15
by @azizat
MAIMUNATU TELAR MATA
22
Da dare nake sanar da khalil sabuwar qawa da nayi yayi farin ciki sosai yace na gode wa Allah daya kawo miki farinciki bayan Isma'il ya cusa miki bakin ciki nace Khalil dama kaji labarin abin daya min ne yace tunda baki sanar dani ba ansanar dani ai eyya dan uwana tunda bakason ko ambatonsa sai sa ban gaya maka ba yace bar shege sai ma na dawo zan dau mataki akansa nayi dariya nace barshi da halinsa ya isheshi haka muka sha hira kamin na kashe wayar ...... Can. Aisha tazo ta kirani wai Baba na nemana da sauri na fita dan nasan kan maganar kudin da hajiya ta bani ne duk da suna hannun umma kuma nasan ta nuna masa ..
A daki na sameshi bayan na gaisheshi na zauna kusa da gado ina wasa da yatsu na yace Gimbiya nadago kai na kalleshi Dan yadda ya kirani kamar da damuwa aransa yace Ummanku ta gaya mini yadda kuka kare da hajiya saidai gaskiya ni ina so kiyi baya dasu dan yau dasafe bayan kin tafi malam barau yazo ya sameni wai ina gani kina bin maza wai sau uku ana ganinki da wani saurayi bature mai kudi kina shiga motarsa da farko na kasa ganewa sai daga baya na tuna wannan dan hajiyar ne daya sauke ki ranar nidai bana son fitina gimbiya mu talakawa ne amma Alhamdulillah muna da rufin asiri bana son abin da zai ja miki magana da kukazo da yarinyar nan kuka gaida ni a shago muna tare dashi malam barau din cewa yayi kin koma kwadayi dabin 'ya'yan masu kudi ...Dan Allah gimbiya idan kin kare musu dinkinsu ki bawa Alfarouq yakai musu bana so ki sake zuwa gidansu kinji na ce naji baba to jeki Allah ya miki albarka nace amin....
Tunda na shiga daki nafara kuka wai ina ruwan mutane ne da Zasu sawa mutum ido haka gaskiya nikan inajin baby araina duk da ita 'yar maikudi ce nikuwa 'yar talaka amma tunda Baba bayaso zan hakura ....sai dai mai ko minti goma banyi da shigo wa dakin ba baby ta kirani sauri nayi na goge hawayen fiskata na dauka wayar tare da sallama ta amsa tare da cewa haba angel tun dazu nake kiranki fa nace sorry ina bayi ne tace no probs kinsan me har nayi missing dinki fa nace nima haka, Kuma zobon Umma yayi dadi sosai zaki min watarana inkinzo ko nace ee angel yanaji sweet voice dinki kamar kinyi kuka nace a'a kawai de inajin barcine tace ok barin barki kiyi barci ko and dream of me nace I will kamar zata katse sai tace and my bro too dariya kawai nayi na kashe wayar .....kasa barci nayi sai juyi nake akan katifata anya zan iya daina kula baby kuwa hirar mu nake tunowa yadda ta bani labarin mubeen nan naji tausayinshi Allah sarki nace araina ina tuna dariyarshi sai nima na kama dariya kamar zautacciya ....
Da asuba jin muryar mubeen nayi yana wake up my tailor na bude ido na a hankali ashe mafarkine kawai nai Murmushi .....bayan na gama gyara gida na shiga shago Dan fara sauran dinkin su baby kala takwas na Hajiya uku na baby biyar ...ina shago amma zuciyata na tunano min mubeen yadda ya shakeni maganarsa wadda yake cikin hausan da bata gama zama a bakinshiba har nakusa cakin yatsa ta da allura ....can wata zuciya tace Maimunatu bar hango wa kanki abin da yafi karfinki fah Mubeen koda wasa ba sa'ar ki bane ....karfe sha biyu nashiga gidan Dan girkin rana Umma ta tafi tilde Ta'aziya amma a ranar zata dawo ....garau garau na dafa mana Dan baba na azumi ina cikin zubawa yaran naji sallama muryar baby ne Dan ko a mafarki bazan manta ba ta jefar da gyalenta akan tabarma ta leqoni a kitchen angel nima a zuba dani yunwa nakeji nace 'yan makaranta kenan sannu da zuwa tace barin shiga bayin Ku ta dau buta zata ja ruwa a rijiya nace akwai ruwa a ciki tace to kafin ta fito na gama rabon na ajye namu a tray ga ribar yaji a gefe data fito alwala tayi na shinfida mata sallaya a daki tayi sallah dayake ni ina on lokacin tagama muka gaisa take cemin ina umma nace taje tilde Anty fa nace dazu ta tafi gidan suna nace ina Hajiya tace taje Islamiyya kinsan tsohuwan nan dason addini nayi dariya keda hajcyn ki ne ai tace Mun gaisa da baba a shago banma zaci yaganeni ba nace oh amma zuciyata tsoro naji ....na zuba mana abincin shinkafa da waKe ne da aka yanka mai salad da albasa da cabbage taci sosai taita santin yajin wai zan daka mata irinshi nace mata ba matsala ....
