Chapter 18
The Amazing Pen ✍️.......
BAHAGON TUNANI
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
018
Murmushin yaƙe Sahura ta yi tare da zurarara masa uwar karya, wai an aiko daga Bégajé a kan 'yan uwansu uku gobara ta ritsa da su shekaran jiya duka sun ƙone,sai ta tafi a jiyan. Ganin ta gama yawon arba'in sai kawai ta ce su dawo gida tun da Gwaggo bata nan. Sosai ya tausaya mata tare da addu'ar Allah ya jiƙansu da Rahama. Da yamma ta ɗora girkin taliya. Bayan ta soya kayan miya ta tsaida ruwan girkin daidai cikin Dauda Imamu sai ta tafi ɗaki ta ɗauko ƙwaryar,ta fito kenan sai ga Nu'aymah ta rugo da gudu saura ƙiris da bige ƙwaryar,da sauri Sahura riƙe kwaryar da kyau,ta matsa gefe ƙirjinta da dukan uku-uku,ta yi amanna idan ƙwaryar nan ta fashe shikenan kashinta ya bushe, ita da Dauda Imamu sai gani sai hange. Madadin ta tsawar mata sai kawai ta wuce kicin tana sauke ajiyar zuciya. Tsaf ta juye maganin cikin ƙwaryar sannan ta ɓoyeta a ɗakinta. Rabin taliya ta dafa masa shi kaɗai ta juye a kula,ta wanke tukunyar sosai sannan ta ɗora girkinsu,sai bayan magrib ta kammala girkin ta zuba musu. Ba sallah balle salati suka zauna cin abincin.
Sahura irin matan nan ne da ba su damu da tarbiyyar yaransu ba. Babu ruwanta da abin da suke yi,mai kyau ne ko akasinsa,ita dai burinta ta ga sun ci sun ƙoshi,sun yi shiga irin ta yaran sojoji 'yan ƙarya. Duk rigimar da yaran za su ɗauko sai dai ta ba yaran wasu rashin gaskiya,zuciyarta ta daɗe da yarda yaranta ne a kullum masu gaskiya. Hamid tun yana ɗan shekara biyar ya san ya buɗe jakarta ya ɗauki naira biyar ko goma ya kashe,har ta kai ya fara saka hannu a aljihun rigar mahaifinsa, sai dai bai ɗore ba, domin Dauda Imamu ya kamashi dumu-dumu,a ranar da ya yi aika-aikar ya yaba wa aya zaƙinta,domin ya daku sosai a hannunsa. Sahura ta yi roƙon,ta yi magiyar ya ƙyalesa amma ya yi biris da ita don ya ga alamar ita ke ɗaure masa gindi yake iya shege. A ranar sun hau ruwa rana sosai da shi,sai faɗi take kwata-kwata shekarar Hamid nawa ne da zai dinga masa irin wannan bugun a kan ya ɗauki nairi hamsin,ai ƙaramin yaro ne idan ya girma zai daina. Tsabar takaici barin gidan Dauda Imamu ya yi,tun daga ranar Hamid bai sake gigin saka hannu a aljihun mahaifinsa. Iya jakar mahaifiyarsa ya tsaya,wanda yanzu da yake shekara ta goma sai likafa ta ci gaba,bai tsaya a jakar mahaifiyarsa ba har jakukkunan 'yan'aji yake lalubewa. An sha dukansa a makaranta amma yaƙi dainawa. Su Aunty Saudah gulma da manyance suka saka a gaba,da nuna su masu kuɗi ne. Nu'aymah kuwa kwaɗayi da roƙo,ko babban mutumi ta gani da abu yana ci za ta miƙa ɗan hannunta ta ce ''Sammin'' idan kuma yaro ne ƙarami sai ta fizge ta ruga a guje. (Hmmm akwai chakwakiya a gaba, kwaɗayi ga 'ya mace matsifa ce babba. Allah ka ƙara mana wadatar zuci da imani🤲)
Bayan Isha'i Dauda Imamu ya dawo gidan. Cike da tsantsar mamaki yake dubanta. Kaya na alfarma wanda Gwaggwon Bugaje ta ɗinka mata a wannan zuwan ta saka,ta yi kyau sosai abinka da jinin buzaye. Ta zuba masa abinci ya zauna, hankalinsa na kanta,yau ta yi matuƙar yi masa kyau. Sai jansa da hira take har ya soma cin abincin, tsabar hankalinsa yana kanta ko bismillar da ya saba yi a duk lokacin da zai ci abinci ya manta. Sahura bata bar falon ba har sai da ta tabbatar da ya cinye abinci tas sannan ta kwashe kwanukan ta kai kicin. Koda ta dawo falon ta iske yana jera hamma tare da mika yana salati.
