BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

Chapter 14

by @narrnarhhbukar00

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

014

Ɗan numfasawa ta yi sanna ta ci gaba da cewa...✍️

''Ni ma malaminmu ne ya bamu a islamiyya,ya ce tana da matukar tasiri sosai,kowani nau'in asiri idan ka lizimcesu da sannu za ka samu waraka. Ki samu ruwan zamzam,kaɗan ko mai yawa duk yanda ya yi miki. Idan kin kammala sallar nafila ko farilla,sai ki zauna,ki matso da ruwan gabanki sannan ki fara da bismillah da karantu Suratul Fatiha kina ƙirgawa da hannunki na dama har sau arba'in da ɗaya kina tofawa a ruwan,ana arba'in da ɗayan bayan kin kammala karanta fatihar sai ki karanta, Suratul Ahad da falaƙi da Nasi sau uku-uku kina tofawa a cikin ruwan zamzam ɗin,sai *_Ayatul Kursiyyu da Amanar Rasulu_ sau ɗaiɗaya,ki yi da tsakakakkiyar niyya a kan babu mai yaye cuta sai Allah,ki sha ruwa sai kki rage saura ki shafama fuskarki da jikinki bakiɗaya har da su Yasir. In shaa Allah da sannu za ki nemi tsoranta ki rasa. Sannan ki ƙulla ƙawance da sallar dare tare da Azkar ɗin safe da yamma,a duk lokacin da kika kai sujjada,ki roƙi Allah ya kareki ,mijinki da yaranki daga sharrin kishiyarki da duk wani masheranci in shaa Allah za ki ga komai ya sauya''

Wani daɗi Mairi ta ji a ranta,ta yi dacen 'yar'uwa mai yaye mata damuwa, yanzu tana da wannan ƙanwar ta yi nauyin baki.

''Na gode Jamila. Ashe ina da mai warware mini matsala na yi nauyin baki. Allah ya saka miki da mafificin akhairi,ya albarkaci rayuwarki ya kawo miki zuri'a mai albarkha''

Murmushin jin daɗi Jamila ta yi tare da faɗin

''Yaya zo mu kwanta dare ya fara yi''

''To'' daga haka ta miƙe, Mairi ta ɗauki Yasir, Jamila ta ɗauki Jalil suka wuce uwar ɗaka.

Washegarin ranar Mairi ta aika kasuwa aka siyo mata zamzam,kamar yadda Jamila ta fada mata yanda za ta yi haka ta yi. Tun ana saura kwana biyar biki gidan kawunsu ya cika da baƙi,da yake ya daɗe bai aurar ba. Da su aka yi komai aka gama,har da rakiyar amarya suka yi,bayan kwana uku Mairi ta zaga dangi suka gaisa washegarin ranar ta dawo Gusau.

