MAIMUNATU Telar Mata

11

by @azizat

MAIMUNATU TELAR MATA

14

CIGABAN LABARI !!!

Da asuba na tashi nayi sallah na ta shi su Ummita ma sukayi ina karatun Qur'ani wayana ya fara ringing dama ringing dinsa daban ne na karasa ayar danake na dauka wayar daga daya bangaren aka ce HAPPY BIRTHDAY MY ANGEL .....nace oh dama yaune, yace kutt U'una dama ko texts dina baki karanta ba nace sorry sweet bro ban duba wayan bane yace princess ya naji muryar ki kamar kinyi kuka na ce no bro mura ne yakamani yace ok Allah ya sawwaka nace amin muka Dan taba hira kamin nakashe na duba messages dina naga texts guda goma shatara na Khalil nayi dariya nace oh ni maimunatu duk na tabbatar da cika shekaru shatara kenan .....naga yaya KB ma ya turo min birthday wishes daga nan naga na Isma'il ko karantawa banyi ba na goge Dan naga kamar na hakuri ne ......bayan na kare karatu na na wuce dakin Baba na gaidashi yanayin idonshi ne ya tabbatar min da yayi kuka dama nasani duk ranar zagayowar haihuwata saiyayi kuka Dan ranar Allah ya karba ran masoyiyarshi ....addu'a yamin sosai yakuma min nasiha akan abin daya faru jiya yace gimbiya inaji ajikina Isma'il ba mijin ki bane akwai maisonki dayake zuwa nan kusa Dan jiya Dana yi addu'a na kwanta nayi mafarkin kina zaune a wani makeken gida kina Murmushi sai ga wani kyakykyawan saurayi yazo ya rungumeki ta baya kuna dariya amma banga fiskarshiba ....nayi dariya nace kai Baba bacci yayi dadi kenan harda mafarki shima dariyar yayi yace Allah ya tabbatar min da mafarkina naga gimbiyata a gidan miji kunya naji nafita da gudu yana min dariya .....Umma naje na gaisar kamin na gaida Anty lokacin shida da kwata na je na gyara falo da yake duk wacce ta kwana a dakin ita ke kula da daki da bayinsa Dan Dana shiga ma a gyare yake .......na je na wanke bayinmu nan na hada ruwan wanka dayake ba wuta naje na tada su Ummita dansuke wanke wanken safe kafin bakwai da rabi na gama hada abin karyawa dumame ne da kunu kowa yaci ya tafi makaranta ina wanke wanke Anty ma ta yi wa Umma Sallama ta wuce .....na kare nashiga bayi nayi wanka nazo na shafa mai nasaka rigar aiki na dama wata riga da wando na dinka su kala uku da hijabi me hannu specifically Dan zaman shago dayake akwai dinkin dazan karasa na Anty Fatima ....karfe takwas da rabi na cewa umma na shiga shago tace Allah ya bada sa'a Baba ma na shago na lekashi shima yamin addu'a na bude shago na karasa aikin karfe sha biyu na hada komai dayake bawani aikin kuma na harhadasu na shigo dashi gida nakai daki .....na fito nasama umma na shirin daura girkin rana shinkafa da wake da miya na tayata muka kare .......

Karfe hudu na sake wanka dama ni ka'ida ta sau biyu nake wanka a rana koda da sanyi ne nashiga na shafa mai da powder nasa lip gloss a lebena wata atamfa ta me ja da zanan flower green da baki nasa na dau jar hijabi iya gwiwa me hannu dayake ni duk hijabaina masu hannu nake dinkawa ......jakar kayan Anty na dauka da wayana na futo naja kofar mu dayake tuni su ummita sunwuce Islamiyya na yiwa umma sallama dama tuni na gaya mata zankaiwa Anty Fatima dinki na fito na leka shago naga Umar ne a gurin na tambayeshi baba yace bai dawo daga masallaci ba nace Kace mai na tafi gidan Anty fatima yace to .....

Keke napep na hau ta wuce dani, Dana je nasameta Zasu fita da mijinta na gaidasu tace gimbiya Dan Allah kishiga da kayan ciki ki bawa laure ta ajiyemin sannan Dan Allah in zaki tafi ki ce Habib ya rakaki gidan Haj.Zainab Munyi magana da ita akan tanason tela nace to na wuce ciki muka gaisa da Laure me aykin tane dayake Anty Fatima nurse ce Kuma tana da yara biyar nata uku na kishiyar ta data rasu tun kamin aurenta ina jinjina mata Dan gaskiya ta rike yaran tsakani da Allah babbar tana Boarding SS2 yanzu sai maza biyu kamin nata maza uku mata biyu ......

