NAYI SAKE DA DAMA TA

4

by @mommuhseen

_*NAYI SAKE....!*_πŸ’˜

    πŸ’˜ '''DA DAMA TA'''

   FREE BOOK ONE

*E.W.F*

Mrs bb

Mom muhseen.

Watt pad name

Humaira3461

      πŸ…ΏοΈ.....7&8

Cikin k'an k'anin lokaci Daddy yai mani fafutukar gurbin karatun na na Masters a jami'ar Buk dake nan cikin garin kano, don tuni nayi duk wasu shirye-shiryen na nayi sabbin dinkuna na sai abaya's masu kyan gaske new design yan kasar turkey da kuma yan dubai, shiri nayi sosai don da karfina zan koma makaranta wannan karon, inajin wani karfin guiwa na shigata da kuma kwarin zuciya,ada da nake ganin Soyayyar Fa'iz tayi mun illar da bazan iya tab'uka ma kaina komi ba, to yanzu inajin sab'anin hakan ba kuma don na shafe bakin kaunar tasa ba, aa nayi ma kaina fad'a ne sannan kuma na hangar ma Kai na abunda zaifi yuwuwa sab'anin wanda bazai yuwu ba, Daddy ya karfafa mun guiwa sosai tare da shawarwari masu kyau,ya kuma yi mun alk'awarin muddin na tsaya ka'in da na'in nayi karatu nafito da result mai kyau,to kuwa duk inda zai shiga ya nemo mun aiki zaiyi bakin kokarinsa, don haka na bada himma sosai har sabuwar laptop ya siya mun,sannan cikin motocinsa sabbi daya siya ya bani key d'in guda yace na ringa zuwa makaranta da ita, wadannan abubuwan yasa nakara jin komi ya warware mun daga kuncin da nake ciki, damuwar da nashiga kaso tamanin ta zabge ganin yadda Daddy yake bakin iyawarsa don farin cikina, tuni na tsufa da fara zuwa makaranta don cikin sati na uku ma nake ciki, a yadda na Lura da Ammah hakan ko kusa bai mata dad'i ba, don ba haka taso ta ganni ba sotai na cigaba da kasancewa cikin k'unci har karshen rayuwata, bansan kiyayyar da take mun takai girman haka ba sai yanzu, shiyasa har takai ga tagaji da b'oyewar tafara fiddo kiyayyarta afili akaina, hakan da Daddy ya lura yasa yake maida dukkan hankalinsa akaina, y'ay'anta kuma ya shata masu layi dani yaban umurnin duk wacce tai mun rashin kunya inci ubanta sannan idan yadawo insanar dashi zai dauki mataki akai, daman kuma khaleesat itace keda wannan halayyar, kuma na lura uwarta ce ke mata karatu a dak'i, Umaimah da Jalila banda girmamawa ba abunda ke tsakanina dasu, duk yadda Ammah ke nuna masu suyi baya dani subi layin yar uwarsu hakan bata samu ba, shiyasa tafison khaleesat d'in daman kuma itace babbar su Umaimah ke binta sai Auta Jalila.

Yanzu ko abincinta bana ci,duk da daman yan aiki keyi idan na dawo inajin yunwa zan shiga na girka abunda raina keso, kuma Alhamdulillah ni ba raguwa bace wajen sanwa, don musamman na karanci catering gab da bikin mu da fa'iz duk don na burgeshi.

Amnat tare muke fita bana barinta agida, saboda raina bai kwanta da Ammah ba, zata iya aikata mata komi don son zuciyarta, idan doguwar lecture gareni ina ajeta gidan kanen Daddy da suke uwa d'aya dashi, inbarta wajen mama baseera har inje indawo, wani lokacin ma nan muke zaman mu sai dare mu dawo gida.

Wani lokacin kuma in kaima sakina ita duk da bana shiga gidan har yanzu, saidai na tsaya waje tazo tatafi da ita idan na dawo tafito mun da ita mu wuce, Allah baisa mun had'u da sagir ba baban hashir duk zuwan da nake.

