34
by @azizat
55
.....I dedicated this page to all those who like Maimunatu Telar Mata ......I love you all....
Za a iya Ganin kurakurai acikin rubutuna zai iya zama typing error ne dan bana samun daman yin Editting ko Kuma nayishi cikin yanayin jin bacci,ko Kuma nayishi a rashin iya hausana dan har yau ina koyon Hausa coz Hausa ba yarena bane kawai naji ne asanadiyar zama da hausawa .....
I don't have any grudges with tailors dan haka duk wata tailor tayi hakuri I did to educate not mock any one or any skill ....ina da yayu biyu tailor so kudos to all those who are tailors it's a skill worth praising ........ (2017)
***
Poor maimunatu one kiss yasa ta dauka mubeen na sonta well let's find out ko da gaske mubeen nasonta ko Kuma he mean what he says cewa baya sonta.....
.... Jiki na har rawa yake saboda yadda na kidime a hankali naja jikina na wuce daki hawaye ma sunki fitowa da sun rage min takaici ....cire rigar jikina nayi na dauko wata jallabiya na saka tare da saka dogon hijabi duka cash din dake jikina na dauka dubu takwas tare da wayata na fito duk da sha daya ta gota banji tsoro ba na fito koda naje ina kiciniyar bude gate Baba maigadi ya fito ya haskeni da torchlight
A'a Hajiya kece lafiya dai ko
Na qaqaro murmushin dole nace lafiya baba zan dan fita ne
Kallona yayi da kyau yace Hajiya ba lafiya ba dai zaki fita da dare haka ai akwai matsala ...
Fashewa nayi da Kuka ina baba kabarni na fita gidanmu zanje, banida ikon cigaba da zama anan ...
Baba maigadi yace Hajiya koda mi ya hadaku ko da rabuwa kukayi fitarki wannan dare da hatsari ki koma gobe da safe Insha Allahu saiki tafi
Duk yadda naso ya budemin gate yaki, yayita bani hakuri akan in bari gobe in tafi,
Da kyar na hakura amma nayi niyyar bazan koma cikin gidan ba dan na gama zamansa tunda mai gidan yace nabar masa gidan sa baya son ganina aciki,
Haka na koma naje na zauna a bakin kofa ban iya rintsawa ba har asuba a zaune na kwana sanyi,ciwon kai,gajiya,damuwa duk sun hanani yin bacci ..
Ana kiran sallar asuba naje na yi alwala a famfo da akeyiwa flower bayi na dawo nayi sallah akan dankwalin doguwar rigata....
Ina idda wa ko addu'a banyiba na tashi naje nasamu su baba maigadi dake shirin yin alwala nace zan tafi ...
Baba yace Hajiya da kin bari gari ya Dada wayewa
Nace dan Allah baba kayi hakuri ka budemin in tafi Ganin banida niyyar jin magiyarsa yasashi budemin na fita....
Tunda motarmu ta tashi nake Kuka na rasa me yakemin dadi a duniyar Allah ada na dauka bayan Isma'il ya yaudareni bazan sake fadawa tarkon namiji ba sai gashi mubeen yamin cin mutuncin da bazan taba mantawa ba akan photo wata banza wai Simran ...
Tunda ya rufe kofa ya kwanta akan gado yana Kuka I'm not sure ko na baqin cikin rasa hoton simran ne (ai akwai wani a bauchi sannan akwai a wayarsa) ko Kuma nacin mutuncin da yayiwa tailon sane haka yayita juyi akan gado har kusan asuba bacci ya kwasheshi ....
Muna isowa park na tari napep na wuce gida
Mai napep na saukeni na shiga gida da gudu ko sallama banyiba na shige dakinmu na kwanta akan gadona nada wadda ya zamto na innarmu a yanzu Kuka nake sosai a haka su umman suka shigo suna tambayar lafiya amma ban kula suba duk yadda sukayi naqi magana har baba ya dawo daga kasuwa ya taddani a haka shima duk yinsa naki magana karshe yace su barni in huta tukunna kafin nan hankalina ya kwanta .....bayan fitan su bai jimaba bacci mai nauyi yayi gaba dani.....
Tailor, tailor, tailor chanza skin zakiyi ne, I'm hungry fah ya fada yayinda yake sau kowa daga stairs cikin shirin tafiya office sau biyu kenan dayake duba dining amma ba komai gashi dama bai tashi da wuri ba, Ganin dining din ba komai ya duba kitchen nanma ba komai saboda yana sauri ya hada cereal kawai yasha a gurguje ya fita crazy larki I'm sure tayi fishi ne about last night but I won't give in saina Punishing dinta cox she hurt me so badly ...yace a ranshi ...
