Shadows of childhood
They say you shouldn't judge a book by its cover, so, don't judge this one by its first few pages either. Give me a chance to find my voice, and I'll give you a story you won't forget. 🤞
The first page is just a shadow, the light comes later. Bear with me until the sun rises. I promise you a journey where disappointment has no place.😇
WARNING:⚠️
This is not a story about a girl who waits to be saved. This is a story about a girl who will burn the world down to keep what she was promised. Zara Amadi is not your typical heroine. She is spoiled, she is obsessive, and she is far from a saint. She makes no apologies for the hearts she breaks or the rules she bends. If you are looking for a story where the 'good girl' wins, this isn't it. But if you’re ready to watch a princess become a predator for the man she loves... bear with me.
NOTE TO READER:
In this manor, love is not a reward for being good; it is a prize for the most ruthless. Zara is both the victim and the villain of her own story. She is flawed, manipulative, and dangerously obsessed. Don’t expect her to do the right thing—expect her to do anything to keep Zafar. You have been warned: the princess bites😈🙌
بسم الله الرحمن الرحيم
It was heavenly raining, kaman da bakin kwarya erin mai hade da iskan nan ga iskan sai kaɗa curtains ɗin ɗakin yake ruwan ma duk ya jika su da feshin da har kan gadon da nake kwance yake isowa amma banyi making wani effort na tashi in rufe windows ba in fact ko motsawa banyi ba ina kwance kaman gawa idona na kallon ceiling ɗin bedroom ɗina I am not even blinking, I was so scared carried away inata tunanin rayuwa ta
well, dole inyi tunanin rayuwata because believe me when I say my life is a total mess.. okay not a mess to some people but to me it is indeed a mess! *sigh*..
a hankali na lumshe idanuna wasu memories na dawo mun acikin idona
all I was seeing was a 11 year old me coming out from my new school, I was in jss1, it was my first day but I already like the school and I’ve already made friends
I was so excited na matsu a tashi naje gida nabawa maamah da daddy na labari
ana tashi daga school na fito da sauri bayan nayi sallama da sabbin kawayen nawa inata sauri na fito
ina ta baza ido ko zanga motar daddy yazo daukana saboda yamin alkawari he’ll picked me up himself but to my disappointment ba shi bane yazo
daga motar da nagani ta gidan mu nasan driver ne saboda babana baya hawa motar mamana kuma bata driving dakanta
chak na tsaya zuciyana namun ba dadi but he promised yace mun fa dakanshi zaizo
ina cikin tunanin naji ana kiran sunana “Zara” ahankali na daga kaina ina kallon drivern mu musa kallona naga yanayi dawani yanayi a fuskar shi mai kamada tausayi idon shi harda yar kwalla kollonshi nima nake with so much confusion shi kuma meya samesa?
ai baima bani daman tambaya ba yayi sauri cemun
“muje ko?” yafada tare da saurin yin gaba nima kawai sai nabi bayansa yana zuwa gurin motar ya bude mun backseat nima ina karasowa na shiga yarufe ya koma gaba ya shiga yafara driving roughly kan kace me ya iso gidan mu dake asokoro acikin garin abuja
tunda muka shigo street dinmu nafara ganin motoci amma still ban kawo komai araina ba saboda yarinta
muna isowa kofar gida musa yayi parking yace karna sauko yana zuwa
yasa hannu a aljihu yaciro wayar sa yashiga kiran god knows who nidai inata kallonsa amma bance mai komai ba danni tunda yazo daukana naga ba daddy na bane jikina yayi sanyi tun a lokacin mood ďina ya canza shiyasa har muka iso banyi magana ba saboda fushi nake kuma ni daman sometimes inada miskilanci..
jim kadan da gama wayar tashi saiga ga big brother na ya fito daga cikin gidanmu
I was surprised saboda he is hardly here
da sauri na fito na rungumeshi ina murna shima yayi hugging dina back but his hug was so tight
cikin murna da dariya a shagwabe nace
“ahhhh ya muazzam you’re suffocating me”
ahankali ya furta “sorry princess” a sangarce nace ”it’s okayy”
“I’m so sorry “ ya kara furtawa his voice emotionally breaking
jin haka na dago ina kallon sa naga idonshi ya kada yayi jaa sosai
take jikina yayi sanyi a hankali na kamo hannunshi ina tambaya
“ya muazzam what’s wrong?”
