Chapter 13
The Amazing Pen ✍️.......
BAHAGON TUNANI
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
013
Wa'azi mai ratsa jini da ɓargo Dauda Imamu ya yi masa. Sosai jikinsa ya yi sanya kamar ruwa ya cinyeshi. Sai da ya dawo cikin hayyacinshi sannan ya aiki Mairi ta kira 'yar ƙuda. Saleh ya so hanawa amma Dauda Imamu ya dakatar da shi. Ta jima 'yar ƙuda bata shigo gidan ba,har sun cira rai a kan zuwanta,sai can ta shigo gidan bagazan-bazagan kamar an korota,tana gaba yaran suna biye da ita. Wawan tsaki Saleh ya ja tare da faɗin
''Ai ka ga irinta,ta shigo giidan mutane babu sallama . A haka kake ba ni haƙuri a kan na mayar da ita''
''Ai babu aure a tsakaninki yanzu Saleh. Karka manta a kunnunwan jama'a jiya ka shelanta ka saketa saki biyu,yau kuma ka ce ka saketa sau babu adadi''
''Baban Yasir! Wallahi ban saku ba! '' ta furta tana zama a gefan tabarmar. Murmushi Dauda Imamu ya yi
''Ga shi nan kusa da ke ki tambayeshi''
''Malam ai cikin ɓacin rai ne na yi sakin'' Saleh ya faɗa fuskarsa kwance da damuwa kamar ba shi ya gama masifa ɗazu ba.
''Uhm! Ai ta saku. Kar ka manta magana zarar bunu ce,idan ka furta baka san ina zata je ta dawo ba...''. Kafin ya ƙarashe maganar 'yar ƙuda ta fashe da kuka tana faɗin
''Wallahi ban saku ba! Ni ina son mijina! Ba zan je ko'ina ba! Heeeeeeee!"
Zuwa yanzu jikin Saleh ya yi sanyi gabakiɗaya. Ba wai baya son matarsa ba ne,ƙazantarta da rashin yi masa biyayya ne ya sabbaba mishi wannan aika-aikar da kuma ɓacin rai. Dukkaninsu ya haɗa ya yi musu nasiha mai shiga jiki. Sosai jikinsu ya sake yin sanyi musammman Saleh da takaicin duniya ya addabeshi saboda katoɓarar da ya yi. A nan 'yar kuda ta hakura a kan zuwa gobe za ta haɗa kayanta ta koma garinsu,yaran kuma Saleh zai kai su wurin mahaifiyarsa,idan da rabon ta dawo bayan ta yi wani aure ta fito sai ta dawon. Saleh ya ji babu daɗi a ransa amma ta wani ɓangaren yana mata fatan gyaruwa saboda nan gaba. Yadda ya yi hakuri da ita ba kowani namiji zai yi ba. Bayan sun fahimci juna suka masa godiya tare da barin gidan. Sai a sannan Dauda Imamu ya sauke wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Ko ba komai hankalinsa da na 'yan unguwa za su kwanta. Cikin ɗakin ya koma sai Mairi ta fito kicin ɗaura abin kari.
Wannan karon ya sake tuntubar Mairi ko Sahura ta dawo,sai ita ta tafi amma sai taƙi a kan tafi son zaman Gusau a kan bariki. Ba don rai ya so ba ya haƙura. Abin da bai sani ba shi ne,zantukan Sahura ne suke mata amsa-kuwwa a duk lokacin da ya yi mata maganar tafiya Bariki. Bata manta gardadin da ta yi mata ba,duk da tsoron da take ji a kan yanzu ya ragu ba kamar lokacin da take gidan. A hankali kwanaki suke ja. Dauda Imamu ji yake kamar kar ya rabu da Mairi,don kulawa ta musamman take ba shi. Watansa daya da kwana uku ya koma Kaduna. Bayan tafiyarsa Mairi ta fara shirin zuwa Mada bikin yaran Kawunta guda biyu da za a yi a rana ɗaya. Ana saura Sati ɗaya biki ta taho Mada. A gidan Jamila ta sauka,da yake gidanta babba ne,akwai wadatattun ɗakunan baƙi a sashenta da na kishiyarta. Da yake mijin babu laifi yana da arziƙi daidai gwargwado. Da yamma suka iso garin,ta tari mai mashin ya kaisu unguwarsu Jamila. Tana sauka ana kiran sallar magrib,bayan ta sallameshi suka shiga gidan da sallama a bisa laɓɓansu.
