MAIMUNATU Telar Mata

29

by @azizat

48

.........Washe gari......

Yau Sunday Kuma yaune Hajcy zata zo ta duba mu saboda gobe Monday Zasu wuce,

Baby kinaga me zan dafa wa Hajcy in burgeta tambayan dana ma baby kenan muna shirya breakfast a dining tace like seriously angel inkinaso ki burgeta yanzu dambu zakiyi dan both hajcy da dad sunason dambu Kuma kinga rabonda hajcy taci dambu ya dade dan tun bayan bikinku sau daya ta ci nace toh shi zanyi ...

Banji saukowarshi ba sai qanshin turarenshi danaji mai sanyaya zuciya na daga ido na kalleshi gaskiya ya hadu cikin bakin shirt anyi rubutu da fari a gaban (You are for me) yasa skiny crazy jeans ash gashinsa ya kwanta lub har wuyansa

Kallon dana ke masa bansan har ya iso muba, yatsar sa yasa ya tsoka ne min ido nace aghrrrr bhayya, dariya yayi yace watarana saina kwakwale idon nan irin wannan kallo ai ko maye iya kaci baby tace bhayya miye laifi danta kalleka, ta na admiring how handsome mijinta is ....ya ja kumatun ta gossip girl kawai tace bhayya me?yace no me....dariya mukayi nida ita ganin yadda ya bada amsar da shagwaba, zama yayi akujera ya dauka potato ball zaikai bakinsa yana this smells good na riqe hannun sa what now tailor I'm starving..... Na karba potato ball din na maida shi cikin plate , ido suka zuba min shida baby nikuwa hankalina kwance naje na dauka wani qaramin gora da Zuma aciki na zuba a spoon na kawo masa daidai bakinsa nace Haa kamar yadda akewa yara in Zasu bude baki, ba musu ya bude bakinsa nasama masa ya shanye na dauka goran ruwan zamzam shima na tsiyaya na bashi ya sha

Dana gama nace you can eat now riqe hannuna yayi yace tunda kika bani magani a baki abincinma sai ki bani a baki nace cab din ai kana da hannu yace ok bazan Ciba yayi kamar zai tashi nace tsaya zan baka

Ya zauna yana dariya baby ma dariyar tayi ....cikin kulawa nake bashi abincin da hannuna baby sai tsokanarmu take dana gama shima ya ciyar dani baby tashi tayi a gurin bayan ta gama cin nata tace gaskiya barin bar wurin nan kar ayi abinda yafi karfin idona mubeen yace gossip girl kawai....

.....tin karfe hudu ta gota kadan na riga na Kammala komai gida sai qanshi yake duk yadda baby taso na bata ta taba haka naki nace abincin na hajcy ne saita ci da kowa yaci fishi tayi dani ta tafi daki nikuwa dama inada niyyar mata surprise nawa dan inaso na mata homemade pepperoni pizza daya ke mubeen ya koya Mani ...

Ina cikin flattening though din ya shigo as usual chakulkuli ya fara min dakyar ya barni. Na cigaba da abindanake na daura akan baking tray tare da fara saka toppings din ban lura da yadda yake kallona ba sai dana gama zan saka a preheated oven na idonshi kyam akaina amma me da muka hada ido ya fara dube dube Murmushi nayi najin dadi koba komai idonshi ya nuna min akwai sha'awa a tattare dashi dan dama wani micro mini skirt ne fari da blue top mai spaghetti hand na saka,tin jiya da baby tazo ta hanani saka dogon kaya....

Nayi kamar bansan yana kallona ba na bude nasaka nazo ina gyara wurin dana yi aikin naji ya rungumeni ta baya har cikin qwaqwalwa ta sai danaji wani zir ban ankare ba ya fara rada min a kunne how old are you ma ? Cikin dashashshiyar murya nace nineteen,shin shina wuyata ya fara daga nan ya koma bayana a hankali ya fara shafa cikina har marata munkai 2 minutes a haka ban San me ya tuna ba wuf ya cire hannunshi daga jikina yayi baya tare da cewa excuse me bai iya hada ido dani ba yayi hanyar fita daga kitchen din Ganin yadda mood dinsa ya chanza lokaci guda nace barin sake tunzurashi bhayya na kwala mai kira ya juyo a hankali ina Ganin haka na watsa mai fulawar dana dumbusa a hannuna tsayawa yayi nima na tsaya dan naga ya murtuke fiska Fiskarsa da duk ya bude da fulawa yace YOU TAILOR!! ya nufo ni na fara ja da baya har ya iso wurin da na ajiye pack na flour din ya dunbusa shima ina ganin ya eeba flour na fita daga kitchen din da gudu a parlor ya tadda ni muka fara gujeguje da kyar ya kamani ya shafa min flour din dake hannunsa a fiskata ina dariya yana cewa you need this on your face more than me tailor saboda kinga zai saki fari nace banaso muna cikin kici kici tsakaninmu muka tsinkayi hajcy na gyaran murya ashe ta shigo duk bamu sani ba wani kunya ne ya turnukeni Ganin irin kayan dake jikina da Kuma yanayin data samemu ai da gudu na haura sama ko gaishe ta ban iya yi ba shikuwa ko ajikinsa yace welcome 'yar tsohuwa tare da rungume ta tace mara kunya kawai kasa 'yata ta gudu cikin shagwaba yace ni ba abin dana sa hajcy ai ita ta fara watsa min flour ni ramawa nayi zungurarsa tayi tace toh ja'iri sai kaje ka wanke fiskar ai dariya yayi yace as you wish tsohuwa mai ran qarfe yayi sama da gudu shima

