ABUNDA KE 'BOYE...

13

by @surayyahms

ABUNDA KE BOYE..1️⃣3️⃣
ruwa akeyi sosai amma bashine yahana jama'ar kauyen majiya tahowa gidan juma kwansu da kwarkwartansu dan sugane ma idanunsu abunda ke faruwa da yayan juma ba. hatta wazirin sarkin buzaye saida aka dagosa da lemansa dan yazo yagani yakai rahoto gaban sarki...

agaban kabarin inayah inda suka gama shushhure mata kasa aka tayar da wani sabuwar hayaniya tsakanin fulani da buzaye, kowanne kabila tana kirga a wanne bangare ne akafi samun abun kunya, inda atake wazirin sarkin buzu cikin izza yake nunawa jama'a cewa dolene kawai juma ya amshi lefinsa snn ya tashi tsaye ya cigaba da daukar tsatsauran matakai akan iyalansa domin kare martaban al'adarsu da mutuncinsu na buzayen majiya, saƙo na farko da sarkin buzaye ya aiko shine marmaza akawo masa juma da yarsa ayanah a fadansa agurfanar da ita, snn a aurar da ita ma almajirin gonan sarki ayau dinnan sabida gujewa afkuwar wani sabon abun kunyar, ko kuma juman ya tattara inashi inashi da yarsa yanzun nan subar garin majiya batare da ya dauki komi daga arzikinsa ba wanda bakaramin tashi hanklin juma yay dajin wann babban maganan ba..

duk dama cikin yayansan duk yafi tsanar ayaanah aransa, amma gani yake kamar daya aurar da ita wa almajirin gonan sarkin buzaye gara kawai ya tsine mata tabi duniya ko ya bada ita kyauta ma kafurai,bisa
a'ladan kauyen babu wani tozarci da kaskanci dayafi ace maka yarka tana auren almajirin gonan sarki, lamari ne babba me shaqe da rayuwar kaskanci, dan muddin almajirin gona ya aure mace no matter how minor she is koda yar kasa da 10yrs ne,toh uban gidansa ne zai soma saduwa da ita kafin nan mijin shima ya sadu da ita, haka zasuyi ta passing passing da ita har iya karshen rayuwarta,iyaka hatsin gona ne zasuna bada ubanta kowani wata amma ko sadaki bazasu biya na auren ba.

bisaga al'adansu haka abun yake tun tun kaka da kakanni shiyasa kowa a kauyen baison ace wani qaddara ya fadawa yarsa ta aure almajirin gona dan kmr babban purnishment ne da ake bawa mace dan a kaskantar da rayuwarta na har abada bisa wani leifi data aikata ko iyayenta suka aikata.

tunda aka sanar wa juma abunda sarkin buzaye yace akan yarsa ayaanah aka fara tada hayaniya da shi agaban kabarin dayan yarsa inayah.

tsawa da kuma hayaniyar mutanen da suka binne gawar inayah ata bayan gidansun shiya soma farkan da ayanaah daga doguwar suman datayi, A mugun razane ta farka rike da kirjinta dayaketa bugu kamar zaifita bakinta dake ɓari na dauke da kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun ciwon zuciyarta sosai yake son ya tashi da karfinsa saidai wnn mental shock da surpressed survival mode din datake ciki ahalin ynxu shi ya hanashi nunawa, mikewa tsaye tay arikice dabataga gawar inayan akusa da ita ba cikin tsananin razana ta kara fashewa da kuka cikin mugun rauni ta rike kanta dake mata juyayi Wani irin runtse idanunta tayi tana kukan me cike da zafin mutuwar yar uwarta wanda yana tahowa ne da radadi tana ji kamar bazata taɓa iya rayuwa babu addanta inayah a duniyan nan ba,cikin yanayin tsumayi take kukan, koinanta na rawa rawa da alaman cewa tana cikin yanayin tsananin fushi, rauni, da tashin hankli.

acikin ranta addua takeyi na neman teimakon Allah musmn daga alkaryar wannan mummunan qaddara dayake shirin tunkarosu, duk saukar numfashinta acike yake da uban nishi mai mugun tada hankali da kada ruwan ciki dayake biyo baya..

tanacikin kukan tafara tsunkayo hayaniyarsu wanda sai a sann ta dawo cikin hayyacinta jikinta na rawa rawa ta iso har bakin windonsu inda hayaniyar yafi tashi din ta kasa kunnunwanta taji inda aka kai gawar addanta inayah dan itama taje..

