019
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 19.*
Dad ya bita da kallon mamaki ya kalli Mum da take kallon sa itama kafin ta sake kallon Narma ya ce, “Bakya sonsa yanzu?.” Ta ɗaga kai alamun eh kamar zata yi kuka. Dad ya ce, “meyasa? Ya yi miki laifi ne?.” Narma ta ce, “bai yi min komai ba Dad, kawai zuciyata bata sonsa yanzu.”
Mum ta ce, “to wa ki ke so?.” Narma ta kalle ta ta ce, “Wani ne Mum, zan faɗa miki in muka gama daidaita kan mu.” Dad ya ce, “Waye shi?.”
“Dad zan faɗa maka, but not now” she said it from the bottom of her heart, and her voice trembled with emotion.
Dad ya ce, “to shi Ashraf ya zaki yi dashi? Kin san yana sonki ko?.” Narma ta ce, “to Dad saboda yana sona sai na cutar da kaina?.”
“Amma bazai ji daɗi ba dai ko?.”
“Amma Dad rayuwata ce.”
“Is okay. Shi wanda ki ke so ɗin a Kano ku ka haɗu?” Dad ya tambaya da kulawa yana kallon ta.
Narma tayi murmushi ta ce, “Yes Dad.” Ya kalli Mum yana murmushi kafin ya sake kallon ta ya ce, “Alright, ki je ki huta in ya so daga zamu sake yin magana.” Narma in a trembling voice ta ce, “Dad zaka amince min na aure shi?.” Dad ya yi murmushi ba tare da damuwa ba ya ce, “why not my baby? Tunda kina sonsa ai shikenan. Ki je ki huta.”
Da sauri Narma ta miƙe ta shiga ciki cikin farin ciki. Dad yana dariya ya kalli Mum ya ce, “ashe wannan ne dalilin da ya saka Narma bata son dawowa daga Kano, she’s in love.” Mum ta yi dariya ta ce, “nayi mamaki fa, ka duba yadda take da Ashraf amma tunda ta ce bata so bata son ɗin ne. Ka san ita free and open ce, bata ɓoye abinda yake damunta ko kaɗan. Gaskiya zan so naga waye wannan da ya kama zuciyar Narma very cheap haka.”
Dad ya ce, “Oh love! Kin manta a ranar da na fara ganinki na fara sonki? Uhum kin manta?” Ya faɗa yana kallon Mum da murmushi. Mum tayi dariya ta ce, “I will never forget that time, shi ake kira da love at first sight.” Dad ya yi murmushi ya ce, “indai Narma zata yi farin ciki hakan ya yi min dadi.” Hira suka cigaba da yi cikin farin ciki da son samawar da ƴarsu abinda take so.
••••••••
Omar bayan ta kashe wayar gabaɗaya kashe masa jiki tayi, ya rasa abinda abinda yake yi masa daɗi. Tana faɗa masa tayi kewarsa, to wai me hakan yake nufi ne? Sannan bata manta dashi ba? Shi ya ɗauka a kwanakin da ya wuce ta manta da shi kamar yadda yake ƙoƙarin mantawa da ita. Ajiyar zuciya ya yi a bayyane ya ce, “ko meyasa ta ce tayi kewa ta oho.”
Wajan Didi ya shiga ya samu tana amsa waya, daga yadda take mayar da amsa ya tabbatar da Yayan mahaifiyar su ne. Kamar bazai zauna ba sai kuma ya zauna, ta gama wayar ta kalle shi ta ce, “Baba Adamu ne, yana magana ne akan kayan ɗakin bikina.” Ya kalle ta a kaikaice ya ce, “Haka aka ce masa bani da kuɗin da zan miki kayan ɗaki?. Didi ya kamata ki ja musu kunne fa su daina shiga lamarina da naki, Ina ruwan su ne wai?.” Didi ta ce, “da ruwan su mana Omar, iyayen mu ne.”
