Chapter 10
The Amazing Pen ✍️.......
BAHAGON TUNANI
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
010
Dariyar Sahura ta yi sannan ta ce
''Zan kuwa bi shawararki, idan ta san wata ai bata san wata ba. Kin ga bari na koma kar a kuma irin na wancen karo. Ya diro garin nan ban sani ba'' ta yi maganar tana mikewa tare da goya Hamid ta bar gidan.
Kamar yadda Sahura ta ɗauki shawarar 'yar ƙuda na janye ƙudirinta a kan Mairi har sai Jamila ta bar gidan hakan ta faru. Kwanaki huɗun da Jamila ta yi a gidan, Sahura bata nuna wani iko a kan Mairi ba,hasalima sabgar gabanta take tana jan Mairi a jiki saboda tsabar iya ƙwarewa a makirci. Jamila dai kallonta take kwata-kwata bata yarda da ita ba,jira take ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi ta sammaceta,sannan kwana huɗun da ta yi a gidan kullum sai ta tashi Mairi sallar dare. Jamila mace ce mai riƙo da addini,a fuskarta kaɗai za ka fahimci hakan,wawakeken tabon sallah ne raɗau a goshinta,sai ya ƙara fito da kyawunta ziryan. A rana ta huɗu Jamila ta koma Mada. Ko awa biyu ba a yi da tafiyan ta ba Dauda Imamu ya yi musu saukan bazata. Cike da farinciki suka tarbe shi tare da shirya masa kirki na musamman a tare kamar ƙawaye a kicin,nan kuwa Sahura sake jaddada mata maganar tafiyan take. Da daddare bayan sun kammala cin abinci ya ba kowa tsarabarsa sannan ya yi gyaran murya
''To Alhamdulillah na je na ga wuri,kuma ya yi mini ɗari bisa ɗari. Don haka Sahura zan sakaki islamiyya sai na tafi da Mairi,zan dinga zuwa wurinki a duk wata uku zuwa shekara ɗaya sai Mairi ta dawo ke kuma Sahura na tafi da ke''
''Malam ina da magana'' Mairi ta ce cike da sanyin murya.
''Ina saurare'' ya faɗa yana dubanta da murmushi. Miyau mai kauri ta haɗiye tana satar kallon Sahura da ta tsareta da manyan idanunta sannan ta ce
''Idan so samu ne ka tafi da Sahura Kadunan,wani zuwan sai ka tafi da ni''
''Mene ne dalilin yin hakan'' ya faɗa a ɗaure yana dubanta. Ɗan muskutawa ta yi tana gyara kwanciyar Jalil a saman cinyarta ta ce
''Saboda makarantarmu,mun yi nisa sosai. Yasir ma daidai gwargwado ya fara ɗaukar karatu. ''
Kallonta yake a hasken wutan lantarkin baya ko ƙyafta ido,ba yi zaton irin wannan furucin zai fito daga bakinta ba. Amma sai ya dake tare da faɗin
''To babu damuwa tun da ke da kanki kika bayar da shawarar. Zuwa jibi ne tafiyar. Tun da yanzu an sauya tsari zan tafi da Sahura madadinki. Yau zan kwana a ɗakin Sahura amma sauran kwanakin da zan yi kafin tafiyarmu zan yi su ne a ɗakinki. Fatan dai baku da wata matsala,ko na rashin lafiya?"
Dukkaninsu suka furta ''A'a''. Cike da farinciki Sahura ta miƙe zuwa ɗakinta don ta yi amfani da kayan matan da Gwaggwon Bugaje ta bata kafin Dauda Imamu ya shigo. A can falo wata uwar harara Dauda Imamu ya wurga ma Mairi yana ficewa daga ɗakin. Ba sai an faɗa mata ba,ta san harar me take nufi. Bata san wasu jimloli ya dace ta yi amfani da su wurin fahimtar da shi ba laifita ba ne,hasalima tana da burin zuwa Kadunan,don yadda take jin labarin tsaruwan garin da wayewar mutanen cikinta. Jin zuciyarta take wasai kamar an cire mata ƙaton dutsen da ya danne zuciyar. Aiwatar da umarnin Sahura kamar ƙayace mai tsini ta yi nasarar cirewa daga maƙogaronta. A wani ɓangare na zuciyarta ta yi farinciki da tafiyan Sahura,ko ba komai za ta kuɓuta daga huƙubarta da take shirin ɗaura mata da rana tsaka na aikin gida da rainon Hamid. Sannan za ta dage da sallolin dare koda kuwa gangar jikinta da ruhinta suna kalubalentarta. Wuridan da Jamila ta bata za ta dinga yinsu koda kuwa bakinta ya yi mata nauyi. Tun washe garin da Sahura ta dawo gidan ibadarta ta fara samun tangarɗa,amma idan ta tafi za ta mayar da hankalinta kacokar ga bauta wa Mahaliccinta. A hankali ta miƙe da Jalil a hannu ta wuce ɗaki ta kwantar da shi. Ta sake dawowa falon ta ɗauki Yasir da ke saman kujera ta wuce da shi ɗakin ta kwantar da shi,daga bisani ta sauya kaya zuwa ɗauron ƙirji ta kwanta.