mannuwa tayi abakin windon ta jingine babu abunda yake tashi face razanannen sautin muryan wazirin sarki yana tada jijiyar wuya yana zagin babanta agaban mutane tare da jadadda masa cewa bazasu bashi wani uzuri ba laifukan da ahalinsa suka aikata yay yawa, na farko yaransa sunje suna karatun kafirci (boko) aboye, na biyu matarsa taawure ta raina maganinsu ta al'ada takai yarsu inayah asibiti wanda tsabar tsanar asbiti da sukay shine suke kiran sa da "kangon kafuraye". na uku kuma yarsa ta mutu musu da cikin shege agari. dan haka, sukace.. baza ai masa wani uzuri ba, ko yabayar da yarsa ayaanah su aurar da ita yau, ko kuma a koresa agarin majiya batare da ya dauke kominsa ba kuma korace na har abada babu dawowa.

tamkar feshin wuta haka ayaanah ta dingajin saukar maganganunsun acikin kunnuwanta, jin duniyar na juya mata, gata da ciwon raunin zuciya wani irin jiri ne ya kwasheta abazata dan batama san sanda tasake windon ta sulale kasa amugun takure tana kkrin cusa kanta a tsakankanun cinyiyonta ba maganan auren kawai ke dawo nata kai tsabar yadda zuciyarta yake bugawa da azaban tsoro yasaka ta cije takara ƙarfafa speed in fitar numfashinta dan kada ciwon raunin zucyar nata ya tashi mata aynxu..

cikin azama ta miƙe tsaye adaddafe bugun balai kirjinta yake sai diffff difff difffff diff numfashinta yakey dakansa yana sauka kamar wanda zai dauke gaba daya..

kara leka windon tay jikinta yadau tsanannin zafi hawaye masu tsananin rauni na zubo mata musmmn data kara zuba ido tanata kallon kabarin addanta rauni me yawa ya rufeta tanaji kamr wuƙa aka soka mata akan kirji.

tana kokarin dauke ido akansu kenan daga can nesa ta hango wani mutum dake kkri ya kalleta suna hade ido kuwa kafin yayi magana da wani damugun sauri ta tsuguna jikinta na rawa rawa atake taji kmr she need to act fast fast kawai de ji take kmr bazata tsaya akamata amata auren dole ayauba itakanta bata san daga ina wani irin karfi yazo mata ba da gudu tamike ta nufi can bakin kofa ganin da tayi kofar ya budu kadan ta leka waje tsakar gidan taga har yanzu babu wanda ya shigo ciki.

tafi mintina uku cikin tsananin tsoro tana tsaye tana ta kallon tsakar gidan ganin kamar babu motsin kowa anan yasata tayi mustering courage da kyar tacire tsoro tafito ahankli a hankli tana tafiya ruwan saman da akeyi na wani irin zuba na dukanta kirjinta na bugawa da karfi karfi kafafunta har suna sarkafewa danji take kmr bazatakai bakin zaurensu ba.

cikin tsananin rauni da tsoro har ta fito waje inda tanajin kanta asararin kofar gidansu bata tsaya ba ta saita hanyar jeji ta falfala da wani irin gudu kamar damisa ne ya korota..

gudu takey batare da ta juyo bayaba tana gudun tana rabza kuka tafadi kasa ta tashi, kai tsaye ta dauki hanyar anguwar tudu amma tacikin ciyawa dan tsabar tsoron karwani ya ganta daga nesa, haka tarinka bibiyar ciyawan jikinta na tsnnin rawa ciyawan yana mata rumfa tana zagaye cikin tsananin tsoro da fargaban kar akamata, gashi ko yar takalmi babu akafarta sai dankwali daya gama jikewa da ruwa


daga doguwar rigarta har doguwar yololon sumanta me shegen tsayi da tsantsi sun balain manne mata awuya da jiki, inda wani dan uban silky smooth natural beautynta yake haskawa bana kadan ba. cikin wnn yanayin ta rarrafa zatafito acikin ciyawar tasaiti hanya da zai sadata da hanyar tudu kenan tana qusa kai kuwa wani dan aikan sarki dake tahowa da lema yay caraf yaji motsinta

arazane ya koma baya da tunanin ko maziji ne aikuwa suna hade ido cikin daka mata tsawa yace keeee ayaanah fito nan dan bura ubanki shegiya ni zaki tsorata? amugun tsoroce mai tattare danyen taurin kai wanda bata taɓa sanin tanada irinsa ba ta shareshi batacemai uffan ba takoma cikin ciyawar da sauri sauri tafara rarrafawa aciki tana komawa baya tanaji yana ihun sunanta amma batako amsashi ba harsaida ta sabule ta fita tawani hanyar da bata taɓa saninsa ba..

