MAIMUNATU Telar Mata

10

by @azizat

MAIMUNATU TELAR MATA

12

Bayan sallar Isha na kira Isma'il na mai godiya muka Dan taba hira na kashe wayan kiran yaya KB ne ya Kuma shigowa ya min barka da sallah nace mai na yaushe Kuma sallah ai jiya ne yace mini wannan na musamman ne nace naji yace barka da sallanshi nace sai yazo yayi dariya yace gobe zamuzo mu gaida umma nace Allah ya kawoku lafiya mukayi sallama .....kwantawa nayi Dan nagaji saidai ban iya bacci ba Dan tunanin maganan Khalil nake to a wani dalilin yake jin haushin Isma'il duk tunani na ban gano komai ba Dan nasan bazai zama kishi ba tunda tsakanina dashi ba aure nono daya muka sha to meye matsalar na yita tunani har bacci yayi gaba dani ....ina cikin bacci naji ana shafa fiska ta na bude idanuna a hankali dakin ba haske amma yakunna torchlight na wayar sa,na tashi da sauri nace lafiya ya kama hannuna duka biyu sai a lokacin naga hannunshi daya a daure nace Subhanallah Khalil a ina kaji wannan ciwon ya ce relax princess, ya dauko turare sak irin wanda Isma'il ya kawomin yace gashi fatan na fita hakkinki na ki karba nace cewa nayi ka biyani ne bazan karba ba ni kasanar dani matsalar ka da Isma'il me yasa Kace zaka iya kashe shi yayi Murmushi yace bazakiso kiji dalilin ba nace zanso mana bana jin dadin abin da kake mai, Dan Allah ka daina ya ce bazan iyaba nace kodan farin cikina ya yi shiru yace to me he does not exist Dan haka karki kara min tadi akanshi nikuma bazan ko daga kai na kalli inda yake ba nace to amma .....yasa hannu ya rufe bakina alamar baisonji yace is ok sweet dama nazo ne nace miki I'm sorry for wat I did earlier ki yi hakuri I've never wanted to hurt you is just that I'm not my self ne shiyasa naja hancin shi nace you scared me don't ever do that to me again yace Insha Allah, sai da safe nace mai yace rufe idon ki tukunna na ce meye Kuma yace kede ki rufe na rufe idona me zanji bakinshi yakai kunnena yace good night angel yamin kiss a hankali a wuyana na yi ajiyar zuciya na bude ido Murmushi yamin ya juya ya tafi kasa komai nayi Dan ban gane ma'anar abin da yaminba me yake nufi goodnight kiss nayi ta tunani har karfe uku kafin bacci ya daukeni ........

Bayan sallah da kwana biyar Isma'il yaxo min sallama akan kashe gari zai koma bayan mundanyi hira narakashi kofar gida daidainan Khalil yafito daga shago zai shiga gida banyi gigin mai magana ba Dan karya jamun fitina baice komai ba yashiga gidan ......Dana shiga gida naganshi ya fito da jakarshi ta makaranta nace Khalil inazakaje bai kulani ba yayi waje narasa duk ranar da Khalil yaga Isma'il sai ranshi ya baci .....to ina zaije yace min sai Monday zai koma school Kuma yau Sunday na shiga na tambayi umma ina Khalil zaije tace be gaya miki ba nace ee naga fitarsane lokacin ina tare da Isma'il tace wai yanada test karfe bakwai gobe shiyasa zaije yayi karatu nace Allah ya bada sa'a amma ni nasan badan haka bane ....