Har Anty ta dawo muna tare da ita ta kunnawa su Albashiru kallo wani cartoon MOANA a laptop nata nikan karshe shago nace zan koma ta Bini nan ina aiki tana tayani hira har 6 na yamma kafin driver yazo ya dauketa ......
Tsoro na baba zaiyi magana amma baiyi ba haka har na kare dinkinsu na bawa Afarouq yakai musu yace naje aika ne saisa ban kawoba Dan kar su zaci akwai wani abu .....Baby ta turo min customers sosai yawanci friends nata ne wasu sukanzo tare wasu ko suzo su kadai ....kullum sai Munyi waya da ita sau biyu ko uku nima nakan kira Hajiya duk bayan kwana biyu mu gaisa intace min yaushe zanzo ince mata aiki ke rikeni amma zanzo ....wasa wasa azumi saura sati biyu Innar mu ta fara rashin lafiya nan baba yaje ya taho da ita daga misau aka kaita asibiti ninake kwana da ita Dan haka bana zama a gida kwana biyu bamuyi waya da baby ba nima kaina banji dadi ba Dan nayi missing dinta Kuma nayi missing din labarin mubeen Dan kusan kullum saita min labarinshi wadda na rasa gane dalilin daya sa nakejin dadin hakan ..... Baby taje gidan mu akacemata ina jinyar kakar mu a asibiti nanfa ta shirya zata zo Hajiya tace itama tanason ladan suka hau mota sai TH Dan anan muke ta kirani nagaya mata dakin da muke suka karaso lokacin daga ni sai umma Dan baba yaje gida dauko mana abinci ....sosai naji dadin Ganin Hajiya da baby suka mana ya jiki nace da sauki baby ta ajiye mana wata Leda da suka shigo dashi Umma tace angode nima godiyar nayi Hajiya tace zata tafi baby tace my hajcy nikan ba yanzu ba Hajiya tace dama bance dake zani ba 'yar rigima mukayi dariya ....Munfito daga dakin zamu rakata baba ya shigo muka hadu nace mai baba ga hajiyar baby tazo mana gaisuwa baba yadan rusuna ya gaidata Dan ta girmeshi Dan baby tace min shekararta 67 yace Hajiya mungode fa Allah yasa ka da alkhairi tace amin ba komai zata wuce baba yace Hajiya kiyi hakuri Dan Allah amma kamar kinmin kama da wata matar Ubangidana Marigayi Alhaji salisu .....Hajiya ta ce Alhaji Salisu wa yace Alhaji salisu Isa Mai hakuri idon Hajiya yaciko da kwallah tace mijina nane baba yace ikon Allah inata Neman iyalen Alhaji shekara da shekaru ban same kuba tace Amma banganekaba yace nine Ibrahim da nake rike da shagon Alhaji na Central market shekarar daya rasu yamin kyatan gida anan nazo godiya na hadu dake Kuma naje na muku Ta'aziya da yaran saidai daga baya danaje gidanku akace min kun tashi tace nagane ka Malam Ibrahim tabbas nasan sadda Alhaji ya baka gida ikon Allah Ashe Kaine Baban Maimunatu yace ee .....nida baby sai kallonkallo muke nan baba yasake mata godiya muka rakata wurin mota baby ta sunkuyo daidai kunnenta tace plz my hajcy banda tunani fa inazuwa nima anjima tace karki damu take your time ...a hanyar komawa nace angel me kika cewa Hajiya ne tace kinsan baba ya tuno mata da tsohuwar soyayya yanzu saitaje tasa hoton Alhaji agaba taita Kuka nace banga laifinta ba mutuwa ba dadi nima nawa tsohon haka yake muka sa dariya tareda al'ajabin cewa Babana ya sansu Hajiya ashe.