“Iyayen ki dai, ni kam babu ni. Kuma babu abinda za a karɓa daga wajan su komai ni zan yi in sha Allah. In kuma ki ka ce sai kin karɓa wallahi na bar garin nan baza ki sake ganina ba, sai ki zauna dasu ki cigaba da rayuwa tunda su ki ka zaɓa.
Tayi murmushi tana kallon sa a ranta tana ayyana bai san hidimar aure bane, in ba dan haka ba bazai furta komai shi ziya yi ba, shida ba sana’a yake yi ba a ina zai samu kuɗi?. Ita har mamaki take yi da bata ji yana zancen bashi da kuɗi dan ta san dai ba abinda yake yi balle tace kuɗi na shigo masa. Sannan tana mamaki in ya siyo mata kaya ya kawo mata, kayan sakawa ko na abinci haka yake siyowa ya kawo mata. In ta tambaya ya ce ta san ba satar mutane yake yi ba.
Tana ji yana ta yi mata mita tayi masa shiru bata ce komai ba dan bazata tanka masa ba indai akan dangin su ne baya gane gaskiya, ko me zata ce bazai amince ba gwara ma tayi shiru. Haka ya dinga faɗa lokacin da aka kai kuɗin aurenta gidan Kawu kamar shine babba itace ƙarama, wai meyasa ba a kawo masa ba ai ya isa ya aurar da ita. Ita dai bata tanka ba tayi masa banza dan tana tankawa zai hargitse ya tashi garin Kano. Ajiyar zuciya tayi tana ayyana rigimar Omar yawa ce da ita.
“Kai ma sha Allah, Allah ya kaimu garin madina. Allah ka sa ina da rabon zuwa wannan gari, Allah ya sa ko a radio na ci wata gasar da za a kaini Madina. Omar kalli yarinyar nan ka gane ta?” Ta faɗa tana nuna amsa wayarta. Bai yi musu ba ya kalla ya ga yarinyar sanye da baƙar abaya tayi rolling kanta fuskarta ɗauke da murmushi. Ɗauke kai ya yi ya ce, “a’a.” Ta harare shi ta ce, “Nayla ce fa, jikar Hajja.” Tsaki ya yi ya ce, “itama dai ban san ta ba.”
“Yarinyar da ka dinga bawa tsoro a gidan nan? Kai Omar har yaushe ta bar Kano da zaka ce ka manta ta?. Yarinyar da ka ceta lokaci……” katse ta ya yi ta hanyar faɗin, “to wacece ɗina da zan kasa mantawa da ita? Mun haɗa dangi ko kuma akwai wani abu tsakanina da ita?.”
Didi ta yi dariya ta ce, “babu komai. Amma na san baka manta ta ba, kawai halin wulaƙancin naka ne ya motsa.” Ɗauke kai ya yi yana mai jin haushin Nayla a ransa, ita kanta Didi haushinta yake ji, haka kawai ta dinga nuna masa yarinyar kuma ta ce lallai sai ya game ta kamar wata ƙanwarsa. Fushi ya yi ya tashi ya bar mata falon bata ma wawaye shi ba ta cigaba da harkokinta dan in ta saka lamarin sa a zuciyarta ciwo zata yi.
•••••••
Nayla kuwa kamar yadda Abiy ya faɗa kaf ɗinsu suka tafi Umra, suna garin Madina suna ibada kafin su tafi makka. Nayla gabaɗaya bata da karsashi zaman, saboda zuwa lokacin ta tabbatar da son Omar take yi, so ba wai na wasa ba na gaske wanda ake kira so. In ta tuna waye Omar da halayensa, ta tuna waye Abiy sai gabanta ya faɗi tsoro ya mamaye mata zuciya ta kasa sukuni gabaɗaya.
