MAIMUNATU Telar Mata

9

by @azizat

10

Note: Tsohon littafi ne, ban yi editing ɗinsa ba.

***

A hanya Khalil ke sanar dani abinda yafaru ai kuwa na dinga hawaye yace wallahi kinga abin dayasa namiki karyar yaya ne ba lafiya dan nasan zaki daga hankalin ki ki bar kukan nan Baba yama sama lafiya kawai sunce ya huta ne kawai nake ga gobe Monday Zasu sallame mu haka yayita rarrashina har muka isa Asibintin.....bayan na shiga na ga yaya Alhassan na zaune kusa dashi na gaida shi baba na kishingide akan gado na hau gadon kusa dashi na rungumeshi na fara kuka ya ce haba gimbiya dena Kuka mana nafa warke ya kika baro can waya taho dake ya jera min tambayoyi na kasa bashi amsa ya fara bubbuga bayana yace yi shiru kinji gobe ma za a sallameni kinji haba 'yar baba nadan sake shi nace baba shikenan shagonmu babu shiru yayi kamin yace haka Allah yaso .....da kaina na bawa baba abinci Kuma yaci sosai, na mai hiran maiduguri sosai naji dadi ganin ya sake ranshi kamin da maghrib sukaje masallaci dasu Khalil .....da kyar baba ya lallabani Khalil ya maidani gida da dare Dan da cewa nayi zan kwana .......a hanya na tambayi Khalil ya akayi gobarar ta tashi yace ba wanda ya Sani sai Allah ......da nakoma gida umma fada tamin wai na fita ba sallama na bata hakuri naje na kawo mata tsarabar Dana zo dasu ta amsa tace angode sai gobe a raba nace to na wuce daki..... Su ummita sunji dadin dawo wa na Dan dama in bana nan basa kwana a dakinmu .....

Washe gari litinin aka sallame baba karfe 10 na safe yaya Alhassan tuni ya wuce makaranta Dan suna da test a ranar by 12 pm. .. Bayan mun dawo daga asibiti baba yataramu ya mana nasiha me ratsa jiki yace mu kwantar da hankalin mu In Allah ya yadda ba abinda zai sauya dama ya bada kudi a wani abokinsa zai saya mai mota a Cotonou to baima tafi ba tukunna Dan haka zai karba kudin sannan ga kudin da mijin Anty Fatima ya bashi dayazo dubiya dubu dari, ga kudin da ya rage mai a account duk da dama ya je yayi sari kenan kudin suma basu haura dubu saba'in ba yace Zai fara gyara shagunan kafin asan me za ayi gaba nace Baba inaso kasaida gonan da marigayi ya bani yace a'a gimbiya ba ayi haka ba nayi nayi a sayar yaki yace Insha Allah ba abin da zai gagara na yadda yasaba ..... Da safe na duba account balance dina na bank naga dubu dari da sittin da uku na hau murna Dan ya dade Dana duba balance dina aikuwa bayan na gama aikace aikacen gida sama baba nace Khalil zai rakani sayan kayan dinki yace ba komai da muka fito nace masa bank zamuje yace shine kikayi karya ko na kaimai dundu nace ina ruwanka yace zan kamaki ai muka wuce dubu Dari da hamsin na cire Dan dama na maida account dina normal tunda na cika sha takwas da muka dawo na je nasama Baba yana falo akan kujera yana lissafin wasu Abubuwa da takarda da calculator a hannun sa na tsugunna kusa dashi yadago kansa yace gimbiya har kun dawo nace ee baba hannunshi na kama na fitar da kudin a jaka ta na daura a hannunsa nace baba gashi a kara jari ya zaro ido yace gimbiya ina kika sama wannan kudin nace baba mamanta na bude account kudina ne danake tarawa na dinki Dan ma baba ina cirewa a ciki ne shiyasa dayafi haka yawa dubu Dari da sittin da uku ne aciki na bar dubu sha uku yanzu haka baba kasan na Dade ina dinki fa ga Kuma Dan kudi danake samu na kyauta tunda nake magana yake hawaye har nakare ya rungumeni ya ma rasa me zaice mini sai hawaye nace baba kayi hakuri Dan Allah da ina da adana sosai da kudin yafi haka da kyar ya tsaida hawayen yace kira mini ummanku da halimatu na tashi na fita ....ba a Dade ba nadawo nace suna zuwa na zauna a kasa kusa da Khalil umma ta fara shigo wa sai daga bayan Anty ta shigo suka zauna a kujera ya fara dacewa lokacin da gimbiya ta nace zata koya dinki ko kadan banji dadi ba amma yau gashi dubu Dari da hamsin ta bani halaliyarta ne ya mika wa umma ta kalla ta mikawa Anty itama ta kalla da mamaki a fuskarta yace Allah ya miki albarka gimbiya yayita zuba min addu'o'i umma ma ta min wannan karan har Anty ta yaba abin da nayi ....

kafin sati biyu an gyara gidanmu sosai saidai shago ba kaya da kudin daya rage da bashi baba ya sake saro kaya saidai wannan karan ba yawa Dan shago daya akasa Kuma ba wani yawa umma ta kara hannu a Sana'ar ta abin mamaki Anty ta na sa almajiri ya dauka mata har makaranta datake koyarwa ta sayar .....sosai baba yaji dadi Dan koba komai iyalenshi suna rufa mai asiri ....