Mundan taba hira da Laure dayake yaran sun tafi makaranta Habib ma wai kansa ke ciwo beje ba .....biyar da rabi muka fito ina biye da Habib Dan shekara takwas har wani makeken gida a layin nasu tsakaninsu gida ukune kawai ni na buga gate din megadi ya leko ganin Habib yasa ya bude batare daya tambaya ba na shiga na risina na gaida shi yaji dadin hakan nace Baba Hajiya na nan yace min ee tana ciki Habib na zungura nace bazaka gaidashi ba yace ai Munyi fada tunda ranan cewa yayi ni ba abokinsa bane wai Dan na hau bishiya Kuma ma ya rankwasheni Megadi yayi dariya yace kaci albarkacin Addarka yanzu ma da bulala zan maka aikuwa ya ruga da gudu muka bishi da dariya .... A hankali na karasa kofar Dan tuni Habib ya shiga na bude kofar na tsaya ina sallama saidanayi sau biyar kamin naji wata murya me dadi ta amsa amsawar ma kaman ana roko amma ba a cemin komai ba kaman minti biyu saiga wata mata tasauko tana rike da hannun Habib ...tace kai ja irin yarone shine kabar Antin naka a bakin kofa shiko sai dariya yake matar tana karasowa tace bismillah 'yata shigo mana cikin sanyin jiki na karasa kusa da kujerar data zauna na tsugunna nace ina wuni Hajiya tabata rai tace tashi ki zauna 'yammata nace a'a nan ma yayi tace banason musu ki zauna na ce nagode kamin natashi na zauna ina wasa da gefen hijabina tace sannu da zuwa nace yawwa tace kai yaro jekacewa saude takawo ruwa inada bakuwa yace ba ba kuwa bace Antina ne yadda yayi maganar yasa Hajiya dariya nima nadan murmusa tace to naji ta kawowa Antin ka ruwa ya fita da gudu da alama yasan kan gidan sosai .....gaisawa muka sake yi Inda ta tambayeni lafiyar su Anty nace tana lafiya sunje ta'axiyyane tace Allah ya jikan musulmi nace amin saude ta kawomin ruwa me sanyi da lemon exotic da cake .....Nace hajiya dama Anty ne tace wai inzo kina neman me dinki tace ee medinkin Baby yayi tafiya kuma tanada dinki nima kuma zan bada nawa tace kina dinki ne nace ee murmushi tayi tace dinkin fa dayawa zaki iya nace Insha Allahu tace agida kikeyine nace a shagon kofargidanmu ne cikin mamaki tace kina zaman shago ne ko nakine nace shagonane babana keda shagon toba komai a ciki shine nasa kekena a shagon tace interesting ta girgiza kai tace barin kawo miki kala goma na baby da na wa biyar idan s

dinkin suka min sai na baki sauran nace to ....ta tashi ta haura sama na bita da kallo .....

