Chapter 21
The Amazing Pen ✍️.......
BAHAGON TUNANI
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
021
Jamila da kishiyarta suna zaune suna hira kamar 'yan'uwa yayin da yaran suke gefe suna wasa, ita kuma HAFIZA tana zaune kusa da Jamila tana zane suka tsinkayi shigowar Mairi gidan, tana zuwa ta durƙushe a gabansu ta sake rushewa da gurshiƙeƙen kuka. Da sauri kowannansu ya miƙe. Jamila a ruɗe ta bugi ƙirji tana faɗin
''Me zan gani ni Jamila! Yaya lafiya! Me ke faruwa ne? Ko rasuwa aka yi?" Ta jero mata tambayoyi idanunta a kanta
Mairi ta kasa magana,ta riƙe saitin zuciyarta tana kuka kamar ranta zai fita,zuciyarta ƙara zafi take. Da sauri kishiyar Jamila ta shiga ɗaki ta ɗebo mata ruwan randa mai sanyi ta bata. Amsar ruwan ta yi ta kafa kai ta shanye,take ta shiga sauke ajiyar zuciya. Suna haɗa ido da HAFIZA wani sabon kuka ya taso mata. Jawo HAFIZA ta yi ta rungume tana ƙara sautin kukan, HAFIZA ma da bata san a kan me take kukan ta shiga rerawa. Jamila da kishiyarta gabansu sai faɗuwa yake, musamman Jamila da take tunanin ko dai an yi rasuwa ne.
''Yaya ki sanar mana me ke faruwa! Wallahi kukanki ƙara tayar mini da hankali yake ''
Mairi cikin kuka ta zuƙi majina, sannan ta fara magana wanda shessheƙar kukan ya hana su ji abin da take faɗa da kyau.
''Ya!...ya!...yaranaaaaa!" Ta furta cikin kuka. Da sauri Jamila ta zauna a ƙasa daɓas! Hankali a tashe ta ce
''Yaya me ya samesu! Ba jiya na barosu lami lafiya ba!"
Girgiza mata kai ta yi tana sake rungume HAFIZA tsam a cikinta kamar tana tsoron wani zai ƙwaceta.
''Maman yara hutu Yaya take buƙata yanzu,idan hankalinta ya kwanta,kukan ya ragu sai ta sanar mana abin da faruwa" cewar kishiyata.
Cire HAFIZA suka yi daga rungumar da ta yi mata sannan suka taimaka mata ta miƙe,don wani jiri-jiri take ji yana niyyar kaita ƙasa,ga azababben ciwon da kanta yake yi. Sai a sannan Jamila ta ga ciwon da Mairi ta ji an rufe da bandage amma akwai ɗan shedar jini-jini. Bayan sun kai ta ɗakin ta zauna a saman kujera,sai ta sake jawo HAFIZA ta rungumeta tana sauke ajiyar zuciya. Ta saka hannu ɗaya ta fyace majina,sannan ta ƙara matsa HAFIZA a jikinta. Jamila da kishiyarta sai kallon ikon Allah suke. Kowanne a cikinsu ya ƙagu ya ji abin da ke faruwa da ita. Sai can ta ɗan ɗago idanunta waɗanda zuwa yanzu sun ƙara girma abinka da mai manyan idanu,cike da rauni haɗi da dasararriyar murya mai nuni da ta ci kuka ta fara ba su labari
''Muna tsaka da cin abinci Baban Yasir ya shiga gidan. Fuskarsa babu fara'ah kwata-kwata sai hakan ya tayar da hankalina na bisa falon. Tun kafin na iso gare shi ya ce, na tattaro kayan su Yasir za su bi shi Kaduna. Sai hakan ya ba ni mamaki ganin bai ambaci har da ni ba. Da na sake tambaya saii yake sanar miki wai Sahura ce ta umurci ya dawo da yaran wurinta. A ambaton sunan nata har da ranki shi daɗe ya faɗa. Mun kai ruwa rana da shi amma saina fuskanci ba ya cikin hayyacinsa duba da yadda yake sakar mini maganganun masu zafi da jaddada bin umarnin Sahura kamar addininsa ne. Wallahi har tsakar gida na fito ina roƙon ya bar mini yarana amma kamar ina ƙara zuga shi. Na riƙe jakar da ya saka kayan su