MAIMUNATU TELAR MATA
23
Da muka shiga ciki nasama baba na gaya wa Inna ai hajiyar datazo itace matar Ubangidansa tace Allah sarki tanada kirki nida baby fita mukayi Dan basu waje tace zata je ta duba Hajiyarta Dan kamar tana da aiki yau muka tafi har office dinta bayan Mun nema izini muka shiga da sallama tana duba wasu takardu sanye take cikin wata doguwar riga light brown da zanen flower red ta yi rolling da farin gyale idonta sanye cikin farin glass in ka ganta zaka rantse bata fi 45 years ba....ko ta kallemu ta amsa sallamar kamar bataso Baby tace Ina kwana Hajiya nima na maimaita me tace amma ko duban mu bata yi ba da alama ma ta gane baby kawai batason kulata ne baby da jikinta yai sanyi tace dama nazo gaida kakar qawata ce da bata da lafiya shine nace inxo in gaidaki Dan nasan kina aiki yau tace oh ashe inada matsayin da zan samu gaisuwa albarkacin wata qawa gaskiya naji dadi angode zaki iya fita min daga office inada abinyi .....Kuka tasaka ta fita da gudu na bi bayanta ina kira dakyar ta tsaya ta rungumeni tana Kuka nace kiyi Hakuri Angel komai me wucewa ne tace shikenan ni da mahaifiyata amma duk tabi ta tsaneni wai dantana gaba da uwar riqo na Dan Allah kiga ko kallo ban isheta ba Kuma koda gida naje haka take min saisa banson xuwa saidai inda Hajcy zamu je ...nace sai hakuri angel bawai ta tsane ki bane tanasonki ba uwar da batason danta haka naita lallashinta har muka kai gate na tara mata keke ta wuce gida ....ina mamakin hajiyarsu Dan gaskiya abin da ciwo ace mahaifiyarka ko gaisuwar ka bata amsawa....
Haka nayita jinjina al'amarin har na koma dakin nasama baba ya bude ledar dasu Hajiya suka zo da ita fruits ne aciki sai kudi dubu Ishirin baba yace gaskiya Hajiya halin mijinta gareta Dan shima akwai yawan alkhairi yace Alhaji Salisu be taba sanina ba amma danaje Neman bashi a wurinsa lokacin motar danake tukawa ta sama matsala dama batawa bace ya tambayeni kozan iya kasuwanci nace masa Insha Allahu nan ya bani kyautar kudin danaje nema da Kuma shago indinga mai zama mai .....Allah yajikan rai muka ce amin
Kwana uku da zuwansu Hajiya aka sallame mu baby tazo sau daya Kuma...Nan baba yace Inna ta dawo bauchi da zama da kyar ta yadda .....azumi yazo nasama aiki sosai ba akwana biyu baby bata leqo ni ba har bude baki tanayi a gidanmu nima baba ya cire min taqunquni ina zuwa duk ranar jumma'ah in gaida Hajiya ....Sallah saura kwana 9 ta aiko mana da kayan sallah kala biyu iri daya Dana Baby sai su ummita da Aisha ma kala biyu harda dubu sha biyar kudin dinki sosai naji dadin haka ga buhun shinkafa data bawa baba tunfarkon azumi saboda nuna godiya Baba ya sayo mata zabi guda biyar da Zuma na asali Dan mune ma muka tace shi jarkar turkey daya muka kai mata nida Umma taji dadi sosai itama ..... Da Hajiya taje Gombe tayi kwana uku baby gidanmu tazo take kwana .....Sallah saura kwana biyu suka tafi Jama'are Dan tace anan suke sallah .......
Sabanin yadda sauran teloli ke ajiye dinki har safiyar sallah nikan Jajiberin sallah na hada kayan kowa na kaimusu na amshi kudina harda wadda nake bin bashi ma kudina yakama dubu 78 na bawa baba dubu hamsin aciki da kyar ya karba yayita samin albarka ......
