BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

Chapter 5

by @narrnarhhbukar00

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

Narrnarhh Bukar

(Lady with the Amazing pen ✍️)

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

005

A hankali ta cire nonon daga bakin Hamid ta gyara rigar sannan ta miƙe. Saɗaf! Saɗaf! Ta shiga takawa tana ɗage dugaduginta sama har ta isa ƙofar ɗakin Mairi. Isarta ke da wuya ƙofofin kunnuwanta suka tsinkayo mata furucin da ya kusa zautar da ƙwaƙwalwarta da sauya farincikin da take ciki zuwa baƙin ciki. A ranta ta furta 'Kutumar dumadu! Idan na yarda na mutu a kafira' a zahiri ta natsu sosai tana sauraransu.

A cikin ɗakin Mairi,su Dauda Imamu da ba su san da wanzuwarta ba suka ci gaba da hirarsu cike da shauƙi.

''Kin ga idan na dawo daga Kaduna na san lokacin Sahura ta dawo daga arba'in. Sai ki je Mada wurin 'yan'uwanki ki yi musu sallama , idan kin dawo sai na tafi da ke can Kaduna ita kuma Sahura na sakata Islamiyya,tana da rauni sosai a kan abin da ya shafi addini, bagidajiya ce ta karshe wallahi babu abin da ta sani sai tsaigumi. Mtsss!''

''A'a Baban Yasir ka yi mata uzuri, zai iya yiwuwa a can bata samu damar zuwa islamiyar ba ne''

Wani irin kallo ya yi mata kasancewar akwai wutar lantarki a ɗakin sannan ya ce

''Kar ki manta Kawuna Kabiru ne mahaifinta, daidai gwargwado yana tsawatarwa a kan karatu, na rasa ta ya ya Sahura bata da ilimin addini. Sai ka ce mai ƙwaƙwalwar tunkiya!. Haba don Allah! Babu abin da ta sani sai yawon bin gidajen maƙota. Zan saka a bi mini duk motsinta,idan na zo a sanar mini. Za ta sha mamakina idan bata sauya halinta ba''

Mairi bata ce komai ba,domin bata gyara ba, ba za ta yi silar lalacewar ba. Haƙuri ta ba shi a kan dare ya yi ya kwanta gobe da wuri za su tafi, amma ya ƙi ta inda yake shiga ba nan yake fita ba. Kwanciyarta ta yi ta ƙyale shi, da ya gaji don kansa ya kwanta. Tas! Kunnuwan Sahura suka ji komai, rai a matuƙar ɓace ta koma ɗakinta. Allah ya sa har ta koma Hamid bai farka ba. Zama ta yi saman gadon tare da kafa uban tagumi. Ita Dauda Imamu zai keɓe da kishiyarta suna cin dunduniyarta. A gaban maƙiyarta yake aibanta ta,ai ko bata faɗi mummunar magana a kanta ba,zuciyarta ta ji daɗi kuma ta yi nasara. Farincikinta guda gobe za ta koma kusa da uwarta duk mai yiwuwa a yi,don ba za ta taɓa barin Mairi ta koma Kaduna da zama ba. Ta san mahaifiyarta za ta iya yin komai a kanta, in har zai samar mata da farincikinta. Dole ya je da ita Kaduna,ta yi zama na dindindin a can. Zamewa ta yi ta kwanta tana rufe idanunta amma bacci ya ƙi yi mata sallama. Buɗe idanun ta yi ta kafe wuri guda da ido. Ta daɗe idanunta a buɗe daga bisani bacci ya ɗauketa.