''Baban Hamid wannan hamma haka kamar za ka haɗiyi ɗan tsako''
Murmushi ya yi yana sake rufe bakinsa saboda hammar da ta taso masa.
''Wallahi wani irin bacci nake ji,duk na ji na gaji. Mts! Bari ki gani,yau da wuri zan kwanta don na tashi sallar dare a kan lokaci... Hhaaaaaaaa!" Ya sake hamma yana miƙewa lokaci guda ya wucewa uwar ɗaka yana rangaji. Taɓe baki ta yi tana turo ɗaurin ɗan kwalinta gaba sannan ta dawo saman kujerar ta zauna. Murmushin mugunta ta saki tana karkaɗa ƙafa
''Hmmmmm! An zo wurin'' ta furta a fili tana murmushi,ta gama yadda maganin ne ya fara aiki a jikinsa, murmushi ta kuma saki a karo na biyu tana miƙewa zuwa ɗakinsu Nu'aymah ta gyara musu kwanciya. Daga can ta wuce ɗakin Hamid ta gyara ledar da yake kwanciya a kai saboda fitsarin kwance sannan ta wuce ɗakinsu. Cike da mamaki ta ƙaraso ɗakin jin munsharinsa. Dududu yaushe ya shigo ɗakin balle ya yi nisa a bacci haka. Shi da sai kusan sha ɗaya yake bacci ya tashi ƙarfe uku da rabi sallar dare,amma yau ko tara bata cika ba ya kwanta. Hayewa saman gadon ta yi tana dariya. Idanunta ƙamas babu alamun bacci,yo bacci a wannan ranar sai dai ya sallama mata. Tun tana jin motsin mutane har gari ya koma shiru,sai kukan tsari da karnuka. Maryam ta farka da kuka,ta ɗauketa ta fara shayar da ita har ta koma bacci ta kwantar da ita. Kallon agogo ta yi ta ga ƙarfe ɗaya ta gota.Da ta gaji da zaman ta miƙe zuwa bayi fitsari,bata jima ba ta dawo ɗakin ta zauna. Ko mintuna uku bata yi da zama ta fara jin sautin muryoyi daban-daban, wasu irin yare ne da tun da ta zo duniya bata taɓa jin kalarsu ba, can wani irin iska mai matuƙar ƙarfi kamar guguwa ya shigo ɗakin ta hanyar windansu duk da a rufe yake amma ƙarfin iskan ya sabbaba buɗewarsa,cikin guguwar sautikan ke fitowa. Nan da nan tsoro ya ɗarsu a zuciyarta, don bata yi tunanin haka abin yake ba. Guguwar ta rikiɗa zuwa wani irin duhu tare da curewa wuri guda kamar dawo ta shige jikin Dauda Imamu. Bayan komai ya lafa ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya, ta sulale za ta kwanta kenan kunnuwanta suka tsinkayo sabbin muryoyin da suka sha bamban da na farko,iska mai ƙarfi da zafi ya shigo ɗakin ta windan,nan da nan ɗakin ya ɗauki tururi. Maryam da ke bacci ta farka da sakin wani azazzaben kuka. Da sauki ta ɗauketa ta fara shayar da ita duk da zafin da take ji,zuwa yanzu har zufa ta fara ketowa a duk ilahirin jikinta tamkar ta fito daga wanka. Tsoro ne fal cikin ƙoƙon ranta,duk wannan zafin bai saka Dauda Imamu farkawa ba,bai san wainar da ake toyawa ba haka yaranta. Wannan karon guguwar ta jima tana ƙugi amon muryoyin na ƙara sama, sai can guguwar ta rikiɗe zuwa manyan jajayen idanu guda biyu ƙwayar cikinsu baƙa siɗik! Sai wawakeken