Yazo zai shiga mota baba maigadi ya tare shi ranka shi Dade inada magana ok baba make it snappy coz na makara ina da aiki a office
Alhaji dama maganan matanka ne ni a nawa tunanin gaskiya bai kamata duk abinda ta maka ka koreta cikin dare ba wallahi ranka shi Dade jiya da tausayinta na kwana yadda na ganta na tausaya mata yarinya mai hankali, banida hurumin saka ka maida matarka amma Alhaji kayi hakuri aure dama Saida hakuri ..
Cike da mamaki mubeen yace niban koreta bafa ta tafi ne ..
Shima maigadi da mamaki yace Alhaji ai tun jiya takeson tafiya ni nema na hanata amma da asuba ta tafi lafiya daiko
Mubeen ya dafa kanshi instead for her to apologize saita choosing ta tafi well ita ta Sani I don't care ..
Baba na gode da advice don't worry zata dawo yanzu barinje office ...
Sai yamma lis na tashi missed calls na babu sunfi ashirin bayan nayi sallah ta sake kira na dauka
Haba amarya bhayya ya baki wahala kenan tun safe wayarki bata shiga data shiga Kuma kinki ki dauka ..
Nace hmm baby kenan network ne dakika kira Kuma ina bacci shiyasa
Hmm an rama baccin da ba'ayiba jiya kenan kin rikita yayana
Hello baby zankiraki an jima ina zuwa na kashe wayar gaba daya ....
Har dare ban iyacin komai ba haka naki cewa komai to ma taya zam fara ce musu saboda hoto ya koreni a gidanshi ...
Washe gari baba da inna suka tisani a gaba dole nace musu korana yayi a gidan sa
Salati suka fara suna sallallami
Baba yace ya sakekine nace a'a
To miyasa kika dawo inkun samu matsala ai saiku tsaya ku warware tsakaninku ba wai ki dawo ba ..
Kuka nasaka Baba ya koreni yace ya tsaneni bayason ganina, yace in fita a rayuwarsa .....Kuka ya kufce min ....
Lallashina suka fara karshe Baba yace dayamma zaije ya samu hajcy yaji mike faruwa ...
Zainab ki saurareni this once please kiji bayanina bazan wuce ten minutes nakiba ....
Ka barni fa bazanji komai daga bakinka ba kayi munafircin daka saba ai an daura maka aure dani to wallahi saidai ka mutu dan ni ban daukeka a matsayin miji ba .....
Ta juya zata tafi ya jawota da karfi Zainab listen to me
Mari ta sharara masa leave me Khalid leave me ....
.Ganin ya saketa baice komai ba yasa jikinta yayi sanyi kallon kallo suka tsaya yi kafin yace shikenan Zainab na barki Insha Allahu bazan sake zuwa Inda kike ba yana gama magana ya juya ya fita
Tun daya fita ta kasa motsi, haushin kanta takeji miyasa ta mareshi mijinki nefa Zainab Kuma yayanki... Da kyar ta iya barin wurin .....
30 minutes later....
Assalamu Alaikum Khalid ya hanya ...
Ba Khalid bane mai wayarne yayi hatsari ankaishi emergency TH shine muka kira last call nashi ...
Innalillahi wa inna ilaihi rajioun inadai yana da rai ..
Ee damuka kaishide yana numfashi saidai har yanzu likita na wajenshi
Mun gode muna hanya ...
Hajcy miya faru ne
Haidar dan uwanka na asibiti yayi hatsari
What yanzu fa yabar nan ...
Later in the day
Bayan baba ya gaisa da maigadi Hajiya tana ciki kuwa ..
A'a malam suna asibiti Khalid ne yayi hatsari ...
Innalillahi ai bamu saniba a wani asibiti ne
Inaga babban asibiti ne ...
Nagode baba Allah ya bashi lafiya,Allah ya kiyaye na gaba amin barinje nima na dubashi ..
A yayi kyau Mun gode malam a gaida iyali ...
Saude hajcy bata dawo bane ...
Ta dawo ta koma asibiti
Asibiti Kuma waye ba lafiya
Yaya Khalid ne yayi hatsari
Na shiga uku da gudu ta fita tana Kuka tana kwalawa driver kira ....
Calm down baby Insha Allah ba abinda zai sameshi ...
Kuka take sosai tana dana sanin abinda ta masa what if he died da fushinta a ranshi ya zata kare kanta a wajen ubangijinta ...
