Chapter 16
The Amazing Pen ✍️.......
BAHAGON TUNANI
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
016
Kallon ƙasƙanci Gwaggwan bugaje ta wurga mata tana yatsina fuska kamar ta ga kashi, sai can ta taɓe baki tana hura hanci. Tasallah kanta a ƙasa jikinta na tsuma kamar ta ji kiɗi disko
''Jikata na son cin taliya...''
''Har da nama'' Nu'aymah ta faɗa tana katseta. Murmushi Gwaggwon Bugaje ta yi sannan ta ce
''Kin ji da kunnuwanki ta ce har da nama, don haka cikin kuɗinki ki aika a siyo taliya a dafa mata da nama,idan ma balangu ne(Gasasshen nama)za ki siya a saka ciki ruwanki,ina so na ga taliyar da nama. Bana don jira! Don bata ci komai ba tun da ta zo''
''Yanzu-yanzun nan mai babban ɗaki'' ta faɗa cike da girmamawa tare da barin ɗakin jikinta bai bar kakkarwa ba. Ƙasaitaccen murmushi Gwaggwon Bugaje ta saki kanta na ƙara girma,giyar izza da ƙasaita suna janta.Tsufa ya fara yi mata sallama,gashin kanta a hankali yana sauyawa zuwa furfura amma jinta take kamar 'yar shekara talatin. Sahura kam shawa'ar yadda mahaifyarta ke juya kishiyoyinta ya cika zuciyarta,burinta a wannan karon bai wuce ta mallaki Dauda Imamu.
Bayan awa guda ta da tafiyar Tasallah ta aiko jikanta da kula ɗakin. Daban ta zuba ma Nu'aymah sai ta ba su Hamid sauran. Tas! Suka cinye har da suɗe kwanon,suka wanke hannu sannan suka kwanta duk da a lokacin ana haramar shiga masallaci ne,babu jimawa bacci ya ɗauki kowannansu saboda gajiya hanya.
Bayan Isha'i
A tare suka tafi sashen malam Kabiru,Sahura ta gaishe shi sannan ta dawo sashensu yayin da ta bar Maryam hannun gwaggwan bugaje . Bata jima da zama ba Gwaggwan bugaje ta shigo ɗakin tana rirriga Maryam. Cikin sauri ta amsheta ta cire nono ta fara shayar da ita,kusa da Sahura gwaggwan bugaje ta zauna tana mata kallon tsanaki.
''Da alama akwai magana a bakinki Sahura?"
Murmushin gefan baki ta yi tana kwantar da Maryam saman gadon sannan ta juyo,idanunta har sun sirka. Ƙwalla ta fara taruwa tun kan da furta abin da ke cikin ranta.Tana da tarin damuwa kwando-kwando ajiye cikin zuciyarta. Dole wannan karon ta yi nasara,dole ta mallake Dauda Imamu,dole kishiyarta da yaranta su dawo ƙarƙashin ikonta,ta juya su kamar yadda mahaifiyarta da yayyanta suke juya nasu. Gyara zama ta yi sannan ta fara magana cikin yanayi na damuwa
''Gwaggwo ban san salon da zan bi wurin burtso miki tarin damuwar da ke cunkushe cikin zuciyata ba. Wallahi ina matuƙar cutuwa. Ni ban ga amfanin mallakar da na yi ma Mairi ba, domin kamar na ƙara rura wutar soyayyarta ne cikin zuciyarsa. A baya wata ɗaya yake a Gusau ya dawo,inda mu kuma wata uku yake mana. Amma yanzu ta sauya zani tsabar rashin imani haka zai tsallakemu ya yi wata biyu cur! wani lokacin har da ɗoriya kafin ya dawo . Kullum idan yana gida bai da magana sai Mairi ta yi kaza! Ai Mairi ta iya kaza! Ko kuma idan fannin yara ne ya dinga yaban nata da saka musu albarkha musamman ƙaramarsu da yake yawan ambata. Kullum HAFIZA,ai HAFIZA tana da kaza. Ni nawa ko oho. Gwaggwo kina ganin zamanmu zai ɗore a haka. Yana yabon nata nawa kuma yana aibatasu. Wallahi da sake Gwaggwo! Ba zan koma bariki ba,sai na tabbatar da na mallaki Yaya Imamu. Ƙarin iskanci,jiya yake sanar mini da zarar mun dawo zai mayar da mu Gusau ita ta dawo bariki da zama na dindindin.Gwaggwo na gaji! Wallahi na gaji! Zuciyata kullum ƙara rauni take! Gwaggwo ki taimake niiiiii!...''