baki haƙoran ciki kamar na (Horori) Vimpire Zaro ido Sahura ta yi tana sakin baki tsabar mamaki,kafin ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi kai tsaye manyan idanun suka zarce cikin idanunta, bakin ya nutse cikin nata kamar almara. Da sauri ta murza idanunta tana jin wani yaji-yaji da ɗan ƙaiƙayi,bakinta kuma ya yi mata nauyi sai dai bata jin komai. Tun tana jin yaji da ƙaiƙayin kaɗan-kaɗan har suka girmama,da sauri ta kwantar da Maryam sannan ta nufa bayi ta wanke fuskarta,kamar ta ƙara raɗaɗi da ƙaiƙayin ne. Sai yarfa hannu take saboda azaba babu halin neman taimako tun da cikin dare ne. Tafi ƙarfin awa biyu tana azabtuwa daga bisani raɗaɗi da ƙaiƙayin suka ragu zuwa lokacin an fara kiran sallar farko. A hankali ta sulale ta kwanta babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita.
A hankali Dauda Imamu ya fara buɗe idanunsa, sakamakon kiran sallar ta kunnunwansa suka farauto masa. Da ƙyar ya iya miƙewa ya zauna,jinsa yake kamar a ɗaɗɗaure. Ya yi addu'ar tashi daga bacci sannan ya miƙe zuwa bayi ya ɗauro alwala. Tayar da Sahura ya fara yi kamar kowani asuba. A natse ta buɗe idanunta a kan Dauda Imamu. Take ƙirjinsa ya ba da sautin Dummmmmmmm! Da sauri ya ja da baya yana karanto duk addu'ar da ta zo bakinsa. Wani irin tsoron Sahura ya dira a zuciyarshi tamkar dirar mikiya, har ya yi nasarar mamaye farfajiyar zuciyarsa a 'yan sakanni. Ganin yanayinsa ya tabbatar mata da komai ya tafi daidai,zuwa yanzu bata jin komai a idonta haka bakinta ya daina mata nauyi.
''Lafiya!'' ta furta a ɗan tsawace,ta yi hakan ne ta tabbatarwa a zahiri. Ilai a gigice ya ƙara ja da baya jin wata iriyar murya mai matuƙar firgitarwa da ban tsoro. A rikice ya ce
''Sahura ke ce kuwa? '' Ya tambaya bakinsa na rawa zuciyarsa na ƙara nutso a cikin kogin addu'a. Wata busasshiyar dariya ta shiga ƙyaƙyatawa,zuciyarta cike da farincikin nasara. Yau Dauda Imamu ya shigo hannunta za ta juyashi kamar yadda Gwaggwonta ke juya ubanta da 'yan gidansu.
''Fitar mini daga ɗaki!" Ta furta a tsawace. Kafin ta sauke numfashi ya bar ɗakin a sukwane. Tun da ta zo duniya bata taɓa riskar kanta cikin farinciki kamar na yau ba. Sosai take jin babu wata shegiya a doron duniya irinta.
''Madalla da boka Ataka! Yanzu za a fara wasan! A yau ba sai gobe ba zan baza ikona son raina! Ni ce dai Sahurar gwaggwan bugaje! Heheheeee! '' ta furta a fili. Tsam ta mike ta fara taka rawa tana waƙar Barmanu mai Coge duk da asuba ne amma ko a kwalar rigarta. Ta sauya sunan waƙar zuwa sunanta da sunan boka
Sahura mai kiɗan ƙwarya! A sha kiɗa a sha daɗi! Areeeeh!
Na ci arziƙin boka! Ba za na raina boka ba! Areeeeh!
Izza tana wurin boka! Mulki yana wurin boka! Ba za na raina boka ba! Areeeeh!