Gefe guda na zuciyata yana gaya mun ya kamata Amnat ta shiga makaranta yanzu, don tana gaf da shekara bakwai yanzu, tayi girma sosai zaune ba makaranta saukin ma ina koya mata duk abunda suka dace anan gida, don bama baccin wuri karatu muke sosai, duk da ba wani nisa nai a qur'ani ba amman ina koya mata kananun surorin da zata iya dauka kodan sallah.

Tsoron dake hanani yima daddy maganar makarantar bai wuce yace zaima ubanta magana ba, kuma hakan na cikin dalilin da zaisaka ya anshe yarsa, ni kuma babban tashin hankalina kenan har bana son tunawa, amman dole ne Amnat tashiga makaranta duk tsoron da nake.

***********

Duk munyi shirin bacci nida Amnat mun saka kayan baccin mun, na bata wayata tana ta tilawar karatun ta ni kuma ina aiki cikin computer, time to time ina yi mata gyara inda ta kakare, naji anyi man knocking na k'ofata nasan bai wuce yaran nan ba dake mun nacin in tayasu assignment, na bada umurnin ko waye ya shigo Jalila ce ta shigo da sallamarta cikin natsuwa, tana zama gefen Amnat tana gaidani.

"Yayah daman Daddy ne yace kizo"

Biron hannuna naje ina cewa, "shikadai ne falon ko hadda Ammah?"

"Aa ita tama kwanta, inajin kamar bak'one yayi"

Gabana naji ya yanke ya fad'i,na tsare jalilar dakallo kamar zata ban ansar wani abun, sai nace taje gani nan zuwa,tana jan Amnat ta fita taja kofar, jimmm nayi ban tashi ba ina tunanin waye yazo kamar yanzu? Duk da Daddy yana Attending mutane da daddare amman zuciyata ta kasa yadda xuwan banau bane, saukowa nai na saka doguwar hijab d'ina bisa rigar baccina dana sanya na sanya silifas dina ina cema Amnat ta zauna in dawo.

Tunda na kusanci falon daddyn nakejin dukan da zuciyata take yi mun yana k'aruwa, har saida na dafe kirjina ina ambaton sunan Allah, na jima sosai bakin kofar ban shiga ba ina adduar samun natsuwa,sannan nai shahada na saka kaina cikin falon, shine abu na farko da kwayar idanuna ta sauka akanshi, wani ras ras gabana ya bada dan danan kuma naji ina tsuma zuciyata tana kerma, ganin sa yai mun ba zata ainun sannan zuwansa ba alkairi bane a wajena, duk bai cika zuwa gidan nan ba inhar ba wani babbak dalili bane.

"Shigo ciki mana Bahiyya kika tsaya anan"

Maganar Daddy ta tsinke mun hanzarina, wanda shi kuma tun kallon farko da muka had'a ido dashi ya kawar da kanshi, yana sake murtike fuskarsa tamau kamar bai san me ake kira da dariya ba ko murmushi, cikin sand'a nake takawa zuwa cikin falon can nesa da su na zauna k'asa ina sadda kaina k'asa yatsuna naketa mirtsika saboda bazan iya tantance a wane yana yi nake ciki ba, cikin rawar murya nace masa "ina wuni"

Ciki-ciki ya iya amsa da cewa "Lafiya"

shima nasan ganin idon Daddy yasa ya ansa d'in, mukai shiru mu dukan Daddy ya gama nazartar mu sannan yai gyaran murya yafara da cewa,

"Bahiyya ga Baban Amnat nan yazo da batun daukar ta takoma da zama hannunsa, saboda yana son sanya ta makaranta...........A mugun rikice na dago kaina ina kallon daddy cikin mugun tashin hankali, "Aa daddy ban shirya ba, bazan iya maida masa Amnat ba don girman Allah ka bashi hakuri,"

Mugun tausayinta ne ya kama daddy amman saiya kawar saboda yasan ba abunda zai hana Fa'iz din ansar yarinyar, shiyasa tun kwanaki da ya sanar dashi a waya ya kasa gaya mata, don yasan dukkan wani farin ciki data samu cikin yan kwana kin nan zasu gudi subarta ta dalilin ansar yarinyar, shi kanshi kullin da tunanin rabuwar tasu yake da Amnat din to balle ita.

