SAƘO MAI MAHIMMANCI!
by @azizat
Wannan Labari mai suna MAIMUNATU TELAR MATA shine littafina na farko dana rubuta a shekarar 2017.
Na rasa shi lokacin da aka sace min waya to sai Allah ya sa na ci karo da shi a GMAIL ɗina.
Da farko na yi tunanin na fara editing ɗinsa kafin na sake shi, amma sai na ga idan na ce zan gyara shi yanzu zan masa editing ne da ƙwarewar Marubuciya Azizat a 2025, hakan kuma zai ɓoye kura-kuren da sabuwar Marubuciya Azizat ta yi a shekarar 2017. (Ashe fa AZEE COOL nake using lokacin😂).
Babban matsalar dake cikin book ɗin shine rashin ƙa'idojin rubutu, kwata-kwata babu alamar zance (") komai a hargitse yake.
Ku karanta da haƙuri.
Azizat Hamzar 2017 da ta rubuta Maimunatu Telar Mata cike da kura-kurai, ita ce ta gina Marubuciya Azizat da kuka sani a yanzu da take rubuto muku daɗaɗan labarai masu ƙayatarwa.
Alhamdulillahi, a cikin shekaru 8 na samu gogewa sosai a harkar rubutu fiye da farkon farawata.
Idan kuna karanta littafin nan ina so ku hasaso ni a shekarar 2017, yadda nake rubuta labarin da wayata ƙirar TECNO Y2😀.
Idan kuka yi hakan za ku manta da kura-kuran ciki ku nishaɗantu da labarin MAIMUNATU da MUBEEN❤