Rushewa ta yi da matsanancin kuka mai tsuma rai wanda hakan ya sakata kasa ƙarasa maganar,kukan tun daga ƙasan zuciyarta yake fitowa ba tare da tangarɗa ba. Tabbas zuciyarta na gab da tarwatsewa idan kunnuwanta ba su daina sauraron yadda Dauda Imamu ke yabon kishiyarta da yaransa ba. Wata nauyayyar zuciya Gwaggwon Bugaje ta sauke mai ƙarfi idanunwata ba su bar kallon Sahura ba. Sautin kukanta tamkar fetur ne da ke ƙara rura wutar da ke ƙone zuciyarta. A hankali ta fara magana
''Shara hawayenki Sahura,indai Dauda Imamu ne to...''
''Gwaggwo kuka na nawa zan share bayan baki aiwatar da komai ba. Tun lokacin da Hamid ya cika shekara huɗu a duniya nake kai kokena wurinki. Duk lokacin da zan zo yawon arba'in sai na miki ƙofari. Kullum cikin ba ni haƙuri kike. To yanzu tura ta kai bango Gwaggwo,idan har ban yi nasara a wannan karon ba,to ba zan taɓa yin nasara ba. Da zarar na bari Mairi da yaranta suka dawo bariki kashina ya bushe. Gwaggwo Idan bokan ya kasa ne,sai mu nemi wani,gari da yawa,ai maye ba zai ci kanshi ba''
Girgiza kai Gwaggwon Bugaje ta yi ta faɗin
''Ko kusa Sahura. Boka Ataka na musamman ne,kirarinsa mutum dubu jiran mutum ɗaya shiga hamadarsa kaɗai sai mai taurin zuciya. Tun da kika ga tsawon shekarun nan baki ga canji ba to ba laifinsa ba ne. Domin baya wasa da alƙawari,duk shekarun da za a yi sai ya cika. Karki manta matsalar daga wurin mijinki take kema kin sani. Shi karan kansa Boka Ataka ya sanar mini aikin mijinki akwai wuya saboda yana tsaye sosai a kan ibadarsa. Duk maluntar malam, Dauda ya damashi ya shanye. Zan sake komawa na ji daga ina matsalar take,don bana fatan ki koma Gusau. Ai kullum ci gaba ake so ba baya ba. Zuwa jibi idan na kintsa da kyau sai na wuce. Amma mallakar iya mijinki ne ko kuwa dukkaninsu? Domin na san abin da ya dace na sanar masa"
''Gwaggwo wa ya yaƙi ƙari idan ya samu! Idan so samu ne har da yaran. Don ina da burin ƙunkatama Mairi kamar yadda Yaya Imamu a kullum yake ƙuntata mini a kanta. Idan asirin ya yi aiki. Duka yaranta zan kwaso su dawo hannuna zan azabtar da su da wahalar yau da kullum. Su zama bayina ni da yarana. Ita kuma Mairi na dasa mata baƙin ciki mai tsanani daga ƙarshe ta hiɗiyi zuciya ta mutu'' ta kai ƙarshen maganar tana murmushin mugunta. Tafi Gwaggwon Bugaje ta yi cike da jin daɗin maganarta ta ce
''Madallah da wannan kyakkyawan tunanin. Shi ya sa nake jinki sosai a raina. Ke kaɗai kika gado halayyata kwabo da kwabo. Ina fatan burinki a wannan karon zai cika. Ki dama kamar yadda ni da sauran 'yan'uwanki muke damawa''
''Haka nake fata Gwaggwo,domin ina da tarin muguntar da zan shirya musu kashi-kashi. Sai sun ji kamar su bar duniyar''