Ganin daya shagon ba komai yasa na je nasama yaya KB a shago bayan mungaisa yace 'yan mata lafiya da tsakar rana haka nace Abban sadiq Dan Allah shawara nazo nema yace to ina zuwa ya cewa yaran shagon shi su Dan bamu ware suka fita ya ce inajinki gimbiyata na nanata a raina gimbiyata ...na yi sauri nakauda tunanin nace Abban sadiq dama inaso in kama shago ne in fara dinki a shago kamar ka ai kuwa dariya ya fara harda kyakykyatawa nace yada dariya aikuwa kamar nakara tunzurashi gimbiya shago ya cigaba da dariya ai kuwa na fashe da kuka nace bafa karuwanci nace zan fara ba kake min dariya ai ganin hawaye a idona hankalinshi ya tashi ya iso Inda nake zaune ya tsugunna ya sa hannunsa ya fara goge min hawaye yace Dan Allah kiyi hakuri da wasa nake fa kidaina zubarda hawayenki masu tsada Dan Allah na tuba ya ce ya kama kunnuwanshi guda biyu nace to shikenan ya rike hannuna duka biyu yana ganin dogayen yatsuna da yasha Jan lalle yace a ina kike son shagon ganin yaki sake hannun nawa nace yaya yannuna oh sorry ya fada yana Sosa kai ya je ya zauna a kujeran kusa da kekensa yace gimbiya a ina kikeson shagon ko da nawa kikeso zan bar miki na girgiza kai nace ba ma nisa daya shagon baba ne naga ba komai a ciki Kuma idan ina son insamu aiki sosai saidai in na fito da kekena yaya kana ganin baba zai yarda Kuma hakan yayi ko akwai matsala ... Ya girgiza kai yace matsala daya ce mutane Zasu sa miki ido Kuma ana gulmarki kinsan mu hausawa nace ni wannan ba damuwata bane indai baba ya yarda ba ruwana da kowa ya yi Murmushi yace zaima yarda Insha Allah nace nagode yaya barin tafi yace to tsaya barina kaiki nace a'a Abban sadiq ba kana aiki ba yace ba wani da Isma'il ne ai zaki yarda na ce yaya bafa haka bane yace to ya nene nace Allah yaya akwai inda zanje ne yace gidansu Isma'il ko yadda yayi maganan ranshi a bace nace a'a railway zanje gidansu Umaima kawata da muka yi koyon dinki da ita yace to naji gashi to ki hau keke nace a'a yace Allah ya kiyaye ganin ya hade rai nace to nagode na dauka dari biyar din a kan kekensa sai sannnan yayi Murmushi yace barin rakaki .......