''Oyoyon Maman Yasir. Bismillah ku shiga ciki '' Jamila ta faɗa tana kammala alwarta tare da riko hannun Yasir suka nufi ɗakin. Mairi na sauke Jalil ta ɗauki buta ta zagaya bayi,tun a hanya take matse fitsarin babu damar tsayawa. Bayan ta fito ta yi alwala sannan ta koma ɗakin,zuwa lokacin Jamila ta kammala sallah har ta zuba ma su Yasir abinci sun fara ci. Dadduma ta shimfiɗa tare da kabbarta sallah,bayan ta idar Jamila ta kawo mata abinci tare da ruwa. Sai ta koma gefe tana hira da su Yasir,idan Jalil ya faɗi wata magana sai ta kwashe da dariya. Jamila na son yara sosai amma har yanzu shiru,ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Yaran kishiyarta ne wani lokacin suke zuwa ɗibe mata kewa. Da yake suna zaman amana da kishiyarta,da wuya ka ji an rabasu ko kuma cacar baki,kowa ya san halin kowa. Jamila da na zafi nan da nan take hawa dokin zuciya,amma tana da saurin sauka kuma bata da riƙo a zuciya. Kishiyarta kuma na da haƙuri da kawaici sosai,duk hukuncin da Jamila take yankewa a kan yaranta ba ɗaga kai ta kalla balle ta ga ko ta yi son zuciyarta. Har cikin ƙoƙon ranta bata ji zafi ba, shi ya sa tafiyarsu ta zo ɗaya,komai tare suke yi,babu mai jinsu. A kodayaushe idan an tashi misali a unguwar indai a kan zaman lafiya da su ake buga misali. A natse take cin abincin,jefi-jefi tana saka musu baki har ta kammala.
''Ba za ki turakar mijinki ba ne? '' ta yi tambayar tana dubansu cike da soyayyar 'yan'uwantaka..
''Yau ba ni ke da kwana ba. Ambalelen mamanshi'' ta kai karshe da ɗaga Jalil sama yana dariya. Kwanukan ta kai kicin na waje sannan ta dawo ciki. Ɗaya daga cikin kujerun ta zauna bakinsa ɗauke da bismillah.
''Yaya saduwa ta yi wuya,rabon da na zo Gusau na y watanni. Wannan makirar kishiyarta ki da jego. Halan yanzu ta yayeshi'' cewar Jamila tana sauke Jalil ƙasa inda Yasir ke wasa,sai ta dawo kusa da kujerar Mairi.
''Sahura na Barikin sojoji na Kaduna''
''Bariki! Wa ya kaita barikin?"
''Shaf na manta lokacin da kika zo na faɗa miki limancin da Baba Yasir ya samu tare da koyarwa a barikin,ranar da kika tafi ko awa biyu ba a yi ba ya dawo''
Mamaki fal ranta ta ce
''Amma gaskiya Dauda bai yi adalci a nan ba,ta ya kina uwar gida,zai tsallakeki ya ɗauki amarya. Ai wannan rashin adalci ne ƙarara. To ke sai yaushe zaki barikin?"
''Hmmm'' Mairi ta ce domin an zo gaɓar da bata da amsar tambayar. Ta san ba laifin Dauda Imamu ba ne,hasalima ya fi so ya tafi da ita a kan Sahura. Duk zuwan da zai yi sai ya sake tambayar ko za ta bi shi Sahura da dawo. Ba za su gane halin da take ciki ba,duk yadda ta so fahimtar da su ba za su gane ba. Zuciyarta ta riga da ta tsorota da Sahura,duk da yanzu da basu tare tsoron ya ragu.
''Yaya an ya matar nan ba kisan mummuƙe take miki ba?"