Ta saka tunanin Omar a ranta ta hakan ya saka ta rame, bata ma zaman hotel ko yaushe tana masallaci tana kaiwa Allah kukan ta amma abin babu sauƙi sai sake gaba da yake yi. Duk ƴan uwanta sun fuskanci canji a lamarinta, in suka tambaya sai ta ce babu komai. A wannan yanayin suka shiga makka suka yi umra Abiy bai ji Nayla tana zancen zata je Makka mall ba, dan ya san indai suka zo sai Nayla taje Makka mall ta yi siyayya ta dawo.
Suna zaune a falon hotel ɗin su gabaɗayan su Abiy ya kalle ta ya ce, “Mamana zo nan.” Ba musu ta ƙarasa inda yake ta zauna, ya kalle ta ya ce, “ban ji kina zancen zaki je Makka mall ba, lafiya ki ke?.”
Nayla ta ce, “bana son zuwa ne, duk abinda zan siya zan siya a nan ba sai naje can ba.” Yadda take magana a sanyaye ya saka ya kalle ta da kulawa ya ce, “Mamana me yake damunki? Na lura da rashin walwalarki, kina ware kanki ke kaɗai bakya son zama cikin mu, sannan baki da ƙwarin jiki, sannan kuma kin rame. Me yake damunki?. Duk lokacin da muka zo ƙasar nan har neman ki mu ke yi muna rasawa saboda yawo, amma gabaɗaya yanzu ki canja. Me ya faru?.”
Zuciyar Nayla harbawa take yi sosai, idonta ya kawo ruwa kafin ta farga har hawayen ya sakko. Abiy ya damu ganin tana kuka ya ce, “Sanar dani damuwarki Mamana.” Nayla ta goge ido ta ce, “Babu abinda yake damuna Abiy.”
“Yaushe ki ka fara yi min ƙarya Mamana?.” Ta sunkuyar da kai ya kalli ƴan uwanta ya ce, “in kuma kina so su bamu waje sannan ki faɗa min sai su bamu waje.”
Nayla ta kalli Abiy ta ce, “A’a Abiy, babu abinda yake damuna.” Abiy ya murmusa ya ce, “Mamana kina da damuwa, damuwar ma ba ƴar kaɗan ba. Ki faɗa min abinda yake ranki.”
Nayla ta sunkuyar da kai ta rasa abinda zata ce, saboda ko giyar wake ta sha bazata faɗawa Abiy abinda yake damunta ba, da ta faɗa masa gwara abinda take ji ya kashe ta. Dabara ce tazo mata sai ta ce, “Ummana, mafarkinta nake yi a kwanakin nan Abiy” ta faɗa tana fashewa da kuka.
Duk sai kowa jikinsa ya yi sanyi ba kamar Abiy da take kusa dashi, fuskarta ya riƙe ganin yadda take kuka sai baice komai ba ya kwantar da kanta a kafaɗarsa ya bata dama tayi kukan. Ita kuwa Nayla kukan rashin mafita da tausayin kanta kawai take yi, sai da tayi mai isar ya sannan ta tsagaita kukan ya ɗago ta daga jikinsa ya ce, “Kina yi mata addu’a?.” Nayla ta ɗaga kai alamun eh ya ce, “To ki yi haƙuri, addu’a itace kawai soyayyar da zaki nuna mata kin ji?.” Ta ɗaga kai alamun to ya share mata hawaye ya ce, “Yanzu ki shirya ki tafi kasuwar ki yiwa Hajja da Salma siyayya, ko baza ki basu tsaraba ba?.”
Sai tayi murmushi ta ce, “zan basu.” Ya yi murmushi ya ce, “to maza riƙe twnity ɗinki ku tafi kasuwar.” Ta ɗaga kai Abiy ya ce, “ki saki ranki bana son wannan ɗabi’ar da kika ɗauko kin ji.” Tayi murmushi ta ce, “To Abiy.” Ta kalli Jidda da take kallon ta ta ce, “Twiny mu je?.” Jidda ta ce, “Zo mu je ɗaki ɗauko kuɗi sai mu je.” Tare suka fita zuwa ɗakin su dan nan wajan Abiy ne, ɗakin suka shiga basu jima ba suka fita. Sai da suka je reception na hotel ɗin sannan Jidda ta riƙe hannu Nayla ta ce, “Twiny.”
