BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

Chapter 17

by @narrnarhhbukar00

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

017

Hamadar boka Ataka

Kamar kowani zuwa,zaune take a kasan wurin ta lanƙwasa ƙafa gaban tukunyar mai ci da wuta kamar mai roƙon gafara

''Boka Ataka na zo'' ta furta a sanyaye

''Ataka na san za ki dawo! '' lokaci guda ya bayyana,sai haske ya kaɗare kogon bakiɗaya.

''Ataka mijin ɗiyarki ya fi ƙarfinmu! Ataka yana tsaye a kan addininsa! Ataka duk hanyar da za mu bi don mu yi galaba a kansa ya daƙile! Ataka mun yi rauni! Ataka mijin ɗiyarki bala'i ne!"

Sosai hankalin Gwaggwon Bugaje ya dugunzuma ya yi ƙololuwan tashi. Yanzu ya za ta yi da Sahura. Duk da sanyin kogon bai hana gumi keto mata ba,tsabar yadda ta ruɗe. Zama ta gyara tana duban ɗinkakkiyar fuskarsa mai munin gaske ta ce

''Boka Ataka ban da mai taimakona a faɗin duniyar nan sai kai. Idan ban koma da kyakkyawan albishiri ga ɗiyata ba zan rasata. Kai taimake ni ko na ɗan wani lokaci ne kafin ka samu damar galaba a kansa''

Siririyar dariya ya tuntsire yana yi hasken kogon na ɗaukewa yana kawowa kamar ana controlling ɗinsa. Sai can ya tsagaita

''Ataka akwai hanya ɗaya! Ataka amma ba za ta dawwama ba! Ataka akwai tarin bala'i,fitina,musiba,tashin hankalin,nadama da da na sani a karshen hanyar! Ataka Sannan idan yarinyarki ta fara tafiya a wannan hanyar ba za ta tsaya ko'ina ba ai ƙarshenta! Ataka ki yi nazari kafin mu aiwatar! Ataka idan kuma kin yarda za mu fara!"

''Boka Ataka indai aikin zai yi wannan ba damuwa ba ne,zuwa nan gaba sai mu san abin yi kafin takai ƙarshen hanyar. Mijinta yana son ta koma wani gari sai kishiyarta ta dawo inda take. Hakan ya ƙara tayar da hankalinta ni ma ta tayar da nawa . Idan so samu ne boka Ataka mallakar kar ta tsaya a kan mijin shi kaɗai. Ita ma tana so har da yaran mijin su kasance a ƙarƙashin ikonta kwatankwacin Irin mallakata''

Wannan karon ma siririyar dariyar ya yi sannan ya ce

''Ataka kamar yadda na sanar miki hanya ce mai ɗauke da abubuwan tashin hankalin idan aka saɓa dokar hanyar! Ataka tun da kin ji kuma kin gani! Ataka zan bata hatsabibiyar mallakar da ban taba ba wani ɗan'adam ba sai dai! Ataka bala'inta ya fi daɗinta yawa! Ataka tun da kin amince! Ataka akwai manyan sharuɗɗa biyu da dole za ta yi taka-tsantsan da su idan har tana son mallakar ta daɗe! ''

Cike da jin daɗin furucinsa ta ce

''Boka Ataka kunnuwana na saurare,haka ƙwakwalwata na fahimta kamar yadda zuciyata da gangar jikina suka aminta''

Siririyar dariya ya yi sannan ya ce

''Ataka sharuɗɗan su ne! Ataka kar ta kuskura ta zauna a inda mijinta ke karatun addininsa! Ataka domin aljanun da za mu tura su yi mallakar sun tsani karatun! Ataka ba mijin kaɗai ba duk inda ta ji ana karatun addini ta yi saurin nisa da wurin! Ataka sai sharaɗi na biyu wanda ya fi kowanne hatsari! Ataka kar ta yarda kuma kar ta aminta da wannan hasken da ke tare da kishiyarta ya raɓeta!"