Washegari da sassafe Mairi ta taimaka ma Sahura ta yi wanka kafin ta gama shiri ta yi ma Hamid wanka ta shiryasa. A gefe guda Dauda Imamu shi ma ya yi wankan.Da yake Mairi bata koma baccin safe ba,sai ta dafa musu ruwan wanka da na shayi,daman a daren jiya Dauda Imamu ya siyo biredi saboda sammakon da za su yi. Bayan sun kammala karyawa Mairi ta rakosu zuwa ƙofar waje tare da addu'ar Allah ya tsare hanya ta koma ciki ta yi kwanciyarta ita da Jalil. Shi Yasir ma bai farka ba. A motar mijin 'yar ƙuda za su yi tafiyar. Tun daran jiya ya shirya da shi. Sai da ya tsaya tasha ya cika motar da fashinjoji sannan suka nosa hanya. Sai wurin ɗaya suka iso Sakkwato daga nan suka yi tashar 'yar ƙumbula har garkar Bala fari mai fata cikin ƙofar kaɗe daidai shiyyarrsu(gidansu). Sun iso lokacin mutane na haramar shiga Masallaci sallar azahar. Kai tsaye Dauda Imamu ya wuce masallaci,ita kuma Sahura ta shige ciki yaran gidan maza da ke waje suka tayata shigo da kayan ciki. Ɗangwas-ɗangwas ta shiga takawa har sashen mahaifiyar tana ma 'yan gidan yanga wai ita ala dole an zo gida wanka. Sai wani ɗaɗɗaga kai take tana amsa gaisuwarsu  ciki-ciki kamar an yi mata dole. Hali zanen dutse,domin barewa bazata yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba. 'yar gwaggwan bugaje ce fa! Macen da ta zamo tamkar miji a gidan,ita ke tsara komai kuma dole a bi. Mugunta, hassada da ƙeta su ne manyan ɗabi'un da take amfani da su wurin juya akalan gidan har da mai gidan. Babu wanda yake jin daɗinta a gidan idan ka cire yaranta da jikokinta wanda su tamkar ƙwai haka take ririta su. Duk rashin kunyar da jikokinta suke mata bata gani sai na sauran jikokin gidan. Kasancewar shiyyar(gidan)babba ne sosai mai sashe guda huɗu. Sashe uku na matansa sai ɗayan ya zama turakan Miji. Sashen da yafi girma shi ne na gwaggwan bugaje wanda a da na uwar gidan ne Tsahara kasancewar tana da yara sosai. Bayan gagarumin tsubbun da gwaggwan bugaje ta yi ma duka 'yan gidan sai ta dawo sashen,Tsahara ta koma nata sashen. Tun kafin Sahura ta iso sashensu gwaggwan bugaje ta fito, da yake jikokinta sun ga saukansu daga 'yar ƙumbula. Sai suka dawo da gudu suka sanar mata. 'yar kimanin shekara arba'in da biyu ce ta fito daga ɗakinta,fuskarta ɗauke da yalwataccen murmushi wanda ya ɓoye girman da ya fara cim mata. Suna matuƙar kama kwabo da kwabo da Sahura har gajartan nasu ya kusan zuwa ɗaya. Ga uwa-uba halinsu da yake kamanceceniya,daman hausawa sun ce magaji mafiyi, Sahura ta zarce uwarta a iya sauya halayya tamkar hawainiya. 

''Maraba lale marhabin da Uwata ta kaina!" Gwaggwon Bugaje ta faɗa murmushinta na ƙara faɗaɗa. Martanin murmushin Sahura ta mayar mata har fararan haƙoranta na gaba na bayyana. Rungume juna suke yi tare da shigewa cikin ɗakin. Zama Sahura ta yi a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin. Babu abin da ɗakin ke tashi sai sassanyen ƙamshin turaran tsinke. Duk da ɗakin babu ledar ƙasa amma za ka iya kwashe tuwanka idan ya zube ka cinye,tsabar yadda simintin ɗakin ke ƙyalli saboda guga. A Hankali Sahura ta ciro Hamid da ke 'yan mutsu-mutsu a baya ta fara shayar da shi. Gwaggwon Bugaje kallon ɗiyarta take cike da so da ƙauna. Duk a yaranta babu wacca take jinta a rai matuƙar ainun kamar Sahura. Ruwan randa mai sanyi Gwaggwan bugaje ta sa a kawo mata. Sai ta umurci wata daga cikin jikokin Tasallah amaryarsu kiran Tsahara. Babu jimawa sai ga Tsahara ta shigon ɗakin jikinta na tsuma. Mummunan kallo gwaggwan bugaje ta watsa mata sannan ta ce