Na shiga daki na kira numbarsa yakai saugoma amma yaki dauka nace can ta matse maka aixaka zo kasameni ....can muna kallo da dare irin takwas din nan aka kirani naga sabuwar number ne na dauka akayi sallama na amsa naji ance Dan Allah .maimunatu ne nace ee yace Yusuf ne nace wani Yusuf yace abokin Khalil ne na tashi nai waje dankar umma taji me za ace hankalinta ya tashi Dan na dauka za ace wani abu yasameshi aikuwa hakane yace maimunatu Khalil yasha kwaya tamai yawa ne sai hauka yake mun rasa yazamuyi dashi gashi yaki bari a kaishi clinic yanzu haka mun kulleshi a daki ne banaso na kira baba ciwonshi ya tashi saisa na kiraki tunda yaya Alhassan bayanan Kuma sai sunanki yake kira nace ina zuwa nayi sauri nayi daki nasa hijab na dauka kudi naje nasama umma nace mata tasleemah ba lafiya mamanta takirani ganin yadda na rude yasa tace inje amma kar na Dade Allah ya bata lafiya na fita harda gudu na ko baba banwa magana ba dake shago na fita nayi hanyar gidansu tasleemah kamin natara mashin nace mai gwallameji. gudu yake dani sosai amma ko a jikina nidai in isa lafiya ne fatana .....dayake nasan lodge nasu Dan randa ya kaikaya ni narakashi ....dana sauka na kira numbar Yusuf din ya dauka ya fito ya sameni nace ina yake ya kaini dakin ya bude ga mutane sun taru sosai anagulma muka shiga dakin nida shi na tadda shi yana kwance ga dakin yayi kacakaca ga kwalaben syrups dayawa a wurin na karasa inda yake na jawoshi jikina ina kuka dakyar ya bude idonsa da ya kada yayi jaa har saidana tsorata yayi Murmushi ya rufe su Kuma na fara jijjigashi ina ka tashi Dan Allah Khalil ......yusuf yace bari mukaishi medical na school nace to muka daga shi yana tangal tangal muka fita dashi wasu maza suka taimaka aka sa shi a napep muka kaishi medical ......a can na kira yaya KB nace Dan Allah yazo medical na poly Khalil ba lafiya amma karya fadawa kowa .......baifi 20 minutes ba ya iso lokacin nurse din ya masa allura ya far fado yayita amai daga baya bacci ya daukeshi ..... Da yaya KB yazo ya tambayi me ya faru na sanar dashi yace dama Khalil na shaye shaye ne nace bansani ba ya kira Yusuf yana tambayanshi Yusuf abokin Khalil ne anguwarmu daya Kuma lodge dinsu daya saidai dakinsu daban .....Yusuf yace gaskiya tunda yana suspecting haka Dan roommate nashi nayi ai kuwa na fara kuka Sosai kaman raina zai fita yaya KB ya dinga lallashina da kyar nayi shiru ..........har sha daya kafin ya farka amma har lokacin kwayar bata gama sake shiba kiran da matar yaya tayine ya ankarar dani na duba agogon wayana naga 55 missed calls duk na baba nace nashiga uku gashi karya nayi na fito gashi bana so baba yasan halin da Khalil ke ciki .....na cewa yaya KB mu tafi tunda ya farka Kuma Yusuf yace zai kwana dashi..... Ko magana banyiwa Khalil ba banda hawaye dake fitowa daga idona ,yaya KB yabawa Yusuf dubu daya in case akwai bukatan kudi ya Kuma amshi numbarsa muka tafi ....a hanya yace amma baba yasan nan kikazo nace mai a'a yace mekikace da zakizo na gaya masa karyar danayi ya ce to Allah yasa mu dace nace amin........

Da muka isa kofar gidanmu baba yana zaune akan benchi yayi tagumi na sauka akan mashin din na karasa wajensa cikin in' i'na nace ba.....ba banji komai ba sai saukar mari daya gigitani wani Marin yasake kaimin ya daga hannu zaisake yaya KB ya rike hannun shi yana baba kayi hakuri kasauraremu Dan Allah karka yanke hukunci .....ya kalleni da jajayen idanunsa yace bace min da gani nayi niyyar shiga gida ya jawoni ya tunkuda ni kafin nakai kasa yaya KB ya rikeni ina kuka sosai baba ya wuce ya shiga gida ya kullo kofa ba irin bugu da magiyar da yaya baiyiba amma baba yaki bude kofar daga karshe yace inzo muje gidansa nace a'a zanzauna a bakin kofa ya ja hannuna yace bana son musu ......da muka Isa gidansa kuwa har lokacin kuka nake ya kira matarsa ta bude kofan ganinmu tare yasa taja tsaki ta juya ta shige daki ...yana mata magana tayi banza dashi, ya bita daki bansan me yace mataba ya fito ya bude daya dakin yace inshiga na girgiza kai nace Abban sadiq zan kwana anan yace bai yarda ba nace inbazan kwana a falonka ba nahakura zan nemi wani wurin kwanan ganin na doge yasa ya fitomin da pillow da bargo yamin saida safe ya shiga dakinsa .....banji komai a raina ba na abin da Anty sajida tayi dankonine bazan ji dadiba .......

Kwanciya kawai nayi amma ko bacci kodaya bezo ba inata tunani har asuba na tashi na eba ruwa na shiga bandaki dayake nasan kangidan nayi alwala na zo nafara sallah ina sallah yaya yazo ya wuce ya tafi masallaci daya dawo yasameni akasa ina addu'a fatana kar ciwon baba yatashi Dan abindanake gudu kenan yasa ban sanar da umma gaskiya ba .......