A ɓangaren Sahura ta yi amfani da kayan matan kamar yadda mahaifiyarta ta sanar mata,na sha ta sha,na mitsi ta yi matsi sai ta goga turaren sannan ta haye saman gadon,murmushi yaƙi barin fuskarta. Bata jima da kwanciya ba ta ji muryar Dauda Imamu a ɗakin Mairi,tsaki ta ja tare da yin ƙwafa, a ranta ta furta 'Kai ma ka kusa shigowa hannuna,duk sonka da zuwan Mairi Kaduna wallahi ba zan bari ba koda kuwa zan tsafi tsirara...'
''Assalamu Alaikum '' Dauda Imamu ya yi sallama yana katse mata tunani. Firgigit da dawo daga duniyar tunani tare da amsa masa sallama tana tashi daga kwancen. A ɗaure ya shigo ɗakin,kai tsayye ya shimfiɗa darduma ya zauna samanta. Al'qur'an mai tsarki ya fara karantawa aya bayan aya a nutse. A gefe guda babu abin da idanun Sahura suke sai hararan bayansa take kamar idanunta za su firfito. Kalaman mahaifiyarta suna mata amsa-kuwwa a na'urar sauraronta
''Ko kusa Uwata. An dace. Sai dai naki ba irin na sauran 'yan'uwanki ba ne. Boka Ataka ya ce za ki mallake kishiyarki yanzu amma mijinki sai nan da shekara huɗu, saboda mai riƙo da addini akwaii wuyar mallaka. Kin san mijinki ya fi Malam nutso a kogon ilimin addini.''
Sake hararan bayansa ta yi sai ta zame ta kwanta zuciyarta na mata ƙuna. Saboda addininsa ne ta kasa mallake shi. Madadin karatun Alkur'anin ya sanyaya zuciyarta,sai ma kara sa zuciyarta tafasa yake. Ta daɗe bata yi bacci ba,a tunaninta zai kammala karatun ya hau gado amma sai ta ga kamar bai da niyyar kwanciyar,sai kawai ta gyara kwanciyarta. Ko mintuna ashirin ba a yi ba bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita. Dauda Imamu da bai san tana yi ba ya ci gaba muraji'ar karatunsa kasancewar mahaddacin alkur'ani ne mai girma. Ya jima yana karatun daga bisani ya rufe al'qur'anin ya yi addu'o'i sannan ya hau gadon ya kwanta. Sahura bata ma san lokacin da ya hau gadon ba.