''Ina geron da malam ya raba ya baki naki?" Gwaggwon Bugaje ta tambaya tana kafeta da daƙwa-daƙwan idanunta farare ƙal! Cikin rawar murya kamar yarinya Tsahara ta ce

''Yana nan Mai babban ɗaki''

''Ki auno tiyya guda ki yi ma Uwata dawo(fura), bana son kowa ya yi aikin sai ke. Kar ki tsaya ɓata lokaci saukanta kenan daga mota. Ba a wasa da cikin mai jego,don haka maza ki hanzarta tana jiranki''

Gwaggwan bugaje ta faɗa tana sake binta da kallon ƙasƙanci. Jinjina mata kai Tsahara ta yi tare da barin ɗakin jikinta bai bar kakkarwa ba. Sake aikan wani jikan ta yi kiran amaryarsu. Ita ma kamar Tsahara jikinta na rawa ta iso ɗakin a sukwane. Kallon ƙasa da sama ta yi mata sannan ta ce

''Ki ciko ma Uwata galar (awarar) da kike soyawa na kasko yanzu,ki saka Ladiyo ta tatso mata nono zan dama mata fura idan Tsahara ta gama dawon''

''An gama mai babban ɗaki'' tana faɗin haka ta bar ɗakin. Wani irin girma kan gwaggwon Bugaje ya yi jin yadda kishiyoyinta suke mata biyayya tamkar za su bauta mata. Hakan yana matuƙar ƙara daɗaɗa zuciyarta da sakata sake yin ƙanƙan da kai ga bokanta da tukunyar tsafinta. Farinciki mara misaltuwa ke rangaji a zuciyar Sahura,yadda kishiyoyin mahaifiyar suke yi ma Gwaggwonta yana matuƙar birgeta,tana fatan ita ma nan kusa za ta fara juya kishiyarta da mijin yadda uwarta take yi.

''Ya kishiyar taki,fatan dai baki samun matsala da makirar ko?" Gwaggwon Bugaje ta tambaya tana dubanta. Tabe baki Sahura ta yi tare da cije leɓanta na ƙasa kaɗan tana cire nonon daga bakin Hamid don ya koma bacci ta ce

''Ai Gwaggwo bari dare ya yi za ki sha labaran kayan takaicin da nake wanka a gidan Yaya Imamu.''

''Hmmmm! Ai ya zo ƙarshe. Daman ina so da zarar kin zo yawon arba'in za mu san abun yi. Tun da kin zo yanzu faɗuwa ta zo daidai da zama. Kawo mijina Hamidudu na ganshi''

Mikewa Sahura ta yi zuwa inda Gwaggwon Bugaje take zaune ta mika mata shi. A hankali ta amshe sa tana murmushi. Jakar da namanta ke ciki Sahura ta buɗe ta ciro ledar naman ta ajiye ma Gwaggwan bugaje a gabanta.

''Mene ne wannan?'' ta tambaya

''Naman sunan ne. kasona da ban gama cinyewa ba na taho da shi...''

''Assalamu Alaikum. Mai babban ɗaki ga shi in ji Inna Tasallah ta ce na kawo''yar matashiyar yarinya ta faɗa tana katse maganar Sahura. Samira ne rufe ta ajiye gaban Sahura sannan ta juya da sauri tun kafin Sahura ta ce wani abu ta bar ɗakin. Don tasan  kaɗan daga cikin aikinta ta ranƙwasheta haka nan don jin daɗi. Buɗe samirar ta yi, lokaci guda ƙamshin soyayyan awara ta daki ƙofofin hancinta. Lumshe idanu ta yi tsohuwar yunwanta na tasowa gadan-gadan. Ba jira ta shiga antaya awara cikinta har ta yi nak ta sha ruwa sannan ta haye gadon mai rumfa tana gyatsa.