Nayla ta kalle ta dan ta san daman sai ta tambaye ta, in akwai wanda ya san halinta a gidan su to Jidda ce. Jidda ta ce, “Twiny kin san dai ban yarda da abinda ki ka cewa Abiy ba ko? Ai ba yau kika sana mafarkin Umma ba, Meyasa baki taɓa shiga damuwa ba sai a wannan lokacin?.” Nayla ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Jidda ta ce, “Twiny ki faɗa min damuwar ki don Allah.”
Nayla ta fashe da kuka ta rungume Jidda tana kuka sosai. Jidda ta riƙe ta tana shafa bayanta a hankali dan ta san ƴar uwarta ta tana da babbar damuwa. Sai da ta bari ta gama kukan sannan ta ɗago tagoge idanun ta ta ce, “mu je mall mu dawo.” A haka suka tafi dukka su babu mai walwala a tare dashi, sun jima sosai duk da basu yi wata siyayya ba, sai dan kawai kasuwar da nisa inda suke.
Ɗakin su ita da Jidda ne kawai sai matar Yaya Anty Halisa dan Jidda babu mijinta suka zo. Da suka dawo Anty Halisa bata nan hakan ya saka Jidda cire mayafi ta zauna kusa da Nayla. Kallon ta tayi sosai ta ce, “Faɗa min damuwarki.” Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, “Twiny wani ne.” Jidda ta ce, “me wanin ya yi miki?.” Tayi shiru bata ce komai ba. Jidda ta ce, “kin faɗa soyayya ko?.”
Nayla ta kalle ta sai hawaye ya sakko mata, Jidda ta riƙe hannunta ta ce, “tun a Kaduna naga yanayinki ya yi min kama da wacce ta fara soyayya, kuma na tabbatar a Kano ki ka yi gamo da ƙaddararki. Waye shi? Ya san kina sonsa?.”
Kai ta girgiza tana kuka ta ce, “ban san sonsa nake yi ba Twiny, da na san zan fara sonsa da ban je Kano ba, da na yi zamana tare da Mama da Abiy a gida, wallahi da bazan je ba.” Jidda ta ce, “ƙaddarar kenan ai. Kuma ita soyayya ai ba kai make sakawa kanka ita ba, Allah ne, kuma yin kanta take yi a zuciyar ɗan adam.”
Nayla kuka take yi sosai tana cewa, “ban san ya zanyi ba, kullum cikin kewar ganinsa nake, kullum cikin son jin muryarsa nake amma ko number wayar sa bani da ita Twiny. Meyasa soyayya zata yi min haka? Meyasa zan fara son wanda bani da tabbaci akan zai so ni?. Twiny ko kallo ban ishe shi ba, hasalima maganar minti ɗaya bata taɓa haɗa mu dashi.”
Jidda cikin sanyi ta ce, “Waye shi?.” Ɗagowa tayi daga jikin Jidda ta ce, “Ki yi haƙuri Twinny, zan faɗa miki amma ba yanzu ba.” Jidda ta ce, “kina addu’a?.”
“Ina yi sosai.”
“Ki sake dagewa kina faɗawa Allah damuwarki, in ba alkhairi bane Allah ya cire shi daga rayuwarki, in kuma alkhairi ne Allah ya daidai ku.”
Da jajayen idanun ta ce, “gwara na yi addu’ar Allah ya cire min shi ɗin, dan ko yana sona bana tunanin Abiy zai amince.”
“Me zai hana ya amince?.” Nayla ta girgiza kai tana aiyana dan bata san waye bane shiyasa take faɗar haka.