Washegari ya koma ɗakin Mairi inda a nan ya yi kwana uku,a cikin kwanakin ya saka Yasir a makarantar boko ,Jalil kuma islamiyya. Sai da ya tabbatar ya bar mata komai da za ta buƙata sannan suka tafi. Daman kuɗin cefane Sadiƙu yake aikowa a kawo mata kullum da rana,wani lokacin har da kifi ko nama. Ta ji babu daɗi a lokacin da suka tafi amma ya ta iya,tana fatan hakan ya zamanto alkhairi agareta da ita da yaranta...✍️
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
Airforce Base. Jihar Kaduna. Nijeriya
Su Sahura da rana suka iso barikin,sai aikin ware ido take tana kallon sojoji cikin kaki da fararen hula,kowa sai harkar gabansa yake. A gate din shiga barikin motar ta sauke su,sai suka karasa inda mutane ke tsaye,suna mika takardar shedar shiga sannan sojojin suke barinsu. Sannu a hankali har suka iso wurin. Wani inyamurin soja ya dubi Dauda Imamu ya ce
''Oga! Make me see your I.D card and your madam''
Da yake Dauda Imamu ya ɗan iya turanci daidai misali ya miƙa I.D card ɗin dinga aka yi masa a lokacin da ya zo barikin sannan ya ce
''My wife na new here. I go do I.D card for her. Sorry officer'' Dauda Imamu ya faɗa yana rungume hannunsa alamun roƙo. Sahura sai rarraba ido take a tsakaninsu tana washe baki,jin suna turanci. Ɗaya daga cikin burinta kenan ta ga tana baza turanci har da baƙar magana a ciki. Sojan matsa musu ya yi suka wuce ciki da kayansu. Sun shiga kenan cikin sa a wata mota ta tsaya suka shiga ciki da kayansu. Da yake direban musulmi ne sai ya tambayi ina ne block dinsu domin ya sauƙaƙa musu tafiyar duba da yawan kayansu. Cike da farinciki Dauda Imamu ya sanar masa ginin da ke kusa da sabon masallacin juma'a zai saukesu. Daga jin haka ya ƙara ma motarsa gudu har suka isa sannan ya saukesu ya juya,godiya sosai Dauda Imamu ya yi masa sannan ya karasa block ɗinsu.
Flat ne babba kusa da sabon masallacin,yayin da sabuwar makarantar ke ɗan gaba da su kaɗan . Kai tsaye Dauda Imamu ya ɗauki kayan Sahura na biye da shi suka ƙarasa ƙofar flat ɗin. Mukulli ya sa ya buɗe sannan ya shiga,Sahura ta biyo shi ciki. Bude baki Sahura ta yi tana kallon yadda falon ya tsaru, kujeru ne na gani na faɗa a falon. Cire mayafinta ta yi ta shiga duka ɗakunan ciki. Uwar ɗaka uku ne sannan kowanne da bayi a ciki. Akwai gado a kowani ɗaki da wurin ajiye kaya. Farinciki mara misaltuwa ya mamaye zuciyarta. A ranta ta furta 'Aljannar duniya. Ina ni ina barin Mairi shigowa wannan aljannar'
'' Kayan na kai su ɗakin da zamu zauna ki shiryasu cikin wardrobe,ni zan je siyo kayan abinci da wasu abubuwan da za mu buƙata.'' ya gama faɗin haka ya bar ɗakin. Fitowa ta yi zuwa ɗayen ɗaki. Kakkaɓa gadon ta fara yi sannan ta ciro zanin gadon da ta zo dashi ta shimfiɗa tare da kwantar da Hamid. Kayan ta shiga cirowa daki-daki tana saka su a cikin wardrobe din tana waƙar mamman shata. Murmushi ya ƙi barin fuskarta har ta gama. Daman Sahura gwanar tsafta ce,kan ka ce me ta gyara flat ɗin tsaf. Ta fesa turare a ɗakin. Dauda Imamu ya ɗan jima sosai kafin ya dawo. Sai kusan bayan Asr ya shigo ɗakin lokacin tana riƙe da Hamid,ya shigo da kaya niƙi-niƙi a hannu ya ajiye sannan ya sake fita ya dauko sauran a ƙaton buhu. Tun a shigowarsa ta farko ta kwantar da Hamid saman kujerar sannan ta mike zuwa inda ya ajiye kayan ta bubbuɗe. Kayan abinci ta wuce da su cikin kicin da ke cikin falon. Kayan shafa kuma ta kai su uwar ɗakansu. Kayan da Dauda Imamu ya shigo da su na buhu ya wuce da su kicin din kai tsaye. Bokiti,risho,kayan saka abinci da duk abin da ya san mace tana bukata na girki,har da ashana sai da ya siyo, duba da inda suke ba lallai su samu a shaguna a ciki ba. Saboda ba ya son ta shiga maƙota roƙon ya sa ya siyo duk abin da ya san za ta buƙata.