''Gwaggwo amma yau ba za ki turaka ba ko. Tare za mu kwana"

''Ina ni ina zuwa turaka ga 'yar lu'u-lu'uta ta zo,zan dai zaɓi ɗaya daga cikinsu Tsahara wata ta je'' Gwaggwon Bugaje ta faɗa cike da alfahari. Tun bayan hatsabibiyar mallakar da ta yi ma kishiyoyinta da mijin ta koma kwana turakar mijin ita kaɗai. Sai a yi wata sama da biyu Tsahara da Tasallah ba su taka ƙafarsu zuwa Tukarar ba. Sai ranar da Gwaggwon Bugaje ta mulla ta mulle take zaɓar wacce za ta kwana. Har godiya wacca aka zaɓa take mata. Ƙaramin gado gwaggwon Bugaje ta kwantar da Hamid sannan ta fita daga ɗakin zuwa sashen Tsahara don ganin ita take aikin ko wani ta ba daga cikin jikokinta su yi dawon. Sahura kuma bacci mai daɗi ya ziyarceta tare da tafiya da ita duniyar mafarki.

^^^^^^^^^^^^^^^

A ɓangaren Dauda Imamu bayan sun kammala sallah sai ya tsinci dami a kala. Kawunsa Malam Kabiru ya yi tozali da shi lokacin sun fito daga Masallaci. Wuri guda suka keɓe sannan ya gaishesa tare da sanar masa aikin da ya samu. Sosai Malam Kabiru ya yi farinciki, don tamkar ɗan da ya haifa a cikinsa haka yake jin Dauda Imamu a rai. Duk da yana da yara maza har bakwai,babu wanda yake jansa a jiki irin Dauda Imamu. Domin daidai gwargwado Dauda Imamu na kyautata masa. Duk zuwan da zai yi sai ya ba shi kyautar kuɗi. Haka idan ya yi noma sai ya ware nasa kason ya taho masa da shi,har da Inna Salame yana mata alkhairi. Awarar da Tasallah ke sayarwa a gida Malam Kabiru ya aiki aka siyo masa. Babu jimawa ɗan saƙon ya dawo da samira a hannu. Yana ci suna hira da Malam Kabiru har ya kammala daga bisani ya miƙe tare da yi masa sallama ya nufi shiyyar (gidan)Inna Salame. Zuwa gobe yake son dawowa Zamfara,don ya samu cikin satin ya je Kaduna. Da yake gidan Inna Salame babu nisa da gidan yayanta Malam Kabiri,cikin mintuna ashirin ya isa gidan. Da sallama a bisa laɓɓansa ya shiga ciki. Fitowarta kenan daga ɗaki ta shimfiɗa tabarmar kaba don ta sha iska. Cike da kulawa ta amsa masa,fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi. A saman tabarmar ya yada zama yana gaisheta cike da girmamawa. Da murmushi kwance a fuskarta ta ce

''Lafiya lau Dauda,ya mazaje na. Fatan ka zo lafiya. Ya me jegon?" Ta karashe ta tambayarsa. A russune ya ce

''Ai tare muka zo. Gwara ta yi wankanta a nan idan ya so bayan arba'in sai ta koma''

''Maa shaa Allah. Ka yi tunani mai kyau kuwa. Sai na je ganin mijina. Asama kawo ma yayanki fura''

''A'a Inna a ƙoshe nake,sai dai ko zuwa an jima. Na ci gala(awara) wurin Kawu'' ya faɗa yana gyara zamanta.

''To shikenan'' Shiru wurin ya ɗauka. Can Dauda Imamu ya ce

''Daman Inna na zo sanar muku na samu aikin karantarwa tare da limanci a babban masallacin da ke cikin barikin sojojin sama na Kaduna.''