MAIMUNATU TELAR MATA

13

Dana gama addu'a na gaida shi yace ya kwanan bakunta nace Alhamdulillah yace gaskiya gimbiya baba bazai yarda da duk abinda zamu gaya ba saidai mun gaya mai gaskiyar lamari ki kwantar da hankalin ki in sha Allah komai zaizo da sauki nace amma yaya ranshi zai baci sosai yace hakane amma in karya ne bayan baba da mukayi wa laifi harda Ubangijin mu nace to yace Bari ki karya sai mu tafi nace yaya muje kawai ya ce to ina zuwa Dan in ya takuramin ma baci zanyi ba ya je ya dauka key din mashin din muka fita karfe shida darabi muka Isa gidanmu tare muka shiga Dan kofar a bude take dakin umma yayi sallama amma shiru Aisha ta fito ta gaida mu tace umma na dakin baba nace Barin shiga yace mini a'a shizai shiga falo ya shiga yai sallama umma ta amsa daga daki tace

Ana zuwa Dan ta gane mai sallamar ta fito idonta duk a kumbure alamar itama tayi kuka suka gaisa yace umma Dan Allah ki bawa baba hakuri ya sauraremu wallahi ba abinda kuke tunani bane dakyar ta yadda ta Shiga dakin kusan minti shabiyar kafin suka fito tare tana tallafa mai dagani jikinshi ba lafiya ......bayan ya zauna yace nabaka minti biyar ka fadi meke tafe dakai ...yaya ya kara rusunawa akasa yace da farko baba kai hakuri maimunatu ta muku karya bawai Dan ta bakanta muku tayi hakaba saidan fargabar mezai faru inkunsan gaskiyar ya zayyane musu abinda ya faru tindaga farko ...salati umma ta fara yi shikuma baba baice komai ba can yace ina gimbiyar take yace tana tsakar gida ce mata ta shigo ya fito ya ce in shigo jikina a sanyaye na bishi na zauna agefen umma da taketa ajiyar zuciya yace gimbiya nadago ido na kalleshi har ya Dan fada kadan ....bai kamata kirika irin tunani hakaba kinsan cewa ko ma menene ya faru ni a matsayina na babba zansan yadda zan daukeshi .....fada yamin sosai kamin yace ina Khalil din nace yana clinic na school nasu yace barin yi wanka muje can .....na fita nima Dan kintsa jikina karfe takwas da kwata muka isa mashin din yaya na hau baba Kuma da Alfarouq .....munsamu an sallamesu Zasu tafi kenan muka isa saidai har lokacin jikinshi ba kwari yana ganinmu yasha jinin jikinsa ....Yusuf ya gaida shi ya amsa yace yamai jiki yace da sauki sunma ce mutafi ya kalli Khalil ya girgiza kai yace karfe biyu na rana tamaka a gida dakai da duk wani abu naka daka mallaka a nan Dan wallahi bakai ba wannan makaranta Kuma indai inada iko dakai ya juya yatafi ko mu baki

Jira ba ....

Kuka Khalil keyi har muka Isa lodge dinsu muka tayashi kwashe kayansa akeke napep muka dawo bayan nasauka a mashin din yaya yace zai wuce nacemai na gode yace don't mention I'll do anything for you , nace yaya ka bawa anty sajida hakuri Dan Allah yace ba ruwanki da ita ya tafi yana Murmushi nima nashiga a zuciyata ina cewa dama ba ruwana tsakanin miji da mata sai Allah .....

Na shiga gida nasama umma tasa Khalil agaba tana mai fada bantaba ganin umma haka ba sai yau da kyar tayi shiru shiko ko uffan be ceba da yamma baba ya taramu yace gobe Khalil ya koma misau har sai ya nemeshi ba me cewa uffan Dan baba ya riga ya rantse Khalil bazai koma poly ba ..... Da dare na je nasama Khalil na hada kayanshi nace meyasa ka fara shaye shaye nasan bahaka kake ba da me yasa kake son zama abinda bai dace da kaiba ko uffan bacemin ba ya cigaba da abinda yake Ganin yayi banza dani naje na rike hannunsa nace please sweet bro kagayamin matsalar ka Dan Allah meyakaika ga shaye shaye meye zaisa ka fara gurbata tarbiyarka da lafiyarka hawaye nagani a idonsa nidinma hawayen nakeyi ganin naki sakeshi yayi aiki yasa shi kallona sosai yace nasan baki da maganin matsala ta Dan haka sanar dake bayada amfani ...nace atleast try and tell me ya yi Murmushi yace kalli idona U'una na dago na kalleshi yace me kika gani a ciki nace tsoro ya girgiza kai yace No gimbiya soyayyace ba tsoro ba ina sonki gimbiya , ina matukar sonki duk lokacin Dana ganki da Isma'il sainaji kaman nayi hauka ina kishinki hannu nasa na rufe bakinshi ina hawaye nace kasan me kake cewa kwayar bata sakeka bane ka daina fadin maganganun nan Dan Allah ya cire hannuna yace duk lokacin Dana tuna cewa umma ce ta shayar dake sainaji bakinciki inji haushin abindayasa baba baikaiki wurin Anty Fatima ko wata ta shayar dake ba I felt angry I hate him for that inajin bakin cikin haramta minke dayayi mari na kaimai nakuma na mare shi na fara dukan shi ta ko ina ina kuka inacewa meyasa haka Khalil ni kanwarkace be kamata ba please ka dena zancen nan kalamanka Zasu iya kashe baba saidanayi me isata na gaji na tsaya ko gizau beyiba nace dan Allah karka kara shan kayan maye Dan darajar mahaifinka dake cikin kasa yayi shiru kafin yace I promise ...na fita a dakin ina tafiya a hankali har nakai daki na fada katifata ina kuka....dama shine dalilin dayasa Khalil yaki jinin Isma'il ya rabbi wace irin soyayyace wannan bayan nikanwarsa ce tare mukasha nonon uwarshi........