Jidda ta ce, “yanzu dai tashi mu je mu shiga mataf ki sake faɗawa Allah damuwarki, zama bai kama mu ba ai Twiny.” Nayla ta miƙe tsaye Jidda ma ta miƙe sai Nayla ta ce, “yau ban ji kina waya da Baby ba.” Jidda tayi murmushi ta ce, “yana can Kano yana neman gida, ya dage sai unguwa ɗaya yake so kuma gidan sai wanda ya yi masa wai ai kuɗinsa ne, siya zai yi ba haya ba.” Nayla tayi dariya ta shiga tayi alwala Jidda ma tayi suka fita zuwa masallaci.
A ɓangaren Abiy bayan fitar su Nayla kowa ya fita ya zama daga shi sai Mama ya yi shiru bai ce komai ba. Mama cikin ƙarfin hali ta ce, “ka yarda da abinda Nayla ta ce maka?.”
Abiy ya kalle ta ya ce, “koda abinda ta faɗa yana damunta to tabbas akwai wani abun da yake damunta bayan wannan.” Mama tayi murmushi ta ce, “ka fahimta kenan, nima na ga haka a tare da ita sosai.”
“Amma me kike gani yana damunta?.”
“To in na faɗa sai ka ce ba haka ba, gwara nayi shiru kawai.” Abiy ya ce, “kina nufin Hajja?.”
Kafin Mama tayi magana ya ce, “kinga mu bar zancen nan, domin bazan amince son zaman Kano ne ya mayar da Mamana haka ba. Akwai dai abinda yake damunta amma ba wannan ba.” Mama ta yi shiru kawai bata ce komai ba amma ya zama dole ya nemo damuwar Nayla ko dan ta san meye in zata amfane ta tayi amfani da ita.
••••••••
Narma gabaɗaya ta susuce soyayya tayi mata mugun kamun da bata yi tunani ba, ta koma wani iri ko yaushe cikin tunani take da faɗuwar gaba. Yanzu gashi in ta kira Omar ɗin ma baya ɗauka, gabaɗaya sai ta sake shiga damuwa ta yi wani iri kamar ba ita ba.
Iyayenta duk sun lura da yanayin ta ranar Mum tayi nufin sake tambayarta. Ɗakin ta ta shiga ta same ta tayi tagumi ta zauna a gefen ta ta ce, “Narma.” Narma ta kalli Mum ta ce, “faɗa min abinda yake damun ki kika zama haka.” Narma ta ce, “Mum nima ban sani ba, amma Ina sonsa sosai Mum, Ina ji in ban aure shi ba zan iya mutuwa.” Mum ta riƙe fuskar ta tace, “Waye shi? A Ina yake?.”
Narma ta ce, “A Kano yake, kuma yanzu na samu labarin baya jin daɗi Ina so nake na duba shi Mum.” Mum ta bita da kallo mamaki ta ce, “anya shima yana son ki kuwa?.”
“Yana sona sosai Mum, yana sona. Tunda Dad baya nan gobe da safe zan je Kano zuwa jibi sai na dawo kin jiMum?.” Mum ta bita da kallo cikin tausayin yanayin da take ciki ta ce, “is okay, sai Najwa ta raka ki.”
“No Mum bana so kowa ya ganshi mamaki nake so na baku, ni kaɗai zan je.” Mum ta ce, “shikenan dai. Amma jibi zaki dawo da safe, kuma ban amince da wannan Tiger ɗin matsayin driver ba. Ki kira drivern Kano su zo su ɗauke ki ki gama abinda zaki yi ki dawo kin gane?.” Jin abinda Mum ta ce sai gabanta ya faɗi, amma da yake an barta zuwa Kano bata damu ba ta amince da hakan.