Zuwa dare duk 'yan gidansu sun zo harda mubeen Abba ne baya kasar bai zo ba har lokacin kuwa Khalid bai farfadoba ....
Koda Baba ya dawo ya sanar dasu umma abinda ya faru sukace a fasa maganan yanzu tinda suna jinya sai abu ya lafa tukunna .... Daganan baba ya jeshi asibitin dan gaisuwa koda yaje mubeen basu iso ba har lokacin dan haka bayan yayiwa su Hajiya dasu mom gaisuwa ya tafi be musu zancena ba .....
Baby da haidar da ihsan ne suka kwana a asibitin ...
Riqe take da hannunshi plz yaya ka tashi kaji, inason Ganin kyawawan idonka,inason jin muryarka,plz yaya plz wake up I didn't mean to hurt you plz, don't leave me, ina sonka kaji, ina sonka sosai plz don't leave me .....
A haka take ta sunbatu har bacci yayi gaba da ita kanta bisa kirjinshi ta riqe hannunsa gam ....Ganin tayi shiru ya bude idanun yana Murmushi duk da ciwon dayakeji amma yana cikin tsananin farin ciki mararmisaltuwa dama tun tuni ya farka saidai jin maganganunta yasashi yayi lamo kamar bai farkaba ....
Haka rayuwa ya cigaba da tafiya Khalid na jinya a asibiti Abba yaso ya tafi dashi Abuja amma yace a barshi, Haidar da baby ke jinyarsa yanzu yaga chanji sosai a tattare da baby dan tana kula dashi sosai har hira take masa wasa wasa ma aurantam sun fahimci junansu Khalid kam Gani yake rashin lafiyarshi is a blessing in disguise dan yasa amaryarshi ta fara sonshi ...
Nikam kullum sai lalacewa nake bana iyacin abincin kirki ga yawan tunani,baccikam saidai ya saceni, duk nasiha na duniya baba da umma sunmin akan in saki raina amma na kasa soyayyar mubeen ya zamar dani tamkar zaucacciya kullum jira nake naga texts dinshi ko kira amma babu kullum ina baza kunne inji kozaicemin my tailor amma babu ....gashi 'yan gulma koda suka ga na dawo gida sati daya sati biyu aka fara gulmata cewa mubeen ya sakeni dama kwadayi yakaini Kuma an koro ni....magamganu dai marasa dadinji
Baba ma a shago bai tsira ba makiyansa suyita tsokanarsa suna mai habaici ...
Alhamdulillah bayan sati uku aka sallami Khalid nan Kuma aka fara hidimar biki duk da an kara wata daya akai .....masu hado lefe sun tafi
Randa baba ya Kuma zuwa Neman Hajiya akan maganata ake cemasa sun yi tafiya ...
Mubeen sai lalacewa yake komai ya dena masa dadi,kowa ya ganshi yasan yana tattare da damuwa so tari ya dinga kwaba a office kenan ko ya dinga sunbatu shikadai idanko yana gida yaji dan motsi zai fara my tailor is that you ya fara dube dube wani lokacin saiya dau waya zai kirani sai Kuma ya fasa yace she suppose to call me first ...duk gidan ya isheshi ...
Yanzu ma yana zaune a office yayi tagumi duk damuwa yamai yawa nothing interest him again ...
Kamal ya shigo MB ...MB...
Yayi firgigit ya ce kamal lafiya
Tambayan dazan maka kenan dazu secretary ta kawo takaddun nan kayi signing amma jiba abinda ka rubuta ya tura masa papers din
Ya kalla da kyau
My tailor .....shine abinda ya rubuta a wurin barobaro ...
Sorry Kamal I was just preoccupied ne ...
MB kana cikin damu wa ka je ka dawo da matarka ko zaka samu nutsuwa for the past two weeks ba randa zakazo office ba kace my tailor ba it means you are missing her ..
Plz kamal ka riqe advice dinka banaso ..
Ok nidai kamin signing a wurin kafin nima sunana ya koma my tailor....
Yau ya shigo bauchi bayan sun gaisa da mom tace mubeen yadai lafiya miyasameka haka kaganka kuwa ...
Babu mom kawai stress na hanya nefa
Ban yarda ba tukunna ma ina maimunatu ne kafin Hajiya su tafi Munyi maganan tunda Khalid ke asibiti batazo ba haka kaima baka zo da itaba lafiya dai babanta sau biyu yazo gaisuwa haka su ummanta sunzo sau daya ....is everything alright
Yes mom shi decided to leave yazan mata should I go running behind her ne ta tafi gidansu and she never bothered to check on me ...