Hajcy Murmushi tayi tace Alhamdulillah ashe dai Zasu saita Kansu ...

Dana shiga daki nasanarda baby halin da hajcy ta samemu dariya ta dinga mana tace shi kenan ai kun kauda gulma dama hajcy na tambaya na halin dana sameku nace kai baby ...baby tace kya goge fiskarki ki sauko ni baranje na samu tsohuwata ....

Wanka nayi na shirya cikin atamfa tare da saka zumbulelen hijabi har qasa da kyar na iya hada courage dina na sauko ....baby sai shagwaba take mata mubeen ma ya chanza kaya zuwa Moroccan jallabiya mai

ash da fari ina zuwa duk suka zuba min ido dakyar na samu na gaida hajcy kaina a qasa ita ko ko ajikinta ta amsa min kamar ba abinda ya faru nikam duk kunya ya cikani ...

Baby ce tayi serving dinta sosai ta nuna farin cikinta Ganin Mun dafa mata abunda take marmari, nikam duk a takure nake ban iya cin abincin ba duk da bayau na fara cin abinci da hajcy ba amma Kuma yau duk kunyanta nakeji. Baby da mubeen kan ko ruwansu sunci sosai tare da pizza din sai karfe shida hajcy ta tafi bayan ta hadamu nida mubeen ta mana nasiha mai ratsa jiki harda addu'a na samun kazantar daki nanda farkon sabuwar shekara nidai duk kunya ya hanani cewa amin, a zuciyata Kuma ina tunanin ko hakan zai faruma, mubeen kan bai gane hausanta ba yace tsohuwa muba Masan kazanta you know I hate it gaskiya ba amin ba, hajcy tace wawa kawai hausar ma bai isheka ba ....

Bayan isha mubeen ya kaimu shopping da shan ice cream nikan ban iya daukan komai ba baby ce tayi ta lodan kaya dama musabbabin zuwanma saboda ita ne ...

Yau monday yaune su baby zasu koma kamar Karsu tafi nakeji dan naji dadin kwana biyu da mukayi, bayan Mun shirya mubeen ya kaimu gidansu Khalid dayake jirginsu karfe gomane dan haka anan ya barmu ya wuce office bayan sunyi sallama da hajcy,

Khalid ne ya kaimu airport as usual tsakaninsu da baby ba ko sannu, mun taki sa'a ma su sury sun wuce school dan haka bamu samu matsala dasu ba, Saida muka ga tashinsu kafin ya kaini gida, a hanya nace masa ya kamata ya apologising wa baby koda ta waya ne saboda ta rage tsanarsa that way zaisa ta saki jiki dashi yace Insha Allah zaiyi hakan ....

Bayan tafiyar su baby komai yana tafiya daidai tsakaninmu da mubeen banida wani matsala saidai na lura wani lokaci in jikinmu yahadu yana shiga wani yanayi, gashi naga kamar akwai wasu tablets dayake sha wanda na rasa na menene..

Yau jumma'a yaune zamu je Bauchi weekend sosai muka shirya gashi yace da mota zamuje Dan haka inata doki dan nafison tafiyan mota, ...

Sai kusan maghrib muka Isa bauchi,sai kusan tara da rabi muka shirya, shikadai yace zaije gaida gida tunda Dare yayi ....

Tun daya Isa gida gabanshi ke fadi dan baisan me zai tarar a wajen hajiyarshi ba bayan ya je wajen mom sun gaisa ta masa sannu da zuwa tare da ban hakuri kan rashin zuwanta Abuja,ya ce mom nasan komai karki damu Nasan Hajiya bata nan ne shiyasa Kuma bazaki iya barin dad shi kadaiba, Murmushi tayi tace nagode son for understanding Munyi maganan da dad yace Monday in zaku tafi sai muje tare bazai yiwu Amminku tayi rashi na kasa zuwa ba, OK mom amma dai yajikin nashi dan da safe da mukayi waya naji muryarsa ya canza, don't worry Son jikinshi da sauqi sosai, yace barinje wajen Hajiya mom tace ka wuce falon dad dinka kawai suna tare Yace ok mom good night tace good night dear ...