“Kar ki damu Daughter, zaki auri wanda ki ke so kin ji?.” Kai ta ɗaga cikin farin ciki Mum tayi hugging ɗinta tana rarrashi kafin ta fita barta. Narma tana fita ta tashi ta kalli kanta a madubi tana so ta gane itace ko kuwa ba ita bace, domin ta san ta canja, halayya ta da kamanninta duk sun canja saboda Omar. Mamaki take yi wai daman zata iya fara soyayya da wanda bai ma san tana yi ba? Soyayyar ma kuma da mutum irin Omar. Itace fa Narma da maza suke so ta yi musu replying message balle kuma ta yi magana dasu, amma ga Omar ya haukata ta lokaci ɗaya ta fita daga hankalin ta.
Ajiyar zuciya ta yi ta lumshe ido tayi tana sake buɗe ido a bayyane ta ce, “Faruk gani nan zuwa.”
Washe gari.
Jirgin ƙarfe takwas ta hau dan haka da wuri ta shiga kano, tana fitowa taga Yahya wanda ya san da zuwan ta tun a daren jiyaa. Gida aka kai ta daƙyar ta iya haƙura aka yi sallar azahar ta hau mota ta nufi gidan Didi kai tsaye. Sai da taje ƙofar gidan sannan ta kira Omar a waya.
A lokacin yana kwance a ɗaki abubuwa sun yi masa yawa, ya kasa gane abinda ya damunsa gabaɗaya wani irin yanayi ya damu zuciyar shi da gangar jikinsa.
Kiran ta ya shigo wayarsa ya kalli wayar, bai yi saving ba amma ya gama haddace ƙarshen number ta ko dan kiransa da take yawan yi a kwanakin nan ne bai sani ba. Kai ya dafe bai ɗauka ba yana kallo har ta katse, wani kiran ya sake shigowa kamar bazai ɗauka ba sai ya ɗauka.
Narma da ta fara kuka yana ɗauka ta ce, “Faruk Ina ƙofar gidan ku.” Da hanzari ya miƙe zaune ya ce, “ ki ka ce?.”
“Uhum, Ina ƙofar gidan ku.”
“Me kika zo yi gidan mu?.”
“Ina kiran ka baka ɗauka shiyasa nazo.” Kasa magana ya yi ya tashi ya fita ya kuwa hango motar ta a ajjiye a gefe, ganin sa sai ta buɗe motar ta fito.
Kallon ta ya yi itama shi take kallo ta ɗauki wayar hannunta sake kiransa ya ɗauka ta ce, “na ƙaraso ko zaka zo mota mu yi magana?.” Omar yace, “meyasa kika zo?.” Narma tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Da yake yana kallon ta tana kallonsa sai ya ce, “ki koma gida zan zo.”
“Na san ba zuwa zaka yi ba” ta faɗa tana yanke wayar ta nufo gidan, yana kallon ta tana tahowa zuciyar sa cike da tsoro da kuma tsantsar mamakin zuwan ta gare shi.
Sai da ta shigo gidan sannan ta zuba masa ido tana kallon sa ko kofta ido bata yi. Numfashi ta sauke ta kawar da kai gefe tana jin haushin zuciyarta da ta saka ta fara son wannan mutum mai shegen shariya da nuna ko in kula kamar sa.
Narma ta kalli gidan ta ce, “Sister fa?.”
“Bata nan” ya bata amsa babu ɓata lokaci dan ya ƙagu ya ji abinda tazo dashi. Tayi shiru bata ce komai ba, hakan ya saka ya ce, “Ina jinki, me ya kawo ki Kano har kika zo nan?. Kar ki ɓata min lokaci ki faɗi abinda yake ranki.”
“Babu abinda ya kawo ni Kano, na zo Kano saboda kai kuma saboda kai zan koma.” Narma ta gyara tsayuwa tana kallonsa ta ce, “ban san me zan ce maka ba, ban iya ɓoye-ɓoye ba haka zalika ban san wani abu tsoro ba indai a kan abinda yake zuciyata ne. Abinda na sani kawai Ina sonka Faruk! Ina sonka so na Aure!.”