Rayuwa ta ci gaba da lafiya da dadi babu daɗi,inda Mairi ta yi tsayi irin na daka wurin addu'a tana sha tana shafawa  haka su Yasir. Kwanaki suka zo suka wuce  haka watanni, shekaru da damar gaske suka shuɗe. Mairi ta ga sauyi sosai jikinta da ruhinta,zuwa yanzu ta yi hannun riga da tsoron Sahura. Jalil na da shekara huɗu a duniya ta haifo kyakkyawar mace mai kama da mahaifinta sak!. Kwana uku  tsakaninta da Sahura,macen ta sake haifa. Tun daga kan Hamid ta fara ƙazamin goyo,bata yaye shi ba ta samu cikin Saudatu,ita ma bata shekara ba ta sake samu wani cikin. Dauda iImamu ya yi zirga-zirga sosai tsakanin Gusau da Kaduna a satin sunan. Yariyar Mairi ta ci sunan Hamida,sai ta Sahura ta ci sunan Amina. Bayansu Hamida, Sahura ta sake haihuwar mace,ranar suna aka saka mata Halima. Da yake Sahura a gidanta take wankan jego,sai bayan arba'in take zuwa Sakkwato ziyara. Mairi tun daga kan Hamida bata kuma haihuwa sai ta Hamida ta cika shekara biyar cur a duniya,ta haifo kyakkyawar mace wacce ta biyota kwabo da kwabo bambanci launin fata ne,wasu har cewa suke da Jamila take kama saboda launin fatarsu ya zo ɗaya,fara ce sosai kamar ka tsagata jini ya fito. Har yanzu Jamila bata haihu ba,sai dai ta yi ɓari 'yan biyu har sau biyu. Soyayyar yarinyar ta kama zukatan mutane da dama musamman Dauda Imamu, tun da ta faɗo duniya soyayyarta ya cika zuciyarsa ta yadda misaltawa ɓata lokaci ne,duk cikin yaransa mazan da matan babu wacce yake jinta sosai a ƙoƙon ransa kamar jaririyyar,a ranar suna ta ci suna Aishatul Humaira,sunan mahaifiyarsa ya saka mata amma shi da kanshi ya ce za a dinga kiranta da HAFIZA Domin yana ji a cikin ranshi ita ce za ta gaje shi. A rana ɗaya Mairi ta haihu da Sahura,madadin a yi sunan a rana ɗaya sai ya ɗaga na Sahura  zuwa wani satin, inda aka fara na HAFIZA wani satin aka yi sunan Saharu a Kaduna,Dauda Imamu ya saka ma yarinyar Sahura suna Nu'aymah. Sosai ran Sahura da 'yan'uwanta suka yi matukar ɓaci,domin 'yan'uwanta sun zo suna suka iske ya ɗaga sunan kuma ya tafi Gusau sunan Mairi. Zuwa yanzu Dauda Imamu na da yara tara cif! Mairi na da huɗu: Yasir,Jalil sarkin zuciya,Hamida sai autarsu HAFIZA Al huda-huda sarkin karatu. Sahura na da biyar: Hamid uban 'yan rashin kunya,Saudatu amma ana kiranta da Aunty Saudah,Amina, Halima sai Nu'aymah 'yar gatan mamanta,don a duk cikin yaran Sahura babu wadda take matukar so irin Nu'aymah,tafi kama da ita sosai a kan sauran.

A duk waɗannan shekarun masu tarin yawa,Dauda Imamu bai fashi duk wata uku sai ya zo Gusau,da tafiya ta yi tafiya wata biyu yake a Kaduna ya zo Gusau ya yi wata biyu,da yake an karo limami ɗaya  don ya  taimaka masa duba da yana da iyayali a Gusau. Ya samu wannan taimakon ne a dalilin abokinsa na Sakandare wanda yanzu ya ke a matsayin lieutenant,shi ma uban gidansa ne ya taimaka,da yake yana da kishin addini. A ɓangaren Sahura kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu tsabar baƙin ciki,don wata ɗayan ma da yake yi a Gusau ji take kamar ta hanashi zuwa balle yanzu da yake wata biyu a can. Ƙarin haushin har  yanzu da ake shirin tafiya shekara ta takwas da zuwan Gwaggwon Bugaje wurin boka Ataka bata sauya zani ba, duk zuwa arba'in din take Sakkwato sai ta yi ma Gwaggwan bugaje ƙokafi a kan har yanzu bata ga aikin boka a kan Dauda Imamu ba. Koyaushe Gwaggwon Bugaje cikin kwantar mata da hankali take a kan ta yi haƙuri ƙila har yanzu ba su samu yin galaba a kan shi ba ne,haka za ta hakura ta dawo bariki,zuwa yanzu ɗawainiyar gida ya yi matuƙar mata yawa,saboda gwarnan da take

Kullum cikin aikin gida take,don ma yaran ƙawayenta na zuwa wani lokacin tayata aikin gida. Har yanzu Hamid na fitsarin kwance,ta nemi magani ita da Dauda Imamu har yanzu ba a dace ba. Gwaggwon Bugaje ta so riƙon Saudatu don ta rage mata ɗawainiyar gida amma Dauda Imamu ya murza ma idanshi kwalli a kan bai san wannan ba,bai da ra'ayin bayar da ɗanshi ga kowa. Abin duniya ya gama kaita wuya,farincikinta har yanzu Dauda Imamu bai ambaci za ta koma Gusau ba,a tunaninta har yanzu mallakar da ta yi ma Mairi bata warware ba. Abin da bata sani ba shi ne. Mairi da kanta ta ce ya bari zuwa nan da shekaru goma ko sha ɗaya lokacin Yasir ya isa shiga sakandare sai su koma can da zama na dindindin, ita kuma Sahura ta dawo Gusau da zama. Tun daga lokacin bai sake maganar tafiyanta bariki ba. Shi ma sai a lokacin ya ga tunaninta,hakan shi ne daidai. Tun daga kan HAFIZA Mairi bata sake haihuwa ba.

