KAZAFI

2

by @meenamajeed

WACECE SAFEEYA

Safiya Mahmud iya ce ga Alhaji mahmud sanbo. Mahaifiyar ta Malama Salma.

Alhaji mahmud yanada kamfanin shinkafa wadda shinkafar sa bata da banbaci da ta waje bayan kamfanin shinkafa da yake da shi yana da tarukan malls a garin kano sai dai yana cikin cin gajiyar arzikin sa Allah ya amsa ran sa.

Ya mutu lokacin Afeeya tana shekara 11 kuma itace iyar shi ta farko sai Ahmad mai bi mata da shekara 2 sai autar su Yusra da ke shekara 4.

Tin da mahaifin su ya mutu Malama Salma bata kara wani auran ba da dukiyar da mijin ta ya rasu ya bar ma su da ita take juya wani kaso cikin dukiyar ta cigaba da daukar dawaniyar ya’yan ta tare da taimakon babban aminin sa Alhaji sa’id. Wanda ya kasance tamkar uba ga su safeeya.

Safeeya ta taso a garin Kano tayi makarantar ta har ta gama tayi service with her young age(20).

Safeeya ta na da saurayi Nawfal wanda kowa ya san shi, yan gidan su suma sun san shi.

Suna san junan su sai dai a wasiyar da mahaifin ta da ya bari itace ya ba Muhammad Adyan Safeeya halak malak wato ya bashi auran ta. 

Cikin wasa da dariyar uwar ke fadi wa Afeeya Adyan zata aura, Afeeya ta Adyan, dan ba ta so yar ta ta cutu balle ta san tana son Nawfal amma wasiya ce dole su cika ta ko da ba mijin ta bai bar wasiya ba hallacin da Alhaji sa’id yayi musu ya isa ta ba Dan sa auran iyar ta safeeya ko Yusra.

WAYE MUHAMMAD ADYAN

Muhammad Adyan sa’id d'a ne ga Alhaji sa’id gafada.

Alhaji sa'id aminin marigayi Alhaji mahmud ne tin yarintar su su na da burin su daukaka zumuntar su ta hanyar hada yaran su auran juna. Alhaji sa'id yana da company mai suna fix’n’fiber kamfanin da ake wool, cotton, fabric, yard da sauransu.

Shahararen kamfani ne a kasar ba a iya garin Bauchi da kano ba. Alhaji sa’id tun kafin ya mutu ya mallakawa dan sa wannan kamfanin.

Muhammad Adyan sunan sa ya shayara amma ba wanda ya san fuskar sa sai na kusa da shi.

Bayan haka mata da yawa sunan crushing din sa wasu Kuma su na son sa domin kudin sa wasu Kuma domin kyan sa.

Yana da budurwa Afnan wadda duk cikin matan da ke bin sa ita ka dai ke da Saar samun zuciyar sa.

Rayuwar baya:(Flash back)

Afeeya na kwance saman gado tana latsa waya Yusra ta shigo dakin da sauri.

"Yaya yaya maganar Mammy ta zama gaskiya.

Afeeya ta dube ta ta ce:"Yusra ji yanda ki ke min kira tamkar na maki sata."

Yusra ta zauna a gefan ta cigaba da ce wa; "Yaya ba kullum Mammy ta na ce mi ki Afeeya ta Adyan to in baki labari yanzun nan naji Mammy na waya da Daddy (Mahaifin Adyan) sun ma yanke hukunci za a zo neman auran ki a sa aure kila ma a daura auren a ranar.

Tsaki Afeeya tayi cikin takaicin labarin da Yusra ta kawo mata ta ce Yusra ban san rainin hankali ni sa'ar ki ce da zaki na min rin wasan nan bana so. Tou

Yusra ta ce:"wallahi yaya da gaske nake kin ga yanzu ke da yaya Adyan sai aure." Ta karasa maganar cikin dariya.

Hannun ta Kai Zata duka Yusra, da sauri Yusra ta mike ta bar dakin.

Zaune Afeeya tay tana nazarin maganar Yusra taya zata auri Adyan bayan an san da Nawfal taya ma zata auri mutumin da ko gaisuwa bai amsa wa balle ya yi murmishi mutumin da ko a baya suna yara kullun cikin fada suke.

Ta dubi bayan hannun ta wani tabo da ya mata tun suna yara ya tura ta cikin rami ta gurje hannu.

Ta na cikin maganar zuci Mammy ta shigo ta karaso kusa daa ita ta zauna tare da cewa Afeeya na Ina son yin Magana da ke.

Afeeya da Jin haka ta San maganar auren ta ne. "Mammy kar dai ki ce min wannan mutumin zan aura mai Zubin samudawa.

