BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

Chapter 7

by @narrnarhhbukar00

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

Narrnarhh Bukar

(Lady with the Amazing pen ✍️)

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

007

''Boka Ataka na zo'' ta faɗa bayan ta zauna a ƙasa,ga kasar wurin ɗauke da damshin ruwa da a sanyi mai tsuma jiki. Kamar walƙiya sai ga shi ya bayyana a kusa da tukunyar wutan. Wani irin haske mai ƙarfi ya karaɗe kogon lokaci guda. Da wata iriyar murya mai cike da ƙaraji da amon gaske ya fara magana

''Ataka mun sani! Ataka mun gani! Ataka faɗi buƙatarki'' duk jimla guda sai ya ambaci kalmar Ataka,wanda shi kaɗai ya san ma'anarta da kuma dalilin da ya sa yake amfani da ita. Gyara zama Gwaggwon Bugaje ta yi tana dubansa da kyau. Boka Ataka baƙi ne sosai kamar baƙin zunubi, jikinsa ɗauke da zane-zanen baƙi. Fuskarsa ɗiɗɗinke take kamar an ɗinke ƙwarya. Gashinsa murmurɗe irin na dada. Yana da taɓaɓɓan hanci da fala-falan kunnuwa. A takaice boka Ataka bai da kyakkyawar fuska irin ta mutane. Bayan ta gyaran zamanta ta ce

''Boka Ataka yarinyata mai suna Sahura ke da matsala a gidan mijinta. Kwata-kwata bata jin daɗin gidan. Ga uwa-uba mijin ya fi son kishiyar a kanta.  Kamar yadda ka taimake ni da sauran yarana,ina so ka sake taimakona a wannan karon,domin ina jin Sahura sosai a raina. Ka bata mallaka''

Siririyar dariyar irin ta yara ya shiga ƙyaƙyatawa yana dubanta,sai can ya gimtse tare da ɗaure fuska. A bazata ta ji ya fara magana cikin muryar nan ta sa mai amo kamar ana dukan garwa.

''Ataka gidan yarinyarki akwai matsala! Ataka kishiyar kadai za ta iya mallakewa a yanzu! Ataka mijinta na da wuyar mallaka! Ataka saboda yana riƙe da addininsa!"

Zaro ido Gwaggwon Bugaje ta yi waje jin uban gayyar ba zai mallaku ba,an yi ba a yi ba kenan, ai gwara mijin ya mallaku a kan a mallake kishiyar. Cike da damuwa Gwaggwon Bugaje ta ce

''Yanzu boka Ataka babu yadda za a yi a mallake mijinta?"

Siriyar dariyar ya yi,wannan karon bai jima ba ya tsagaita sannan ya ce

''Ataka akwai wuya! Ataka amma zamu taka zuwa shekara huɗu mu gani ko zamu samu dama! Ataka ba sai kin dawo ba! Ataka ita da kanta za ta ga ya fara bin maganarta! Ataka daga nan ta mallake shi! Ataka amma mallakarsa bazata jima a jikinsa ba! Ataka kin amince?!"

Da sauri Gwaggwon Bugaje ta ce

''Eh Boka Ataka na yarda na amince"

Siriyar dariyar ya kuma yi,wannan karo ya jima yana siriyar dariyar daga bisani ya tsagaita tare da ɗaga hannunsa na hagu sama. 'yan surkulle ya yi wanda kamar walƙiya wata 'yar ƙaramar ƙwaryar ta bayyana a tafin hannunsa. Ƙarama ce sosai ƙwaryar baƙa da kwalliyar ratsin fari da ja kaɗan. Ɓacewa ƙwaryar ta yi,sai ta bayyana a gaban Gwaggwon Bugaje. A hankali ta ɗora idanunta saman ƙwaryar. Kunnuwanta suka tsinkayi Boka Ataka na faɗin

''Ataka ki kai mata! Ataka ta tabbata sai ta je gidan za ta yi amfani da ƙwaryar! Ataka idan ta koma gidan! Ataka a tsakiyar dare za ta wanke fuskarta da duka ruwan sai ta kira Ataka sau goma! Ataka washegari ta dafa abinci ta ɗiba da ƙwaryar ta juye a kwanon kishiyar! Ataka idan ta ci abinci shikenan za ta mallaketa! Ataka ta bar mallakar miji a hannumu! Ataka nan da shekara huɗu za mu mallake shi! Ataka amma mallakarsa bazata daɗe ba ɗuii! Ataka na sallameki! Ataka akwai sharaɗi!"