Yanzu haka Sahura wankan jego take, Nu'aymah na da shekara huɗu ta sake haihuwa,ita ta cike ta goma cif kuma auta. Sahura koyaushe cikin cewa take daga ita ta kulle ƙofa. Ta so Dauda Imamu ya saka mata sunan mahaifiyarta Maimuna,amma sai ta ji akasin haka a ranar suna inda ya saka ma diyar suna Maryam wato sunan kishiyarta. Sai da ta zubar da ƙwallan baƙin ciki . Dauda Imamu ya gama tozarta a duniya,a ce cin fuskarsa ya kai ya saka ma ɗiyarta sunan kishiyarta. Ta sha wuyan rainon ciki da haihuwarta amma ya rasa sunan da zai saka mata sai sunan kishiyarta. Ko a fuska bata nuna mishi ta ji haushin hakan ba,amma ta yi amanna wannan zuwan da za ta yi Sakkwato sai dai a yi mai yiwuwa,idan ta kama su canja boka ne,sai sun canja don ba za ta zuba ido ya dinga takata son ransa baa. Shekara sama da goma sha babu abin da take kurɓa sai maɗi. Gashi idan ya dawo daga Gusau bai da magana sai maganar HAFIZA, kullum cikin yabon HAFIZA yake,ga ta dududu shekarunta huɗu zuwa biyar  sa'ar Nu'aymah amma sai yaba ƙoƙarinta yake a boko da islamiyya. Nu'aymah da ko maganar kirki bata iya ba balle a zo gaɓar karatu. Tsabar ƙarya yake cewa HAFIZA ta haddace izu ɗaya a Al'qur'ani. To Hamid da Aunty Saudah ba su iya Al'qur'ani ba,su da suke manya balle su Amina da Halima,ƙarshensu Nu'aymah. Tun kan ta yi tozali da wannan HAFIZA ta ji ta tsaneta tsana mai tsanani. Kamar haɗin baki haka yaranta suka tsani HAFIZA da jin haushinta duk da ba su taɓa ganinta ba,idan ya tashi buga misali a kan mayar da hankali a karatu da HAFIZA yake kwatance.  Kwanci tashi babu wuya wurin Ubangiji,gobe Sahura take kammala wankan jekonta,zuwa jibi ta za ɗaga zuwa Sakkwato daman ta jima rabonta da Sakkwato tun yawon arba'in ɗin Nu'aymah,sai dai idan Dauda Imamu ya dawo daga can ya sanar mata suna lafiya sannan suna gaisheta. Wani lokacin gwaggwanta na aiko da sako ya bata wanda bai wuce maganin mata. Wani hauka da Sahura take shi ne ba su Aunty Sauda kayan mata,tun daga tsumi,tabaje,gumba da nakiya har waɗanda ma bai ta ce su shaba suna sha. Tun suna ƙi a tunaninsu magani ne har suka dawo suna sha cike da murna musamman Aunty Sauda da Amina,da kansu suke ɗaukowa a inda ta ɓoye su sha.

^^^^^^^^^^^^

Yau ta kama asabar ranar hutu amma hutun na su kusan duka ne saboda decemba suke,sun kammala jarabawa an ba su hutu, islamiyya ce ya rage a ba su hutun. Sai hakan ya yi ma Sahura daɗi a rai,sai su sha hutunsu a can,duk da yau take saka ran dawowar Dauda Imamu daga Gusau. Amma a gaskiya sai ta keɓe da uwarta don samun maslahar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Cikin dare ya dawo lokacin su Nu'aymah sun yi bacci sai Hamid da ke kallo a TV shi kaɗai. Sannu da zuwa ya yi mishi sannan ya ruga uwarɗakan mahaifiyarsu ya tashe a kan Baba ya dawo. Hamma ta yi tana mika sannan ta fito falon. Zuwa yanzu Sahura ta zama 'yar lukuta,ta ajiye shirgegen tumbi,ɗuwawukanta sun ƙara cikowa da girma haka nonuwanta. Sannu da zuwa ta yi mishi tana zama kusa da shi lokaci guda.