Kai tsaye ya wuce falon dad nashi....a tare ya samesu dad na kallon News ita kuwa tana danne danne a laptop nata cikin farin ciki ya qarasa ya rungume dad nashi, saida suka gaisa sosai kafin ya gaida hajiyarsa a daqile ta amsa shikan bai damu ba Ganin dad dinsa cikin farin ciki yafi mai komai

Sosai suke hira har karfe goma ya gota kafin dad yace Ya koma gida saida safe yace da Hajiya tace inada magana dakai, jiki a sanyaye Ya dawo ya zauna, dad yace well tunda mother and son conversation ne nikam Saida safenku, tuqa kekensa yayi ya wuce daki ...

Shiru ya biyo baya kafin Hajiya tace maganan da mukayi Kace in kazo zaka gaya min decision naka ina saurarenka ... Da kyar ya composing kanshi ya gaya mata yadda mukayi dashi

WHAT!.....Ashe baka da hankali mubeen kana nufin ka maidani qaramar yarinya, five months me zakayi a five months kudin aure na tambayeka, ko nace maka ina buqatar sisi naka, wallahi ka maida hankalin ka gobe da safe inkazo ka sanar da dad dinka cewa zaka auri Yusra and komai zaiyi just make sure yayi accepting because nanda two months nake son auren and listen failure to convince your dad yana nufin matsiyaciyar gidanka zata fita cause har yanzu ban dauka kana da aure ba the decision is yours,

Cike da fargaba yace Hajiya plz listen to me zan auri yusra but not this soon plz .

Kai!....ta daka masa tsawa banida lokacin saurarenka now leave my presence ...

Da kyar ya iya tashi ya bar falon

Tsaki taja tace ina zan iya cewa wata tailor ka aura acikin dangi kajamin raini wallahi kana auran yusra yarinyar nan zata bar gidan ka

Bayan ta kashe wuta ta shiga daki Ganin dad a zaune a kujerarsa tattare da bacin rai tace lafiya Alhaji jikin ne .....

Wani kallo ya watsa mata yace Khadija naji duk Abinda kika gayawa Muhammad wato har yanzu baki bar zancen nanba Ashe abinda kikaje yi a yola kenan,

Ee Alhaji ban bar zancenba Kuma bazan bari ba har saina cin ma burina dan ni har yanzu to me yaron nan is still a bachelor,

Khadija kidaina tursasa yaron nan akan qarin aure kwatakwata yaushe yayi aure dazai sake wani

Lallai Alhaji naga auren da Kuka mai kaida yayarka ma tursasashi Kuka yi yanzu Kace wai karna tursasa shi dan dana haifa din bazai yiwuba wuceshi tayi ta je ta zauna agaban mirror tana shirin cire jewelries dinta

Matsowa yayi kusa da ita yace Khadija ban hanaki hada auren zumunci ba tsakanina da Imran amma abinda kike shirin yi yanzu bai daceba kamar yadda yace give him time atleast ya samu nutsuwa tukunna ,

Wani nutsuwa Alhaji akwai wata nutsuwa daya kamata ya samu da yarinyar nan ne, babu matsiyaciyace ba abinda zata Mai sai dai ta tsotse shi, kaida yayarta ka you are just deceiving yourself ne ba abinda zata qareshi dashi ..

A fusace dad yace kinsan abinda yarinyar nan tayiwa Muhammad ko ni ban iya yiba ta hanyarta Allah ya shiryar da shi

Alhaji banason jin magananta ya Isa haka tun ranar da magananta ya shigo gidan nan ban gane kanka ba, koda yaushe idan yayarka ta kawo abu mai kyau ne a idonka inba munafirciba ai tana da dan dabai yi aure ba miyasa bata hada shi da tailor ba sai nawa dan, tsabar munafirci ta dauke Zainab a wurina mubeen ma tanason raba ni dashi bazai yiwu ba wallahi sai yarinyar nan tabar gidan dana

Cikin bacin rai dad yace wallahi Khadija ko bayan raina ki kasa Muhammad ya rabu da maimunatu ban yafe ba

Wurgi tayi da sarqar da ke hannunta ta tashi tsaye tace Aliyu sai yarinyar nan ta bar gidan mubeen ko kaki ko kaso...

Cikin masifa dad yace Khadija wallahi karki kuskura ki .......

Mi zakayi Aliyu zaka sakeni, I've seen your worst ai tun ranar daka auri Sakina, ka riga ka nuna min kalarka, kaida Munafukar yayarka, as if that is not enough ka dauki 'yar cikina ka kai mata,.....

Kha...di...jah .... Ya kwala sunanta gameda riqe kirjinshi yana so yayi magana muryarsa ta sarqe ga jini daya fara fita daga bakinshi ...

Hankalinta ya tashi ta qarasa kujerarsa tana Aliyu!Aliyu!Aliyu amma ina ko motsi baya yi ...

Wani qara ta saka tana kiran Sakina!Sakina!.............

Toh komi yasamu Dad???

©AzizatHamza2017