MAIMUNATU Telar Mata

31

by @azizat

50

Tunda naji hayaniya yayi yawa da kokekoke jikina yayi sanyi, Bansan lokacin da hawaye suka fara gangaro minba, hijabina na saka har qasa na fita ...

Kamar yadda Dad ya buqata mubeen ne yamai wanka,

Lokacin da aka mai sutura aka ajiyeshi a falo dukkanmu muna zaune kowa a wurin inka kalleshi idonshi taf da hawaye banda mubeen da Abba

Hajcy ce tafara Isa gaban gawan ta kalleshi tace Allah ya maka Rahama Aliyu nah,Allah ya gafarta maka, Kuka ne ya kubce mata yayinda mubeen ya jata a wurin ...

Daidai nan Baby ta shigo a bircike tana kiran Dad Dad amma ina Dad kam ya mana nisa da gudu ta nufi wurin gawar ta rungume tana Kuka mai tsima zuciya ...

A hankali mubeen ya taka wajen khalid yace jeka rarrashi matarka ...

Ba musu ya nufi Inda take ya yi kokarin janta

Ta wafce leave me! Ba inda zanje ina tare da Daddy na ba Inda zanje

Da karfi ya jata ya rungume ta yana kiyi hakuri baby Dad gidanshi za akaishi

Duka,cizo,ba abinda bata mai amma bai saketa ba,

A haka aka fita da gawar Dad ga dunbin jama'ar dake jiran ta dan rakashi gidansa na gaskiya ....

Qara baby tasa ta sume a wurin ..

.....Mutuwar Dad ya girgiza mutane daya wa ciki harda Hajiya dan tun randa ya fara jinya bai mata magana ba sai safiyar rasuwarshi datazo gaisheshi ya amsa mata hakuri ta bashi a wannan lokacin yace na yafe miki Khadija amma kiji tsoron Allah duniya ba matabbata bace ,

Dukkan iyalen Alhaji sun zo sai Imran da Anty Zahra dake qasar waje, dama a ranar su Sury suke hanyar zuwa dan mishi ban kwanar tafiyansa Germany Ashe bazasu tadda shi ba

Kashe gari Anty zahra da iyalenta suka iso zuwa yamma Imran shima ya iso duk da Mubeen ya cemai kar yazo amma biris yaqi

Da Babana akayi karbar gaisuwa dan idan yazo tun safe Sai yamma yake tafiya,haka 'yan gidan mu kaf sunzo gaisuwa ....

Yau kwana shida da rasuwar Dad bayan anyi sadakan uku gidan ya ragu yanzu iyalenshi ne kadai da Kuma Iyalen gidan Abba, dan yau Uncle Idris dake UK ma ya koma haka Uncle Muhammad dake Kano ...

Nikam tun ranar rasuwan ban Kuma sa Mubeen a Ido naba inaso na ganshi na masa gaisuwa amma ba hali dan a part din mom na tare nida Baby, Baby sai datayi kwana biyu ko ruwa bata sha ba aranar na ukun ne Hajcy ta sata a gaba dole ta sha tea,

Yanzu kam Alhamdulillah tana dan cin abinci Kuma ta dena Kuka saidai ta dena walwala kwatakwata ...

Su Sury ma yanzu sun sauko idan na gaishesu suna amsawa Mardiyya kam har bhabi take cemin (matar yaya)

Zaune nake a daki tare da baby ina taje mata kai Mom ta shigo ta samemu

maimunatu ta kira suna na cikin girmamawa na amsa mata tace kije falo ki dauki breakfast din mubeen a dining ki kai masa yana part dinshi ki tabbatar yaci kinji, khalid yacemin tun ranar da Dad dinku ya rasu baici komai ba

Tea kawai yake iya sha

Nace mata toh

Bayin dake cikin dakin na shiga na wanke hannuna da fiskata na fito, hijabi nasa bisa doguwar riga ta material maroon color dana sa.

Koda na shiga dakin yana kwance akan gado yayi ruf da ciki

Ajiye abincin nayi na qaraso kan gadon na zauna kusa dashi a hankali nace bhayya ya hakuri, bai kulani ba

Janyo kan shi nayi na daurata kan cinyata nace bhayya ka tashi kaci abinci koda kadan ne kaji

A hankali yace bazan Ciba leave me alone ...

Na sake cewa bhayya kaci abinci koda kadan ne saboda lafiyarka rashin cin abincin ka bazai dawo da Dad ba....

A harzuqe ya tashi yace leave me alone tailor,ki tashi kibar dakin nan I don't want to see anybody,

Tashi nayi na nufi Inda ya tsaya nace bhayya plz ka saurareni ...... Leave tailor, I don't want to see you .....

Juya wa nayi zan tafi ya kirani

..Tailor.... Na juyo ya tako kusa dani ya ce don't leave me plz rungume shi nayi ya riqe ni so tightly tare da fashewa da Kuka kamar yaro duk kukan dabai samu yayiba lokacin rasuwa shi yafara yanzu ban hanashiba dan nasan inba kukan yayi ba bazai samu nitsuwa ba ....