Sahura mai kiɗan ƙwarya! Asha kiɗa a sha daɗi! Areeeh!
Ɗan nisawa ta yi sannan ta ce
"Kai kai kai! Ashe ni ma na iya waƙa. Bari na ƙara ƙirƙirar wata''
Sa'a tana wurin boka! Har mallaka tana wurin boka! Ta ya zan raina ɗan boka! Areeeh!
_Cikan buri na wurin boka! Biyan buƙata tana wurin boka! Ba za na raina boka ba! Areeeeh!
_Sahura mai kiɗan ƙwarya! A sha kiɗa a sha daɗi! Areeeeh!
Sai da ta yi rawa mai isarta sannan ta tsagaita ta dawo da kwanta,idanunta sun yi mata nauyi sosai, sakamakon rashin baccin da bata samu a daren yau ba. Nan da nan bacci mai daɗi ya salallaɓo ya yi wuff da ita zuwa duniyar maji daɗi. A ɓangaren Dauda Imamu sosai ya yi matuƙar firgita da al'amarin Sahura,wani irin kwarjininta ya cika idanunsa. Haka muryarta mai cike da ƙaraji ta cika dodon kunnuwansa kamar ba muryarta ba. Har ya bar gidan zuwa masallaci hankalinsa bai dawo gangar jikinsa ba. Har ya manta ya tayar da Hamid ya tsarkake jikinsa ya shirya zuwa Masallaci. Yana isa masallacin ya ɗauki Al'qur'ani mai tsarki ya fara karantawa. Wata iriyar natsuwa a hankali ta fara bin jijiyoyin jikinsa zuwa zuciya,zafin da yake ji a zuciyarsa ya nema ya rasa,wani irin musulmin sanyi ya kewaye ko'ina na jikinsa. Har lokacin sallar ya yi ya tsaya a gaba ya kabbarta sallah cikin natsuwa yake karatun. Koda aka idar da sallan bai yi gigin komawa gida a lokacin ba,zamansa ya yi a masallacin ya ci gaba da karatun Alqur'ani har rana ta fara hasko duniyarmu.
Ba Sahura ta farka daga baccin ba sai wurin 8:13am na safe. Nu'aymah ta tayar da ita don cikinta mai faɗa mata gaskiya indai harkar abinci ce ko kwaɗayi. Tsam ta miƙe zuwa bayi ta wanko bakinta sannan ta fito falon, Nu'aymah na biye da ita tana kukan yunwa. Sauran yaran kuma suna falo sun kunna kallo.
''Aunty Saudah ɗan ɗauko Maryam a ɗaki ki zauna da ita kafin na gama muku abin karin''
''Mtssss! Haba mama muna kallonmu za ki zo ki isheni da aiki. Ni wallahi ba zan je ba!'' Aunty Saudah faɗa tana tsuke fuska.
''Yi haƙuri Auntyn yara. Abin kari zan haɗa muku. Ba zan daɗe ba zan amsheta'' ta yi maganar tana lallaɓata har ta miƙe zuwa ɗakin. Tana tafiya tana ƙuƙuni har ta je ɗakin ta ɗaukota.
Shayi ta fara ɗorawa,ya tafasa ta juye a flask,ta haɗa ma Nu'aymah nata ta yanka mata biredi sannan ta fasa ƙwai guba goma ta soya. Idan da da ne ƙwai huɗu zuwa biyar take soyawa,amma yanzu jinta take za ta iya soya duka kwai guda ashirin ta zauna lafiya.(Hmmmmm Sahurar gwaggwan bugaje a bi duniya dai a sannu😂. Ni da my Esteem fans muna baki shawara. Idan kuma kin ƙi ji to mu 'yan kallo ne,idan abin dariya ya sameki zamu dara 😂)
Tsaf ta kammala komai sannan ta fito da kayan karin falo,a daidai lokacin Dauda Imamu ya shigo gidan. Suna haɗa ido ƙirjinsa ya yi mugun bugawa. Kafin ya ari mayafin natsuwa sautin muryar da bai santa da ita ba ta antayo cikin na'urar sauraransa babu zato.
