BAKIN ALKALAMI...

Babi na huɗu

by @maryamlitee

Wannan link shi ne kashi na hudu na labsrina BURI da ke cikin gasar marubuta ku shiga ku yi mini like na gode
***

BAKIN ALKALAMI*.....

RUBUTUN
    MARYAM LITEE

FREE BOOK

MARUBUCIYAR

WA GARI YA WAYA
*CANJIN BA ZATA
RANAR NAKA
*
*MUTUM DA KADDARARSA
HATTARA
*
*SON ZUCIYA*
*SHIRIN ALLAH*
*BURI
UMMU RADIYYYA

4

Yaya Atika ta ɗaga mata hannu  "Yanzu dan ki ci mutuncina kika je kika kira ni idan irin wannan muzanci naki ya tashi kar ki kuma kira na."
Ta mike ba ko waiwaye ta fice. Na share hawayen da suka zubo mini na wuce kitchen ina jin fadan Engineer da matarsa kaca-kaca ya yi mata wulakancin da ta yi masa a gaban yayarsa ita kuma ta ja ta tsaya kan ba abin da ta yi tana kan hakkin ta.
A kitchen ɗin ya same ni ta baya ya rungume ni sai na fashe da kukan da nake rikewa duk kuma yadda ya so na yi shiru na dage kan gidanmu zan koma ni ba zan iya zama da Jari ba.
Da ƙyar ya lallaɓa ni muka koma ɗaki har dare yana tattashi na sai ga tuwon dare an kawo mini daga sasan Yayansa da yake tare suka zo da Yaya Atika, kadan na ci bayan na yi sallah na zuba wanka da kwalliya sai sheƙi nake ya ja ni muka koma falo, zaman mu ke da wuya sai ga Jari ita ma cikin kwalliyar take ga kunshi na zuba sheƙi kafa da hannu.
"Ina ta jiran ka Engineer."  Wani kallon tsanaki ya yi mata ya ce "Ina zuwa." Ba ta tafi ba zama ta yi, ni kuma tana zama ina mikewa na tafi daki ina samun kaina da matsanancin takaicin ta, na abin da ta yi mini yau gaban yaya Atika da kuma wanda ta yi mini jiya na cewa ni ce na yi ma Engineer asiri.
Kayan jikina na soma cirewa na mayar da na barci na zauna bakin gado ina karanto ayoyin ƙarshe na suratu Hashr sai ga shi ya shigo, kallo daya na yi masa sai na mayar da kaina ƙasa ya tako gabana ya zauna ya sa ni a jikinsa ya rungume ni, kiss ya fara mini kafin ya saurara "Allah ya yi miki albarka Allah ya ji kan Halisa. Na gode bisa ɗawainiyar ki gare ni ki yi haƙuri zan je dakin yar'uwarki ba don ban son kasancewa tare da ke ba sai don na sauke hakkin da ke kaina. Dan murmushi na yi duk da kishin da na ji ya taso mini ba ya gama saki na ba ne na ce "Sai da safe." "A'a har da kora." Na girgiza kai  "To ki yi mini rakiya. "
Rakiya ta da ya nema ta sa na gane ta tafi, ya sake ni sai na bi bayan shi kafin mu kai kofar ta na yi mishi sai da safe na juya har kuma sai da na buɗe kofata ya shige. Na daɗe barci bai dauke ni ba ina juya zama na da Jari kafin na yakice komai na shiga barci.

Ranar barci na yi har da makara don yaushe rabon da in samu barci kamar na ranar? Tare suka shigo shi da Salahu zai wuce kasuwa, muka gaisa Salahu ya fita shi ma bai jima ba ya koma wurin Jari.

Ranar samun lafiyar Engineer ta watsu ko'ina yan'uwa da abokan arziƙi suka yi ta zuwa duba shi har dare cikin su har da Ammi babana da yan'uwana.