Cike da jin daɗi Gwaggwon Bugaje ta ce

''Ina sauraronka boka Ataka''

Siriyar dariyar ya kuma yi wannan karon bai jima ba ya tsagaita sannan ya ce

''Ataka za ta samu matsala nan gaba! Ataka allon tsafina bai hasko mini inda matsalar take ba! Ataka kishiyarta za ta haifi haske mai yaye duhu! Ataka ban san me hasken yake nufi ba! Ataka allon tsafina ya nuna mini ɗiyarki za ta ji dadi na ɗan wani lokaci!Ataka amma ba zai dawwama ba! Ataka 'yarki za ta sha wuya a ƙarshe! Ataka hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh!" Ya ƙarashe maganar da sakin Siriyar dariya. Lokaci guda hasken mai ƙarfi ya ɗauke sai na wutar tukunyar kaɗai.

''Ataka na sallameki'' daga haka ya ɓace.A hankali Gwaggwon Bugaje ta miƙe tana ganin jiri-jiri na shirin lulluɓe na mujiyarta. Zuciyarta cike da damuwa,jin wannan mummunan labarin da boka a Ataka ya sanar mata. Har ta fito kogon bata sani ba. Dusar ƙanƙarar tare da azababben sanyin wurin suka tabbatar mata da ta fito daga kogon. Cike da kasalar jiki da na ruhi ta fito daga yanki. Kasancewar akwai 'yan'uwan mahaifinta a ƙauyen Aouta, gida-gida ta bi suka gaisa sannan ta koma Bégajé. Kwananta biyar tana bin gidajen 'yan'uwanta ,a kwanata na shida ta dawo Sakkwato. Cikin dare ta dawo lokacin har Sahura ta yi bacci. Bata tayar da ita ba,ta ciro ƙaramar ƙwaryar da boka Ataka ya bata,ta yi mata kyakkyawan ɓoyo sannan ta bi lafiyar gado.

Washegari da safe, a bazata Sahura ta yi tozali da Gwaggwon Bugaje,cike da farinciki ta yi mata sannu da zuwa. Tsahara ta shigo kamar koyaushe ta ma Hamid wanka sannan ta taimaka ma Sahura ta yi wanka. Bayan ta saka kaya kunun kanwan da Tasallah ta aiko mata da shi ta sha. Cike ta zumuɗi ta tambayi mahaifiyarta ko an dace. Yalwataccen murmushi ta sakar mata,abin farincikin za ta sanar mata ban da na baƙin ciki da boka Ataka ya ce zai afkun mata. Ta yi imani kafin lokaci za ta samo mata wata maslaha tun da ba shi kaɗai ya iya sihiri ba. Akwai waɗanda suka fi shi...

''Gwaggwo kin yi shiru. Ko dai ba a dace ba ne?" Sahura ta faɗa a sanyaye.

''Ko kusa Uwata. An dace. Sai dai naki ba irin na sauran 'yan'uwanki ba ne. Boka Ataka ya ce za ki mallake kishiyarki yanzu amma mijinki sai nan da shekara huɗu, saboda mai riƙo da addini akwaii wuyar mallaka. Kin san mijinki ya fi Malam nutso a kogin ilimin addini.''

