27
by @azizat
45
Dakina na shiga na dinga kuka saida nayi mai isata sannan na tashi nayi wanka tare da alwala nayi sallar azahar bayan na idda nayi addu'a wa mijina kan Allah ya yaye mishi matsalolinshi ya Kuma cire masa son simran, na daura damarar yaqi da soyayyar simran koda kuwa kullum zai dinga walaqantani zan jure, amma yanzu saina san ko ina da matsayi a wurinshi ko babu, duk da nasan a 'yan kwanakin Mun shaqu Sosai ....
Ina tunanin nan bacci ya yi gaba dani ...
Tunda ta fita yake zubda hawaye gashi maganganunta suna yawo a kwakwalwarshi musamman wajen da tace dashi ( shin simran ko soyayyar da kake mata zata iya kubutar dakai daga azaban Ubangijinka?)
Kokarin tashi yayi amma bai wani miqe sosai ba ya fadi gwajab a qasa sai bacci mai nauyi yayi gaba dashi..
Sai hudu na tashi nayi sallah na wuce kitchen dan hada mana dinner duk da inason ganin halin dayake ciki amma na daure ban leqa dakinshi ba .....
Bayan na gama hada mana white rice and stew da mango and watermelon juice na koma dakina na cigaba da tilawa kafin a kira Maghreb
Sai karfe bakwai ya tashi ga tsananin ciwon kai dayake daminshi a hankali ya tashi Ganin dakin yayi kacakaca yasa ya tuna abinda ya faru dakyar ya wuce toilet yayi hot bath ya gasa jikinsa,ya dauro alwala zuwa yayi dakin dake gefenshi ya rama sallolin da ake binshi sosai yayi ta kuka yana Neman tuba a wajen Ubangijin sa sai karfe tara ya fito ya shiga dakinsa ya tatara shi duk kwalaben giyan dasuka rage a cikin fridge ya fito dasu ya shiga bayi ya tuttular dasu yayi flushing, kasa ya sauka ya nemi wani kwali ya zuba kwalaben yaje ya zuba a dustbin dake waje ...
Sosai ya gyara dakin ya fesa room freshner dan korar warin giya a dakin.
Laptop dinshi ya dauka ya kira Dad ta Skype sai a nabiyu Dad ya dauka yana ganin dad ya fashe da kuka,cikin rudewa dad yace Muhammad lafiya miya faru ?wani abu ya samu matarka?
Da kyar mubeen ya saita nitsuwarshi ya shiga bawa mahaifinshi hakuri kan giyar dayake sha, dad I know I hurt you a lot nasan kullum ka tuna cewa ni mashayine kanajin baqin ciki,plz forgive me dad,nayi alkawari wa Allah cewa bazan sake shan giya ba har Allah ya dauki rayuwata,plz dad kaima ka yafe mini
Dad ma hawayen ya fara yace na yafe maka dana Allah ya yafemu gaba daya,amin , so tell me what happened son what miracle changes you,
Bai boye wa mahaifinshi komai ba ya sanar dashi,dad ya rinka sa mini albarka,tare da addu an samun zaman lafiya da zuriya dayyaba sunfi awa daya yana mai nasiha kafin ya kashe ...
Cikin fara'a ya nufo dakina ganin a kulle yasa shi murmushi yace good night my tailor, kitchen ya nufa dan samun abinda zai ci ya tarar da abinci a dining ya zauna ya ci ....
Da safe ma bayan na gama gyara dakina ban je nashi ba kitchen naje na hada masa breakfast naji dadin cewa yaci abinci dan ina tunanin tun safe baici komai ba jiya ma banyi bacci ba saidana leqashi naga suna video call da dad tukunna hankalina ya kwanta
Ina jerawa akan dining ya sauko cikin shiri yana zuwa ya ja kujera ya zauna ya fara hmmmmm yummy as always good morning my tailor fiskarshi dauke da Murmushi ko kallonshi banyiba nace morning tare da barin wurin nahau sama yayin dayabi bayana da kallo ...cike da takaici yace I'm in a hurry right now we'll sort this later yaci breakfast dinshi a gurguje ya fita
Sai danaji fitar motarsa na sauko nima na karya ...
Da dare ma ina jera masa abinci a dining na shige daki na kulle .....yana saukowa dabai ganni ba yace tailor is avoiding me and I don't know why? Yace koda yake zata sauko ai ...
Wasa wasa kwananmu uku yau na hudu bama magana iya kaci good morning, ko sannu da dawowa ne tsakaninmu, bama zama muci abinci tare,bama kallo,bama hira, duk da abin baimin dadi ba amma ina so yasan koba ya sona ya kamata ya darajani ....