Mun yi ta fama da jama'a har aka yi kwana goma yaya babba kuma ya yi kokarin rufe zancen wanda ya yi ma Engineer wannan abu.
Ya tara mu ni da Jari za mu ci gaba da yin girki tare kamar yadda muka saba kafin ya kwanta jinya.
Store din a tsakar gida yake akwai key hannun kowaccen mu ranar girkinta ta shiga ta ɗebo abin da take bukata Jari ta ɗauki almajiri mai taya ta aikace-aikace. Matsalar da na fara fuskanta da ita abinci kaɗan da take ba ni a ranar girkinta, ban damu da wannan ba kasantuwa ta ba mai cin abinci da yawa ba.
Inda matsalar ta fara ranar da na yi baƙi yayyena kasa fito da dan abincin da ta bai wa almajirinta ya kawo mini na yi na ɗauki key ɗin store na je na bude na debo abin da nake bukata zan fito ta faɗo kamar an jeho ta  "Lafiya? Na dube ta don ban gane tambayar ba  "Kika shigo store ba ranar girkinki ba."
Na girgiza kai  "Baki na yi su zan dafa ma wa kai kawai ta kada ta ciro wayarta jin mai gidan ta kira har zan wuce sai na dawo ƙara ta ta kai ta yi girki kuma don barna na zo na bude store na ɗebi wani abincin.
Na raɓa ta gefen ta na wuce.
Na dora girkin na dawo na zauna cikin su ana hira kiran Engineer ya shigo wayata na tashi na shige bedroom na amsa kiran tambaya ta ya yi me ya sa an yi girki na kara girka wani? Na ce Baki na yi ya ce na tambaye ta ta ba ni wanda zan ba baƙin? Na ce a'a ya ce to na kula bai son ɓarna, daga yau kat na ƙara yi masa haka.
Na ce to na dawo wurin su zuciyata ba daɗi.

Da ya dawo ma sai da ya yi mini faɗa na kara ba shi haƙuri tun daga nan idan na yi baƙi ranar girkinta sai dai na saya musu lemo ga ni yar dangi ina kuma cikin unguwar mu.

Wani dare Salahu ya shigo karbar wasu takardu Engineer ya ce in ba shi ya duba ya ba ni na ajiye mashi, abin da bai cika yi ba zaman falona in dai ba Engineer na zaune ba ya zauna yana duba takardun Jari ta turo almajirinta da abincina Salahu ya ɗaga ido ya dubi robar da barbaden abincin, na ajiye na ci gaba da duba wayata almajirin ya juya Salahu ya ce "Ina nawa abincin?
Yaron ya ce  "Yanzu zan ɗauko in kai maka."
Ya ce "Idan ka ɗauko ka kawo mini nan."
Ya ce  "To."
Ba daɗewa ya dawo da abinci ya ajiye gaban Salahu.
Da ya gama abin da yake nan ya bar shi har ya kusa ficewa na ce "Ka bar abincin." Ba tare da ya waiwayo ba ya ce "Ki ci."

Haka rikici ya balle tsakanin ta da Faisal yaron yaya Atika tun rasuwar mahaifinsa ya dawo Katsina da zama wurin Engineer. Korafi ya yi mata abincin da take ba shi ba ya isar shi ta ce ya je gidansu ya karasa koshi don ma ya samu shi ne zai kawo mata wata zakewar banza. Shi ma ya taso mata yana cewa gida na kawunsa ne, hayaniyar ta sa na leƙo Salahu ma da ya shigo gidan a lokacin ya yi ma Faisal ɗin magana kan ya wuce ita kuma ta ci gaba da maganganun ta tana cin alwashin sai ta raba shi da gidan.