''Zuwa jibi zan je Bégajé na yi duk yiwuwa. Yanzu ki kwantar da hankalinki,na tabbatar miki ba za ki koma bariki ba sai da kambun ikonki a tafin hannunki. Yi kwanciyarki ki saka ranki a inuwa,komai ya zo ƙarshe'' ta kai ƙarshen maganar tana miƙewa lokaci guda. Kwanciya Sahura ta yi a saman gadon. Gwaggwan bugaje ta haye ɗayan gadon kasancewar yanzu bata da gado mai rumfa. Zuciyar Sahura cike take da farin ciki tare da fatan su dace a wannan karon har bacci ya yi awon gaba da ita. Washegari Gwaggwon Bugaje ta fara shiri inda Sahura da yaranta suka shirya tsaf zuwa gidajen 'yan'uwa da abokan arziƙi yawon arba'in. Ba su suka dawo gidan ba sai kusan bayan Isha'i,abinci kaɗai suka iya ci sannan suka bi tafiyar gado. Gwaggwon Bugaje cikin daren ta kammala shirin sannan ta kwanta. Washegari da sassafe kusan kowa na gidan na bacci ta wuce. Kamar kowace tafiya wannan karon ma a gidan abokiyar wasanta ta sauka. Da safe bayan ta karya ta ɗauki hanyar da zai sadata da hamadar boka Ataka...✍️
^^^^^^^^^^^^^^^
Ina 'yar ƙuda ta shiga a waɗannan shekarun
A ɓangaren 'yar ƙuda washegari ta koma garinsu. Yaranta kuma mijin ya kai su wurin mahaifiyarsa. A tunaninta za ta samu karɓuwa wurin mahaifanta kamar koyaushe,sai dai tunaninta ya rikiɗa zuwa zallar mamaki. Tun lokacin da bakinta ya furta kalmar saki suka sauya fuska. Mahaifinta ya shiga surfa mata zagin ƙare dangi,mahaifiyarta na tayashi,abin haushin taƙi sanar musu dalilin sakin har uku. Tsaf! Suka zageta soso da sabulu. Kwata-kwata 'yar ƙuda bata nuna nadamar faruwan hakan ba,hasalima sai ƙanƙanta mitsi-mitsin idanunta take tana cure fuska kamar dawo,tamkar ba da ita suke ma faɗan ba. Ruhinta ya daɗe da nisan kiwo a gajimare,a yadda ta ƙanƙance idonta hasko majigin yadda za ta faso gari take tare da fantamawa a unguwa. Washegari sai ga Saleh ya iso garin tare da wata mota daban ɗauke da kayanta,a nan ya sanar ma mahaifinta dalilin sakinta, duk abubuwan da ya san take masa munana bai ɓoye komai ba ya sanar masa. Sosai ran mahaifinta ya yi mugun ɓaci,ko sallama bai tsaya sun yi ba ya shige gidan ya ƙwalla mata kira kamar zai ari baki. Sum-sum Saleh ya ja motarsa ya wuce bayan ya sallame mai motan kayan. A diririce 'yar ƙuda ta fito daga ɗakin 'yan matan gidan tana hamma haɗi ta miƙa,a lokacin ta tashi daga baccin asarar da ya bi jikinta.
''Ki sameni ɗaki sannan ki kira mini mahaifiyarki!" Daga haka ya wuce ɗakinsa. Ba tare da damuwar komai ba ta kira mahaifiyarta sannan ta wuce ɗakinsa,tana tafiya tana ranƙwashin kanta saboda ranar na tsuma kan,sai hakan ya sabbaba mata jin ƙaiƙayi,domin rabonta da kitso wata biyu kenan,kitson kanta har ya kai ba a yi ganin tsagar. Ko zama bata samun damar yi ba ya wurgo mata tambayar da ta kusan sakata wuntsilawa tsabar firgicin da ya ɗarsu a zuciyarta. Daɓas ta zauna a ƙasa tana marairaice fuska
''Baba wallahi ina da tsafta. Amma baba wa ya sanar maka...?''