Shiru Sahura ta yi tana kallon mahaifiyarta,idanuwanta har sun fara tara ruwa. Wannan ai saci-faɗi ne, an sare kan maciji ba a birne kansa ba. Ita da take da burin mallakar Dauda Imamu me za ta yi da kishiyarta. Yoo ko ta mallaketa hakan ba zai hana fitowa fili ya nuna yafi ƙaunarta sama da ita ba. Cike da raunin murya Sahura ta ce

''Gwaggwo ta ya zan mallake kishiyata alhalin shi uban gayyan ban mallakesa ba. Ban rabu da bukar ba zan haifi habu, Soyayyar da yake nuna mata a fili ba zai bari ba,hakan na nufin ban rabu da ɓacin rai ba''

Sauke tagwayen ajiyar zuciya Gwaggwon Bugaje ta yi tare da gyara zama ta ce

''Wannan duk mai sauƙi ne Uwata. Cikin kaso ɗari saura hamsin,kin ga kuwa ai munci ƙarfin aiki. Sannan ba wai bazaki mallaki mijinta ba ne fa. Sai nan da shekara huɗu boka ya ce. Da guntun gatarinka ai yafi sari ka ba ni. Ki juyata son ranki,idan mijinki ya ce da ita zai je Kadunan ki hanata,sannan ki umurci ta ce lallai-lallai da ke zai yi tafiyar. Haba Uwata kamar ba mace ba. Ina kisisina da makircin da na sanki da shi tun kina budurwa? Ta ya saboda ɗan ƙaramin abu ki tayar da hankalinki''

''Haka ne kuma Gwaggwo. Sai yanzu na fahimci abin da kika haska mini. Yo ai Mairi ce za ta zama makamina. Ina matuƙar godiya Gwaggwo. Samun uwa kamarki a duniyar nan da matuƙar wahala. Cikin dubu da ƙyar za a iya samun biyu.''

Sosai kalaman Sahura suka faranta ran Gwaggwon Bugaje . Babu abin da a duniya yake sakata farinciki irin ta ga yaranta suna annashuwa.

''Idan kin ta shi komawa Zamfara zan ɗauko miki ƙwaryar,sai na faɗa miki yadda boka ya ce ki yi amfani da ruwan ciki da ƙwaryar bakiɗaya''

''To gwaggwo.''

Wani sabon shafin hira suka buɗe. Cike da shauƙi suke hirar har da dariya, Hamid na kwance a saman gafon runfa ya yi bacci...✍️

^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

Tudun Wada premier road, Gusau. Zamfara state Nijeriya

A ɓangaren su Mairi cikin satin Dauda Imamu ya yi tafiya zuwa Kaduna. Sai da ya tabbatar ya bar musu komai da suke buƙata sannan ya bar gidan. Kafin ya tafi ya kai Yasir islamiyyar da yake koyarwa,daga baya idan ya ƙara wayau sai a saka shi boko. Da sassafe take kai shi makarantar zuwa goma idan an tashe su sai ta ɗaukoshi daga can ta wuce islamiyarsu ta matan aure da shi,zuwa sha biyu su dawo gida. Yau ta kama Alhamis ranar hutu, Mairi na zaune tare da yaranta a tsakar gida,tana duba arba'una hadith wanda aka koya musu jiya. Yasir da Jalil sun duƙufa wasa da mota. Kwatsam suka jiyo sallamar 'yar ƙuda tare da yaranta. Ba ita ba,ba yaran ba kamar an tsamo su daga kwata, da alamu kayan ya jima a jikinsu musamman yaran. Hancinsu kamar hancin kare tsabar yadda majina ke yoyo. Cike da fara'a ta iso inda Mairi take zaune da yaranta. Samun wuri ta zauna tare da faɗin

''Bisimillahi Allah! Ina kwana Maman Yasir''

''Lafiya lau 'yar ƙuda,ya yara''

''Lafiya lau suke wallahi'' ta amsa tana rarrraba ido a tsakar gidan ko za ta ga gilmawan Sahura. Don kwana biyu ta rabu da jin ɗuriyarta. Mairi bata sake bin takanta ba,littafin da ke hannunta ta ci gaba da dubawa. Ganin idan ba ita ta fara mata magana ba ko za su kwana a haka bazata ce mai ka ci shara bakinka ba. Domin Mairi ba mai yawan surutu bace da hayaniya,shi ya sa ta su bata zo ɗaya ba tun a farko. Gyara zama 'yar ƙuda ta yi sannan ta ce