''Ka je ɗakin Hamid ka kwaso kayan fitsarinsa ka wanke yanzu!" Kafin ta sauke numfashi kamar wanda ake sarrafa shi da na'urar TV ya nufi ɗakin Hamid jikinsa na tsuma ya ɗauko kayan fitsarin zuwa harabar gidan,ya dawo ɗakin ya ɗauki bokita ya zuba ruwa sannan ya hau wankin kayan bil haƙƙi da gaskiya. Ɗaiɗaikun mutane na wucewa suna kallonsa cike da mamaki. Yau Babban Limamin masallacin Juma'a sunkutun guda ke dirzar kaya sai ka ce Gauro. Duk yadda ya so yaƙar zuciyarsa a kan bin umarnin Sahura ya gagara, jinsa yake idan bai gama wankin da ta saka shi a kan lokaci ba,zai iya mutuwa tsabar yadda zuciyarshi ke zafi tana azalzalansa. A ɓangaren Sahura murmushi yin nasara ta yi sannan ta zauna kusa da yaranta. Hamid da mamaki ya kusan nutsar da shi cikin ƙasa duk da ƙarancin shekarunsa ya dubi Sahura
''Mama kika saka Baba wankin kayan fitsarina? Kar fa ya dukan idan ya gama" ya yi maganar cike da tsoro wanda ke kwance mararan a fuskarsa. Murmushi Sahura ta yi tana zuba ma kowanne soyayyan ƙwan a ƙaramar roba ta ce
''Sha kuruminka Hamid babu abin da ya isa ya yi maka a yanzu. Saka ranta a sassanyen inuwa ka ji yarona'' Ba don ya gamsu da zantukanta ba ya ce ''To'' yana ɗaukar ƙwan.
''Kun dai wanke bakunanku da kuka tashi ko'' dukkaninsu suka furta ''Eh''
Bayi ta nufa ta cire ma Maryam nafkin ta tsaftaceta sannan ta fito falon ta soma karyawa. Suna tsaka da karyawan Dauda Imamu ya shigo ɗakin. Bata ko kallesa ta ce
''Zo ka karya''
Babu musu ya zauna ta hada masa abin karin sannan ta koma inda take ta ci gaba karyawa. Shi kuwa jinsa yake a takure. A haka ya kammala kari,duk yadda zuciyarsa ke son tambayar yaransa zuwa hadda kasancewar ɓangaren ba su je hutu ba ya kasa kamar an rufe masa baki. Haka ya haƙura da tambayar har suka kammala karin.
''Ka ɗaura ruwan wankan yara,idan ya yi zafi ka sirka kama Aunty Saudah da su Nu'aymah wanka ka shiryasu sannan ka kaima Hamid ruwan wankansa ba yi shi ma ya yi,sai ka fito masa da kayan sakawa,sannan ka gyara ɗaki da wankin bayi. Ni zan koma ɗaki na kwanta zuwa an jima ni da Maryam sai mu yi wankan. Idan ka gama komai za ka iya tafiya. Ka ji ni ko!"
''Eh! Eh! Sahur..."
''Daga rana irin ta yau karka sake kirana da Sahura. Sunan da za ka dinga kirani da shi Ranki shi ɗade ''
Da sauri ya furta ''To ranki shi daɗe''
Taɓe baki ta yi sannan ta wuce ɗaki hannunta ɗauke da Maryam suka kwanta. Babu jimawa bacci a sake ɗaukarsu. Bawan Allah haka ya yi ta tiƙar aikin yana gumi abinka da ba a saba ba. Ya yi musu wanka ya shiryasu. Ya soma aikin gidan,Halima da Amina suka tayashi duk da ba wani abin a zo a gani suka iya ba,amma tausayin mahaifinsu ya cika zuciyarsu. Hamid da Aunty Saudah ko a kwalar rigarsu hasalima kallo suka ci gaba da yi. Nu'aymah kuma ta tasa sauran ƙwan da aka rage gaba tana ci...✍️
Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️
***