7
by @azizat
7
Note: Tsohon littafi ne, ban yi editing ɗinsa ba
A Daren ranar ina goge kayan Dana karbo daga wurin yaya KB Alfarouk ya shigo yace mini ina da bako a waje na zaro ido nace bako kuma yace ee Baba nema yace ki fito cikin sanyin jiki na kashe iron din na sa hijabi nayi waje. Baba nagani da wani a kofar gida nace Baba gani ya kalleni ya kauda kai yace ga me nemanki ya wuce shago na maida kallona ga saurayin ban gane shi ba yace ranki shi dade Gimbiya ina wuni na kasa amsawa yace kin yi mamakin ganina ko ?. Nan ma shiru. kamar yadda na sanar dake dazu da rana sunana Isma'il kiyi hakuri gimbiya nasan bakiji dadin zuwana ba amma zuciya ta kasa samun sukuni tunda na ganki. yayi shiru kafin yace gobe nakeson komawa school amma bazan iya tafiya ba har saina sanar dake sakon zuciyata .....Gimbiya nakamu da sonki, bada wani nufi ba sai ta alkhairi ... . tun da yake magana zuciyata ke bugawa da sauri da sauri maganganunsa sun min nauyi ga Tsoron Baba daya cika mini zuciya ban san sadda yake cewa gimbiya baki ce komai ba ai da gudu na shiga gida na wuce dakinmu ina kuka tsorona me Baba zai cemini tunda nake ba namijin daya taba zuwa wajena zance sai yau kai ni namiji ma banda yaya KB ba wanda yake zuwa har gida in kulashi.....
Turo kofan da aka yine yasani tashi idonshi na kalla na ga tsananin bacin rai a tattare dashi aikuwa bugun zuciyana ya karu ya karaso wurin danake ya tsaya yace bansan dalilin ki nakin karatu ba sai yau ashe aure kikeso, nawa kike gimbiya yaushenki da har zaki turo saurayi gidanku, ke gaki kinkai matsayin tsaida saurayi ko to bari kiji inda gaske yake ya turo magabatansa su nemi izini wa dansu ba wai ya dinga zuwa min gida bansan asalinsa ba imba haka ba kar ya kara zuwa min kofar gida. Kuka nake sosai amma haka ya fita bai ko kula da yanayin dana ke ciki ba ....na cigaba da kuka har umma ta shigo da su ummita ta musu addu'a ta juya zata tafi tace gobe walimar ku ki kwanta da wuri ta fita a dakin .. Kusan 11 Khalil ya shigo lokacin na dena kuka amma na kasa bacci ya karaso inda nake ya dago kaina yace kukanki na daga min hankali my princess kinga yadda pretty eyes dinki suka yi jaa plz dont cry dear ya rungumeni ai nan naji wani sabon kuka yace plz princess dont cry can nayi shiru nace khalil nifa ban sanshi ba yau na hadu dashi a shagon yaya KB, bance mai komai ba banma san ya akayi yasan gidanmu ba yace its ok kwantar da hankalinki zan mawa Baba magana gobe kin ji ....nayi shiru yace yi min murmushi mana na harareshi, yace hararata zakiyi to barin tafi ya mike kaman zai tafi ya juyo yace 'yar baka basabon ba anyi saurayi har da kukan so. Ai kuwa na wurga mai pillow ya fita yana dariya nima dariyar nayi kamin na kwanta...
Washe gari bayan nayi sallan Asuba da 'yan azkar dana saba naje na gaida Baba a hankali ya amsa nace Baba kayi hakuri ya ce fita min a daki na kasa tashi da ya ga haka sai ya tashi ya fita ai kuwa sabon kuka nafara a wurin da kyar na iya komawa dakinmu na cigaba da kuka har gari yagama wayewa aka fara ayyukan gida naki fitowa harsu yaran kowa ya wuce hadda gashi saukanmu karfe sha daya za a fara amma ina kwance a kasa kaina nakan katifar idona ya kumbura. Umma ta bude dakin ta ce Kije inji Babanki daga haka ta fita da kyar na tashi na fito waje na nufi falo Baba na gani da Khalil da yaya Alhassan ban masan yazo gida ba na zauna akasa kusa da khalil baba yayi gyaran murya yace Gimbiya khalil ya min bayanin komai kuma na gamsu ba wai ina takura miki bane ko kuma ina muzguna miki ina guje miki samarin zamani ne amma bakomai na riga nacewa yaron in da gaske yake ya turo magabatansa dan haka in har yayi hakan ya nuna da gaske yake kenan amma inbai kuma dawowa ba dama makaryaci ne ......zo nan 'yar baba ya nuna min wajenshi na karasa ya jawoni jikinshi yace yau ranar farinciki ne Allah yasa albarka a rayuwarki gaba daya jeki shirya wajen walimarku lokaci ya tafi nayi murmushi na tashi sai a sannan muka gaisa da yaya .....
Karfe sha daya saura kwata muka fita nida Tasleemah mun sha anko ga hijabi da nikab duk iri daya a keke napep muka tafi .....
Wurin sauka yayi kyau anshirya komai anfara gabatar da masu sauka na hadda kafin namu na tartil .....ana kiran kowa a buda mai wani shafi daga alqur'ani ya karanta aka iso sunana MAIMUNATU IBRAHIM MISAU naji ance na tashi na isa kujerar aka budemini nakaranta cikin murya me dadi da san yaya zuciya bayan na gama aka yi kabbara aka cigaba da kiran mutane har aka kare daga nan aka fara raba kyaututtuka na karba kyauta ta daliba mai hazaka da kuma kyautar tsabta da zuwa da wuri ....sai da aka gama naga su Ummana da Anty ashe sunzo suma nayi farincikin haka sosai ...
©AzizatHamza2017