''Ni kuwa Maman Yasiri. Ina kishiyarki ta je ne. Na rabu ta sakata a ido''

Murmushi Mairi ta yi,zuciyarta na raya mata gulma ce ta kawota ba komai ba. Shi ya sa mijinta ya yi matuƙar birgeta da ya hanasu shiga biki ko suna. Ta ga amfanin hakan yanzu, ƙarya ne a yi biki ko suna a unguwar gagarumin faɗa bai kaure a gidan ba, idan aka bi salsala gulma da tsaigumi ne suka janyo hakan. Ajiye littafin ta yi gefe sannan ta dubi 'yar ƙuda ta ce

''Maman Hamid na Sakkwato wankan jego''

Waro ido waje 'yar ƙuda ta yi tsabar mamakin da ya dirar mata

''Wankan jego Sakkwato!" Ta maimaita.

''Eh 'yar ƙuda. Faɗi ki ƙara'' cewar Mairi.

Taɓe baki 'yar ƙuda ta yi sai ta ce

''Biri ya yi kama da mutum. Wato sai da ta gama haɗa miki kitimurmuya a unguwa,matan unguwa sun ɗauka sannan ta tsare ta bar garin.Eh Lallai Sahura ta iya barikanci. Kin san Allah babu gidan da bata je a unguwar nan ta faɗi aibunki ba. Har gidana sai da ta zo ta ce mini wai mijinku ba...''

''Dakata 'yar ƙuda! Bana buƙatar wannan maganar! Jeki kawai na gode da ziyarar. Allah ya ba da lada!'' Mairi ta faɗa a hasale,tare da ɗaukar littafinta ta ci gaba da dubawa. Wani irin mugun kallo 'yar ƙuda ta watsa mata ba tare da ta sani ba,a ranta tana faɗin 'Banziya! Wawiya!Wacca bata waye ba! Shi ya sa Sahura take birgeni' a zahiri kuma ta miƙe tare da faɗin

''To ai shikenan! Ni dai Allah ya ga zuciyata. Bana son a cutar da ke saboda zumuncin da ke tsakaninmu. Amma tun da kin ce kar na sake miki maganar, to bakina alaikum. Ni kin ga tafiyata'' ta ja hannun yaranta fuuuu! Kamar za ta tashi sama ta bar gidan. A fili Mairi ta furta

''A sauka lafiya. Haka kurum muna zaman lafiya za ki shigo don ki wargaza zamantakewarmu,to ta Allah ba taki ba. In shaa Allah kamar yadda nake zaune ƙalau da Sahura, haka zai ɗore har tsufanmu in da rai da lafiya. Mtsss'' ta ci gaba da duba littafinta. Da ta gaji da zaman wajen ta nannaɗe tabarmar suka koma ciki. Mairi mace ce mai matukar haƙuri da ladabi,shi ya sa Dauda Imamu yake alfahari da samunta a matsayin uwar yaransa. Duk inda ya ajiyeta nan take tsayawa,ba faɗa balle jayayya. Tun auransu zuwa yanzu wani saɓani mai girma bai taɓa gittawa a tsakaninsu ba. Ba Mairi ba Dauda Imamu ba,kowannansu daidai gwargwado yana kyautata wa ɗan'uwansa. Babu inda take zuwa idan ta dawo daga makaranta,cefane ma kawo mata ake daga kasuwa. Duk abin da take buƙata na rayuwar yau da kullum akwai shi a gidan. A makaranta bata yarda ta bankaɗa sirrinta kamar yadda wasu matan suke ba. Suna bayyana abubuwan da mazajensu suke musu na alkhairi,a tunaninsu sun fi kowace mace sa'ar miji,a baɗini ba su san hanya suke buɗe wa maƙiya damar yin gwaggwaɓar nasara a kansu ba. Mairi ta ci gaba da ba yaranta kula da ita kanta, daga makaranta sai gida,a gida bata ba wata 'yar unguwa fuskar shigo mata gida har ta kawo gulmar wata ba. Wannan kenan...✍️