''Boka Ataka ban fahimci hasken da kake magana a kai ba''

Siririyar dariya ya yi mai matukar tsayin gaske sannan ya tsagaita yana dubanta

''Ataka shekaru goma da suka wuce na sanar miki kishiyarta za ta haifi haske! Ataka yanzu hasken da doron duniyar nan! Ataka sai dai har yanzu allon tsafina bai hasko mini me hasken yake nufi ba! Ataka ban san hasken biladama ne ko wani halitta ba! Ataka allon tsafina bai nuna mini lokacin da hasken ya bayyana balle na san me yake nufi ba! Ataka don haka karta raɓe kishiyarta har abada idan tana son kar hasken ya raɓeta! ''

''Zan sanar mata komai boka Ataka ''

'yar siririyar dariya ya yi kaɗan ya gimtse ɗinkakkiyar fuskarsa sannan ya ce

''Ataka hatsabibiyar mallakar za ta shafi mijin da yaran kishiyar biyu! Ataka za mu saka tsanar kishiyarta a zuciyar mijin! Ataka yaro  ɗaya ba zai mallaku ba! Ataka saboda rauhanan kansa suna bashi kariya! Ataka! Ataka! Ataka! Kakaka! Kukuku! Kuuuu!"

Ya ci gaba siddabaru yana ɗaga hannunsa na hagu sama, kamar ƙyaftawa da bismillah wata mitsitsiyar ƙwarya ta bayyana a tafin hannunsa. Sai kwaryar ta ɓace tare da bayyana a gaban Gwaggwon Bugaje. A hankali ta sauke idanunta saman ƙwaryar. Jar ƙwarya ce ba kamar kowace ƙwaryar da yake bata ba sannan an rufeta da baƙin fata. A bazata ta ji maganarsa

''Ataka wannan ita ce kwaryar da ke ɗauke da hatsabibiyar mallaka! Ataka sannan wannan shi ne aikin ƙarshe da zan ji miki ke da yaranki! Ataka wannan umarni ne daga aljani Ruƙuƙús! Ataka kamar yadda na sanar miki tana da matuƙar haɗari! Ataka ga yadda za ta yi aikin! Ataka dole ta samu jinin Jaɓa namiji da mace ta zuba a ƙwaryar! Ataka dole ta samu jinin kasa (python) ta zuba a ciki! Ataka sannan ta yanki tafin hannunta na hagu jinin ya zuba cikin ƙwaryar! Ataka ta samu ganyen akwara ta daka cikin tsakiyar dare ta zuba cikin ƙwaryar! Ataka daga nan ta saka yatsanta manuniya na hagu cikin ƙwarar ta juya sau uku tana ambaton Ataka sau tara! Ataka ta dafa abincin ta juye duka maganin cikin girkin ta bashi ya ci! Ataka ta gama komai! ''

Tun da Boka Ataka ya fara bayanin yadda za a yi amfani da maganin ta shiga share gumi. 'Ni Maimuna ina zan samu waɗannan jinanan da ake buƙata' ta furta a ranta. A zahiri ta ce

''Boka Ataka babu matsala idan jinin an samu ba lokaci guda ba?"

''Ataka ƙwarai kuwa babu laifi domin ƙwaryar tsafi ce bata ƙafewa! Ataka idan ta yi komai ta girka abincin da maganin ta bashi zai yi bacci! Ataka a daren mu kuma za mu farmakesa! Ataka karta runtsa a daren har wayewar gari! Ataka domin aikin sai da ita! Ataka amma ki sani! Ataka iya tsoranta da mugun kwarjininta za mu saka ma zuciyarshi da yaran! Ataka sai yana tare da ita mallakar za ta yi aiki! Ataka ba zai daina ibadarsa ba na yau da kullum! Ataka ta tabbata yaran kishiyarta sun dawo hannunta! Ataka domin a nan ne mallakarsu za ta yi aiki! Ataka na sallameki sallama ta har abada! Ataka idan ke ko ɗaya daga cikin yaranki ya kaucewa umarninmu ya ja muku! Ataka zuri'arki za ta dawwama cikin bala'i da tashin hankali!Ataka hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh!" Yana gama furta hakan ya ɓace hasken ma haka.