''Ƙanin ubanki Garba ya sanar mini! Sheɗaniyar yarinya mara mutunci! Ashe ƙarya kika shirga mana jiya a kan baki masa komai ba. Ƙazanta da kishi su ne abubuwan da ke jan igiyar auranki ashe! Wuyanki har ya yi kaurin da za ki dinga bin mijinki har ƙofar gidan kika masa tijara! Tarbiyyar da na ɗoraki a kai kenan?"
Turo baki 'yar ƙuda ta yi tana ƙuƙƙuni
''Baba wallahi sharri ake mini! Duk wanda ya sanar maka yana son haɗa ni da kai ne. Maƙaryaci...''
''Saleh ke ƙarya kenan! tun da shi ya zo ya sanar mini baki da baki'' mahaifin ya katseta cike da mamaki har yana karkatar da kanshi yana dubanta. Shigowar mahaifiyarta kenan ta tsinkayi furucinsa,sai ta dasa da cewa
''Yanzu Talatu abin da kika ga ina wa mahaifinki kenan! Talatu ki ji tsoron Allah! Mijinki ne maƙaryacin, wani riba zai samu idan ya miki ƙaryar. Yanzu ai sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha tun da kin tsinke igiyar auranki. Mu ci gaba da goga kafaɗa da ke a cikin gidan tun da haka kike so,burinki ya cika''
''Ni wallahi ƙarya yake mini! Kawai don ku mini faɗa ya sa ya yi hakan amma...''
''Rufe mini baki wawiyar banza! Sannan ki buɗe kunnuwanki da kyau! Daga yau babu wanda zai dinga aiki a gidan nan sai ke,daidai da ɗauke tsintsiya ya dawo aikinki. Wankina da na mahafiyarki yanzu sun rataya a wuyanki,haka girkin gida da sauran ayyukan gida ke ce da alhakin yin su. Tun da zaman gidan kika zaɓa. To Bismillah! ga fili ga mai doki. Idan kuma kina son na yi mugun saɓa miki,kwatanta ƙin ɗaya daga cikin ayyukan nan ki gani!''
Ɗaura hannu 'yar ƙuda ta yi a kai tana kwarma ihun ta shiga uku ta lalace. Ta fi kowa sanin tarin aikin gidansu. Kuka ya taso mata duk yadda ta so dannewa hakan ya gagara, lokaci guda tausayin kanta da ɗumbin nadama suka lulluɓeta. Rashin sani yafi dare duhu,domin da ta san hakan za ta faru da ko Saleh ya jata da faɗa ba za ta yi gigin biye masa ba. Furucin mahaifiyarta ya sake sakata rushewa da kukan da ya fi wanda take.
''Idan ma kin kashe auranki ne don ki fito yawan bin gidajen unguwa kin yi a banza. Ƙafarki ba za ta taka ko'ina a unguwar nan ba. Sannan zan saka ido a kanki matuka ainun. Wanka sau uku zaki dinga yi,kitso duk sati za ki wanke Huwaila tamiki kitson. Tun da kin ƙulla abota da ƙazanta, to ki sani ta ƙarfi da yaji zan yakice miki shi. Wawiya wacce bata san abin da ke mata ciwo ba. Ban ji haushin abokiyar zaman da ya karo miki ba. Don ma yana da haƙuri,wane namiji ne zai zauna da mace ƙazama irinki har ya ɗauki shekarun nan bai ƙara aure ba. Kuma wannan kan da kike da faman susa tun jiya ki je ki tsefe shi,zan aika a siyo soda ki wanke shi''
Sosai 'yar kuda take sharɓar kuka kamar ranta zai fita,ta fi kowa sanin halayyen mahaifanta,idan suka kafe sun kafe kenan,me canja su sai Allah. Cike da nadama ta fara roƙo
''Baba na tuba na bi Allah sannan na bi ku,ku duba girman Allah ku sassauta mini hukuncin,wallahi ya mini tsauri da yawa! Yiiiiiiiiii! Yiiiiiiiiii! Yiiiiiiii!'' sosai take da na sanin biyewa zuciyarta har ta samu saɓani da mijinta. Kuku wiwo har da majina.