"Subahanallahi wani irin mai Zubin samudawa dan saurayi da shi mai hankali da nistuwa."

"Amma  Mammy kin san Nawfal na ke so shima yana so na."

Mammy ta ce hakuri za ki yi ki cire shi daga zuciyar ki ni mahaifyar ki ce bazan so miki abinda zai cuce ki ba Sannan tin ba yau ba kin san waye mijin ki "

"Amma Mammy Nawfal mutumin kirki ne ahalin su ma mutannan arziki ne kuma suna da rufin asiri."

Ranta duk Bai so haka ba.

Na sa ni Afeeya amma ba wannan zaki duba ba shi Nawfal barai ne shi kuma Adyan dan uwane, mahaifin sa shine gatan mu kina kallo bayan mutuwar mahaifin ku an so a nu na mana fin karfi amma Alhaji sa’id ya jajirce a kan haka a ka bamu hakkin mu. Ki duba ki ga irin hallacin da ya mana.

Afeeya ta ce:"Mammy bana son sa in har dan hallacin da ya manai to a bashi Yusra ba ni ba dole sai ni ni ko ganin sa ban san yi. Ta Kara sa maganar tare da kwafa Baki.

"Safeeya ba yanda zaki yi hakuri zaki yi domin wasiyar mahaifin ki ce shiyasa nake ce miki matar Adyan dan tun wuri kisa shi a zuciyar ki amma ki ka ki toh yanzu hakuri zaki yi ki aure shi dan cika wasiyar mahaifinki. 

Ta tatshi ta fita.

Tin da Mammy ta ce wasiyar mahaifin su Afeeya tayi shiru bata kara cewa komi ba sai hawayen da su ka zo mata ba shiri. 

Yanzu rabuwa da Nawfal ya zamai mata dole. Dole za ta auri mai zubin samudawa mutmin da ko murmishi bai yi kullum fuskarsa a dunkule take tamkar kokon da ya daskare.

A wurin su Adyan bayan ya dawo daga wurin aiki Alhaji sa’id yakira shi ya mai maganar auaran;

Adyan ba komai ne ya sa na kira ka ba face in ce ma za aje nema ma aure da yar gidan marigayi wato Afeeya.

Adyan ya daga kai ya kalli baban sa sai ya janye kan sa. Ya nanata sunan a cikin ransa,

Alhaji sa’id ya cigaba; "In sha allah jibi ni da malan Yakubu zamu je kano dan nema ma aure.

Adyan da yake ta hararowa kan sa Afeeya ya ce:"Daddy yanzu yarinyar nan ka ke so na aura??

Alhaji sa'id yace toh ba kanwar ka bace ko ka fi so ka shigo mana da barai cikin gida.

"Daddy ga ni nay ko cikin family akwai yan mata ba dole sai ita ba."

"Adyan ban san Jin komi wurin ka ba shawara nake baka ba umarni nake ma auran ka da Afeeya kamar anyi an gama.

Adyan ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Allah ya shige mana gaba."

Ya mike ya fita ya koma dakin sa ya fara tunanin rawar kan Safeeya.

Rabon da su hadu da ita sheker 8 sai rana daya a ce za a aura mai ita.

Yana zaune cike da taikaicin mgnr auran sa da Afeeya wayar sa tayi beeping ya duba id yay tsaki ya ki daga kiran har ta yanke a ka kara kira. Ya daga kiran tare da cewa "Wai ba nace miki ki rabu da ni ba." Ya kwatsa mata tsawa

Mai maganara cikin waya wato Afnan ta ce:"Haba Adyan shike nan ba ka yafiya nace ma ka yi hakuri bazan kara ba amma ka ki ji dan Allah kayi hakur."

A hassale ya ce:"na ce ma ki babu ni babu ke."

"Dan Allah Ad kar ka min haka I'm sorry."

"A tunanin ki zan auri mace irin ki wadda bata san daraja ta ba da mutuncin kanta ba??

"Wallahi sharrin shedan ne amma zuciyata kai kadai ta ke so dan Allah kayi hakuri ka zo a yi maganar auran mu da kai, please.

"Ke ba wani zancen aure tsakani na dake dan jibi ma za a min baiko dan haka daga yau karki kara kira na." ya ja tsaki ya kashe wayar...

A wurin Afnan wani kutungurin abu yadagar mata zuciya jin za a mai baiko da wata yariya tayi alwashin ko ma wa cece Adyan zai aura sai ta ga bayan ta adoran kasa in har bata samai shi ba to ba wanda zai samai shi…

Tirkashi🙄🙄

Ku cigaba da bibiyan novel din mu  wato KAZAFI. Dan yazun Muna clearing road ne

Don't forget to vote and comments.🙏

Meenamajeed love you 💋♥️