Da sauri Mairi ta girgiza kanta da faɗin ''Ko kusa Jamila''
Kallonta take bata ko ƙyafta ido, kwata-kwata zuciyarta bata gasgata zantukan yayarta ba,akwai abin da take boyewa wanda yake cutar da ita. Matsowa ta yi kusa da ita, fuskarta shimfiɗe da tsantsar damuwa,hannayanta biyu ta kamo idanunta na kallon fuskar Mairi ta fara magana cikin sanyin murya
''Yaya! Me ya sa kike son ɓoye mini damuwarki alhalin fuskarki ta gama fallasa sirrin da ke cikin zuciyarki? Me ya sa kike son binne damuwarki alhalin ƙwayar idanunki sun nuna damuwarki a zahiri! Ke kaɗai na mallaka a doron duniya! Ba mu da uwa haka zalika ba mu da uba, mun taso a ƙarƙashin inuwa ɗaya da taimakon Ubangiji muka rayu,da daɗi babu daɗi mun yi haƙuri. Yanzu Yaya idan baki fada mini damuwarki ba,wane ne a duniyar nan za ki faɗa ma damuwarki. Me ya sa Yaya!" Zuwa lokacin idanunta sun kawo ruwa. Ba a maganar Mairi,domin kamar Jamila ta fama mata mikin da ke cikin zuciyarta ,tun da ta fara magana jikinta ya yi sanyi,idanuwanta suka fara zubda ƙwalla bi da bi. Tabbas zuciyarta na cunkushe da tarin damuwa. A tunaninta auran da Dauda Imamu ya yi zai zamanto mata sauƙi cikin rayuwarta,ashe ba a nan gizo ke sakar ba. Mijinta da take hanyen a matsayin tubali yanzu sai ta yi wata uku bata saka shi a ido ba. Ga tsoron kishiyarta da ya cika ƙoƙon ranta ,don ma yanzu ta dage da addu'a ba kamar lokacin da take gidan ba. Tana son bin mijinta Kaduna amma bakinta da zuciyarta sun ƙi bata haɗin kai. A duk lokacin da mijinta ya furta ko za ta bi shi Kaduna,sai ta ji zuciyarta na mata zafi,bakinta kamar an saka kwaɗo a kulle,take kalaman kishiyarta su shiga kai-kawo a ƙwaƙwalwarta,idanunwanta su rika hangen majigin kishiyarta tana zare mata ido kamar a lokacin take magana.
''Yaya kin yi shiru! Ko ban cancanci sanin damuwarki ba ne...''
''Ko kusa Jamila! Kin cancanci sanin abin da yafi ma damuwata. Ban san ta ina zan fara sanar miki ɗumbin damuwar da ke cikin raina ba. A gaskiya baki yi karya ba,ina cikin kogin damuwa tsamo-tsamo''
''Bari mu yi sallah yaya. Na ji ana kira yanzu'' Jamila ta faɗa tana miƙewa lokaci guda. Shimfiɗa daddumar ta yi,Mairi ma ta miƙe tare da ɗaukar Yasir da ya fara gyangyadi ta kwantar da shi saman kujera mai cin mutum biyu,ta matsar da Jalil da ke wasa a gefe,suka kabbarta sallah a tare. Sun dora da shafa'i sannan suka sallame. Suna cikin addu'a mijin Jamila ya shigo ɗakin da sallama. Mairi ta amsa sallamar,cikin mutuntawa suka gaisa yana tambayar yaranta har Jamila ta kammala addu'o'in ta ajiye hijabin a gefe sannan ta yi mishi sannu da zuwa. Sun jima suna hira daga bisani ya yi musu sallama tare da ajiye leda ɗaya ya fita. Daddaɗan ƙamshi ne ya daki ƙofofin hancin Jamila har tana lumshe ido lokacin da ta kwance ledar, tsire ne ya ji albasa da kabeji sai tashin ƙamshi yake, lokaci guɗa ƙamshin ɗakin ya sauya zuwa ƙamshin tsire. Buɗe takardar Jamila ta yi da kyau sannan suka fara ci suna hira kamar basu da wata damuwa. Sun ci sosai sannan Jamila ta ajiye sauran cikin kwalla da safe sai ta ba su Jalil. Zuwa yanzu Jalil ya yi bacci sai Mairi ta kwantar da shi a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin. Kusa da Jamila ta zauna.