haka mutumin ya ci nemanta acikin ciyawar da bai ganta sai yadauki dankwalinta daya samu akasa wanda agarin rarrafen ne ya zame akanta ya fadi batama sani ba. girgiza kansa yay ya wucewarsa da dankwalin yana sauri sauri ya isa wajen su juma dasauran mutanen dan ya gaya musu saqo snn yace musu yaga yarsa ayaanah ahanyar tudu zata gudu. bangaren ayanah kuwa tunda ta fice aciyawar gudu take da iya karfinta, bata ko juyawa. kuma ahalin ynxu bata san ina ta dosa ba sabida canza hanya datayi gudu ta dingayi har saida tay nisa taga ashe babu wani hanyar billewa gaba jeji baya jeji cike da karayar zuciya ta nemi wani waje tafadi akasa tanata rabza kuka me kara ruwan saman nan kaf dinsa akanta yaketa zuba taji tarasa abunda yake mata dadi..

tafi minti goma ahaka akwance daga can can nesa sai ta fara jin motsin kafafu can kuma taji muryan samarukan majiya suna tahowa suna ihuuu yadda suke tahowa yuuuu da alama dai an biyota ne za'a kamata.

arikice ta miƙe jiknta yana wani irin kar karwa sabida gabaki daya karfinta ya kare har tangal tangal take bata tsaya duban inane gaba ba kawai ta duru cikin jejin da sauri tadinga bin ciyawa tafadi ta tashi tanawani irin kukan tsoro, bata hankara ba wani irin mugun tsantsi me hatsari ya jawota phewwwww kamr iska sai jin kanta tsuuuuu tay tana tafiya akasa kamr ana janta amugun firgice ta tsala wani irin ihuuuuun razana sai ji tay tsantsin ya fettota kan hanya wani irin karan taka burki da wawan tsayuwar motar dataji a kunnunenta yasa atake tabi taja zuciyatta ta suma..


innalillahi wa inna ilaihi rajiun

cikin lunshe ido da budewa ibaad ya furta hakan da karfi ayayin daya bude lumshahen idonsa da suka tsaya cakkk dan bazai iya bayanin yadda yaga fettowar yarinyar waje daga jeji kmr an jehota acikin kiftawar ido ba.

cak ya tsaya yanakan salati baikuma motsa ba, dan shi ba mutum bane me saurin rudewa iyakan hannunsa dake rawa rawa akan stiring yasake da tunanin ko ya bugetane ko kuma karar gudun motarsan ne ya razanata, after like 3 scnds yabude motar yafito cikin tafyarsa mai kama da sauri sauri dan ruwa ake sosai, cike da jan aji gami da lura jin kirjinsa na matuƙar bugu ya karaso wajen ganin ashe motarsan baima taɓata ba yasa yaji sanyi aransa kasar wuyar sa ya furta hamdala snn ya mayar da hanklinsa kanta da sauri

wanda tun bekai ga tsugunawa  ba yahau kare mata kallo duk ya dauka ma tafi haka girma saiyaga ashe yarinyace karama jikinta tay futu futu da turbaya tabita dukunkune akasa asume da alaman kamr anjefota dan fuskrta kasa yake kallo tadan kwanta aringine acikin ruwan datti dake kasan hanyar duk turbayan data debo ya rufe mata kafafunta, yy tsammnin ko tafito wasar banza ne kawai na yara but something feel soo odd abt her, da niyyar masifa ya karaso kanta, ya tsuguna yanakai hannu yana taɓata kuwa tamugun firgita ta farfado a suman cikin dawo hayyacinta. kallonsa take a mugun tsorace kamar taga aljani dama can gata da mugun jin tsoron maza.

tsananin survival instinct post-traumatic stress da take fama dashi aynxu yasa tazama very scared nd alert, kota suma kana taɓata sai ta firgita ta farka a mugun tsorace, a cikin rauni da kasala take kallon kwayar idanunsa ayayinda idanun nata sukayi luiiiiii kmr zasu rufu baisan sanda yay sauri ya tallabota jikinsa ba gani dayay tana numfashi daddaya ga panic attack and palpitations nishi sama sama kmr zata mutu masa ynxun nan.