''Idan kin ga mun rage wani abu daga cikin ayyukan da muka baki to mun ga canji a tattare da ke. Don haka haƙuri bata ma taso ba ma. Babu mazaunin hakuri a nan. Ta shi ki je ki kwance kitson kafin na zo'' cewar mahaifiyarta. Babu musu ta miƙe tare da barin ɗakin hawaye ba su daina gangarowa daga gurbin idanunta ba.
Tun daga rana 'yar ƙuda ta koma mai aikin gidan,idan ta yi aikin ba daidai ba,mahaifiyarta ta dawo da ita duk yawan aikin. Wani lokacin har kuka take kamar ƙaramar yarinya idan aka ce ta sake aikin. Abin duniya ya gama isarta,kullum cikin nadama da da na sani take. A ɓangaren tsaftar jiki,mahaifiyarta ta tsaye irin na daka a kanta. Wanka sau uku take a rana,sannan kitso duk sati sai ta kwance kai ta yi wani sabon. Karta-kartan fason da suka ƙawata duddugen ƙafarta nan da nan suka ɓace kamar almara. Tsaf 'yar ƙuda ta dawo asalinta. Yanzu aikin gidan ya soma bin jikinta, tun tana ƙyuiyar aikin har ya zamana tun kan a ce ta yi take kayanta. Wankan ma yanzu mahaifiyarta ta daina ɓaɓatu a kai. Cikin shekaru biyu 'yar ƙuda ta sauya zuwa wata daban mai tsafta da kwalliya. Kyawunta na ainihi ya bayyana. Sai a lokacin mahaifanta suka sauƙaka mata aikin gidan. Fita jefi-jefi take yinsa. Duk babban sallahh Saleh na kawo yaranta su yi sati biyu su koma. A haka shekaru su kai yi wucewa har Ubangiji ya azurtata da samun miji a wani ƙauye da ke gaba garinsu. Matansa uku sai shiga a matsayin ta huɗu. 'yar ƙuda ta yi horuwar da tsananin kishi ya fita a ranta. Ko shekara ba a yi da auransu ya rasu ta dawo gida idda. Da yake akwai sauran shan ruwanta a gidan Saleh,sai aka sake ɗaura musu aure,ya dawo da ita sabon gidan da ya yi a Talatan mafara kasancewar wancan gidan da ke Gusau ya sayar, yaranta ma sun dawo hannunta,daidai gwargwado tana ba su kulawa haka mijin...✍️
^^^^^^^^^^^^
Tudun Wada premier road Gusau jihar Zamfara Nijeriya
Kamar koyaushe suna zaune a falo suna ɗan taɓa hira da mahaifiyarsu, Yasir da Jalil suna bata labarin boko. Hamida na ma 'yar babyn karanta kitso yayin da HAFIZA ke kusa da Mairi tana zanen da ta saba. Kwatsam kunnuwansu suka jiyo sallamar yara. Ras! Gaban HAFIZA ya buga ji muryoyin ƙawayenta. Kafin su Jalil su amsa sallama HAFIZA ta wawushi littafin zanenta ta ruga da guda uwar ɗakan Ammunta ta rufo ƙofar,don jaraba har da maƙala sakata. Dariya su Yasir suka yi,Mairi kuma da girgiza kai,wannan halin autan nan nata na bata mamaki,a ce mutum ya tsani jama'a haka kurum. Ko minti ɗaya lafiyyaye bai cika ba yaran suka shigo ɗakin da sallama a laɓɓansu. Kowacce riƙe take da 'yar baby da wasu kayan wasan na daban. Gaishe da 'yan ɗakin suka yi sannan wata daga cikinsu ta ce
''Maman Yasir mun zo wasa da HAFIZA ne"
Kafin Mairi ta ba su amsa Hamida ta caɓe da cewa