Sallah kowa yazo Yaya Alhassan sunyi final exams nasu first class ya fita dashi saura service shiko Khalil yagama level one har anbashi scholarship saboda shine best student a level one Computer science with CGPA 4.92 baba yaji dadi sosai koba komai kudin next session school ne zata biya mishi .....
Haka sallah yai dadi sai dai nayi missing Angel dina gashi kusan kullum sainayi mafarki da mubeen wadda rabona da ganinshi tun ranar daya min dariya a gidan Hajiya .....
Sallah da sati daya su Hajiya suka dawo aranar baby tazo wai tayi missing dina wai mufita ziyara lokacin karfe shabiyu nai wanka na saka atamfar datasa wadda Hajiya ta mana dinkin ma iri daya na mana banyi kwalliya ba Dan bansaba baby ta fidda make up kit dake Jakarta ta tsara min kwalliya sosai nayi kyau kodan bansaba irin haka bane ..dazamu fita muka sha Selfie da 'yan gida hardasu Umma da Anty ...tun sha biyu da muka fita sai biyar na yamma muka kai gidansu Hajiya Dan yawon da mukayi har fada Dan akwai qawayenta dakuma wata 'yar uwarsu dake aure aciki ....muka je aka mana hoto kala uku .....
Da mukaje Mun iske Hajiya nada baki Dan haka kai tsaye mukaje dakinta bayan mungaisa hirar Sallah mukayi nan take cemin ai su Yaya haidar dan Hajiya saura wata daya su dawo tace min mubeen yayi hawan sallah a Jama'are tace zata kawo min hotunan gobe in gani nace to ....sai bakwai driver yamaida ni gida bayan Hajiya ta hada ni da tsaraba dayawa ciki hadda sabuwar waya Infinix ce babba ...danaje gida na tarad da sakon Hajiya Kuma ta saiwa Khalil sabuwar system Dan dama Munyi hirar da baby kan ansace nashi a makaranta kafin yadawo .....murna awurinshi ba a magana yace har sunje sunyi godiya ma da yaya Alhassan da Alfarouq ....nima kiran Hajiya nayi namata godiya Umma ma ta mata sannan na kira baby itama na mata tace haba Angel bakomai banefa naso ace ma IPad amma karki damu next time nace kai baby wannan ma yayi ai ni dama ban iya rike Android ba kila ma in IPad din ne ko kwana daya bazatayi ba tayi ta dariya tace saiki yi installing whatsapp na turo miki hotunan sallah danayi a can nace to ......
Ranar dai har biyu kafin mukakwanta Dan chatting Muke sosai hotonan data turomin sunkai kala hamsin yawanci itada friends ne sai Hajiya,mubeen,da dad dinsu dai cousins Dan ko kadan banganta da sury ko diyyah ba Dana tambayeta tace basuyi hoto tare ba .....bayan na sauka nasaka hoton ta da mubeen ina kallo sunyi kyau sosai saidai ni hankallina akan hoton mubeen yake nayi zooming nashi na qura mai ido yayi kyau sosai nafi minti goma ina kallo kafin na ajiye wayar ina Murmushi na kwanta .....
Hajiya ce zaune tana lazimi akan sallaya Baby ta shigo sanye da rigar bacci riga da wando iya gwiwa kalar lemon green ta karasa wajen Hajiya tamata kiss a goshi good morning my hajcy Hajiya tace morning dear addu'a data saba mata ta rinqa jero mata tana amsawa da amin bayan ta gama baby tace hajcy kamar akwai wani abu aranki tace 'yar Albarka na dade ina tunanin wani alkhairi sai Kuma jiya nayi Istikhara akai tace wani irin alkhairi kenan Hajiya ta kama hannunta biyu tace maimunatu baby tadan zaro ido tace maimunatu Kuma Hajiya tace kwarai maimunatu da mubeen dariya baby tayi tace Hajiya are you thinking what I'm thinking tana daga gira ...Hajiya tace I think so suka tafa baby tace hajcy tun ranar danaga munat nayi Sha'awarta wa MB saidai kinsanshi ai ba a masa gwaninta Hajiya tace nima abinda ke damuna kenan kar yaje ya walaqanta 'yar mutane baby tace indai keki saka baki bazai yi musu ba ta rungume Hajiya tace I love you so much mother tace I love you too daughter nah ...Amma Hajiya dakikayi istikhara me kikaji tace Dana tashi yau maimunatu ta kirani tamin godiya kinsanme ina ajiye waya ko minti daya baiyiba shima mubeen ya kirani muka gaisa waiyayi missing dina kinga ai akwai alkhairi kenan tayi dariya my Hajcy I'm 100% sure munat alkhairi ce ga MB .....to sakeni in karasa addu'o'in danake inje insami dad dinku kan zancen tamata kiss a kumatu tace that's my hajcy ta fita da gudu.....
