MAIMUNATU Telar Mata

13

by @azizat

MAIMUNATU TELAR MATA

18

Ina jin mubeen yana cewa Hajiya zai koma Abuja gobe ni dai hankali na naga stairs din can kamar minti uku saiga wata yarinya tana sau kowa cikin takunta mai jan hankali tana sanye da top pink mai spaghetti hand da denim miniskirt ash color kafar ta tana sanye da wani pink room slippers gashin kanta tadaure da pink ribbon tamai style kamar doughnut fiskarta dauke da Murmushi har ta karaso sai data zo kusa naga tsananin kamanninta da mubeen,saidai shi yafita fari da tsayi kai tsaye taje ta rungumeshi tana wani turo baki bhayya shine tunda na dawo sai yau zakazo ko? ta wani kauda kai irin tayi fishi din nan ya mata peck a goshi yace sorry yaar I'm a kind of busy ne tace ok bhai amma next week inka dawo zamu fita ko? har yankari zamu je Yace ta wani yi tsalle tace that's my bro sai a sannan ta lura dani nikuwa tunda tasauko idona na kanta Dan haka kawai naji ta kwanta min arai....ta daga min hannu tace Good morning Beautiful ....na yi Murmushi nace morning angel ...aukuwa nan mubeen ya tuntsire da dariya Hajiya da baby suka kalli juna baby tace MB I thought she's your babe fah yasake kwashe wa da dariya yanuna ni yace baby are you blind you mean this local blacky yace Hajiya kinsan wani funny name data sawa shagonta wai "Maimunatu Telar Mata" yana fada yana dariya suma dariyar suka fara ....

Hawayene ke shirin zubowa nayi sauri na yi hanyar fita zuciyata namin quna ina kaiwa kofa nasa hannu zan bude naji an rike min hannu najuyo domin ganin waye hawayen danake boyewa suka fara zubowa tasa hannunta tafara sharemin ta rungumeni tana cemin I'm sorry dear ba halinmu bane walakanta baki nida Hajiya muna farincikine saboda MB dakike ganinshi yafi shekara biyar bamu taba ganin dariyar shiba Dan Allah kiyi hakuri nasauke ajiyar zuciya nace ba komai haka ta jani hannuna cikin nata har muka isa warensu Hajiya har lokacin mubeen na dariya kasakasa .....lokacin Dana zauna Hajiya tace gimbiya kiyi hakuri Dan Allah nace bakomai .....shikuwa ya kalle ni yace Tailor meyasa baki koyi dinkin mazaba so that kisawa shagonki (Maimunatu Telar Maza da Mata) kinga sai nima nakawo nawa dinkin Hajiya ta wurga mishi takalminta ya tashi da gudu yai hanyar fita tana cewa ka irin yaro kawai shiko sai dariya yake yana maimaita sunan shagona dayakai bakin kofa ya bude zaifita sai Kuma yajuyo yace tailor cikin wani salo mai sanya ya zuciya nadago idona yace zankawo dinki nima yana dariya nadaga maikai alamar ba matsala ya fice daga gidan yana dariya .....

Hajiya tace 'yata kyale shi Dan Allah kinsan Dan fari wawa akace to shike damunsa, nace ba komai hajiya....baby tace Allah hajiya na dauka budurwa MB ya kawo mana tace da hakane danafi kowa farin ciki .....Baby ta juyo ta kalleni tace suna na Zainab amma saboda sunan Hajiyata ne anakirana Baby kefa nace Maimunatu amma ana cemin gimbiya ta mika min hannu mukayi musabaha tace nice meeting you princess nayi Murmushi nace same here ...Hajiya tace ni kadai aka bari a gefe kenan baby tace ohh sweetheart ke ai overall ce ......na ce Hajiya ga kayan aduba ko sunyi baby tace dama kece tailor din da Hajiya ta bawa kaya nadaga mata kai tace wonderful ta jawo jakar ta fara fidda kayan ta ware na Hajiya a gefe ta ce my hajcy barinje na gwada su ta dauka jakar ta haura sama da sauri Hajiya tayi dariya tace shiririta Dan tagankine fa da anan zata gwada su nayi Murmushi tace nima barinje na gwada kayan ta kira saude ta dauka mata su suka haura sama ni kuwa nayi ajiyar zuciya ina addu'ar "Allahumma La sahla illa maja'altahu sahla wa anta taj'alul hazna iza shi'ita sahla " ina burin kayan ya musu yadda suke so...