^^^^^^^^^^^^^^^^^^

Garkar Bala fari mai fata,Ƙofar kaɗe. Sakkwato. Nijeriya

A ɓangaren Sahura wankan jego take sosai,wanka irin na mutan da Gwaggwon Bugaje ta koma yi ma, maganin sanyi ya zama tamkar ruwan shanta. Ga kulawa ta musamman da take bata da Hamid. Cikin ƙankanin lokaci Sahura ta murje,ta ƙara ƙiba,haskenta ya sake bayyana kamar ka latsa fatarta jini ya fito. Hamid ya ƙara girma ka ce ɗan wata shida ne. 'Yan'uwanta na kawo mata ziyara da sake bata sabon darasin zama da kishiya wanda bata san da shi ba,ga wanda Gwaggwon Bugaje take bata na musamman. Ta ƙara samun ilimin kisisina,makirci,bita da ƙulli waɗanda za su taimaka mata samun gindin wurin mijin,tun da bazata samu damar mallakar Dauda Imamu yanzu ba. Tafiya ta yi tafiya,tun ana ƙirga kwanakin da suka rage Sahura ta kammala wankan jego har ranar ta zo. Galleliyar atampa super Gwaggwon ta sa a ɗinka mata ta saka. Gidajen 'yan'uwa da abokan arziki ta je yawan arba'in. Daga karshe da yada zango a gidan innarta,da yake mai kuɗi take aura,sai da ta shafe kwanar biyar can yana narkar daɗii sannan ta dawo gidan ta fara shirin komawa Zamfara. A daren ranar da za ta koma Gwaggwon Bugaje ta ɗauko ƙwaryar da boka Ataka ta miƙa mata tare da cewa

''Ki kula sosai  Uwata da ƙwaryar nan har ku isa Zamfara. A tsakiyar dare za ki wanke fuskarki da duka ruwan da ke cikin ƙwaryar nan,sannan ki kira Ataka sau goma. Washegari da kuma ki dafa abinci sai ki zuba abincin da za ki bata a kwaryar,daga bisani sai ki mayar cikin kwanon da za ki bata. Idan ta ci abinci shikenan kuma,sai abin da kika ce za ta yi. Fatan kin fahimta''

''Na fahimta sosai da bayananki,zan yi yadda kika ce.''

Murmushi Gwaggwon Bugaje ta sakar mata tare da miƙewa da ɗauke wata 'yar ƙaramar jaka ta buɗe cikinta. Hannu ta sa da ciro kayan da ke ciki. Ƙullin magani kala-kala,gumba,turare mai ɗauke da wasu itace ciki,sai zuma da wasu tarkacen kayan mata. Ɗaya bayan ɗaya take mata bayanin yadda za ta yi amfani da su lokacin da mijin na ɗakinta da wanda idan baya ɗankinta za ta yi amfani da su. Jinjina mata kai ya yi alamar ta fahimta tana murmushin jin daɗi. A ranta tana faɗin wace uwa za ta ma 'yarta gata irin wannan. Galoli biyu ta ɗauke na tsumi da tabaje ta miƙa mata. Ta sanar mata yadda za ta yi amfani da su idan ta koma. Daga nan ta tayata shirya kayan a ƙatuwar ghana-must-go ta zage zip ɗin. Duk abubuwan da ta sani nata ta haɗe wuri guda saboda halin mantuwa sannan ta bi lafiyar gado,ranta fes! Kamar an yi mata bushara da gidan aljanna. Zuciyarta cike take da ƙudirin gallaza wa Mairi da yaranta. Kamar yadda mahaifiyarta take juya kishiyoyinta haka take fatan ta yi ma Mairi har ma nata ya fi na uwarta. Da wannan BAHAGON TUNANIN bacci ya lallaɓo ya sureta zuwa wata duniyar ba tare da ta farga ba...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***