Ringing din waya naji can aka dauka yaren danaji anayine yasa na leka ta inda nake ji ta wurin dining ne wani mutum da bayan sa kawai nake gani gashinsa baki ya kwanta har wuyanshi ya na sheki ....na dinga sauraren yadda yake magana cikin jin kai duk da bana jin yaren da alama dai wannan bawan Allah shi ya amsa sallamana Dana shigo dazu....ina ta kallon wurin ko zai juyo naga fiskarshi amma har yagama wayar be jiyoba naso na tabbatar koshidin Indian ne Dan yadda yake indiyanci ka dauka Dan can ne .....karan takalmin Hajiya danaji a stairs yasa na gyara zama na sunkuyadda kaina ta karaso da wata jaka me kyau a hannunta brown ta kamin a karaso na mike na karba jakan na karaso wajen danake na ajiye tace nagode .....ta miko min wata jotter tace akwai size dina Dana baby aciki sannan kayan baby sune goma nasama nawa biyar a kasa kimani Riga dazani uku sai siket biyu ita kuma baby biyar kiyi siket biyar kiyi dogon riga na karba jotter din nace nagode ta kalli kayan dake gabana tace haba 'yata ko ruwa baki sha ba nace zansha na tsiyaya ruwa a cup nasha tace wannan me kikayi kenan ko dai kunyana kikeji gara ma ki saki jiki ta mika min kudi ga wannan dubu biyarne kisaya kayan aiki inkin kawo seki fadi kudinki nace a'a kibari innayi zan fadi duka kudin ta ajiye kudin akan jakar tace ke sai kunya kamar bafulatanar daji nayi Murmushi tace barinzo wani kofa tayi inda Habib yashiga dazu ina jiran fitowanta naji wani kanshi ya bugi hanci na sosai kanshin ke ratsa jikina na dago Dan kallon inda kanshin ke fitowa aikuwa naganshi tsaye wurin stairs yana danna waya tundaga kafa nake kallonshi har sama jikinshi sanye da blue jeans da farar T-shirt an rubuta Be my love da blue a gaban rigan kafarshi sanye cikin blue sneakers na kura mai manyan idanuna saboda tsananin kama yake da indiyawa ni kan har a raina kallon Indian nake mishi tunda dazu naji yanayi .....kallon danake masa ne yasa shi tsarguwa ya dago eyes nashi masu rikitar da tunanin mace. kallon danake mai yasa ya daga min gira alamar lafiya kunya ya kamani nayi saurin sunkuyadda kaina yai Murmushi yacigaba da danna waya saiga Hajiya ta fito rike da Leda a hannunta Habib na binta a baya da sweet a hannunsa na mike nace Hajiya zamu wuce tace to nagode bani number ki nafara gayamata tana sawa a waya Dana kare tace yasunan kamin nace wani abu karab Habib yace Anty gimbiya tayi dariya tace to Dan Anty nima dariyar nayi ta mika min ledan natsugunna na karba nace nagode .....nace Habib zo mu wuce yace naki kicewa mommyna ina gidan kaka tsohuwa Hajiya tadan zungureshi tace nine tsohuwar ya kyalkyale da dariya ya koma ciki da gudu na bude baki ina kallon ikon Allah Hajiya tace kinga ki tafi abinki zansa akaishi gida anjuma nace to nafara kokarin hada kayan .......Hajiya tace MUBEEN won't you be a gentleman and help kallona yayi ya kalli hajiyar yace baga saude ba yafada cikin sakalci ......ta ja kunnenshi ya fara 'yar kara yana haba tsohuwa zaki cire min kunne fa cikin gwaran hausanshi.....dariya nafara a hankali ganin yadda yakeyi kamar yaro .....saida yace ok I'll help kafin ta sakemai kunne ya dauka ledar tayi Sauri tace not that one the bag ya dauka jakar yana kunkuni ni wallahi tsohuwar nan kinshiga min ido fa tace sekayi ai kuma and the bag to your car .....na dauka ledar muka bishi wurin ajiye motoci yanufa na tsaya nace Hajiya dakin barshima zan Tara napep tace a'a bana son musu muje ya kaiki gida ....muka karasa motar harya shiga na tsaya Inda inda Dan bansan ko gaba zan Shiga ba ko baya Hajiya ta budemin gaba nashiga inajin kirjina na dukan uku uku ta rufemin kofar tace mubeen banda gudu fa baikulata ba .....nace Hajiya na gode tayi Murmushi tace a sauka lafiya.

15

Bai cemin komai ba ya nufa gate Baba maigadi ya bude mana muka fita ........kaman bazai cemin komai ba sai ya ce sai ina .....yana fada a hankali ko duba Inda nake baiyiba murya na rawa nace du...tsin tan.....shi .... Ya juyo ya kalleni ya kauda kai yace dazu agaban tsohuwa kikai min dariya ko ......na zaro ido nace ni fah banyi dariya ba ...ya girgiza kai yace rubbish .....muka cigaba da tafiya ni ko cikina har wani kulululu yake fadi dan fargaba can ya playing wani Indian song yana binwakar nidai ba abin dana keji sai "teri galliyan" nakega sunan wakarne .....yadda yakeyi kamar shi ya rera wakar duk da niba ma'abociyar jin waka bane amma saina tsinci kaina dajin dadin wakar ....damuka iso angwar mu ni nake nuna mai har kofar gidanmu lokacin baba na kulle shago zaije sallar maghrib nace mai nanne gidan ya ja ya tsaya ko dubana bai yi ba na fara alamar bude kofa na kasa ya juyo ya kalleni yamin kallon 'yar qauye kawai na sunkuyad da Kai na ya sa hannu ya bude min lokacin da hannunsa yadan goga jikina naji wani shock ya kamani ..na fito mukayi ido hudu da Baba na ce ina wuni baba yace lafiya ya wuce na tsaya ina jiran mubeen ya fito ya bani kayan Hajiya saidanayi tsayuwar minti daya naga yafito zaibi bayan baba nace "kayan fa"bai kulani ba yabi bayan baba jikina ya fara rawa nace komai zaiyi oho na tsaya a wurin ina kallon ikon Allah har suka tsallaka titi na juya na shiga gida cikin sanyin jiki nasama Umma na faman soya doughnut na gaidata tace sannu da dawowa ya kika sama fatimar nace tana lafiya amma bamu zauna ba saboda nasamu zasu fita da baban Habib tace Allah ya kyauta nace amin na wuce dakinmu