Khalil ya koma misau wurin Inna amma gidan ba dadi kullum tunani na makarantar sa da aka katse koba komai shi namiji ne karatu shine gatansa haka muka zauna har aka fara registration na jamb tasleemah tacika tamin tayi nace mata karatu saidai a gidan Isma'il Dan bazan takura baba ba .....maganan da mukayi yasa nakira Khalil nace yacika jamb yace a'a nayita magiya harda kuka kafin ya yarda Dan cewa yayi tunda baba bayason karatunsa shi ya hakura ...ni na turamai kudin registration bawanda na fadawa dagashi saini aka yi jarrabawa dayake computer base ne kashe gari aka tura mai yasama 289 points ai nayita murna ranar har sallah godiya nayi da zan Sanar da baba sai na bari har sai yasama admission aikuwa cikin ikon Allah yasama BUK nayi farinciki sosai nace ya kawo admission letter din yace a'a shi bazai dawo bauchi ba saidai in baba ne yace ya dawo nayita bashi hakuri dakyar ya yadda washe gari ya taho gidan Anty Fatima yaje nasameshi a can na karba yarame sosai na dinga tsokanan shi wai shima yayi baki haka har yasa ki ransa Anty ta jinjina min da basirar da nayi amfani dashi tace in baba be yarda ba Khalil ya dawo wurinta zatayi mai komai ......

Da dare na nunawa umma admission din tayi farinciki sosai tayita samin albarka nace mata saura baba ya yadda tace Allah yasa .... Nasama baba a dakinsa nace baba ina Neman alfarma yace gimbiya tah menene nayi kasa da murya nace baba mutum yana laifuffuka Kuma Allah ya yafemai, baba Kaine baban Khalil a yanzu da Kuma ko yaushe amma haka bazai taba canza cewa asalin mahaifinshi kaninka bane,baba Koran Khalil bai zama lallai ya gyaruba Kuma zai iyasama ya kara baci ne .......tarbiyarmu kana kokari akai Kuma Allah ya sheda saidai hana Khalil zuwa makaranta tauye hakkinsa ne Kuma Allah zai tambayeka, mahaifinshi bazaiji dadi ba, ko Khalil kana yawo dashi ko ina kamar Dan goye duk inda zakaje idan zai yi halin banza zaiyi tsakaninka dashi duk inda yake karinka mai addu'a ......Baba kayafema Khalil Dan Allah na rike kafarsa ina kuka ......shiru yayi sosai kamin yace tashi 'yata Allah ya miki albarka ya rungumeni yana zuba mini addu'a danan na fito da admission letter din na nuna mai har hawaye ya yi Dan yadda Allah ya wadata ni da basira haka ...da kansho ya kira Khalil yace yadawo gida yanzu tinda dama nace mai yana gidan Anty Fatima ....

Nasiha sosai baba ya yiwa Khalil randa zai wuce makaranta haka umma yaya Alhassan ma yamai Dan ya zo Hutu shima yana semester na karshe shima ya hada degree nashi ...... Da ya zo min sallama da daddaren kafin ranan ya ce mini I'll miss you a lot gimbiya Kuma ina godiya da dukkan kulawarki akaina, lokacin danake misau inna ta nutsar dani rayuwa sosai duk dabatasan dalilin shaye shaye na amma I really regret it all na barwa zuciyata soyayyarki and I'll cherish it forever duk da it's a forbidden love but I'll always keep it memorable everyday ya yi kissing goshina yace take care my princess......

Khalil ya tafi makaranta amma kullum sai ya min good morning da good night text nakan tura mai katin 200 duk sati duk da hana ni amma banfasawa haka indai nasama dinki sosai a watan zan turamai dan dubu daya ko biyu duk da baba da anty fatima na nasu kokarin .....first semester nashi yasama gp nashi 4.8 .....tasleemah tana ATBU amma day take dan tana taya mamanta dinki .....nima dinki Alhamdulilah dan ina samun costumers ba laifi ....... Wannan shine labari na har yau da Isma'il yace ya fasa aurena ......