BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

Chapter 8

by @narrnarhhbukar00

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

Narrnarhh Bukar

(Lady with the Amazing pen ✍️)

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

008

Zuciyarta cike take da ƙudirin gallaza wa Mairi da yaranta. Kamar yadda mahaifiyarta take juya kishiyoyinta haka take fatan ta yi wa Mairi har ma nata ya fi na uwarta. Da wannan BAHAGON TUNANIN bacci ya lallaɓo a hankali ya sureta zuwa wata duniyar ba tare da ta farga ba. Washegari da safe bayan ta yi wanka ta karya ta fara shiri. Mazan gidan suka taimaka da kayan zuwa waje, daman tun jiya Gwaggwon Bugaje ta daidaita da mai 'yar ƙumbula, kayan aka saka a ciki. Duka 'yan gidan suka fito har waje yi mata sallama ciki har da mahaifinta. A hankali ta hau 'yar ƙumbular zuciyarta fal tsoron kar ƙwaryar da ke cikin jakarta ta girgiza har ruwan su zube duk da a rufe take ruf!. A gabansu 'yar ƙumbular ta wuce sannan suka koma gida. Kai tsaye ya kaita tasha ta hau motar Gusau. Ta ɗan jima a motar saboda babu fashinjoji sosai,ɗaya bayan ɗaya fasinjojin ke zuwa har ta cika suka nosa hanya. Tafiya ta yi nisa,Hamid da ke baya ya fara mata kuka. A hankali ta ajiye jakar a gefanta,da yake ta ci sa'a akwai wani ɗan lungu a gefanta. Ta kwance goyon ta ciro Hamid,sai ta fara shayar da shi har ya yi bacci. Sun jima suna tafiya daga bisani suka sauka a Gusau. Drop na 'yar ƙumbula ta samu suka yi ciniki ya kaiya har gidan, lokacin ana kiran sallar azabar. Bayan ta sauka ta miƙa masa kuɗin tare da roƙonsa arziƙin ya shigar mata da kayan ciki bata da wanda zai taimaka ga kuma goyon. Babu musi ya sauko tare da tayata shigar da kayan cikin gidan. Mairi da ke alwala ta miƙe cike da farin ciki ta ce

''Maraba lale marhabin da zuwa Maman Hamid"

Murmushin yaƙe Sahura ta yi  sannan ta ce

''Barkha da gida''

Da sauri Mairi ta kammala alwalar ta matso tare da tayata shiga da kayan falo. Za ta amshi jakar hannunta da sauri Sahura da girgiza mata kai da faɗin

''Haba kar ki damu wallahi. Ai kin yi ƙoƙari. Je ki yi sallarki kar lokaci ya wuce''

Murmushi Mairi ta yi sannan ta ce

''To bari na ƙarasa miki da sauran kayan cikin ɗakinki''

''Na kuwa gode Maman Yasir''

Ɗaya bayan ɗaya ta ɗauki kayan zuwan ɗakin Sahura ta ajiye. Ta koma kicin ta zubo mata abinci a plate da ruwa ta kawo mata ɗakin sannan ta wuce ɗakinta ta kabbarta sallah. Yasir da Jalil na saman gado suna shaƙar baccinsu. Bayan ta ciro ƙwaryar daga jakarta ta yi mata mugun ɓoyo sannan ta kwance goyon Hamid ta kwantar da shi saman gadon. Ba tare da tunanin Sallah ba ta ɗauki abinci ta fara ci. Tass ta cinye abincin ta sha ruwa. Gefe ta ajiiye plate ɗin tana yatsina fuska,jinta take ba wata shegiya kamar ta. Tun kan ta aiwatar da aikin boka har ta fara cika tana batsewa ita kaɗai. Abinka da mai gajiya bata jima ta kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da ita. Ba ita ta farka daga bacci ba sai kusan bayan Asr,shi ɗin ma Mairi ce ta zo ta tasheta saboda lokacin sallah ya wuce kuma babu kyau bacci bayan sallar Asr. A fuska bata nuna mata ta ji haushi ba,amma a ƙarshen zuciyarta tsinuwa da zagin ƙare dagin ne ta yi mata. Bayan Mairi ta fita ta ja uban tsaki tana harar ƙofar kamar ita ta yi mata laifin. Alla-alla take dare ya yi ta fara aiwatar da ƙudirinta. Da daddare a falo dukkaninsu suka ci abinci, daga nan kowa ya wuce ɗakinsa bacci. Hamid da ya tsiri kukan dare ya fara sana'arsa,da ƙyar ta samu ya kwanta,Mairi sai da ta shigo ta ji ko lafiya.