Karfe 11am a gidan Alhaji Aliyu yayiwa Hajiya bayan gaisuwa da 'yar hirar ya da qani tace Aliyu dama alfarma nazo nema yace haba Hajiya kome kikeso zan baki inhar ina dashi tsakanin mu yawuce wannan ta nisa tace akan mubeen ne yanzu .mubeen shekarar
shi 32 inde lissafina daidai ne yace hakane Hajiya tace Yanzu Haka zamu zuba mai ido yana nan ba mata ni ayadda na karanceshi ko shekara 40 zaiyi inba yarinyar nan ba bazai fidda mata ba ya riga yayi nisa akan sonta saidai ni anawa tunanin yadace mu masa auren har Allah yasa ya nitsu yabar tunaninta gaba daya ...Alhaji ya sunkuyadda kai yace Hajiya kamar kina raina kullum rashin auren yaron nan nadamuna a Jama'are ma saidana masa magana akan yazaba cikin 'yan uwa yace wai zai duba har yau ba maganan ....tace intashi mubeen din ne ma baiki mudena masa maganar mata ba amma dole ne muyita nidai na masa Mata Wata Qawar baby ce tanada hankali ga ta nitsatstsiya iyayenta mutanen arxiki ne thou ba karatu take ba tayi secondary amma yanzu tailor ce tana samun na rufa asiri kaga mace mai zuciyar nema haka bazata walaqanta dukiyar mubeen ba asalima badan kudi zata aureshiba ...Alhaji yace Hajiya Mubeen dankine duk yadda kika tsara yayi mini daidai Kuma nagode da wannan karamci dakika min yanzu yaushe za aje ayi tambaya ....Hajiya tace inaso yau Insamu mahaifinta inya amince zan sanardakai yadda zata kasance Dan bana so abin yadau lokaci yace shikenan Hajiya suka cigaba da hira.......
Karfe biyar na yamma Hajiya da baby sukazo gidan mu bayan sungaisa da su Umma Hajiya tace wajen baba tazo lokacin baba yaje gaida abokinshi da ba lafiya Khalil ne yaje yakirashi yayinda Hajiya da Inna ke tadi abinsu Dan inna tsofin nan ne masu surutu .... A daki baby ke tsokalata wai matar MB nace yau 'yan tsokalar ne sukaxo tace koma dai miye zansani muna Dan taba hira ta ce munat ina Neman alfarma a wurinki dafatan zakimin nace haba Angel dina koma miye indai baifi karfina ba xanyi tace baifi ba saidai in bazakiyi ba nace haba zanyi mana ta riqe hannuna tace Dan Allah ki amince da auren yaya na Mubeen nazaro ido nace ban ganeba tace kinsan Hajiya tazo wajen baba nemar aurenki wa .mubeen ne na tashi tsaye na dafa kirjina nace nashiga uku aure Kuma ta tashi ta dafa kafada na tace tabbas gaskiya ne abindayasa nake roqonkima Dan tace inhar baki aminceba shikenan bazata tursasa kiba ta hada Hanna yenta biyu tace plz angel marry my brother I promise you won't regret it na riqe hannunta baby bazaki gane bane inka auri mutumin da baya sonka wahala zaka sha tace mubeen baida wacce yakeso na zaro ido nace Simran fa tace to me she's dead ta Riga tayi aure shikanshi kusan shekara 8 be gantaba balle ma plz angel in aka tambayeki kice kin amince kinji nace No angel bazan iya miki alfarmar nanba Kuka ta fara hankalina ya tashi na fara bata hakuri.....