she was subconsiuosly a bit relieve dataga a hannun stranger ta farfado ba ahannun samarukan kauyensu ba, ibaad yana jira yaji tay magana amma sai shiru sai nishi, like she is figthing to breath...a daddafe ya tallabo fuskarta suna hade ido cikin wani iriyar baqon shauƙi ta damke masa hannunsa da karfin tsiya da sigar neman taimako tana kakalo iska daga kirjinta amugun wahale jin karfin ruwan dayake sauka akansu na karuwa harta saman kirjinta yana raunata mata gangan jikinta sosai.

shide tunda ya rikota jikinsa gabansa yaringa faduwa da wani irin balain ƙarfin bugu wanda bai san namene ba. the girl is too fragile nd beautiful to be termed a human being, gata yar karama kiris ya rage ya kawo aransa ko aljanace but she looks too real to be unreal, dan tsugunawar scnd biyu yy akanta ganin takasa dena kallonsa arude da alaman distorted confusion kmr batama sanda isowarsa ba wnd hakan ya kara ruda mai tunani

she looked so scared and in dire need of his help, tamkar yadda ruwan ke zuba akansu haka nan ruwan hawayenta yake zubowa ahannunsa datay ma mugun damkar karfi.

voiice dinshi adan ƙasaitance game da sake wata shakuarryar gyaran murya Yay tapping face inta ahnkli kuma cikin sauri yace "keeee...keee...ina iyayenki? daga ina kika fito, meya kawoki nan acikin ruwan nan?

jin yay magana sai ta kara razana dashi, duk abubuwan da suka faru na mutuwar addanta suka fara dawo mata kai a mugun firgice ta sakeshi zata mike tsaye ta arce da gudu jiri me karfi ya karo wainota jikinsa caraf kuma taji ya riketa, suka kara haɗe idanunsu waje guda jin wani irin electric shocking mai tsananin qarfi daya sarkafe su waje guda tanajin sassan jikinta yana kara ragwabewa da mummunan tsoro. kirjinta na tsananta bugu tanajinshi fat fat zucyarta yana racing yana daka tsalle tamkar wnda zai ballo waje..

wani azababben kuka ne ya kwace mata, tana kkrin kwace kanta ahannunsa danta gudu taga sam yaki ya saketa, cos he is trying to observe her, waiko kurma ce dan yaga numfashi kawai take iyayi dakyar bata magana shima numfashin datakejan dakyar take janshi waje...

ya dada rikota yace "nace ina iyayenki suke ko ke kurma ce? daga ina kika fito?? kina ji kuwa... tun be gama rufe bakinsa ba yaga ta kalleshi, snn ta juya ta kalli jejin ta fashe da wani irin tsoraccen kuka

daskarewa yayi a tsaye shima yana kallon jejin ransa yace kode kidnappers ne suka saceta ta gudu babu abunda baisaƙa aransa akanta ba.

gabaki daya saiyaji ya kasa samun karfin gwiwar barinta, she is soo young, gata da kyakkwar halittarta da kwayar idanunshi bai taba ganin irin sa ba, he was lost for a moment cikin rasa nayi da ita, first time in his life dayaji gabansa nq mugun fadi akan stranger gata karama sosai ta bashi tausayi,

hasken fatar jikinta dayake nan kamar an wankeshi da ruwan madara yay wani irin kyau wanda ya mugun tafiya da imaninshi yanajin dukkan tsigar jikinshi suna mimmiƙewa duk dama karamace but she sure loook absolutly sexy nd breathtaking barin ma da jikakken sumar kanta ya mammanu agefen wuyarta da kyakkwan fuskarta da wani jarababben diso dison ruwa daya salkafe kan labban dan ƙaramin pinkish lips dinta atake koinanshi ya dauka da wani irin rikitaccen yanayi mai tafe da wata muguwar azabar kokonton ko dagsken ita ba mutum bace.


