya amsa AbdulHamid ya ce, “Yanzu Baba kana da matsayin mai kiran sallah ma a unguwar nan amma ka ke faɗar irin wannan maganar akan yaran wasu? Ko baka da yara matsayinka na babba wannan ba girman ka bane balle na tabbatar kana da yara kaima da ka ke burin aurar dasu. Ko da da gaske abinda ka faɗa gaskiya ne ka taɓa gani da idon ka?.”


Shi dai yayi shiru sai hannunsa da yake rawa sosai. Omar ya kalle shi ya ma rasa abinda zai yi masa, baya son yiwa manya wani abun ko ya yi niya sai ya kasa amma babu abinda zai saka ya ƙyale Malam Salihu, sau biyu kenan yana kama shi da irin wannan munafurcin a kan su. 


Malam Salihu ya ce, “Ni fa wasa nake maka yaro, so nake naga ko maƙaryatan unguwar nan sun faɗa maka haka, dan Aisha mutuniyar kirki ce.” Omar ya ce, “Zaka tabbatar da mutuniyar kirki ce in nayi maka illa yanzun nan.”


Malam Salihu ya ce, “Ka bashi haƙuri don Allah” ya faɗa yana kallon Abdulhamid. Shima ya kalle shi ya ce, “Baba ai ko ya yafe nima bazan yafe ba, matar da zan aura ka ke yiwa ƙazafi a gaban idanuna. Ko shi ya ƙyake ka ni sai hukuma ta raba mu da kai.” 


Tk da goje Omar ya hango da ido yayi musu alama su riƙe Malam Salihu, caraf Tk ya kamo shi daman haushinsa yake ji shekaran jiya ya yi masa munafurci hakan ya saka ya ce, “Malam Salihu yau ka zo hannu, ƙarshen munafurcin ka ya ƙare.”


AbdulHamid ya kalli Omar ya ce, “Omar ka ƙyale shi kawai kar ka yi masa komai, ka bar shi da halin sa.” Omar kallon sa ya yi jin yana bashi umarni kamar wani wanda ya haifa. Omar ya ce, “ai ba a dakatar dani in nayi niyar abu sai nayi.” Ya yi murmushi ya ce, “kar ka manta kamar yayan ka nake tunda yayar ka zan aura.” 

“Ko ita bata faɗa maka bana bari ba?.” Ya yi murmushi ya ce, “a yi min wannan alfarmar.” Kallon sa ya yi zai sake magana sai kawai ya fasa ya kalli su Tk da suke tsorata Malam Salihu ya masa alama da su ƙyale shi ya juya ya shiga gida, shi kuma ya hau mota ya tafi yana mamakin munafurci irin na mutane.


       Omar yana shiga gida wayarsa ta fara ƙara ya duba ya ga number ce ya ɗauka, ana fara magana ya gane Yahya ne ya sanar dashi Narma zata fita in anjima. Bai amsa ba ya yanke wayar dan ransa a ɓace yake sosai ko wajan Didin bai koma ba.


Sai bayan sallar i’sha yaje gidan ya tarar da Narman ma ta hau mota ta tafi wai ta gaji da zaman jira ita ba baiwarsa bace ba. Tsaki ya yi da ya san hakan mai zai fito dashi daga gida yanzu. Gabaɗaya zuciyar saa cushe take akan kalaman Malam Salihu, duk da ba haka aka saba ba amma ya ji zafi sosai. Ɓacin ran da yake ji ya saka shi takowa a hankali yana tafiya ya saka pcap wacce ta rufe fuskar sa.


Narma kuwa a ƙasan gadar ƙofar nasara motar da take ciki ta mutu, tayi-tayi ta kunna ta kasa kunnawa gashi bata da number kowa balle ta kira azo a tafi da ita gıda. Tsaki tayi ta fito daga motar tana kallon hanya, wajan babu mutane sai mota da take wucewa kuma babu haske sosai hakan ya bata tsoro. Napep take so ta tare ta hau ta tafi amma bata san ma ya ake tare mai napep ba dan ba taɓa hawa tayi ba, bisa kuskure ko tsautsayi bata taɓa hawa napep ba. Shiyasa take kallon su ɗaya bayan ɗaya suna wucewa ta rasa me zata yi.


Abu taji an saka mata a bayanta kamar wuƙa zata juya aka ce, “kina juyawa wallahi sai na farɗe miki bayanki, kawo wayar hannunki.” Narma jiki ya fara rawa hannu na karkarwa ta kuma kasa miƙar wayar.

“Baza ki bayar ba sai na kashe ki?.” Hannunta rawa yake yi garin ta miƙa masa wayar garin ya yanke ya da wuƙar a hannuta. Narma tayi ƙara tana kallon hannunta, shi kuma ya yi cikin duhu a guje bai sake waiwayen ta.


Hannunta jini yake yi tana kuka ga tsoron tashin hankali, sai rawa jikinta yake yi dan bata taɓa tsintar kanta a irin wanna tashin hankalin ba sai a lokacin.