Cikin lallashi da kwantar da hankali yace dani, "ki natsuwa ki kwantar da hankalinki, bana son wani tashin hankali Bahiyya,kin san dai yana da hak'ik'in hakan shine ubanta shi alhakin rik'onta ya rayata akansa bake ba, kuma yai maki adalci tsawon shekarun nan daya bar miki ita hannunki, yanzu kuma yana bukatar yarsa kiyi hakuri kinjiko"

Bansan sadda kuka ya kubce mun ba, na kama k'afafun Daddy cikin rawar jiki ina kukan ina rok'onsa, "Daddy nasani, wallahi nasan hakan amman kace yai mun rai yabar mun Amnat, wallahi zan kula da ita fiye da yadda bai tunanin,amman bazan iya cigaba da rayuwa babu Amnat ba Daddy ka taimakeni!!"

Wani yana yi yakejin kanshi ciki,inama yana da damar rokon sa,inama zai iya d'in da yai hakan kodan farin cikin Bahiyya, mik'ewa yai cikin karfin halin saboda kukan yana tab'a masa zuciya bazai iya jurewa ba,

"Kuyi magana dashi Bahiyya,bazan iya hana shi ansar yarsa ba in nai hakan na cutar dashi, amman kuyi magana inhar yaji don kanshi zai iya bar miki shikenan"

Yabar falon cikin sauri saboda sosai kukan da take yake sosa mashi ranshi, duk cikin y'ay'ansa ba wanda yake tausayi da tsananin kauna irinta, duba da yadda ya rabata da tata mahaifiyar lokacin da take cikin bukatar hakan.

Falon bakajin komi sai kukana dake fita cikin karyewar zuciya, kusan minty biyar da tashin Daddy baice man uffan ba kuma kuma kukan nake sosai, don bansan ta inda zan rok'esa ba, fa'iz ya koyi wani hali na kafiya wanda tankwaranshi ba abu mai sauki bane, to balle yana jin tsananin haushinta da tsanarta, kodan hakan zai iya ansar yarsa don ya k'untata mata.

Tun shigowarta da maganganun su da Daddy duk yana jinsu,inhar ya fahimta shima daddy baison ansar yarinyar,to amman bazai iya barinta ba da ace zai iya kodan shi da yai hakan, kobai ansheta da kanshi ba ya tabbata anty zata iya zuwa ta ansheta da karfin tsiya wanda baison hakan, yana ganin girma da mutuncin Daddy har gobe, bai cika son jin kuka ba don yana sashi damuwa don haka kawai saiya mik'e yana cewa,

"Kishirya mata kayanta zuwa gobe zan turox driver yazo ya tafi da it.............ban san sadda na isa inda yake ba cikin tashin hankali,na durk'usa gabansa kamar wacce take neman rai ko lafiya hannunsa na had'e hannuwana waje guda ina kukan sosai har numfashina yana yin kamar zai dauke, nake masa magiya da rok'o.

"Kar kayi mun haka fa'iz katai makeni! Ka rufa mun asiri ka barmun Amnat, nasan ban canci kai mun alfarma ba amman ba danni zakai ba, ka duba girman Allah karka rabani da yarinyar nan, nai alk'awarin duk karshen wata zata zo maku hut.............kinga ni banzo naji wani dogon labari daga wajenki ba, hasalima ba wajenki nazo ba bani da damar hanashi kiranki ne shiyasa, don haka ni na gama magana koki shirya mata kayanta?ko karki shirya bazai hana ni ansarta ba, inyaso ki had'iye zuciyarki ki mutu hakan balaifi bane"

Ya d'aga k'afa afusace zai bar wajen, banyi fushi ba banyi zuciya ba saboda naji kalaman da sukafi wannan muni daga wajensa, burina ya barmun y'ata kozai mun komi,bansan na rik'e kafarsa ba cikin rikicewa ganin tafiya zaiyi,

"Fa'iz Karka yi mun haka, don Allah fa'iz don girman Allah, don darajar iyayenka Allah yajikansu,katai makeni please please Fa'iz don Allah...........duk wanda kejin kukana dole zaiji rauni ga zuciyarsa, ni kaina da bake yinsa raunin da tausayin kaina nakeji, amman hakan bai damesa ba ya hab'arar dani da k'afar tashi yai ficewarsa yabarni nan kasa ina kuka matsananci.