,..itama dukkan kallonta zage ta ƙare masa ta rasa yadda zatayi dakanta sai uban rawa rawa da jikinta yakeyi tana kuka tabita tattara wuyar rigarta da sauri ta makureshi har wuyarta cikin jarumta, dan takwaco kanta da ga hannunsa tayi, tana shirin barin wajen da wani irin snyin kasaitacyar murya mai daskarar wa taji yace mata "suwaye suke binki? please tell me, ni zan taimaka miki kinji ko?? wani cak kukan ya dauke mata ta juyo tana kallonshi da sigar rashin yadda, dan shiru tayi tana shirin kufcewa taji ya kara damko hannunta wani irin lumshe idanunta tayi cikin sauƙe karyayr numfashi dan har tsagar kanta taji wani irin tsoro me tsanani na tsaga mata zuciya.

yana kkrin juyata ta wani irin kufce hannunta daga nshi da sauri wani irin juyi tayi  tare da yarfa masa shauran burbudin jikakken sumanta acikin kwayar idanunshi, da sauri ya sake ta yana kkrin goge ruwan dasuka feppetu masa acikin idanun kan ya gama ya bude idanun sa yaganta can gaba ta arce da gudu, ya tsaya cak baiyi motsi ba ya yanata kallon yadda take falfala gudun tana zuba kukan
tashin hankali da tsoro da bai taɓajin irinsa ba, step daya biyu zuwa na uku tay agabansa sai ragwaf jiri ya kwasheta tafadi kasa wann karon da mugun karfi ciwon raunin zucyarta ya tashi....

he stood der for a while da tunanin ko kawai yashiga motarsa ya shareta ya wuce inda zashi ne koko ya karasa ya dagota inta sake farfadowa sai ya kyaleta ta karata atacan tunda bazatace mai komi ba

wani abu acikin ransa kuma ya kasa idda lissafi, cos he knows when a person is soo scared kamr haka and is experiencing sudden symptoms of heart failure they may exhibit a range of behaviors and physical symptoms irin natan nan, ryt from her Behaviors yaga tulin Anxiety, with panic attacks she is Restles nd agitatated, kmr she is Confused,  disoriented, duk dama yay zaton kurma ce amma yasan Difficulty speaking or responding coherently maybe a clear sign of sumting serious musmn ma dayaga afari ta suma kuma ta farfado a firgice so weak nd scared, acikin duka alamomin ciwon raunin zuciya abu dayane tall yarage bai gani ba wanda shine  loss of consciousness sai kuma gashinan yaga ta sake sumewa yanzu...

yana gama wann lissafin yakarasa kulle motarsa ya jefa key din a aljihunsa ya juyo, lkcin ruwan saman ahnkli yafara raguwa, motsi motsi ya soma ji daga nesa cikin jejin amma bai kula ba cikin sauri ya karaso kanta yaga bata ko dandanin motsi duk dama ya taɓata.

acikin sauri yafara duban physical symptoms na hrt failure ajikinta yana kuwa dora kansa asaman kirjinta yaji faint parpalpitations with strong Shortness of breath ma'ana ba suma tay bama kawai numfashinta ne yakage ataciki yana mata wahalar fita waje, she started to look so pale nd more weaker, yasan badon ana ruwa ba da zufa tuni ya rufeta

thank god for his elite private club practicals da duk bazai san wayannan abun ynxu ba, dagota yay hannunsa yakaita motarsa seat din baya danya bata up front emergency help dan karta mutu masa ya shiga ukku,

niyyarsa saita farfado kafin ya wuce da ita can wajen haj mairo inyaso daga can anemi iyayenta dagatacan

kai tsaye yafara Loosening zip din doguwar rigarta then he sat her down comfortably ajikinsa ya fara Monitoring vital signs inta kafin can ya fara supplying mata extra oxygen baki da baki cikin ikon Allah kuwa tafara responding...

daga yadan hade bakinsu yahura mata iska yana shafa mata gadon baya ahnkli ahnkli sai kaga ta saki nishi me dan uban karfi wani hammmm sai tasake komawa lagwas ajikinsa amugun raunace, suna cikin wann yanayin bai hankara ba kawai yaga maza da sanduna suna ihuuuu suna fitowa wasu tagaba wasu ta bayansa duk sunga ayaanah kwance ajikinsa yadda yake fmr hura mata iska abaki yay kamar kiss sukeyi ga kuma hannunsa zagaye da ita ta baya nd he had no way to loosen her up face saida ya zarge zip din bayan rigarta..


kafin kace wani abu matasan fulani da buzayen nan kaf suka zageye masa mota suna kkrin zasu faffasa motar da sanda yay sauri ya kullesu aciki bai tsaya kintsa ta ba ya haura kan driver seat ya kunna motar ya taka motar da karfi ya dan razanasu har saida yaga sun ja baya baya.