''Alhamdulillahi! Ai kuwa na tayaka murna! Allah ya sanya alkhairi''

''Ameen  Inna'' Hira sosai suka ci gaba da yi. Inda a nan Inna Salame ta tambayi ya zamansa da Sahura fatan babu wata matsala. Bai faɗi aibun Sahura ba duk da yasan tarin matsalolin da take da shi. To aikin gama ya gama tun da dai yanzu matarsa ce,dole ya rufe wani sirrin. Duk da ba ya samun matsala da ita wurin biyayya,har abokiyar zamanta ba su samun saɓani,daidai gwargwado sun fahimci juna. Shi dai matsalar shi da ita bai wuce abu ɗaya zuwa biyu; rashin ilimin addininta da kuma shiga maƙotan da take yi hakan nan. Bayan haka bai ga wata matsala a tattare da ita ba,sai dai idan daga baya ne za ta ɓulle da wasu matsalolin. Sun jima sosai suna hira har wurin sallar Asr. Sallama suka yi don sammako yake son yi gobe. Cike da daɗin rai suka rabu bayan ya ajiye mata kuɗi a gefe.

Bayan sallar Asr ya shiga cikin gidan,ya bi sashen matan kawunsa ya gaishesu inda a karshe ya yada zango a sashen Gwaggwon Bugaje. Cike da farinciki da tarbesa. Furar da ta dama ma Sahura ta ɗebo masa a ƙwarya da ludayi. Ya sha kaɗan sai ya amshi Hamid yana masa wasa. Ba su yi wata hira ba saboda sirkuntar da ke dabaibaye da su ba kamar a da ba. Ya jima a ɗakin daga bisani ya miƙe tare da ajiye ma Sahura kuɗi a gefe ya ce idan tana da buƙatar siyan wani abu,don asubanci zai yi gobe,ba lallai su haɗu ba. Godiya sosai ta yi masa sannan ta rakashi har ƙofar sashen suka yi sallama ta dawo ciki.

Bayan ta dawo sai ta iske Gwaggwon Bugaje na ƙirga kuɗin tana murmushi. Ranta fal! Da farinciki

''Kina samun irin wannan silallan! ina ga mun mallake shi,ai ta aljihunki kuɗin zai dinga fita.Kin ga yanzu mun samu wani kaso na zuwa wurin Boka Ataka. '' Gwaggwon Bugaje ta faɗa tana ɗaga fillonta ta ajiye.

''Kamar kin shiga raina Gwaggwo. Tunanin da na yi kenan. Idan ya san wata ai bai san wata ba.'' cewar Sahura tana hawa saman gado mai rumfa ta yi kwanciyarta. Gwaggwon Bugaje kuma ta zari mayafi ta bar sashen.

BAYAN ISHA'I

Zaune matan suke a farfajiyar gidan da yaran gidan. Gwaggwon Bugaje na gefan malam yana cin abinci tana ba shi labari har ya gama. Sauran matan da yaran gidan suna harkokinsu a gefe guda. Kai ka ce Gwaggwon Bugaje ce kaɗai matarsa. Hamid na riƙe a hannunta,bayan ya kammala ci ne ya amshesa. Sahura ta koma ɗaki bayan ta gaishesa. 'yan koke-koken da ya fara yi ne,sai Gwaggwon Bugaje ta sa aka kai shi wurin mahaifiyarsa. Gyara zama ta yi tana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

''Tsahara!Tasallah! Ku matso ina da magana da ku! Sannan yaranku su koma ɗaki don maganar bata shafesu ba.'' Ta yi maganar cike da gadara da tsantsar iko.Kafin ta sauke lumfashi sun kaɗa yaran da jikokinsu ciki sannan suka matso inda take da Malam jikinsu na tsuma. Malam dai na zaune kamar hotiho sai abin da ta ce yake yi. Sai da ta ɗan ja 'yan wasu sakanni tana karkaɗa ƙafa sannan ta buɗi baki kamar an yi mata dole ta ce

''Yau a sashena zan kwana saboda ina son keɓewa da ɗiyata mu tattauna. Don haka zan zaɓi ɗaya daga cikinku, wacce nake ganin ya dace ta....✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***