Mubeen lafiyarka kuwa kana nufin tun da dadewa Baku tare amma you never tell us,so kake a zage mu a gari ne
Ka saketa ne?
No mom I didn't
Gaskiya mubeen da sauranka bari Hajiya su dawo jibi muyi maganan dan ni ban san me zance maka ba,ka bani kunya wallahi ....
Mom ita tamin laifi fa and you are taking her side ...
Koma dai minene bari Hajiya ta dawo ...
Later that day.........
Mubeen naji duk magananku da Sakina ....
Amma ka saurareni inaso ka rubutawa yarinyar nan saki kafin Hajiya ta dawo tasaka ka maidata gidanka this is an opportunity that I don't want to miss .
But Hajiya I made a promise to Dad bazan sake taba saidai idan ita ta nemi sakin ...
Bana sonjin komai daga bakinka so do as i tell you...
Jiki ba kwari ya dauka takarda ya fara rubutu ...
Saki uku zaka mata dan bana son ta dawo we don't need her ....
Yana gama rubutawa ta wafce takardar ta nade shi tace saura kacewa Hajiya Nina saka banason tashin hankali yanzu ...barinje in kaiwa matsiyata foolish people kawai .....ta fita a dakin ...
Kwantawa yayi akan gado yace where are you tailor are you even thinking about me?...
.......Yau tun safe nake fama da zazzabi gashi damuwa tamin yawa dakyar Baba ya lallabani naje chemist aka min allura dan naki zuwa asibiti .....gashi jiya Anty sajida matar yaya KB da tsohetsohe ciki tazo tamin talas wai na dawo zan karbe mata miji sai alokacin na fahimci dalilin dayasa yaya KB ya daina shiga sabgata tun kafin biki na da Kuma bayan biki, shi baisan ma ina gida ba yazo gaida umma ne ya tarar da ita tasani a gaba inci abinci daganan Kuma yazo ya gaida ni sau biyu, tunda Anty sajida ke masifarta ban tanka mata ba sai hawaye dana ke tayi gashi Umma batanan lokacin Inna ce kawai a gida Haka tayi ta gama ta fita Inna na mata Allah wadai da halinta,
.....sallama akayi da Baba dake cikin shago yayi tagumi duk tunaninsa bai wuci yadda zai bullowa lamarin nan ba yayi danasanin amincewa dayayi da auran gimbiyarsa da mubeen domin yanzu mutanen layinsu sai dariya suke masa wai kwadayi mabudin wahala,...
Mal Ibrahim ana magana dakai a waje Wani saurayi daya shigo siyen maltina ya ce dashi ..
A waje Kuma ..
Ee wata jeep ce a waje driver dake ciki dazan shigo yace nayi maka sallama
To Allah yasa dai lafiya ....Albashiru ka kula da shago ina zuwa ....ya fita jiki a sanyaye wurin da aka Parker jeep din ya nufa saitin driver ya zagayo dayake window din a bude ne ya masa sallama yace akace ana neman Mal Ibrahim ..
Driver yace ee hajiyace ke nemanka ka zaga ta baya ..
Cike da fargaba ya zagaya wajen owners sit shidai yasan bayan Hajiya zainab baya da wata Hajiya daya Sani Kuma yasan haj.Zainab idan tazo tana shigo wa cikin gida ne ....
Yana tsaye jikin wurin yana jira a bude kofa a fito ko Kuma a zuge window amma ba wanda yayi hakan ....yafi Minti uku a haka yana baza ido yaga mai nemansa amma shiru..
Chan aka zuge window din koba a fada masa ba yasan Hajiyar mubeen ce tunda ga kamanni gashi ya ganta sau daya lokacin dayaje musu Ta'aziya ...
A walaqance ta kalleshi.
Baba yace Assalamu Alaikum ina wuni Hajiya duk da kallon datake masa yasan da wuya ta amsa gaisuwar tashi ...
Tsaki tayi tareda cilla masa takarda wannan takardar sakin matsiyaciyar 'yarka ce dan haka daga yau ba ita ba dana karka damu gobe zan sa a tattaro maka kayanta gaba daya dan bama buqatansu, Kuma ka ja mata kunne bana son ganinta anywhere near my son ko Kuma danginsa tariga ta sami arzikinta tunda gonar da aka bata is worth 2 million sai ayi jari a koma Sana'ar dinki ......