Kwance take amma idanuwanta biyu ta kafesu a agogon bangon da ke kallonta,ta ƙosa ƙarfe ɗaya na dare ya yi ta tashi. Sannu a hankali lokaci ya cika. A hankali ta mike ta nufi inda ta ɓoye ƙwaryar ta ɗauro. Murfin da aka rufe ƙwaryar da shi ta buɗe, bayanin da Gwaggwon Bugaje ta yi mata yana kai-kawo a kwanyar kanta. A hankali ta karkata kwaryar ta zuba ruwan wanda baki ne ga ɗoyin gaske,haka ta daure ta zuba a hannunta ta wanke fuskar,sai da ta tabbatar ta karar da ruwan kamar yadda mhaifiyarta ta ce sannan ta ambaci Ataka sau goma. Sake ɓoya kwaryar ta yi ta gyara wurin da ruwan ya ɗan zuba sannan kwanta. Murmushi ta sakarwa kanta tana lumshe ido lokaci guda. Tana gab da cim ma burinta,duk da ba duka burin za ta cim ma ba,amma ta san ta taka babban matsayi a hanyar ta cimma ƙudirinta gabakiɗaya. Gyara kwanciyarta ta yi tana fuskantar Hamid. A hankali ta fara lumshe ido tana buɗesu daga bisani ta rufe su ruf!.

Washe gari da safe bayan sun karya sai Sahura ta dubi Mairi ta ce

''Maman Yasir bari yau na rage miki aiki na ɗora girki''

'yar dariya Mari ta yi sannan ta ce

''Haba Maman Hamid. Duka-duka yaushe kika dawo da za ki ɗora girki ga ɗanyan goyo. Kar ki damu wallahi,ki bari sai nan da sati biyu haka sai ki fara girkin. Ƙila ma lokacin Baban Yasir ya dawo''

Murmushin yaƙe ta yi a ranta tana faɗin 'Kutumar ubancan kayyasa! Ai yau babu fashi sai na girka abinci a gidan nan kinci kamar yadda Gwaggwona ta sanar mini. Lallai ma' a zahiri ta ce

''Babu damuwa Wallahi. Na kwana biyu ban shiga kicin ba ne,sai nake ji na wata iri. Kin san a can gidan babu abin da nake daga ci sai shayarwa da bacci. Tun da nake gidan ban leka kicin ba. Yau dai ina da sha'awar shiga kicin, karki hanani Maman Yasir''

Wannan karon dariya sosai Mairi ta yi har hakan ya so ɓata ran Sahura,amma ta ɗaure ba tare da ta bari ta ga canji a fuskarta ba. Cikin dariyar Mairi ta ce

''To Maman Hamid. Na ga alamar tsohon tsiminki na aiki ne ya taso gadan-gadan. Tun da ke da kanki kike bukatar shiga kicin ɗin ban da matsala. Daman kwana biyu na yi kewar daddaɗan abincinki.''

Murmushin yaƙe Sahura ta sake saki domin tagane inda maganarta ta dosa. Watau dai ta mayar da ita jaka wacce bata gajiya da aiki. Har da iya ce mata tsuminta ne ya motsa. Lallai kuwa za ta ga tsumi. Yadda take daukarta jaka ita za ta koma jakar. Da Sahurar gwaggwan bugaje take zancen. A zahiri ta ce

''Kamar kuwa kin shiga ƙokon raina Maman Yasir. Bari ki gani da wuri zan girka abincin na huta'' ta yi maganar tana miƙewa lokaci guda ta fita. Kai tsaye ta wuce kicin ɗin ta ɗaura sanwar rana. Jollof na taliya ta girka,sai da ta fakaici idanun Mairi ta ɗauko kwaryar ta taho da ita kicin ɗin. Da ta kammala abincin sai ta zuba wanda za ta Mairi a ƙwaryar sannan ta juye a plate ɗin. Cike da taka-tsantsan take aikin,tana 'yan waige-waige kar Mairi ta shigo ba tare da ta ankara ba. Tsaf ta kammala komai lokacin a masallatai ana sallar, ta kai kular falo ta dawo ta kai mata plate ɗin abinci da cokali lokacin tana Sallah,sai ta dawo kicin ta ɗauki sauran abinci. Koda ta shiga falon ta tarar tana cin abincinta hankali kwance. Wani munafikin murmushi ta sakar wa kanta zuciyarta fari ƙal. Ɗakinta ta koma ta ɓoye ƙwaryar sannan ta ɗauki plate ɗin abincin ta soma ci cike da farinciki da annashuwa. Don ta tabbatar da aikin ya fara cin Mairi, tana a cikin ɗakin ta ƙwalla mata kira

''Mairiiii!" Kafin ta sauke numfashi Mairi ta amsa tana shigo ɗakin da gudu jikinta na tsuma. Tana zuwa ta zugunna tare da faɗin

''Gani Maman Hamid ''

Ƙasaitaccen murmushi Sahura ta sakar wa kanta tana jinjina kai lokaci guda. Mairi kanta a ƙasa, zuciyarta na halbawa,wani irin tsoron Sahura take ji a hankali yana bin jini da ɓargonta ba tare da tasan  dalili ba.