Na yi girkina na kwana biyu ta karɓa ranar da za ta fita da yamma, motar Engineer na shigowa gidan tana fitowa daga falonta tana tsalle daga ita sai tawul  jikinta duk kumfa sai famar kuka take.
A kidime Engineer ya fito shi da Salahu suka yi kanta suna tambayar ba'asi, ni ma daga kitchen ɗina don yana saitin tsakar gidan ina kallon komai da karfi ta kara fasa kuka ta ce Faisal ne yake leƙa ta idan tana wanka bai ishe shi ba yau sai ga shi ya shigar mata.
Daga inda nake na ji gabana ya doka cikin matukar fushi ya ce ta koma ciki, ya nufi baya inda dakin Faisal yake wanda suke  tare da  Salahu na fito Salahu ya bi bayan shi da hannu ya janyo Faisal zai fitar da shi gidan na sha gaban shi ina kuka "Wayyo wayyo kar ka yi saurin yanke hukunci cikin fushi kar ka tozarta zumunci saboda mace."
Cak ya tsaya yana kallon irin kukan da nake Jari ta iso cikin zumbulelen hijab tana fadin  "Saboda ba ke a ka yi ma wa ba? Ni fa yarinyar nan ki fita mini ido  don ba ki ishe ni yi ba."
Banza na yi da ita na ci gaba da kukana musamman da na ga magana ta ta yi tasiri don da alamu jikinsa ya yi sanyi .
Ya saki yaron  "Amma ka sani ba zan ƙara zama da kai a gidan nan ba kana leƙa iyalina,  ka tattara kayanka ka koma gidan yaya .
Ya tasa shi zuwa dakin ni da Salahu muna tsaye cako-cako har suka fito da jakar kayansa, ya rataye wasu a kafaɗa. Ya mike hanyar bangaren Yaya babba duk da ba sa nan suna Kaduna.
Juyawa kawai na yi na shige falona na sanya tafukan hannayena na rufe fuskata hawaye na zuba me ke damun maza kan abin da mace za ta fada masu ba bincike ka ci zarafin ɗan yar'uwarka? Na tausaya wa maraicinsa da ya ja ma wannan yaro da yanzu yana gidan ubansa.
Ban ji shigowar Salahu ba sai maganarsa na ji daga kofa "Kifi ne ya ce ki gyara masa idan Allah ya kai mu gobe zan fita masa da shi kasuwa."
Na janye hannayen fuskata sharkaf da hawaye na miƙe sai ya juya.

Washegari bai fita kasuwa ba sai da aka sauke bulalluka da yashi ma'aikata suka shiga aikin katange tsakanin gidansa da na yayansa.
Da ya shigo dakina yana ta faɗa mini korar shi ya so ya yi ya za a yi ya keta masa alfarmar iyali?
Da kyat na roki ya bari ya dinga shigowa karbar abinci ya ce iyakar shi tsakar gida. A ranakun girkina ina zuba mishi abinci a wadace.

Ranar wata Asabar na faɗa wa ogan shinkafar mu ta ƙare haka ma taliya, ya ce idan ya fita zai aiko da ita.
Hakan aka yi kafin lokacin tashin shi ya aiko Salahu ya kawo.
Washegari Jari ke da girki ina kitchen na hange su ita da shi sun shiga store ba su jima ba suka fito tana riƙe da roba da ta ɗebo abinci tare suka fita da shi bayan ta kammala girkin don ba ya fita da wuri a ranakun ƙarshen mako.
Da daddare ma tare suka shigo ya shiga dakina yana tuɓe kaya muka ji maganar ta  shi ya leƙa ta ce an kwashe shinkafa a store ya ce wa ya kwashe? Ta ce "Dazu ai da kai muka shiga na nuna maka inda bera ke hudawa yanzu ina shiga ba rabin shinkafar taliya ma ba ta fi rabi ba.
Ya ce "Mu je."
Suka tafi na bi su a baya.
Kamar yadda ta ce an kwashe ni kawai na ga yana kallo bai kuma ce mini komai ba sai da muka kwanta ya tambaye ni ya aka yi da abincin na ce wallahi ban sani ba ni ko wurin ma tun da suka fita ban je ba..

Tun daga nan sai aka mayar da ɗabi'ar kwashe abinci ta zama jiki, ni kuma da ya kare ni zai ma faɗa.
Ranar da ya yi mini fada sosai har yana fadin ban da kimar iyayena da yake gani da ya tura ni gida an yi mini faɗa. Durkushewa na yi a falo ina sharbar kuka Salahu ya shigo ya same ni kudi kawai ya ajiye mini ya ce "Ki ƙara haƙuri sai ya juya ya tafi.
Tun daga nan a  duk ranar aikin Jari zai ba ni abu a boye nama ne ko kifi ko kayan marmari.
Na yi matuƙar sanya abin a raina hakan ya ja na fara ramewa ina ganin ko ramar tawa ya sa yake kawo man, ban taba sanin Jari ta sani ba sai da ta hado mana bomb wurin Engineer bai yi ma Salahu magana ba sai ni ya yi ma kashedi kala-kala ya ce ya  yanke kowace irin alaƙa a tsakanin mu.