Ɗaukar kwaryar ta yi ta saka a jaka,sai ta fara tafiya a hankali har ta fito daga kogon. Babban damuwarta dawowan da ya ce karta kuma yi. Ga wannan hatsabibiyar mallakar da ya bata mai matuƙar haɗarin gaske har ta zarce ta ta mallakar. Tashin hankalinta bai wuce inda za ta samo jinin kasa (python)ba, gwara jaɓa ana ina samunsu a ko'ina da ganyen akwara. Tafiya take amma kwata-kwata hankalinta ba ya jikinta,ga azababben sanyin wurin da ke shigarta. Wani tunani ya fado mata,sai ta saki murmushi tare kara sauri har ta bar hamadar. Ba komai ya sakata murmushin ba illa tuna ɗan yayanta da ke shiga manyan dazukka farauta shi da sauran abokansa. Ta taki sa'a a lokacin ne ya dawo gidan,ba jira suka keɓe ta sanar masa jinin kasa(python) take so za a haɗa ma mijinta magani. (Gwaggwon Bugaje an yi ilmin ƙarya😂. Mu je dai zuwa idan tusa na hura wuta,indai duniyata ce tana gab ta miki atishawan 'yan tsaki da yaran naki irinsu Sahura, mu koma gefe mu sha kallo har da dariya idan ta kama😂 ko ya kuka ce my Esteem fans🥰)

Ɗan yayanta ya tabbatar mata a wannan zuwan sun zo da kasa (python)amma ba shi ya kama ba,zuwa dare zai kawo mata jinin idan sun yanka kasancewar tana bacci suka kamata. Cike da murna ta koma gidan abokiyar wasanta. Ta fara shirin komawa gida don wannan karon bata yi niyyar zaga dangi ba kasancewar ko wata biyar ba a yi ba za to garin. Cikin dare ya yi sallama ya kawo mataa jinin a farar leɗa baƙi ƙirin sannan ya koma. Gwaggwon Bugaje ta fakaici idon Sajida ta wuce bayi da jakarta ta juye jikin ciki sannan ta fure ta dawo cikin ɗakin. Murmushi Sajida ta yi domin ta san dalilin yawan zuwan Gwaggwon Bugaje Bégajé. Ta yi nisan da bata jin kira sai addu'a. Kwanciyarta ta gyara tana addu'ar bacci,yayin da Gwaggwon Bugaje ta shirya tsaf sannan ta kwanciya zuciyarta fes! Da samun jinin macijin. Washegari ta dawo Sakkwato wanda sai cikin dare sosai ta sauka. Babu wanda ya san da dawowanta kasancewar gidan babu ƙofa sai kawai ta shige ciki. Kwanƙwasa ƙofar sashenta ta yi. Cikin bacci Sahura ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa,ta dubi agogon ɗakin da hasken Torchlight ta ja tsaki ganin ƙarfe 1:30am na dare,mikewa ta yi zuwa wajen. A ƙufule ta ce

''Uban waye ne wai!"

''Ni ce Sahura buɗe mini kofar,dare muka yi a hanya'' cewar Gwaggwon Bugaje

Da sauri Sahura ta ƙaraso tana cire sakatar jin muryar Gwaggwonta.

''ku ne cikin dare haka! Sannu da zuwa Gwaggwo.'' ta yi maganar tana amsar jakar hannunta suka shige ciki. Abincin da ya yi saura ta zuba mata tana mata sannu har ta kammala. Wata magana bata shiga tsakaninsu ba suka kwanta. Nan da nan bacci ya yi awon gaba da Gwaggwon Bugaje,don wannan tafiya ta sha baƙar wahala a hanya.

Washegari

Bayan sun kammala karyawa Sahura ta aika yaran gidan yayarta amso sako. Ta yi hakan don ta samu damar kebewa da mahaifiyarta saboda Aunty Saudah da Amina akwai gulma da shiga maganar manya.