Yau Jumu'ah ina gama shirya breakfast na haura sama kicibis mukayi dashi yana saukowa yasha baqar shadda jumper,baqaramin kyau yayiba abinka da farin mutum, ga qanshi dayakeyi muna clashing a stair na shidda nayi sauri nace morning batare dana kalleshiba zan wuce ya jawoni har na kusa faduwa ya riqe ni yace what's the meaning of this tailor you are avoiding, I'm your friend, I know that day I hurt you but is over now I won't ever drink again, I don't like your silence plz, let's get back together, bana jin dadi inci abinci ni daya,bana jin dadin kallo ni daya,I missed our fights,our arguments, plz tailor punish me if you want to but I need my friend back ...kallonshi nayi naga tsakani da Allah maganganunsa sound sincere amma nace i don't believe you yace you don't believe me tailor nace yes cakulkuli ya fara min na fara dariya ina I believed you,I believed you,amma bai bari ba, cizon hannunshi nayi da karfi yace aghrrrrrrr ya sakeni yana tailor you hurt me da gudu nayi qasa shima ya Bini yana sai ya rama haka muka fara gujeguje a falon duk min birkitashi,da kyar ya hakura yace you won tailor bazan rama ba ina tsayawa ya kamani yace dummy girl har kin yarda dani nace you cheater! Sakeni yayi tare da rungumeni daidai kannena yace thank you my tailor because of you I change my ways thanks, har zuciya na naji dadi amma na ja kunnenshi nace No sorry No thank you let's eat ...yau a plate daya mukaci abinci yana bani ina bashi kamar wasu masoya saidai in our case the love is one sided ni nake sonshi yayinda shi yake tsananin son wata daban ...
Da karfe sha daya ya kirani yace in shirya driver ya kaini asibiti nace lafiya mi ya faru yace relax tailor dazu danaje office Khalid ya kirani wai Ammi ta haihu amma dan ba rai so an riga ankai yaron ma but basu sallami Ammi ba, nayi salati nace Allah yasa yaron mai ceton iyayensa ne yace amin
Ina cikin mota driver zai kaini asibitin Baby ta kirani take sanardani ai suma yanzu suna airport da Hajcy Zasu biyo jirgi suzo nace Allah ya kawosu lafiya tace nikan angel ko a bikin ku datazo ban lura tanada ciki ba nace nima sai da mukaje gaishesu na biyu na lura da tanada shi haka dai muka jajanta abin muka kashe waya ...
Dana je kiran khalid nayi ya zo ya kaini dakin muna tafiya yace matar yaya Hajcy tace tana zuwa amma i dont know ko baby zata zo? Tsab na gane yana son baby tun ranar da naje gidansu naga yadda yakemin tambayoyi akanta, nace yaya khalid angon zee baby kenan kwantar da hankalin ka baby tare Zasu zo da Hajcy wani sanyi yaji a ranshi amma ya wayance yace niba nufina ba kenan na tambaya ne kawai dan naga hajcy inta zo ita daya za'a bari a gida saboda Haidar ya tafi Gombe ... Daidai munzo dakin nace yaya Khalid nasan kanason baby kuma Insha Allah zan taimakeka ka samu soyayyarta, ya dan sosa kai yace Nagode sosai ......
©AzizatHamza2017
46
Koda muka shiga Ammi da wata kawarta ce a dakin na gaishesu tare da jajanta musu abinda ya faru ammi taji dadin ganina dan Allah na gani bata da girman kai
Shiko khalid ya wuce sallar jumma'ah ...
Ina tare da ammi a asibiti har aka sauko daga masallaci,matar da muke tare ta tafi ni daya nake dakin sai ammi da bata dade da tashi daga bacci...
Khalid ne ya fara dawowa kafin Abba yaxo shi da Ihsan da Sury, ko kallo ban ishesu ba balle gaisuwa suna ta wani kwayyane
Nidai bayan na gaida Abba gefe na koma ina kallon ikon Allah da yadda Sury ke zuba sakalci wa ammi sai cewa take ammi gaskiya yaron nan danaga hotonshi yashiga raina kamar su daya da ya Khalid wallahi, why did he have to leave us like this so soon ... Ammi tayi murmushi tace surayya kenan Allah ya bamu shi Kuma ya karba abunshi baima fito da raiba Allah yasa mai ceto ne muka amsa da amin ...
Shigowar Abba da Khalid wadda tun fara maganar sury suka fita ya katsemu da cewa an bada sallamar ku shirya mu wuce suka ce toh suka fara hada kaya Nikam Ammi dake faman tashi na tallafa mata yayinda khalid ya riqe hannunta muka fita muna tafiya naji an buge min kafada na juya a hankali naga sury ce ta rada min a kunne sake mata hannu dan ba sa'arki bane hararanta nayi muka ci gaba da tafiya har bakin mota muka kaita Khalid ya taimaka mata ta shiga Abba ya shiga daya bangaren driver ya jasu, saura mota biyu ta khalid da wadda ta taho da su Ihsan amma dan neman fitina dukkansu suka tsaya tsagotsago a jikin motar shi kallonsu yayi yace lafiya kuka tsaya min a jikin mota ba ga can driver na jiranku ba sury ta karairairaya murya haba yaya canfa ansa kaya Kuma akwai maid a gaban motar,su wuce kawai mu zamu bika harara ya watsa mata yace ba a haka kukazo ba dan rashin kai yanzu kicemin wani zaku bini, gara ma ku wuce ku shiga mota driver yakaiku ni airport zan wuce su Hajiya Babba sun kusa sauka, matar yaya shiga mu tafi na wuce zan bude kofa Ihsan ta tare wallahi bazaki shiga motar nan ba baqa mummuna matsiyaciya inba neman suna ba harda wani zuwa ki zauna da ammi kamar ke akaiwa haihuwar ban kulata ba naja gefe na tsaya
Khalid ya zagayo ya bude kofar yace matar yaya ki shiga inga wadda ya isa ya hanaki anan nayi murmushi nace yaya khalid daka bari ma zan kira bhayya yazo ya daukeni
Yace a'a ki shiga kawai na wuce na shiga dukkansu biyu sai hararata suke ina shiga ya kullo kofa ya juya yace ku Kuma ku kiyayeni wallahi i don't like creating a scene here amma da sai kun gane kuranku stupids
Ya juya ya shiga mota har muka bar harabar asibitin suna tsaye a inda ya barsu ....