Zuge glass din akayi motar ta wuce tabar Baba da yayi mutuwar tsaye yafi Minti biyar a haka kafin ya dauka takardar a kasa hannunshi har rawa yake tunda ya shiga gida walwalarsa ta kare ...tunaninsa bai wuce yadda zai sanardani mubeen ya sake ni ba bayan yasan yadda nake tsananin son shi ...
Da dare baba ya kirani yake tambayata abinda ya hadani da mubeen Kuka na fara ya rasa Ya zaiyi dani .....
Gimbiya tah kiyi hakuri ki sanar dani domin yanzu auren ku ya qare ...
Rinannun idanuna na dago na kalleshi nace Baba aurena bai qare ba Kuma bazai qare ba Ka daina biye 'yan gulma Baba aurena bai qare ba ....nafashe da Kuka ...
Rungumeni yayi yace kiyi hakuri Allah zai baki wani mijin ...
Fisge wa nayi daga jikinshi nace karya ne bhayya baya Saba alkawari yace bazai sakeni ba karya ne ....na fita daga falon da gudu ina Kuka ...
Baba ya matse kwallar dake shirin fito mishi ya Ciro takardar a aljihunshi yace gimbiya ban San yadda xakiyi ki fahimci auranku da mubeen ya kare ....
Umma ta shigo ta dafa kafadarshi malam kana Ganin gimbiya zata samu nitsuwa ba tare da mubeen ba nikam al'amarin na bani tsoro kullum fa sai anyi da gaske take cin abinci ga rashin bacci ...
Ya zamuyi Hafsah ya riga ya saketa Kuma yadda mahaifiyarshi tanuna min dazu ya nuna dama basa jituwa bazata taba bari ya dawo da ita ba ...
Umma tace malam ka duba kar ya kasance saki uku ne ma ya mata ..
Baba hannu na rawa ya bude takardar saidai me rubutun layi biyu da suka gani shiya daure musu kai ....
Umma tace a'a malam kode ba takardar bane .
Itace tunda na dauka a kasa da Hajiya ta wurga shi yake aljihuna ban fidda ba ..
Sake karantawa sukayi amma Sam hankalin su ya kasa yadda da abinda suke gani to me wannan ke nufi ? .....
....kwance nake ina Kuka yanzu kam ko muryana baya fitowa sosai .....Inna ta tayi rarrashin harta gaji ...
Shigowar Baba tace yawwa Ibrahima na gaji da wannan kukan an bata hakuri ta ki yau aka fara mutuwar aure ne iye
Baba ya karaso ya tallafoni jikinshi yace kinyi gaskiya gimbiya tah mubeen bai sake ki ba saidai akwai ayar tambaya a takardar da aka kawo yi shiru kinji. ..
Baba da gaske kake bai sakeni ba...
Ee bai sakeki ba gimbiya ...
Na yi saurin goge hawayena nace baba yace in dawo koh,yace yana sona koh, ...
Jikin baba yayi sanyi tabbas ba karamin so gimbiyar tasa takewa mubeen dan kuwa ko lokacin da suka rabu da Isma'il bata tada hankali haka ba cikin sati daya ta warware amma sai gashi kusan wata biyu da dawowanta gida kullum kara lalacewa take ....
Ya shafa kumatunta yace gimbiya ki sanardani komai kinji, karki boye min komai gameda rayuwar aurenki dama mubeen na cutar dake ne,dama baya kula dake ...
Nayi sauri na rufe bakinshi nace baba bhayya yana kula dani sosai, haka nayita bashi labarin zaman mu mai dadi kafin ranar da na qona hoton simran mubeen yayi fishi yace in bar masa gida .....
Jin cewa mubeen bai sakeni ba yasa na saki jiki na har na samu nayi bacci ....
Washe gari a gidan Anty Fatima.......
Ni yaya abin ya daure mini kai bisa wannan takardar ya nuna mubeen na kewar gimbiya saidai nakega sharrin hajiyarsa ce ita takeso ta raba su ...
Nima abinda na gani kenan amma ni abinda ya kawoni shine zan kaiwa ita Hajiya Zainab takardar na Kuma sanarda ita abinda ke faruwa dan nakega bata Sani ba inhar bazai yiwu a sasanta ba kawai ya saketa idan yaso na maidata Maiduguri ko hankalinta zai kwanta ...
Yaya nidai bana son sakin nan there most be a way dan gimbiya tayi karanci da za ace aurenta ya mutu aure da ko shekara bai cika ba ina mudai je musamu Hajiya Zainab din muji ko mai zata ce ...