''Hamid! Je ka kwanta dare ya yi. Madadin ka ɗauko litattafanka ka duba ko karatun Alkur'ani sai ka ɓige da kallon wannan shiriritar. Zuwa gobe zan ji sakamakon kowa a makaranta''

Mikewa Hamid ya yi yana zumɓuro baki yana ƙuƙƙuni ƙasa-ƙasa kar mahaifinshi ya ji ya wuce ɗakinshi. Shi kaɗai yake kwana a ɗakin wanda babu abin ɗakin ke yi sai zarnin fitsari,wai don ma Sahura na iya bakin ƙoƙarinta a kanshi. Ƙazami ne na ajin farko. Ga shi da magagin bacci,idan ya farka da magagin har ɗakinsu Aunty Saudah yake zuwa ya fito da gabansa ya tsulala musu fitsari,su yi ta rantsuwar ba su ba ne,da yake ta san halin kayanta kuma ta san yana magagin bacci sai ta share tare da tsaftace wurin. Ranar da iskancin ya kai shi tsula fitsari a bisa jikinsu Dauda Imamu da Sahura ya ci duba kamar babu gobe. Ran Sahura ya ɓaci har suka so samun saɓani don ita bata ga laifinshi ba tun da magagin bacci yake ba a zahiri ba ne.

Bayan ya wuce ɗaki sai Sahura ta dubeshi ta ce

''Na kawo mata abinci ne,ko wanka za ka fara yi?''

''Wanka'' ya faɗa a gajarce yana ɗora kansa a hannun kujeran ɗakin tare da lumshe ido. A matukar gajiye ya dawo garin,motarsu sau uku tana tsayawa a hanya daga karshe ma juye driban ya yi a Zaria. Kai tsaye Sahura ta nufi kicin wanda zuwa yanzu an sauya komai na ciki zuwa na zamani,don Dauda Imamu akwai ƙoƙarin kyautawa iyalinsa. Ta fito da kuloli biyu ta ajiye a saman centre table da ke tsakiyan ɗakin,ta koma ta dauko plate da jug na ruwa da karamin kofi ta ajiye. Bayan ruwan ya yi zafi ta katse rishon tare da juyewa a bokitin wanka ta kai masa bayi ta riska. Tana fitowa ta ce masa ta kai ruwan bayi,za ta wuce ɗaki ya ce ta dawo ta jira shi akwai maganar da yake son su yi. Take ƙirjinta ya buga da matuƙar ƙarfi. Ɗauko Maryamu ta yi sannan ta dawo falon tana shayar da ita. Sai da ya shirya tsaf sannan ya dawo falon ya ci abinci. Ya yi gyatsa tare da hamdala ya ce

''Daman batun komawarki Gusau ce ya taso ke da yaranki''

Dummmmmm! Ƙirjinta ya yi mugun bugawan da ya kusan tafiya da numfashinta. Miyau mai kauri ta haɗiye sannan ta ce

''Kuma yaya Mairi ta yarda da hakan. Na ga bata son zama bariki''

'yar dariya Dauda Imamu ya yi sannan ya ce

''Mairin da kika sani ban da ta yanzu. Sosai take farinciki da hakan,hasalima ita da kanta ta ce sai Yasir ya shiga sakandare sannan su dawo da zama nan. Tun waccan shekaran na so dawowanta amma sai ta ce na bari wannan shekarar. ''

Shiru Sahura ta yi kamar ruwa ya cinyeta,take zufa ta shiga kwaranyo mata duk da a watan decemba ne kuma lokacin sanyi . ' Kai anya Mairi ce da kanta ta faɗi hakan! Ko dai ƙayar da yanzu ya koya ne yake son yi mini don ya dawo da Mairi! Ta furta a ranta. Ta yi amanna ta rufe bakin Mairi a kan wannan zancen,sannan ta yi mata mummunan kashedi! Bai ci a ce mallakar har ta warware ba duba da mallakar da Gwaggwonta ta yi ma kishiyoyinta,har yanzu tana baza ikonta a gidan,kullum gaba-gaba take ba baya ba,ta ya sai ita. 'Yan'uwanta ma suna cin karansu babu babba a gidan mazajensu,sai abin da suka ce ake yi. Ta ya na ta zai kasance daban.

''Ko bacci kike yi ne Sahura?"

''A'a baban Hamid,gajiya ce ta lulluɓe ni. Uhm! Yaushe ne za su dawo nan ɗin''

Gyara zama ya yi sannan ya ce...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***