Ban gano inda abincin mai gidan yake tafiya ba sai wata rana ina kwance a daki ana tabka uwar rana ga babu wuta sai na yanke in watsa ruwa na miƙe ina tuɓe rigar jikina idona ya yi kyakkyawan gani a get ta window na, kanen Jari ne da alama tuntuɓe ya buga jakar bagco da ke kansa ta faɗo  shinkafa da taliya sun zube, cikin gidan ya juya ya shiga ina tsaye har ya dawo tare da Jari, ita ta kwashe komai waige-waigen da take ya ƙara tabbatar mini ba ta da gaskiya ita ke kwashe abincin kenan sai ta ɗora mini zargi .
Ina tsaye har yaron ya tafi ta koma ciki, sannan na shiga wankana na fito na kwanta a falo a ka yi sallama daga kofa na gane muryar Aunty Naja ita ce ta farko a ɗakinmu na tashi zaune ina murmushi har ta shigo na mike na kwanto yaron da ke bayan ta sai na nufi kitchen na fito da ruwa ina gaishe ta ta amsa na tambayi daga inda take ta ce Asibiti ta fito shi ne ta biyo ta duba ni kwana biyu.
Na yi murmushi ta ce  "Na ga duk kin rame Nana Asma'u ko ciki ne? Kaina na sunkuyar don zancen ta na karshe.
Muna hira zuciyata na can ga tunanin abin da zan ba ta, muna nan zaune almajirin Jari ya kawo mani abinci, na dauko kudi na ce ya karbo mini lemo mai sanyi.
Na sanya cokali a flate ɗin abincin da aka kawo mini na ajiye gabanta sai na zauna kusa da ita ina dibar abincin ina ba yaron na ce "Ki ci Aunty."
Ta sauke hannunta daga tagumin da ta yi ta ce "Idan na cinye ke kuma fa? Na ce  "Zan  je ta ba ni wani."
Ta ce in je in karɓo.
Na tashi jiki ba karsashi na fita zuwa kofar Jari na kwankwasa ta ce daga ciki  "Abincin ka na nan a waje na faɗa maka za ka dame ni da kwankwashe-kwankwashe ." Na ja ajiyar zuciya na ce  " Ba Abbati ba ne ni ce."
Dan shiru ta yi kafin ta ce "Ya aka yi? Na haɗiye yawun takaici na ce "Bakuwa na yi ki ba ni abinci in ba ta." "Ni ban yi abinci da baƙi ba." Amsar da ta ba ni kenan na juya cikin sauri na koma inda na fito.

Na samu ya kawo lemon na zauna ba karfi sai na shiga buɗe mata "Ki sha Aunty. " Na fadi da son share zancen karɓo abinci da na je.
Amma sai ta ƙi karɓa "Ina abincin? Ta tambaya "Ta ce ya ƙare. " Ta ja mumnunar ƙwafa "Kishiya kishiya! Shi ya sa bayan an ɗaura aurenki ya ce ya yi aure muka yi bakin ciki ba ɗan kaɗan ba, ina za ki iya da wannan matar ba ma budurwa ba bazawara. "
Hawaye na ji sun balle mini na yi ta zubar da su tana lallashi na karshe na ba ta labarin halin da nake ciki da ganin da na yi ta bayar da shinkafa. Ta ce  "Idan ba ka iya kama barawo ba sai ɓarawo ya kama ka, yanzu kar ki fada mishi ki yi ta fakon ta har ki kama ta tun gaban ta ki kira wayarsa ko ki yi mata vedio.
Na ce "To." Ba ta ci abincin ba lemon kawai ta sha ta sa ni sai da na ci abincin nan ta kara mini da shawarar a ranakun gitkina in dinga dibar abinci da yawa ina dafawa ranar da ba ni da girki in daina zama da yunwa.
Na ce "To."
Na ji dadin shawarar Aunty Naja ban kara samun mas'alar abin da zan ba baƙi ba a ranakun girkin Jari har aka zo ranar da dubun ta ta cika.