''Wace magana na ji kuna tattaunawa ke da mijina ana gobe zan tafi Sakkwato?" Sahura ta tambaya fuskarta ɗaure tana tsareta da manyan idanunta. Da matuƙar ƙarfi zuciyar Mairi ta halba tana rintse idonta, furucinta tamkar mashi ne mai matukar tsini da ke caccakar zuciyarta tare da silasta bakinta bayar da amsar da bata shirya ba. Kokawa take da zuciyarta, tana son ta ƙarfi da yaji ta kice tsoron Sahura da ke shirin yi wa zuciyarta ɗaurin gwarmai amma hakan ya faskara.

''Da ke nake!" Sahura ta furta a tsawace tana zare mata ido. Su Yasir da shigowansu kenan sai da suka firgita. Da sauri Jalil ya rungume mamanta yana shigar da kanta cikin jikinta tsabar firgicin da ya saukar masa tamkar dirar mikiya. Wasu zafafan hawaye suka shiga rige-rigen sauka daga gurbin idanunta,ta rasa wace kalar musiba ce take shirin afkowa rayuwarta. Cike da sanyin murya ta ce

'' Mun tattauna ne a kan idan ya dawo daga Kaduna lokacin kin dawo wankan jego,zan je Mada wurin 'yar'uwata da sauran dangina na yi musu sallama,daga bisani sai ya wuce da ni Kaduna,ke kuma ya saka ki a...''

''A Islamiyyar garunku! Hhhhhhhhhh! Wato ke 'yar daɗi miji za ki bi shi Kaduna ku bar ni a Gusau ina tsotar tsamiya! Buɗe kunnuwanki!"

Da sauri Mairi ta yakice ɗankwalin kanta hannuwanta na rawa ta riƙe su. Yasir da Jalil sun taruke jikinta saboda yanayin da ba su ganinta a ciki ba.Murmushin mugunta Sahura ta saki sannan ta ce

''Daga yau har zuwa ranar da mijina zai dawo gidan nan ke za ki dinga aikin gida da renon ɗana. Kin ji ni ko! ''

Da sauro Mairi ta ce

''Eh Maman Hamid''

Gyara zama Sahura ta yi tana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ta ce

''Sai magana ta biyu, idan mijina ya ce zai tafi da ke Kaduna kar ki amince. Ki ce masa kina son ya je da ni can. Sannan idan na tafi can kar watarana ya zo ya ce zai ɗaukeki ni na dawo ki amince. Kar ki kuskura ki yarda ko da kuwa za yi fushi da ke. Idan kuka kika tsallake maganata,ha ha ha za ki ɗanɗani kuɗarki. Ahir ɗinki na ji kin faɗa wa wani halin da kike ciki,daga ƙarshe na dakatar da ke zuwa islamiyya,koda kuwaun tafi Kaduna,ban amince ki je islamiyya ba,sannan idan sahibin zuciyata Yaya Imamu ya tambayi rashin zuwanki makaranta ki ce masa haka kike da ra'ayi yanzu.Kin ji niiiiiiiiiiii!"

''Na ji ki maman Hamid. Ban zan taɓa tsallake maganarki ba.''

''Gyara ɗankwalin sannan za ki iya tafiya''

Da sauri Mairi ta mayar da ɗankwalin tare da miƙe ta rike hannuwan su Yasir ta ja su a sauri suka bar ɗakin. Mairi na fita Sahura ta sheke da dariya har da tafawa tana faɗin

''Ho ni Sahurar gwaggwan bugaje 'yar ƙunan baƙin wake! Duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha! Kaɗan kika ga ni daga cikin nau'in baƙin cikin da na tanadarwa rayuwarki ke da 'ya'yanki. Sai na zama silar mutuwa Mairi. Kina gab da haɗiyar zuciya ki mutu da zarar na mallake Yaya Imamu. Zan shayar da ke da  'ya'yanta gubar mamakin da baku taɓa sha ba! ''

Kwanciya ta yi ta matso da Hamid ta ciro nono ta fara shayar da shi. Guguwar farinciki na sake mamaye farfajiyar zuciyarta. Tun da ta zo duniya bata taɓa tsintar kanta cikin farinciki kwatankwacin wannan ba. Ta yi dacen uwa mai share mata hawaye, burikan da suke kwance cikin zuciyarta da burtsosu.