Saboda kunyar sake had'a ido da Daddy bai iya yi masa saida safe ba, kawai shiga motarsa yai driver yajasu suka bar gidan, yayin da yakejin wani zafi yana taso masa tun daga zuciyarsa yana lullub'esa, wani irin yana yi da bazai iya tantance wane kala bane yake neman sashi rasa kanshi, huci kawai yake yana fesarwa bazai iya zuwa gida a wannan halin ba, text ya tura ma Husna kawai yace ma driver ya wuce dashi guest house d'insa kawai.

Sadda daddy yazo ya iskeni acikin wannan halin shi kanshi hankalin sa ya tashi, hakan ya nuna bai hakura bakenan, baiji haushin sa ba yai masa uziri ya zauna yana ta lallashina tare bani hakuri, wannan dare najima banga dare kamarsa ba ya zame mun wani irin dare mai cike da k'unci da tarin damuwa, ban rintsa ba naita sallah ina neman afuwa wajen ubangijina ya kuma samun hakuri da salama akan rabuwara da y'ata mafi soyuwa agareni, saida nayi asuba na kwanta ranar ban iya zuwa makaranta ba zazzab'ine ya rufeni, har saida takai ankira likitan mu na gida, don har suma na ringayi saboda zafin zazzabin dake jikina, saida muka dangana zuwa asibiti nasha ruwa kuwa sosai ga kuma bp na daya hau cewar dr kabir d'in.

Sakina tazo ita da Abban Hashir lokacin na kwana d'aya acan, Amnat duk ta damu tana lik'e dani bata matsawa can da can ko wanka saidai Jalila tayi mata nan cikin toilet d'in asibitin bata zuwa gida,naita sauraron zuwan dan aiken da yace zaizo ya tafi da ita shiru,sai nadan kwantar da hankalina duk da nasan ba mancewa yai ba.

Ammah sau daya tazo khaleesat ma batazo ba ko sau d'ayan, umaimah kuwa itace ke kawo mana abinci.

Naji sauki sosai amman jinin yak'i sauka yadda akeso, shiyasa yaki sallamata, zuwan sakina sai yasa naji kamar na samu karfin zuciya,muka gaisa da Abban Hashir d'in yana mun yajiki.

"Jiki yai sauk'i Alhamdulillah"

"Allah ya karo sauk'i,Allah yasa ba ciwon tafiyar baby bane don munyi magana dashi yace zai ansheta"

Murmushi kawai nayi sakina ce ke bashi ansa da cewa, "inma tayi ciwo don haka aiba laifi bane, ai mugunta ce tasa zai anshi yarinyar yanzu, duk da bai ansa ba sadda tana yar tayin ta sai yanzu da ta zama mutum"

Dariya yai yace, "to lauya ni dai bani nakar zomon ba rataya aka bani, Bahiyya ayi hakuri dai inaga da zaku yi magana da juna ta fahimtar juna inaganin zaifi"

Kwalla suka cika mun ido cikin sanyin murya nace, "bazai tab'a saurarena ba Abban hashir,kawai nabar hakan da nufin yana son k'untatani ne kawai"

Tausayinta yaji sosai duk dakomi Fa'iz yai mata ita tajawo,ita ta maida fa'iz mai zuciya da kafiya.

"Zan jaraba yi masa magana muji yabarta ko zuwa nan gaba,"

Cikin jin dadin kalaminsa nace, "ai kuwa daka taimakeni Abban hashir,duk da nasan bazai yi abunda akeso ba Baiji kunyar daddy ba haka yasa kafarsa ya tafiyarsa"

"Zan jaraba in sha Allahu"

Nan yabar sakina munata tattauna maganar tana ban hakuri da bani shawara, tana cewa "inhar ya nace bazai bar maki ba,ki hakura kawai so yake kiyita binsa yana janki a k'asa, ki kyalesa duk tsiya bai isa ya canza ki matsayin mahaifiyarta ba,kuma duk inda taje dole zata nemoki wata rana"

Sai dare suka tafi naji kamar karta tafi, k'awata danai a makaranta itama tazo zakiyya sunanta, ban samu sallama ba sai da yamma washe gari muka dawo gida.

Mom muhseen✍🏻