Munkai Minti sha biyar a haka daga bisani naji yayi shiru Ashe bacci ya daukeshi ....

A hankali na qarasa dashi gado kwantar dashi nayi duk da qafafuwansa basu gama haurawa ba amma banaso garin gyara masa ya farka ,

Na tashi zantafi naga ya riqe hijabina don't leave me alone Dad .....

Hawaye masu zafi suka zubo min, na tausayamasa sosai

Komawa nayi na kwanta nasa kai na a kirjinshi

Ahaka nima bacci yayi gaba dani ...

Karfe biyu da kusan rabi na farka banganshi ba amma naji qaran ruwa a bayi ya tabbatar min da wanka yake .....

Kayan dazaisa na fidda masa ina fesa musu turare ya fito daga toilet din ...

Ina gamawa na tashi dan mayar da turaren kan dressing mirror na ganshi tsaye wani qaramin towel ya daura,sai dayan yana goge gashinsa dashi duk da bayau na fara ganinshi ya fito daga wanka ba amma ban taba ganinshi haka ba cause a chan Abuja bathrobe yake sawa in yayi wanka .

'Yar qara nasaka turaren ya fadi a hannuna nayi sauri na sa hannuna duka biyu na rufe ido na kamar wadda naga dodo ...

Karasowa yayi yace what's wrong tailor?

Cikin stuttering nace ehm....ban...dama... barinje...waje saika saka kayan ...

Dariya ya saka dan shi da farko baisan mi nakewa tsoro ba ...

Sosai yake dariyar cikin raina inajin dadin yadda ta dalilina yayi dariya it's been days since he last smile or laugh ..

Sai daya gama dariyar shi yace tailor you are too much, so you mean seeing me like this frightened you ....hahahaha ....

Come to think of it when you decided to get married, kin manta cewa your spouse is not your privacy anymore ...

Local girl I'm not even naked yet you are shivering what if I'm naked what will happened to you huh?

Now open your eyes

Nace a'a

I said open your eyes tailor

Plz zan fita a dakin yanzu plz

Hannunsa yasa ya cire hannuna daga idona nikuwa na damke idona.

51

Tailor open your eyes now...

Nace No plz

Ok idan na kirga uku baki bude ido ba zan cire towel din nan and saikin kalleni a haka

One,..... two ....

Kafin yace three na bude idon da sauri,

Murmushi yayi ya kai hannunsa ya shafa fiskata yace local girl kawai on seeing me wrap in towel you shivers I wonder what you'll do when you see naked ....you'll go pagal right ....

.....tare muka ci abinci Kuma Alhamdulillah yaci sosai ....

Da dare bayan sallar isha aka kira meeting a babban falo ....

Ban fita ba tunda naga family meeting ne, daga baya mom ta zo tace na fito ....

Zaune muke a falon Mu yara muna qasa,nidai ina manne da baby ..

Abba,Hajcy, Hajiya, Mom,Mubeen da Ammi kadai ke zaune akan kujera ...

Addu'a Abba ya fara dashi Inda ya sake yiwa kowa Ta'aziya na babban rashi da akayi ...sannan ya nisa yace ...

Da farko dai taron nan nayi shi ne dan kowa yasan halin da ake ciki yanzu ....

Kafin yaya ya rasu ya bada wasiyya Kuma ya aiwatar da wani babban al'amari ....

Wasiyyar itace yanaso dukkan iyalensa su zauna cikin soyayya da zumunci, da kaunar juna, sannan ya damka ragamar gidan sa gaba daya wa babban dansa Muhammad Mubeen dani nan dakuke gani domin duk abinda ya mallaka a duniya sunan mubeen ne next of kin nashi Inda aka buqaci guda biyu kuwa yakan hada da sunana ...

Alhaji yabar dukiya da kadarori da dama wanda baza muyi zancen shi yanzu ba har sai matansa sun gama takaba,

Ni nan Alhaji Abubakar na dau nauyin ciyar wa da shayarwarku gaba daya duk wani buqatu naku yanzu ku dauka yana kaina,

Cikin muhimman lamura da Yaya ya gabatar sune kamar haka:

Na farko duk wani wanda yake aiki a gidan nan ake biyanshi Alhaji ya bashi kyautan dubu hamsin wadda nida mubeen Mun riga mun aiwatar

Daga yanzu duk wanda ke aiki agidannan nizan ke biyanshi

Na biyu matar mubeen, cikina ya fara qululululu saboda tsoron abinda za ace

Alhaji ya bata kyautan gona daga cikin gonakinshi dake Jama'are wannan kyauta ce gareta Kuma takardun gonan na bada shi wa mijinta wadda zai bata tayi signing akai shedar ya zama nata idan an tashi daga nan ...

Na uku shine lokacin da Kamal abokin mubeen yaxo gaisheda Alhaji ranar lahdi, agabana , mubeen, da yaya babba (hajcy) ya bashi auren Surayya

Gaba daya falon akayi tsit kowa na kallon kowa idon Surayya yayi tsuru tsuru ....