....

Baba kuwa yana tafiya yaji ana mai sallama ya juya yaga mutumin da ya sauke gimbiya ne ya daure fiska tare da amsa sallamar mubeen yace dan Allah baba masallaci nake nema yace wurin zani nima yace Alhamdulillah suka jera baba a zuciyarshi yana waye wannan daya sauke gimbiya haka dai suka isa masallaci yayi alwala yashiga aka tada sallah ....daka idda ma tare suka fito suka jera dasuka iso wurin motar sa yace nagode baba ..Baba cikin jin dadi yace bakomai dan koba komai yasan yaron baya da girmarkai ....Umar dake zaune a dakalin shago yana tsura wa kyakykyawan saurayin dake magana da babanshi ido yaji ance dan uwa please come and help ya karasa wurinshi yana wage baki yace i'm here sir ya bude boot din motar ya fitar da jakar Hajiya yace kashiga da gidan nan ka bawa wata. Bakar yarinya mai dinki ya amsa yace to ya shiga gida da sauri harda tuntube shikuwa mubeen ya shiga motar sa ya kara wuta.....

Ina dakin umma nagama zayyana mata yadda mukayi da Hajiya tare da nuna mata tsarabar da ta bani samosa ne da cake da dambun nama sai exotic babba guda daya, tayi Allah yashi albarka mukaji sallamar umari ya shigo yana ajiye jakar yace haba Adda gimbiya kinada hadadden guy haka kika makalewa Isma'il wallahi kinyi kuskure ta harareshi tace saikayi Kuma Dan nema kabar mana wuri Dan Allah yayi dariya yace ai muzamu bada ke Wallahi sai wa Dan Indian nan yayi gaba yana dariya nakaimai duka yariga ya fita Umma tace meyake cewa ne nace kawaifa yaga Dan hajiyan dayakawoni ne yake min iyashege tace to Allah yasa dinkin yayi musu yadda sukeso nace amin na dauka jakar nayi daki ......saidanayi sallar isha nace nadau wayata inkira Anty Fatima na mata godiya nasanarda ita yadda mukayi da Hajiya waya tace daukeni naduba duk dakin bawaya nace konakai dakin umma naje naduba amma babu haka na dauka wayar umma nafara kiran numberna saidai har sau uku ba a dauka ba nace kila na bari a gidan hajiya da haka na hakura nace gobe zan tambayi Anty fatima ko an kaimata....

Da baba ya kulle shago karfe goma ya shigo ciki yana cin abinci umma ta sanardashi yadda mukayi da Hajiya da Kuma waye mubeen Dan dama yana jira ne yaci abinci ya tambayi waye wadda ya sauke ni, data gama gaya mashi yace to Allah ya bada sa'a umma tace amin ....

Mubeen kuwa yana tafiya yaji ringing din waya ba irin tashiba ya juyo yaga wata tsohuwar waya akan kujera yayi tsaki yace very local ..ya nufa gida yana isa ya fito sai rufe kofar yasakejin wayar na ringing ya ce shit ya dauko wayar yace gaskiya bazan iya maida wayar ba sai gobe ya dauka wayar da tasa Ipad din ya nufi gida ......yana shiga ya ga babbar falon yamai duhu badai rashin wuta bane to me ya faru yana kokarin kunna torchlight ne yaga haske ya cika falon gaba dayansu suka hada baki SURPRISE!!!!