A ɓangaren Mairi daga ɗakin Sahura ta wuce ɗakinta,da kuka ta ƙarasa saman gadon. Wannan wace kalar musiba ce haka, a ce farad ɗaya zuciyarta ta kamu da tsoron kishiyarta,me ke shirin faruwa da ita ne. Me ya sa bakinta yake mata nauye idan za ta bujire ma Sahura ko ta faɗin akasin abin da take muradi. Me ya sa masarautar zuciyarta take gayyato tsoron Sahura cikin fadarta. Me hakan yake nufi! Hawaye masu ɗumin suka gangaro saman kuncinta.

''Ammu tuta kike?" Yasir ya faɗa da tsamin bakinsa. Jalil kuma gwaranci yake maata wanda ta kasa gane inda maganarsa ta dosa. Murmushi Mairi ta saki lokaci guda tana ɓoye damuwarta. Hannu Yasir ya sa ya goge hawayen fuskarta yana faɗin

''Ti daina tuta Ammu''

Rungumesu tsam ta yi a jikinta wasu sabbin hawayen na sake gangaro mata,har yanzu bata karaya ba,kokawa tare da zuciyarta a kan tsoron Sahura da ke son shigowa cikin duniyarta amma kamar tana ƙara rura wutar tsoranta ne a ciki. Suna a haka Sahura bankaɗe labulen ɗakin,ba tare da ta shigo ba ta ce

''Ki je ki kira mini 'yar ƙuda ya yanzu'' tana gama fadin haka ta sauke labulen

Kafin Sahura ta sauke numfashi har Mairi ta sauke su Yasir daga jikinta ta miƙe, mayafinta ta lulluɓa sannan ta riko hannayen su Yasir ta fito,kai tsaye ta wuce gidan 'yar ƙuda. A ƙofar gida ta sameta ba tare da sun gaisa ba ta sanar mata saƙon Sahura ta juyo zuwa gidan. Cike da tsantsar mamaki 'yar ƙuda ta biyo bayanta ba tare da ta kulle gidan ba, kasancewar yaranta na gidan maƙota wasa. A kusan tare suka isa gidan. Dakatar da Mairi Sahura ta yi da tsawa. Da sauri 'yar ƙuda ta dafa ƙirjinta da matuƙar ƙarfi tana ware 'yan mitsi-mitsin idanunta waje tsabar mamaki. Wani irin girma kan Sahura yake. Cike da gadara Sahura ta ce

''yar ƙuda kin yi gyaran gidanki yau?''

Da sauri 'yar ƙuda ta ce ''A'a. Sai zuwa an jima da yamma''

Taɓe baki Sahura ta yi tana duban Mairi

''Mairi jeki gyata mata gidan. Duk abin da kika san ya dace ki yi,ki tabbatar da kin yi. Sannan kar ki daɗe''

''Sahuraaaaaa!" 'yar ƙuda ta faɗa tana karkata kanta. Yau ta haɗu da wacce ta goge mata hadda,lallai ko a gidan giya akwai oga. Cike da gatsali Sahura ta ce

'''Na'ammmm! Ko baki son gyaran ne na ce ta bari!"

''Wace ni 'yar ƙuda. Allah ya ba ni tsuntsu gasasshe daga sama taya zan ƙi ɗauka. Yau dai na tsinta dami na a kala''

Matsowa kusa da Sahura 'yar ƙuda ta yi,sai da ta tabbatar Mairi ta bar gidan da yaran sannan ta rage murya

''Maman Hamid! Na ɓace a kan hanya. Don Allah taimaka ki dawo da ni. Kaina ya yi gingirin ya huhin goro''

'yar dariya Sahura ta yi tana zama saman kujerar tsakar gidan Hamid na hannunta 

''Ya kika ga salo! Ba na sanar miki idan na je Sakkwato za ki ga canji ba. Sahura ce fa! Ɗiyar Gwaggwon Bugaje mai babban ɗaki''

Zama 'yar ƙuda ta yi a ƙasa kusa da Sahura kamar baiwa da uwar ɗakinta ta ce

''Sahura ki duba girman Allah ki ɗora ni a wannan lafiyyar hanyar''

Murmushi Sahura ta yi har fararen haƙoranta na bayyana. Ta yunƙura za ta bata amsa suka ji sallama,da sauri suka waiga hanyar ƙofar gidan. Lokaci guda zuciyar 'yar ƙuda ta tsinke, babu shiri bakinta ya furta...✍️

jama'a ba mu fara komai ba a wannan zazzafan wasan,ban tunanin ko sharan fage mun yi🥰. Ku gyara zama don ganin yadda wasan zai kaya,domin baku da tsoro balle fargaba tun da kuna da gangariyar mai ɗauko muku rahoto. Ni ce dai NARRNARHH BUKAR, lady with the Amazing pen✍️. Ku biyo ni don samun damar kwankwaɗar madarar karatu mara garwaye. Let's goooooo!

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***