''Gwaggwo tun dawowarki na matsu na ji ko an dace,ganin kin yi dare ga shi kin gaji ya sa na danne zumuɗina na bari zuwa safiyar yau. Wallahi na yi matukar ƙaguwa na ji ko an dace''

Murmushi Gwaggwon Bugaje ta yi tana gyara kwanciyar Maryam a saman cinyarta

''An dace sosai amma hatsarin da ke cikin mallakar ya wuce gaban kwatance''

''Gwaggwo ba dai an dace ba. Zan mallaki Yaya Imamu har da matarsa da yaransa?"

''Kwarai kuwa Sahura! Sai dai bai ambaci matarsa ba,hasalima cewa ya yi ki yi nesa da ita idan kina son mallakar ta daɗe,amma Dauda da yaransa biyu za ki mallaka,sai yaro ɗaya da ya sanar mini ba zai mallaku ba saboda aljanun kansa. Sannan akwai sharuɗɗan da za ki bi''

''Wannan ai duk mai sauƙi ne Gwaggwo. Tun da ya zo hannu no frobulem in ji turawa. Sanar mini da sharuɗɗan da yadda zan yi amfani da maganin''

Kwantar da Maryam ta yi saman gadon sannan ta ce

''Ya ba ni jar ƙwarya ƙarama,sannan ya ce bai taɓa ba wani ɗan'adam irin mallakar ba. Ya umurci na samu jinin maciji kasa amma tun a jiya na samu da taimakon yaron yayana wanda na taɓa faɗa miki yana farauta. Sannan za a samu jinin jaɓa mace da namiji a zuba,a daka ganyen akwara cikin dare a zuba,za ki yanki tafin hannunki na hagu jinin ya zuba cikin ƙwaryar,sai ki saka yatsanki manuniya na hagu ki juya sau uku sannan ki ambaci Ataka sau tara,ki juye komai cikin abincin ki bashi. Ya sanar mini zai yi mugun bacci, a lokacin za su samu damar galaba a kansa,ke kuma ya ce kar ki kuskura ki yi bacci a daren. Sharaɗin kuma ya ce duk lokacin da yake karatun addininsa na san Al'qur'ani yake nufi ki matsa daga wurin,ba ma shi kaɗai ba ko ina ake karatun Alkur'ani ki tashi daga wurin har sai an gama,Ya ce ki dawo da yaran kishiyarki wurinki domin mallakar sai suna wurinki za ta yi aiki. Daga nan kin gama komai''

''Abu mai sauƙi. Hmmm wannan ne haɗarin da ke tattare da mallakar. Yooo Gwaggwo ai da sauƙi aikin.''

Murmushi Gwaggwon Bugaje ta yi tana jinjina taurin zuciyar Sahura. Duk da ta san ba duka abin da ya faɗa mata ta sanar mata ba,,dole ta nemi sabon boka mai aiki kamar boka Ataka tun da yanzu ya haramta mata zuwa wurinsa. Munanan abubuwan da ya ce za su iya afko musu idan ɗaya daga cikinsu ya karya sharuɗdansa suke tayar da mata hankali. Bata fatan wani mummunan abu ya samu ahalinta ko bayan ranta,farincikinsu shi ne kwanciyar hankalinta,damuwarsu shi ne fargabarta,dole ta samu sabon boka koda zuwa nan gaba. Don zuciyarta ta yi matukar karaya da hatsabibiyar mallakar da ya ba Sahura,tana tsoron kar wata rana ta saɓa ɗaya daga cikin sharuɗɗan. Sauke ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce

''Sahura zaman Sakkwato ba naki ba ne yanzu. Tun da kin ziyarci dangi sun ga jaririya,zuwa jibi idan komai ya kammala ki ɗauki yaranki ki koma. Da zafi-zafi ake bugun ƙarfe''

''To Gwaggwo hakan za a yi''

Daga haka suka bude wani babi da hira,cike da shauƙi suke hirar suna dariya...✍️

^^^^^^^^^^^^^^

Tudun Wada premier road Gusau jihar Zamfara Nijeriya

*ƙarfe 1:45pm na rana:

A daidai wannan lokacin Yasir ya shimfiɗa tabarma,yayin da Jalil da Hamida suka ɗauko abinci, HAFIZA kuma ta ɗauko kofukan ruwa. Mairi ta ɗauko sauran kayan. Tire biyu shaƙe da shikafa garau-garau. Mairi ta zuba mai da yaji, ta umurci kowa ya saka latas a gabansa maganin faɗa. A nutse suke cikin abincin,baka jin motsin komai da sai cokula,Yasir da Jalil a tire ɗaya sai Mairi da su Hamida a tire ɗaya. Sun yi nisa a cin abinci kunnuwansu suka tsinkayo musu muryar Jamila.