Hakuri ya bani nace masa ni wallahi ba komai anzama daya ai sury da ihsan yanzu 'yan uwana ne ...text nayiwa mubeen kan khalid zai wuce dani airport mu taho dasu Hajcy bayan minti uku ya turo min da reply kamar haka: my tailor ya Riga ya gayamin nima yanzu zan tashi a office na wuce gidan Abban....
Da muka isa sai da muka jira kusan minti takwas kafin jirginsu ya sauka ...Baby na ganina ta rugo da gudu ta rungumeni tana wayyo angel dina haka kikayi fresh nace ke baby ana kallonmu fa tace and so I misses you shiyasa nayi Murmushi nace I missed you too
Hajcy ta qaraso tace baby bansan yaushe zaki girma ba kekan a haka zankaiki gidan Sagir din kije kiyita masa shirme Khalid jin maganar yayi ya toshe mai makoshi gaisuwar dayake shirin yi ma ya hadiye
Har kasa na tsugunna nagaida Hajiya ta dagani tace sannu my daughter fatan ja'irin yaron nan na. Kular min dake nayi Murmushi nace Alhamdulillah Hajiya ....
Dakyar Khalid ya iya gaida Hajiya duk mood dinshi ya canja daga jin ta ambaci sagir wadda ya tsani jin sunan a kusa dashi
Hajcy ce tashiga gaba nida baby na baya muna shan hiranmu har muka isa gidan
Da muka shiga falon ammi direct muka wuce muka tarar da wasu 'yan dubiya guda biyu da ammi sai kannen ihsan 'yan biyu mata da murna suka tare mu nan aka fara gaisawa baifi Minti biyar ba masu gaisuwan suka tafi aka barmu ammi da hajcy ke magana mukuma muna gefe muna qusqus dinmu shigowar Abba ya katsemu Ganin manya na cika gurin muka yi baban falo muka barsu . .
Anan ma hiran mike faruwa mukeyi can na tambayeta angel dan Allah mi yasa kika tsani yaya khalid ne dazu fah ko gaisheshi bakiyi ba, ta harareni lallai ma in gaya miki irin marin dacin mutuncin daya min a wajen picnic ranar a gaban cousins dinmu kinga yadda sukayita yadani a group namu kuwa wadda basa wurin ma saida suka sani wai I'm dating dan acaba harda kawoshi cikin family picnic, toh ai baby ba kince sury da ihsan suka miki magana ba ina ruwan yaya Khalid aciki da ruwansa dama shi ya planning komai ya hada picnic ya sa budurwarsa da kanwarsa suka disgracing dina suka embarrassing din saurayina agaban family
Na kalleta cikin rashin fahimta nace wace budurwarsa Kuma ta ce sury of course nayi Murmushi Allah baby sury ba budurwarsa bane kinga yadda yake musu masifa dazu ne I don't think yana sonta babu soyayya tsakanisu fah
Ta kalleni tace what did you know munat kinsan yadda sury keson sa kuwa, to bari kiji tunda suka dawo daga india duk hutu sai tazo Abuja ko yana nan ko baya nan,inta tashi comments tace duk familyn gidan sarki dana wazirin Jama'are bayan MB babu mai kyaun khalid, bla bla bla tayita following nashi a media twitter,facebook etc,lokacin da MB ya dawo daga Seoul watarana ina jin hiransu da ihsan wai daga Khalid ya gama karatunsa zai aureta sai MB ya auri Ihsan Imagine fah
Nayi dariya lallai baby shine kika concluding cewa ta zama budurwarsa what if wata yakeso ba ita ba,kika sani ko wadda yakeso takusan sury ce amma ba ita ba whatever gimbiya spare me this Khalid talk ya isheni haka koyanason sury koba yasonta ruwansa niba hadina dashi kinga ma saboda shi da tawagarsa sury da ihsan bazan kwana a gidan nanba balle wani daga cikinsu ya daga min hankali gidanku zan kwana nace really baby tace ofcourse kodan naga irin zamanku dakukeyi nace kiyi gulma bah tayi dariya call it sa'ido if you like ....
©AzizatHamza2017