Sannan ya nemawa Haidar auren Ihsan dina Kuma na bashi ...

Ihsan tace wallahi bazai yiwuba ...

Abba ya daka mata tsawa yi min shiru anan ....

Duk wanda ya sake magana a wurin nan batare dana qare ba zan saba masa ...

Shiru ne ya biyo baya amma kana Ganin idonsu sury kasan da tashin hankali ...

Ita Kuma Zainab (baby) Yaya ya aurar da ita wa Khalid ranar litinin bisa sadaki dubu biyar wadda sadakin yana hannun mubeen, bansan dalilin sa nayin auren da gaggawa ba duk da na bashi hakuri akan ya bari sai ya samu lafiya ayi auren ya qi Ashe ma ajali ke kiransa ....

Dan haka kasan cewa Baby na karatu ga Kuma halin da ake ciki yanzu nida sauran uncles dinku Mun sanya biki wata uku bayan su Hajiya sun fita takaba nanda wata bakwai dan haka baby zata cigaba da zama agida har lokacin da za ayi musu biki saita tare ...

Duk da sanyin AC dake falon bai hana baby gumi ba jikinta sai rawa yake ...

Ina fata kowa zaiyi hakuri da hukuncin da Alhaji ya yanke Allah Ubangiji ya jikanshi da rahama amin

Idan da mai tambaya ko magana zai iyayi ...

Baby ce ta daga hannu Abba yace Bismillah ...

Cikin muryan Kuka tace Abba Allah bana son Yaya Khalid, Dad yayi hakan ne because he was sick and confused plz Kace wa yaya Khalid ya sakeni, bama son junan mu plz Abba ...

Hajcy cikin bacin rai tace kul Baby kika sake magana akan wannan, ba tarbiyan dana miki bane, domin ba wadda ya isa ya sauya hukuncin Aliyu ...

Jikin kowa yayi sanyi a wurin

Mubeen ne yayi magana wannan karan, on behalf of kowa yayi wa Abba godiya kan abinda ya musu ....

Abba bansan da wani baki zamu maka godiya ba Saidai muce Allah ya saka maka da alkhairi, ya Kuma qara danqon zumunci .

Amin Abba yace dukkanku 'ya'ya nane dan haka yiwa kaine

Hajiya da mom ma godiya sukayi kafin aka rufe taro da addu'a....

....Wallahi bazai yiwu ba dama Dad Hajiya da 'ya'yanta ya fiso saisa kome dasu yake Mom kice musu bamu yadda ba wallahi bazan auri kamal ba dan munafirci ita Zainab din sai a hada ta da Khalid dan munafirci ni a hadani da dan talakawa Dad ne fa ya biya masa kudin makaranta ..

Wani mahaukacin mari mom ta mata ta sake ta mareta ashe baki da hankali Surayya Mahaifin naki kike cewa munafiki

Toh mom ba haka bane gaskiya baiyi adalciba

Wani marin ta sake bata Wallahi Surayya saina ci miki mutunci idan kika sake gayan mummunan magana akan mahaifinki, mahaifinki adalci ya miki ya bada ke wa wanda ya dace dake wanda yake sonki

Kuka ta fara wiwi tana bubbuga kafa ni wallahi Khalid nake so mom do something mom I only love Khalid .. Kuka take sosai abin tausayi

Mom ta rungume ta tana bubbuga bayanta kiyi hakuri Surayya Khalid Baby yakeso saisa Dad dinku ya hada su aure

No No No karya ne ni yakeso mom ni yakeso, mom plz do something I love Khalid mom plz mom...

Mom ma hawaye take dan ta dade da sanin cewa 'yartata Khalid take so amma ya zatayi tunda tasan Khalid baby yakeso Kuma aikin gama ya gama tunda anriga an daura musu aure ..

A hankali take rarrashin surayya wadda da kyar baccin wahala yayi gaba da ita ...

A wurin baby ma haukan ta tada sai ihu take wai bazata yadda ba duk yadda naso na nutsar da ita taki Kuka take sosai kamar wadda aka mata mutuwa ko lokacin rasuwar Dad batayi kukan hauka irin haka ba

A haka Hajcy ta shigo ta samemu, baby ta riqe kafanta tana Kuka dan Allah Hajiyata kice a warware auren nan bana son Khalid I hate him I hate him

Hajcy ta janye kafan ta tace bansan ke butulu mahaifinki ya yanke hukunci yana cikin qasa kinzo kina masa ihu kina hukuncinsa bai miki ba Alkawari kika dauka masa zakiyi biyayya wa mijinki Ashe duk karya ne to wallahi ki kiyayeni tunda zumunci kike son batawa har ki dubi idon mutane kice kina qin dan uwanki inkin gama haukanki Ina jiranki a daki akwai maganan dazan miki

Tana gama magana ta fita

Rungume baby nayi ina bata hakuri ta ture ni leave me alone, gimbiya just leave me alone bana son Ganin kowa plz ...

Kara rungume ta nayi nima ina kuka abin gwanin tausayi......