11

Da dare nayiwa Abba maganan shago yace min a'a nayi nayi dashi yace bazai barni ba haka na hakura raina be so ba ....na kira Isma'il ina gaya mishi shima cemin yayi a'a bai yarda ba na rasa ya zanyi inyi convincing din baba ya barmin shagon ....haka na hakura da yake ankusa Babbar sallah na Dan sama dinki inayi wata rana baba ya shigo ya ganni a tsakar gida ina kan keke namai sannu da zuwa ya amsa min ganin be shiga ciki ba nadaga ido na kalleshi naga ni yake kallo nace baba in dauko kujera ne ya ce min a'a ya shiga ciki bai ce komai ba washe gari Baba ya kirani ya bani key na karba nace baba na mene yace na shago ne na yarda kisa kekenki aciki nan nafara murna nace nagode babana na tashi nayi dakin umma na sanarda ita yadda bata nuna mamakiba yasa nasan sun riga sunyi maganan da ita nasiha tamin sosai na tashi na tafi dayake anty batanan taje misau an musu rasuwa na dau waya na kira khalil na gaya masa shima yayi murna yayita tsokanata wai tailor maimunatu muka sha hira dashi na kashe wayan dayake a gwallameji yake sai weekend ya ke zuwa gida, yaya kb na kira shima na sanar dashi ya min murna sosai yace zaizo yaga shago nace sai yazo na kira ismail be dauka ba dan haka namai text aikuwa bayan maghrib ina karatun qur'ani ya kira ni yafara min fada wai ya zankama shago kamar namiji nace mai a kofar gidanmu ne fa yace and so ganin yana so ya bata min rai na kashe wayar ya Kuma kira ban dauka ba ..... Daga baya yamin text wai nayi hakuri da safe nida Umari muka share shagon na sa room freshner da turaren wuta yana ta kanshi muka sa leda kamin ya tayani fitar da keke da kujera ta ... nan nacewa baba zan sayo labule shi ya bani kudin Duk dana ina dashi labule me sharashar na daya umari ya samin na ki ra baba yamin addu'a umma ma ta zo tagani tasa albarka ......da yamma yaya KB shima yazo yagani na kira tasleemah da umaimah na sanar dasu suma sukace Zasu zo ganin shago ban fara aiki a shagon ba sai washe gari daya kasance jumma'ah karfe tara na fita na fara aiki aikuwa duk wanda yazo wurin baba sayan abu sai yayi gulmar shagon niko ko a jikina tinda bamai shigo mini ya tare ni da maganan ....da yamma khalil yazo gida ai nasha tsokana har saida yaga na fara hawaye ya barni .....ran asabat da safe ina wanke kayan umma da na sauran yaran dan ni ban taba ban banta yaran umma dana anty ba ....khalil ya ce insa hijabi infuto waje naga ikon Allah ai da sauri na dau hijabi nayi waje a kofar shagona na ganshi nace meye hakan zaka wani katse mini aiki ina surprise din ya yi dariya yace rufe idonki na ce meye hakan yace haba 'yar baka rufe mana na turo baki na rufe idon yayi dariya ya sa hannu ya daga kaina ina kallon saman shagon yace bude idonki na bude manyan idanuna a hankali na kafesu akan rubutun saman shagon da akayi da siga mai kyau na karanta a fili "MAIMUNATU TELAR MATA" na fara dariya na kaimai duka kaiko shima dariyar yayi yace ko insa gimbiya ne nace hakama yayi .......

Aiki kan inasamu ba laifi duk da babbar sallace sedana sama dubu ishirin da biyu na bawa baba dubu shirin nasa dubu biyu a account dina nasha addu'o'i sosai a wurinshi ......'yan gulma har gida suke zuwa su ma ummana magana wai ta barni nakama shago kamar arniya bata kulasu suyi mita su fita subar mata gida ......

Washe garin Sallah Ismail yazo da yamma da yake mun kare aikin nama tunda safe dan wannan karan rago da taure aka yanka mana sabanin da da akwai wadata sosai na mishi tarba me kyau Dan dama nasan da zuwansa na kawo mishi meat pie da doughnut da zobo me sanyi da mukayi da soyayyan nama dan bamuyi dambu ba yaci kadan ya bari dayake baba a ranar ta tafi misau gaisuwar sallah munsha hira dashi sosai da zai tafi na hado mai snacks din da kayan tsaraba wa kannenshi na raka shi har wajen mashin dinsa muna sallama khalil yazo zai shiga gida nace khalil ga ismail ku gaisa wani harara yamin ya ja tsaki ya shiga gida nace wa Ismail dan Allah kayi hakuri ranshi ne a bace yace gimbiya albarkar ki yake ci badan haka ba wallahi saina jimasa ciwo nayi ta bashi hakuri har ya tafi ....

Na shiga gida na nunawa umma turaren daya kawo mani tace in nuna wa anty dama nasan hakan zatace Dan umma bata so muna banbanta tsakaninsu ....

Bayan na nunawa anty da zumudi na nayi dakinsu Khalil nayi sallama na shiga a kwance na sameshi nace Dan uwa lafiya kuwa kake kwance haka bai kula ni ba nace Dan Allah Khalil bana jin dadin abin da kake yiwa Isma'il fa kasan sirikinka ne shiru baice komai ba nace tashi kaga turaren daya kawomin ina kokarin daga shi aikuwa ya tashi ya karba turaren ya maka da kasa ya fashe nace Khalil lafiyanka kuwa ya shako wuyana na tsorata sosai ganin yadda idanunsa suka canja kala yace sai akayi me Dan ya baki turare nace ba turare ba ko kamfanin turaren ya baki ina ruwana meye hafina dashi ee yafara jijjigani karki kuskura kisake min magananshi karki kara kiran sunanshi agabana Dan zan iya kasheshi zan kasheshi nace ... Ya sakeni da gudu nabar dakin ina kuka .......na dade adaki ina jin maganganunsa namin echo a kunne to meye matsalar khalil da ismail ne ....me yasa meshi haka na dinga jinjina abinda ya faru har aka kira maghrib...

©AzizatHamza2017