bai iya kallona ba yana kauda kanshi dan kar naga hawayenshi yaja hannu na zuwa cikin gida
nan fa nafara ganin jama’a babu masaka tsinke
I was never been so confused in my life saboda nidai nasan ba biki ake a gidan mu ba nan fa ya ratsa dani cikin mutanen maza ne a compound din but muna shiga ciki nafara ganin mata kowa sai kallon tausayi yake bina dashi duk inda muka ratsa
duk da bawai wani sanin mutuwa nayi ba a time din amma nasha jinin jikina haka kawai naji mamana nakeso son gani at any cost dago kaina nayi na kalli yaya na ina tambayar sa meyake faruwa? Ina maamah? and who are these people? because only few of them nayi recognizing bai cemun komai ba
har muka isa bakin kofar bedroom din mommy ahankali ya mirda ya shiga bakin sa dauke da sallama few people dasuke cikin dakin suka amsa muna shiga naga maamah a kwance akan gado ga drip a hannun ta ga wata nurse a tsaye agurin sai kuma best friend din maamah mai suna Umma Deeza dake zaune a gefen gadon sai yaya Omar dake kan bedside din gadon azaune kanshi a kasa
da sauri na karasa gurin gadon na haye ina kiran sunan maamah tare da tambayar ta meya same ta a hankali ta bude idonta dake lumshe tana zubda hawaye tana daura idonta akaina nan take ta fashe dawani kukan mai karfin gaske da tsuma zuciya gwanin ban tausayi tana kiran “sabr ya Allah” nan ta jawoni jikinta tana tayi umma Deeza na tayata kukan yayin da brothers dina suka zo suna consoling dinta duk suka rungume ta dani nima da bansan meke faruwa ba tuni na fashe da kuka ganin uwata na kuka
munkai 20mins ahaka sai gashi an banko kofa da karfi ko sallama babu well, if not my stepmom then who? nan tafara magana cikin zafin rai tana daga murya tana cewa “Maryam how dare you? I said how dare you? I always knew you’re heartless but I didn’t know it was to this extent” maamah ta dago kai ta kalleta a raunane tana cewa “Oma please not now” a zaffafe stepmom dina itama tana kuka tace “if not now then when maryam? how can you do this to me.. to us? why would you give the order to my husband burial without me or any of his family seeing him? why are you so selfish or you think just because you are the only one that gave him a child means you are his only family?you are wrong maryam so so wronggg I am also his wife and he has an elder brother, uncles and cousins and you knew that maryam but you decided to go your way selfishly like you always do when it comes to making decisions concerning him you act like you and your daughter are his only family! why?tell me f**king whyyy”
takara maganar cikin wani erin tsawa dake bayyanar da fushin da take ciki
kafin kace me jama’a sun fara taruwa dakin sosai anyi anyi a fahimtar da ita amma sam taki fahimta sai saida hali take cikin mutane nurse din da ke kan maamah dakuma brothers dina suke dan kora mutane sitting-room saboda rashin lafiyar maamah wanda daman jininta ne ya hau ba kadan ba
nikam sai alokacin nasan meke faruwa ashe babana mahaifi ne ya rasu
bayan awanni yan uwansa suka shigo suma garin abuja daga delta state ai kuwa suma ba kalar tijarar da basuwa maamah ba ammah haka ta toshe kunne bata kulasu ba saboda ita ta mutuwan mijinta take da kuma lafiyarta
Well, the thing is my father is an igbo man that converted to islam since he was 19
akasin sauran daginsa da first wife dinsa daba musulmai ba..
