4
by @azizat
Episode 04
Farinciki wurin masoyan biyu baya misaltuwa Maiduguri da Misau duk 'yan uwa murna suke ....Mal Ibrahim kamar ya hadiye Maimunatu kullum cikin hidimarta yake baya Fita shago ma sai 11 na safe gashi cikin nata yazo da laulayi. Hafsah ma ba abarta abaya ba tana matukar taimaka mata duk da itama na fama da nata cikin ......
A hankali cikin Hafsah ya Isa haihuwa lokacin cikin maimunatu na wata bakwai ta haifi namiji yaci sunan Ibrahim suna kiran shi Khalilullahi tunda cikin maimunatu ya cika wata takwas ake sintirin asibiti Dan likita ya shaida mata tana da hawan jini ....
Wata rana suna kwance da Malam tace mai Malam ji nake kamar bazan haihu lafiya ba kamar bazan ga abin Dana Haifa ba. Subhanallah haba Maimunatu kidena fadin haka kinsan likita yace kidinga kwantar da hankalinki In sha Allah zakiga danki ko 'yarki tare zamu kula da yaranmu kinsan me idan namiji ne sunan Baba zan sa masa Abdullahi (mahaifin Maimunatu) idan mace ne Kuma yai shiru tace mezaka sa yayi shiru kafin ya rungumeta ya rada mata a kunne Gimbiya Maimunatu .....Murmushi tayi tace malam idan nasauka lafiya Kuma bantashi ba kaba Hafsah 'yata ko dana nasan zata kular min dashi kaman nata .....yace mubar wannan maganan Dan Allah yana tada min zuciya ......
Ranar da cikin ta ya cika wata wata tara da kwana uku tafara nakuda tun da asuba ranar jumma'a aka kaita asibiti tun asuba har lokacin sallar Jumu'ah yayi da kyar malam ya wuce masallacin dayake kusa da asibitin zuciyar shi bugawa yake da karfi ....San da suka shiga asibitin shida Umar su ka tarar ta haihu dama Hafsah ce da Fatima kanwar Ibrahim da itama ke aure a bauchi suke tare da ita ganin idon Fatima da ya koma jaa yace Fatima lafiya, ta haihu ko? ta kakaro Murmushi ta mika masa 'yar tace ansamu mace yaya yai hamdala ya karba hannunsa har rawa yake yana tofa wa yarinyar addu'a hawayen farinciki a idonsa shekara sha uku kenan da aurensu sai yau Allah ya karba addu'ansu bayan ya mata huduba ya mika wa Umar yace ina Maimunatu zamu iya shiga mu ganta ko? kukan da Hafsah ke makalewa ne ya kufce mata Fatima ma kukan tasa jikinshi na rawa yace Fatima me yasameta? kuka take takasa magana dakin ya nufa ya ce ba abin daya samu Maimunatu likita ne dawata nurse aciki likitan na rubutu a wata takarda gadon ya hango an rufe ta daga kai har kafa .......ya karasa gurinsu yace likita ina Maimunatu likita ya dafa kafadarshi yace mal Ibrahim kayi hakuri Allah ya karba abinsa Ai bai karasa ba ya sume a wurin likitan ya tallafoshi yana jijjigashi nurse ta fita da sauri ta dawo da ruwa a Kofi aka shiga yayyafa mai har ya farfado ......sau biyar mal Ibrahim ke suma a asibitin da kyar Umar ya samu ya nutsar da shi har aka samu aka karba gawar aka je gida dashi 'yan uwa da abokan arziki kowa mutuwar ta girgizashi Dan maimunatu mace ce ta gari har aka kaita da yamma mal Ibrahim baya magana sai hawaye mutane sun tausaya masa aranar 'yan Maiduguri sukazo Dan an gaya musu ta call center aka kira mahaifinta Dan yana da rai mahaifiyarta ce dama ta Dade da rasuwa mal Abdullahi ma yayi kuka sosai Dan cikin yaranshi yana tsananin sonta sosai.........
Hafsah ce ta karba yarinyar ta fara shayar da ita tare da Khalil Inna tana tayata kula da yaran biyu inka kalli yarinyar kamar uwarta sak saidai tadanfi uwarta baki saida akayi suna kafin 'yan Maiduguri suka koma yarinya taci sunan mahaifiyarta MAIMUNATU amma Gimbiya ake cemata ba ayi taron suna ba amma yarinyar ta samu kaya sosai .......
A haka rayuwa ta kasance mal Ibrahim yana kara samun cigaba cikin kasuwancinsa amma daga ka ganshi kasan yana cikin damuwa sosai yake son Gimbiyarsa Dan lokacin da ta cika wata shida yafara zaman shago da ita sai intana kuka zai maidata wurin Hafsah amma ko yaushe tana makale dashi watan Maimunatu biyar a duniya, Umar yai hatsari a hanyarshi ta zuwa misau a general hospital na misau ake kula dashi ya jikata sosai ranar daya cika kwana uku a wurin yana kwance mal Ibrahim na gefensa itama Hafsah na gefe tana hawaye yaran na wajen Inna .... yayi wani nishi yace yaya, mal Ibrahim ya matsa kusa dashi yace kana son wani abune ya girgiza kai yace Dan Allah ga Hafsah amana, na san imbana nan zaka kula da ita sosai...... Yaya ka zamewa Alhassan da Khalil uba Dan Allah, tari ya fara mal Ibrahim yace umar ba abinda zai sameka gobe zamu wuce babban asibiti In sha Allah zaka sama lafiya ganin tarin yaki tsayawa yasa ya fita ya kira likita .....bayan likita yashigo ko minti daya bai yiba. Umar ya cika .....
Kuka da bakinciki ba'a magana awurin mal ibrahim amma yazaiyi Allah ya fisu sonshi .....a Bauchi Hafsah tai takaba inna da wata kanwar mahaifiyar hafsah suka zauna tare da ita .....bayan tagama takaba da wata biyu ta yaye Khalil da Gimbiya , gidansu takoma tare dasu duka saidai satin ta biyu da dawowa mal ibrahim ya fito nemanta duk da tasan cewa tun suna asibiti mijinta yace mata in rai yai hali ta auri yayanshi amma fir taki .....da kyar iyayenta suka bata baki ta amince lokacin watanta uku da fita takaba aka daura auren mal Ibrahim da Hafsah ....
©AzizatHamza2017