''Yawwa yaya! Sanar mini damuwarki yanzu-yanzu ba da jimawa na kawo miki maslaha in shaa Allah,idan na tayaki addu'a ne zan kara ƙaimi,idan kuma kishiyarki ce take hanaki rawar gaban hantsi,zan yi mata takakka daga nan har zuwa Kaduna in cicci mata mutunci ko gaban Dauda Imamu ne''
'yar dariya Mairi ta yi,tabbas abin da ƙanwarta ta faɗa babu ƙarya,domin babu abin da ba za ta iya aikatawa a ciki. Tun suna yara take shige mata faɗa ko cacar baki,da hannunta take siyan faɗanta duk don ta faranta mata, saboda ta san ba iya ramawa za ta yi ba. Babu wacce a duniya ya dace da ta san damuwarta sai Jamila. Gyara zama ta yi tana duban ƙanwarta a hasken lantarkin da ya wadaci ɗakin,ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce
''Jamila akwai abu ɗaya da ya rikiɗa zuwa alburushi yana harbin ruhina. Ba kowa ya rikiɗa zuwa wannan alburushin ba illa kishiyata Sahura. Ban samu matsala da ita lokacin da tana amarya ba,duk wani aikin gida da wankan yara ta ɗauke mini su,duk da na hanata amma sai ta ce mini babu komai,har zuwa haihuwarta ban samu matsala da ita ba. A washegarin ranar da ta dawo daga wankan jego ne komai ya sauya. Tun lokacin da ta girka mana abinci na ci,na rasa gane kaina. Tsantsar tsoranta ya dirar wa zuciyata tamkar dirar mikiya,sunana kawai ta ambata amma kamar ana juya gangar jikina da ruhina,a sukwane na je ɗakinta duk da kiran rainin hankali ta mini. Ina tozali da idanunta tsoronta ya shiga bin jijiyoyin jikina yana isa ƙwaƙwalwata. Kamar uwata haka ta shiga zare mini idanu da gasa mini maganganun da duk suka zo bakinta. Jamila wallahi ban san me ya shiga kaina ba,har na tsaya kishiyata na sakar mini baƙaken maganganu kamar uwata ko mijina,duk hakurina akwai abubuwan da ba zan ɗauka ba. A lokacin ne take sanar mini kar na kuskura na yarda na bi baban Yasir Kaduna,na kuma dage a kan lallai da ita zai je Kadunan,sannan koda watarana ya ce zai tafi da ni a kan ta dawo kar na aminta. In takaice miki kamar wacce ake kaɗawa da ruwan hanji,na shiga jinjina mata kai, wani sashen zuciyata na riya mini kar na aminta,wani sashen da tilastani aminta. A ranar har aiki ta saka ni gidan 'yar ƙuda, lokacin da kika ganni daga gidanta nake. Don har aikin gida ta ce ni zan dinga yi,inda Allah ya tarfa ma garina nono kuwa ya ceceni sai gaki kin zo,kuma da alamu tana shakkarki,a ranar da kika ta fi a ranar Baban Yasir ya dawo. Duk da tsoronta ya ragu sakamakon addu'o'in da kika ba ni da sallar daren da nake yi,amma har yanzu gangar jikina taƙi ba ni haɗin kai. Ko zuwan nan da Baban Yasir ya yi ya so mu tafi amma abu kamar almara,sai ga zantukanta suka sake dawowan cikin kwanyata kamar yanzu take faɗa mini. Wallahi ina cikin damuwa 'yar'uwaaaaaaa!....'' ta ƙarashe maganar tana sakin kuka mai tsuma rai. Jamila tamkar ta fashe tsabar ɓacin rai da hucin da take, biri ya yi kama da mutum,shi ya sa kwata-kwata zuciyarta bata yarda da ita ba. Ashe da bindigar ƙasa take kai ma tilon 'yar'uwarta farmaƙe. Lallai kuwa za ta san ta taɓo Jamila,da ayar Allah za ta yi maganinta. Don ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara ba aikin asiri ne wannan. Wata nauyayyar ajiyar zuciya Jamila ta sauke,a hankali ta saka hannu tana goge hawayen yayarta,zuciyarta na tafasa, a ranta tana fadin 'Sahura ki guji ranta zan yi arba da ke,wallahi mai rabani da ke sai Allah. Yadda kika saka yayata kuka,sai na sakaki kukan jini' a zahiri ta ce
''Tabbas kina cikin damuwa yaya. Daga jin labarinki na gasgata aikin sihirin mallaka ne. Yaya kishiyarki ta mallakeki ne,Allah ya sa baki da rabon shan wuya a hannunta. Da ta mayar da ke kamar baiwa. Ubangiji ya ce Kowace cuta tana da magani in shaa Allah komai ya zo ƙarshe. Akwai wasu sahihan addu'o'in da zan baki ki yi,da yardar Allah sihirin da ke jikinki da sannu a hankali zai lalace''
Ɗan numfasawa ta yi sanna ta ci gaba da cewa...✍️
Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️
***