Nan da nan Sahura ta gyara kicin ɗin tare da ɗaura girki mai saukin dafawa. Dauda Imamu na falo yana wasa da Hamid don zuwa yanzu yana dariya duk da bai fara zama ba. Cike da annashuwa take girkin tana 'yan waƙe-waƙenta. Jinta take kamar su dawwama a haka,ita tana musu girki a kicin ,Dauda Imamu na falo da Hamid su kaɗai abinsu. Jollof ɗin taliya ta yi,ta wanke plate ta sako mishi ita ma ta sako wa kanta. Ba wata hira suke ba,a nutse suke cin abinci,Hamid na tsotso. Bayan ya kammala ci ya fita,ita kuma ta kwashe kayan ta wuce da su kicin da wanke. Falon ta dawo,can ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Tsam! Ta miƙe zuwa ƙofar ta buɗe. Wata matashiyar mata ta gani sa'ar yayarta Halima wacce ta rasu. Da alamu ba musulma ba ce
''Welcome madam''
Kalmar madam kaɗai ta iya tsinta daga maganarta . Ta rasa yadda za ta bata amsa,ko harafin A bata sani ba. Ɗif! Take ba bokon ba islamiyyar.
''Ni ba turanci fa" Sahura ta faɗa tana sakar mata murmushi. Abinka da 'yar bariki,yawan tafiyansu barikin sojoji musamman na arewacin Nijeriya ya sa ta iya Hausa duk da ba sosai ba
''Ni na iya hausa kadan kadan. Ina zuwa bariki na north. Shi ya sa nake maka Hausa. Ni neighbor naka ne matar pastor John. Sunana Ngozi ko mama Eze, Yarana four. Chioma,Obichukwu,Emeka and Eze''
Murmushi Sahura ta yi,babu laifi ta fahimceta.
''Na gode sosai. Ni sunana Sahura yarona ɗaya,kin ganshi nan sunansa Hamid'' ta faɗa tana miƙa mata Hamid. Babu musu mama Eze ta amshi Hamid tana dariya. Sai wasa take masa tana cewa ''fine boy! Fine boy'' Sahura ba ta fahimci maganar mama Eze ba ne,sai dai yadda take mishi rawa tana maganar ya tabbatar mata wasa take masa. Sun jima a tsaye daga bisani mama Eze ta wuce bayan ta miƙa Hamid,Sahura ta koma ciki. Haka rayuwa ta ci gaba da gudana a nan barikin inda Sahura ta yi sabbin abokan zama Hausawa sa'onninta bayan mama Eze. Duk kashedin da Dauda Imamu ya yi mata a kan babu ruwanta da shiga sabgar mutanen barikin amma ta yi fatali da zankutansa. Idan ya tafi Islamiyya ko masallaci sai ta fito waje su yi ta hira da mantan hausawan,wani lokacin har da mama Eze idan maganar ta shafeta. Cikin ƙanƙanin lokaci kowa ya santa a ɓangaren,duk da ita ɓarayinta daban. Flat din Imam da pastor daban yake da sauran blocks ɗin,amma tsabar son gulma,sai da ta san yadda ta jawo matan hausan jiki,suna kiranta da matar Imamu ko maman Hamid.
A can Zamfara tun bayan tafiyansu su Sahura Mairi ta samu kwanciyar hankali,sannan tana zuwa islamiyya abinta, tsoron da take ji a kan Sahura ta rage jinsa. Ta yi ƙiba da ita da yaranta,babu wata damuwa a ranta.
Wata uku da zuwansu barikin Dauda Imamu ya tafi Zamfara,Sahura ta yi baƙin cikin tafiyarsa duk da bata nuna a fili ba amma hakan ya kona mata rai sosai. Watansa guda cur ya dawo Kaduna. Sahura ta yi sabo da 'yan bangaren da suke da na kusa da su sosai,har mazan sojojin sun santa,don akwai aukin gaisuwa da maza. Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya. Watansu Sahura shida da zuwa bariki. Hamid kuma yana da wata takwas a duniya. Zuwa yanzu Hamid ya iya rarrafe sannan ya yi wayo sosai. Ana gobe Dauda Imamu zai tafi Zamfara Sahura ta fara zazzaɓin mai tsanani tare da amai,Hamid kuma zazzaɓi .Hankali tashe ya kai su asibitin barikin.Inda a nan aka yi mata 'yan gwaje-gwaje, shi kuma Hamid aka ba shi magunguna sannan suka fito reception jiran sakamako. Hamid na hannun Dauda Imamu yana masa wasa,ita kuma ta langwaɓe saman kujerar ta lumshe ido. Can wata nurse ta fito tare da kiran Sahura Kabiru ta shigo. Tare suka ciki da Dauda Imamu. Wurin zaman marasa lafiya suka zauna suna fuskantar likitan. 'yan rubuce-rubuce ya yi ya ɗago yana dubansu ya ce...✍️
Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️
***