19

Da gudu ta sauko tana I love it ,I love it ....ta karaso wurina ta rungumeni tana jijjigani tana you are amazing princess nidai tsoro nakeji kila baiyi bane dakyar ta sakeni tareda min peck a kumatu tace you are a Darling ...Hajiya tasauko tana haba baby yaushe zaki girma ne wannan ihun namene wai ta karasa wajen Hajiya tace my hajcy I'm just excited ne kawai gaskiya munat ta iya dinki she's an expert bata taba ganina ba amma dinkin kamar saidata gwadani and my hajcy duk styles din sunyi banma tabayin ko daya daga cikin style din ba Hajiya ta shafa fiskarta tace I'm glad maimunatu ta wankeni Dan nasan da yanzu ihun nan ani akewa ta langwabe kai tace ohh sweetheart I won't dare do such a thing Hajiya tace na yaushe Kuma ....nidai kallonsu nake inajira naji mezasu cemin dukda amaganansu nagane cewa dinkin ya musu kyau ....Hajiya ta dubeni tace gaskiya naji dadin aikinki Dan kuwa kinmin irin dinkin danakeso dama ni bani da matsala tsoro na baby Dan tunda nace mata nabayar da dinki a wata tadinga min kumbure kumbure wai za'a bata mata kaya amma kin wankeni agunta ......nidai murmushin jin dadi nayi tace 'yata nawa ne kudin .. Na sunkuyar da kaina nace Hajiya nayi ko wanne guda daya naira dari takwas Yakama dubu sha biyu kenan tunda kin bani dubu biyar da farko saura dubu bakwai ....Hajiya tace gaskiya maimunatu dinkin nan sunfi karfin Dari takwas ai nace haka nakeyi tace to ina zuwa ta haura sama ...baby ta matso kusa dani tace Munat kin iya dinki meyasa kike karban kudi kadan kinsan nawa ake mana dinki kuwa nace baby Ku da kuke da kudin kenan a angwarmu Dari takwas dinma yayi yawa ake gani ni fa asali dama Dan inason dinkin ne bawai Dan kudi ba, to damuka shiga matsala shine yakasance dinkin ma tallafa mana ...ta nisa tace still Dan dai kawai na gida ne amma yanzu karki damu zan kawo miki customers Kuma karki yadda ki charging nasu kudi kadan Dan manyan 'yanmata ne masu ji da kudi nace nagode tace bari Hajiya tazo mu haura sama ki zaba min wadda zansa gobe inje lectures nace to ...Hajiya ta sauko ta miko min kudi na tsugunna nace nagode amma Hajiya wannan yafi dubu bakwai tace ee dubu ashirin ne nace a'a Hajiya Allah yayi yawa tace Maimunatu naji dadin dinkin dakikamin ne shiyasa nace Dan Allah barin dau dubu goma acikin kudin yayi yawa tace Haba maimunatu kinaso ki maida kyauta kenan kinsan dai ba kyau nace Nagode Allah yasaka da alkhairi Hajiya Tace amin ....baby taja hannuna tace my hajcy muna zuwa barin shiga da kawata daki nabita saman .....

Babban dakine Dan girmanshi yakai falon gidan mu komai naciki pink and purple ne akwai bandaki a cikin dakin kan gadonta na zauna a gefe tajuyo min da laptop nata ta playing min wani series film data ke kallo wai The Originals ta mika min cream cracker data bare tace Angel barinzo ta fita a dakin nikuwa sai kalle kallen yadda nakin yake nakeyi gashi a gyare ga kashin turaren wuta da dakin yake .....baifi minti biyu ba tashigo dauke da plate da cups guda biyu a hannunta ta ajiye plate din dambun nama ne a ciki sai kanshi yake ta dauko min ruwa maisanyi a karamin fridge dake dakin tace Angel mekikeso Dan akwai maltina,exotic,viju,dudu,yoghurt, in basu miki ba in sauka kasa in nemo abinda kikeso nace ruwan ma yayi ta bata fiska haba munat bakyason kawance dani kenan nayi sauri nace bahaka bane fah to dauko min viju ...ta dauko ta zubamin a cup tare da turo min plate din dambun tace kici dambun nan kiji dadi my hajcy ce tayi da kanta wai a MB komai inzai tafi tayi tamai hidima kaman wani yaro nidai Murmushi nayi ina kurban vijun ......tace Allah angel kinmin a raina ban tabajin wata tashiga min rai farat daya ba sai a kanki will you be my friend ? Ta fada tare da miko min hannu nace yes tare da mika mata nawa hannun tace now we are officially friends ....nidai dariya kawai nayi Dan baby akwai abindariya haka muka cigaba da kallo muna cin danbun har ya kare gaskiya Kuma yayi dadi sosai ....

Can muna kallo nace baby dazu kikace min wai Yayanki yafi shekara biyar baiyi dariya ba tace yes kinyi mamaki ko labarin MB Nada ban tausayi poor thing tafada ...nace mutuwa aka Maine daya girgizashi tace Angel idan zan baki labarin MB sai na hada da na familynmu duka but first tell me your story Who is maimunatu? Nayi shiru na Dan wani lokaci kamin na fara gaya mata labari na tun daga farko har karshe tun kafin nayi nisa take zub da hawaye nima nayi hawayen Dan sai a lokacin nakara jin zafin abin da Isma'il yamin ta jawoni ta rungumeni tace Angel lallai labarinki da ban tausayi kiyi hakuri Insha Allah saikin sami wadda ya fishi Kuma saiyayi danasanin rabuwa dake ...can ta nisa tace barin baki labari na dana MB......

©AzizatHamza2017