ihuuu da hayaniyane ya cikkke wajen shikansa ibaad yasan inhar ya fito toh tabbas zasu kashe shi da duka dan yaga ga dukkan alama jahilai ne sosai kuma sunfishi girma da karfi

he was confused as to keep driving them off koya dau wayarsa ya kira gida akawo masa dauki, gashi aayanah ta kankame jikinta abayan seat, ko zip din rigarta bata mayar ba sai kuka kawai take mishi a motar kamr wanda yasota duk yarasa abunda ke masa dadi minti goma basuyi ba sai gasu juma da wasu dattajai sun faso..

nan akafara hayya hayya matasa sukace aisun ga me mota anan suna iskanci da ayaana shiyasa suke so su kashe su atare.

dakyar wani dattijon da ake ganin girmansa ya dakatar da hayaniyar ya karaso wajen ibaad ya kwankwasa masa window ibaad ya bude dan kadan, dacan har mutumin ya fara masa magana cikin bude ido dayaga ibaad din bai nuna alaman tsorata ba ne yatsaya yaji ba'asin sa. ibaad ya gaya masa shima ana ya sameta, snn zai basu yarsu amma inkuma suka tabashi already ya riga da ya kira hukuma ya basu information na inda yke ynxu haka suna hanyar zuwa nan kawai ajirasu su iso shi bazai ma fito ba sai hukuma sunzo.

dake yan kauye akwaisu da mugun tsoron hukuma sai kuma aka samu rarraben kai suka fara negotiating dashi, wai lallai saidai ya fito daga motar, ya basu yarsu hannu da hannu kawai ya wuce dama nemanta sukeyi in kuma be fito ynxu anyi magana ta nitsuwa dashi ba zasu kasheshi anan da duka inyaso duk wani abunda zai faru ya faru


dakyar da wuya ibaad yadau risk ya bude motarsa yafito tare da ayaanahn datake kukan tsoro sosai da alama ma batamasan zip din rigarta yana bude ba.

daga dattijon sai kuma juma sune akurkusa da motarsan sauran matasan dukkansu an umarce su da su tsaya agefe

...yawansu da makaman dake hannun su da ibaad yagani yasa kansa yafara juyawa kamr abun arxiki su juma suka fara magana da shi, da juma da dattijon ibaad ya musu bayani dalla dalla yadda ya same ayanah anan.

fuska ba yabo ba fallasa juma yace mish sun gode dama shine mahaifinta.....neman ta sukeyi ɓace musu tay.. amma tunda ansameta shikenan.

ibaad was kind of relieve dayaga sun fahimceshi, dan juyawa yay bayansa zai cewa ayaanahn ta karasa wajensu yana budan baki kamar kiftawa da bismillah yaji an buga masa wani abu akai da mugun karfi for good 30 minutes baisan inda yake ba sai kamr bayan mintina talatin masu kyau ya bude idonsa yaga hannunsa adaure gashi nan awani fadar kauye agurfane agaban wasu sarakuna su biyu, taron mata da matasa da dattajai sun zagaye su...

yana daga kai abunda yafara ji a kunnensa shine "ni juma maharazou naba da auren yata ayanah, inyaso yaje canshi bariki ya karasa abunda ya farayi da ita, danko mun kashe shi bamusan dan waye bane kuma yariga ya kira hukuma gara abashi yarinyar tunda yafara lalata yaje can da ita nayafeta ma duniya su je duk inda zasuje suyi iskanci suyi muna fatan har abada karta sake dawowa mana wann gari....

ran sarkin buzu ya turmusa ya baci baice komi ba dan sosai yaso abashi yarinyar sabida yaga tana da kyau sosai, amma kuma tunda akace musu a motar kafiri aka sameta  harkuma ya cire mata riga yana shafa mata jiki sai yazama na bazai iya fitowa fili yace abashi aurenta mashi da almajiransa bakuma.

sarkin fulani ne yace shin kowa ya amince da wann auren??

kusan kowa ya amsa da ehhhh..

sarki ya mike tsaye ya kalle ibaaad cikin ido yace toh kowa ya shaida ayau Mun bayar da auren ayaanah yar gidan juma maharazou wa wnn mutumin mai mota..

agogon ibaad me tsada da suka cire a hannunsa sarkin fulani ya daga sama yace jama'a ashaida wann shine sadakinsa...

amugun rude ibaad ya daga kansa cikin daka ma sarkin burkitaccen tsawa yace 'a'a dakata min malam...wallah ban amince ba.
SURAYYAHMS
***