''Ammu Jamila!" Cewar HAFIZA tana sakin cokalin tare da rugawa wurinta tana mata oyoyo.

''Wai wai wai jaririyata ce ta yi wannan ƙibar haka! Maa shaa Allah!''

Dariya Hafiza ta yi tana faɗin

''Ai kullum sai munci nama da shayi. Sannan Ammu Jamila na gina mana gida har da ke idan na girma sai mu koma ciki''

Dariyar maganar HAFIZA Jamila ta yi.

''Kai kai kai an jima sai ki nuna mini gidan na gani.''

Cike da zumuɗi HAFIZA ta ce

''To! Har da asibiti na zana. Ai kema baki kukan allura ko''

''Ina yi irin yadda kike kuka idan ana miki allura''

Waro ido ta yi tana rufe baki saboda dariyar da ta taso mata. Daga haka ta gimtse bakinta har suka ƙaraso tsakar gidan. Gaishar da Mairi ta yi saisu Jalil suka gaisheta. Wannan karon har ta 'yar kishiyarta ta zo wacce ba za ta wuce shekara uku a duniya ba. Abinci Mairi ta sako musu  ta haɗo da ruwa sannan ta dawo tsakar gidan. Suna ci suna hira musamman HAFIZA da ta cika da farincikin ganin Ammu Jamila har suka gama. Tsaf Yasir ya tattara wurin,Hamida da Jalil suka kwashe kayan, HAFIZA ta bi Jamila ɗakin tana hararan yarinyar da Jamilan ta zo da ita tare da riƙe hannun Jamila saboda kishi. Sun yi hira sosai har labarin komawarsu bariki da sanar mata. Sosai Jamila ta yi farinciki har ta ce idan sun tashi komawa tare da ita za a je ta ga wuri..✍️

^^^^^^^^^^

Garkar Bala fari mai fata Ƙofar kaɗe jihar Sakkwato Nijeriya

A ɓangaren Sahura duk abin da ake buƙata na aikin mallakar sun samu domin sun daren jiya ta saka yatsanta manuniya cikin ƙwaryar ta juya bayan ta dan yanki tafin hannunta na hagu jinin ya ɗan juba kaɗan,ta yi yadda boka Ataka ta umurce,abun mamakin har yanzu jinin na nan bai sauya kala ba ko wari . Ta fara shirye-shiryen dawowa. Su Aunty Saudah sai kuka suke a kan ba za su dawo bata bari su ƙara kwanaki. Murza ma idanunta toka ta yi ta ce dole su koma rai ba don ya so ba musamman Nu'aymah da ta ji daɗin gari,sai abin da ta ce za ta ci shi ake bata. Washegarin ranar suka dawo Bariki. Sosai Dauda Imamu ya yi mamakin dawowansu,har ta tambayi lafiya shi da suka rabu a kan sai yara sun koma makaranta to ya aka yi suka dawo. Murmushin yaƙe Sahura ta yi tare da zurarara uwar karya a kan, an aiko daga Bégajé a kan 'yan uwanta uku gobara ta ritsa da su shekaran jiya,sai ta tafi a jiya. Ganin ta gama yawon arba'in sai kawai ta ci su dawo gida tun da Gwaggo bata nan. Sosai ta tausaya mata tare da addu'ar Allah ya jiƙansu da Rahama. Da yamma ta ɗora girkin taliya. Bayyan ta soya kayan miyan sai ta je ɗaki ta ɗauko ƙwaryar a jaka,ta fito kenan sai ga Nu'aymah ta rugo da gudu...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***