''Tana ɗaki,bari na kira muku ita'' ta yi maganar tana miƙewa lokaci guda zuwa ɗakin Ammunsu. Duk yadda Jalil ke hararanta sai ta basar tana murmushin mugunta. Kwanƙwasa ƙofar ta yi tare da cewa
''Ki fito HAFIZA ''
A tunanin HAFIZA ko ƙawayen nata sun wuce ne ya sa ta kirata. Cire sakatar ta yi tana murmushin ta fito zuwa falon. Kafin ta ki tsakiya idanunta suka sauka a kan ƙawayenta,nan da nan annurin fuskarta ya ɗauke,ta sauya yanayin tafiyarta kamar wata marar lafiya ko kuma wacce ƙwai ya fashe mata a ciki har ta ƙaraso cikin ɗakin. Hamida ta koma gefe tana mata dariyar mugunta. Tsabar iya barikanci na HAFIZA sai ta fara marairaice fuska tana riƙe kanta,kai tsaye ta haye saman cinyar Ammunta tana faɗin
''Ammuna kaina zai fashe! Ki mini addu'a''
Sarai Mairi ta fahimci ciwon kan a kan mene ne,amma sai ta basar cike dda kulawa ta mata addu'a tana tofawa a gashin kanta. Jalil ya dubi ƙawayen HAFIZA ya ce
''Kun ga! abokiyar wasan ta ku bata da lafiya,ku je zuwa gobe sai ku yi wasan,ni ma zan tayaku''
Jin firucin shi ma zai tayasu sai hakan ya faranta ransu, suka murmusa suna barin gidan. Zumbur HAFIZA ta tashi saman cinyar Ammunta,da sauri ta je ta kulle ƙofar gidan sannan ta dawo zuciyarta cike da farinciki. Tana shiga ɗaki ta ɗaga hannu sama idanuwanta na duban sama ta ce
''Astagfirullah! Astagfirullah! Allah na tuba ka yafe mini ƙaryar da na yi '' sai kuma fuskarta ta sauya kamar mai shirin kuka ta ɗan dubi Hamida sai kuma ta juya wurin Mairi .
''Ammuna kin ga Adda Hamida ta saka ni yin ƙarya alhalin Ammu Jamila ta ce mai ƙarya ɗan wuta ne!" Ta furta a shagwaɓe tana narai-narai da idanu
''Niiiii Hamida! Kar ki mini sharri,yaushe na sakaki yin ƙarya!" Ta faɗa tana gimtse dariyarta.
''Ba ke kika ce na fito ba alhalin su Ameera na nan'' ta yi maganar tana share hawayen da suka fa jiƙa kuncinta.
''Zo zo Lu'u-lu'uta! Amma Hamida baki kyauta ba, ta ya za ki saka mini auta kuka. Sai mun ɓata miki rai''
''Ai tana sane ta yi hakan,tun kan ta kai haka take ƙin wasa da su kuma ta sani,tsokanace kawai. An yi girman doya'' cewar Yasir. Jalil kuma rankwashi ya kai mata yana faɗin
''Muna gab da yi miki taran dangi idan kika sake saka auta kuka''
Ko a kwalar rigar Hamida,hasalima dariya ta yi ta tana ma HAFIZA gwalo, HAFIZA kuma da cunno mitsitsin bakinta tana sake shigewa jikin Mairi kamar kyanwa. Korar Hamida daga ɗakin Jalil ya yi yana faɗin
''Ki je waje ki gama dariyarki muguwa''
Tsabar tsokana sai ta leƙo ɗakin suna haɗa ido da HAFIZA sai na mata gwalo tana kanne ido ɗaya...✍️
^^^^^^^^^
Hamadar boka Ataka
Kamar kowani zuwa,zaune take a kasan wurin ta lanƙwasa ƙafa gaban tukunyar mai ci da wuta kamar mai roƙon gafara
''Boka Ataka na zo''
''Ataka na san za ki dawo! '' lokaci guda ya bayyana,sai haske ya kaɗare kogon bakiɗaya.
''Ataka mijin ɗiyarki ya...✍️
Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️
***