sai da suka zo nake Jin cause of dead din babana shine car accident from nassarawa to abuja I was so heartbroken saboda jiya da daddare mukayi waya yamun alkawarin he’ll pick me up from my new school ashe Allah baiyi ba.. and that is how I lost my dad at young age alokacin ne nasan mutuwa kuma nasan zafinta because I was very close to my father and I was an only child to him
Maamah kam I was the third born agurinta I have two elder half brothers wanda ba baban mu daya ba amma mahaifiya daya ce ta haife mu so agurin maman mu mu uku ne
yaya Muazzam shine first child din maamah he was 21 time din
then yaya Omar who is 18…
yaya muazzam nada shekara 4 while ya Omar na shekara 1 Abbansu ya rasu inda maamah taci gaba da rainon su da taimakon yayan abbansu wanda dama a gida daya suke family house ne kuma su masu arziki ne sosai, da abbansu ya muazzam Alhaji Ahmad Galado da yayanshi Alhaji Omar Galado are both ‘wealthy businessmen, they own and also are share holders in many companies around the world
bayan rasuwar baban su ne maamah ta haɗu da daddyna a wani hospital ɗin daddyna inda nan family ɗinsu suke zuwa daman, lokacin yaya Omar yayi rashin lpy akaiyi admitting ɗinsa shikuma daddy ya shiga asibitin ranar ya ganta…
ta aure shi ne lokacin yaya muazzam was 7 shikuma ya Omar was 4 anyi rikici sosai a lokacin saboda dangin babansu sunce yayan su baza suyi agolanci ba inda maamah kuma taki bada su abun har aka sa manya inda anan ne aka bata ya Omar kadai da sharadin shima yana kai 7 years zata maida shi dangin maifinshi hakan ma bai musu dadi ba dandai ba yanda zasuyi ne
auren maamah sosai yakawo cece kuce duba da daddy na inyamuri ne kuma shi kadai ne musulmi a daginsa aka ringa kananan maganganu wai maamah zata auri tubabbe amma hakan bai sa maamah ta saduda ba because she found her soulmate!
Soyayya sukayi sosai ita da daddy na wanda shima yanada mata wadda ba musulma kuma Allah bai taba basu haihuwa ba amma sunyi adopting yara guda biyu mace da namiji
bayan kuma auren su da mommy ne Allah yabasu ni
son duniya da gata na gani a gurin iyayena da yayyi na harda ma dangin mahaifina kasancewata only child agurin babana kuma yar auta agurin maamah sannan kuma ɗiya mace tal agurin ta so na taso a sangarce ga shagwaba ga miskilanci ga son jiki bana son aiki sam shiyasa ban iya komai ba
bayan rasuwar daddyna a gidan mukaci gaba da rayuwa daga ni sai maamah stepmom ɗina ta kama gabanta da yayan rikon ta daman a kaduna take aiki she’s a lecturer so mostly sai weekends take shigowa Abuja daman so she resided there completely
gida kuma dagani sai maamah my brothers hardly come saboda US suke school ɗinsu tareda sauran yayan yayan abbansu yaya muazzam na studying architecture while ya Omar kuma medicine in one of the best universities in the world “Columbia university New York”
haka rayuwa taci gaba da tafiya dagani sai maamah sai masu aikin mu guda biyu sai kuma kanwar maamah da take yawan zuwa mana Aunty Hannah shekarar 25 lokacin daga niger 🇳🇪 take zuwa
oh na manta ban fada muku ma maamah buzuwar nijar ce gaba da baya shiyasa take fara sol kamar kataba jini ya fito iyayen ta sun rasu amma duk sauran dangin ta na nijar
mukan je can din once in a while inda suma ba matsiyata bane da arzikinsu sosai
maamah yar gayu ce wayayyar mace yar boko ga kyau da dogon gashi har gadon baya shima margayi daddyna farine sol erin farin igbo with a little bit of yellow dinnan gashi giant dogo ga jiki wanda hakan ne yasa nima natashi doguwa kuma fara sosai erin farin buzaye saboda duka iyayena fararene sosai haka na taso da fari da Gashi ga kyau mashaAllah
Kuma one thing that my maamah don’t joke with is my hair duk wani abun gyaran gashi maamah na mana amfani dashi and duk laziness dina bana wasa da gyaran gashi na saboda na taso naga maamah na daraja gashi sosai
alokacin da nakai SS3 at the age of 16 nafara zama cikkakiyar budurwa duk wani diri da Allah yamun yafara bayyana kansa wanda tu alokaci duk wanda ya kalleni yasan za’ayi dirarriyar mace gani saboda yawan ƙoɗani da friends keyi da kuma maza ana cewa inada kyau saiya zamana na tashi da jijji dakai ga confidence komai na confidently nakeyi abun da yajamun farin jini sosai agurin teachers dama sauran jama’ar school..
I was a happy child and carefree person and also a spoiled brat a mugun shagwabe nataso
abu ɗaya yake hadani da maamah kuma shine my lack of modesty samsam banajin kunyar kowa a cikin gida yanda naga dama haka nake zama mostly daga ni sai inner wears kamar under wear da vest or half vest ma most decent kayana shorts ne kuma Allah yagani bawai training din maamah bane because she really tried her best kawai dai tun ina yarinya ne sai abun yabi jikina natashi ahaka banajin kunyar cire ko saka kaya agaban kowa even my brothers maamah takanyi faɗa tace
wai ke bakisan kin girma ba?
to wannan kaɗai problem ɗina