Jalil sai ya fizge wanda hakan ya sabbaba na bige goshina a windon ɗaki. Jamila tun da na zo duniya ban taɓa shiga damuwa irin ta yau ba. Har waje na fito babu mayafi ina roƙon shi ya bar mini yara amma kamar ina ƙara tunzurashi. Jamila ina ji ina kallo ya wuce da su Yasir suna kuka suna kiran sunana. Jamila me na tsare wa Sahura! Me na mata take son ganin baya na! Ta tsaya a kan Baban Yasir mana! Me zai saka ta saka yarana cikin shirmenta! Idan saboda zuwa bariki ne ta yi hakan! Ni wallahi na yafe har gaban abada! Ta dawo mini da yarana don ban san wace kalar tarbiyya za ta ba su a can ba! ''
''Innalillahi wa inna ilahi raji'un! Lallai Sahura ta cika mara imani da tausayi! Yanzu dan tsabar iskanci da rainin hankali za ta aiko Dauda ya ɗauki yara ya kai mata!.'' Jamila ta faɗa tana tsotar leɓanta na ƙasa saboda takaici. Jinta take kamar ta zama mikiya ta dira gaban Sahura ta fara yagalgalan naman jikinta.
''Kai amma wannan kishiyar taki bata da imani! Allah ka tsarkake mana zukatanmu! Yanzu saboda tsabar mugunta ta rabaki da mijinki sannan ta zagayo ta rabaki da yaranki! Wallahi ba za ta taɓa ganin daidai ba ita da zuri'arta. '' cewar kishiyar Jamila da ta cika da mamakin Sahura. Ita dai har ga Allah ba haka halinta yake ba,bata da wannan mugun hali a kan kishiyarta. Ita da kishiyarta sai alkhairi. Wani tunani Jamila ta yi,sai ta dubi Mairi ta ce
''Yaya yanzu ki kwantar da hankali! In shaa Allahu babu abin da zai samu su Jalil! Allah na tare da su a duk inda suke! Babban abin da suke bukata a wurinki ita ce addu'a! Ki dage da sallar dare da sadaka in shaa Allah babu abin da zai samesu sai alkhairi! Sannan mijinki ma yana buƙatar addu'arki,domin yana tsaka mai wuya. Duk wanda ya ji labarin nan zai sheda aikin asiri ne,shi ya sa hankalinsa ya koma kanta! Kar ki manta yaya,Allah ba ya bacci,yana ganin duk abin da muke aikatawa mai kyau ko akasinsa. Yanzu mu zuba ido idan an dawo hutun makaranta bai dawo da su ba,sai ki je takanas ta kano ki amso yaranki,ita kuma ta cinye Dauda idan hakan shi zai nuna tana mutuwar sonsa. Idan kuma taƙi sai su kawu su shigo ciki,an jima da daddare idan baban Ruƙayya ya dawo sai muje wurin kawo mu fara jin ta bakinsa tukunna,don ba za a bar mata yara ta lalata musu tarbiyyar ba,ko kuma ta dinga azabtar da su. Don daga ganinta bata da imani! Sannan ta jira ƙarshenta! Wallahi tallahi ba zai taɓa yin kyau ba,domin sai ta yi nadama a lokacin da nadamar ba za ta yi mata amfani ba. Haka sai ta zubar da hawaye a lokacin da hawayen ba za su tausasa komai ba. Don Allah ki kwantar da hankalinki ci gaba da addu'a,ni ma zan dinga ta ya ki in sha Allah babu abin da zai samesu sai alkhairi. '' Ta ƙarashe maganar tana riƙo hannun Mairi da ta duƙar da kanta tana kallon ƙasa kamar mai ɗaukar darasi. Jamila da kishiyarta ba su yi ƙasa a gwiwa ba suka shiga yi mata nasiha da ban baki,har ta fara sassauta damuwarta ta hanyar sauke ajiyar zuciya akai-akai. Sun jima a ɗakin suna abu ɗaya daga bisani kishiyarta ta fito ɗaura sanwar dare ta bar Jamila tana mata nasiha..✍️
^^^^^^^^^^^^^^
Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya
A ɓangaren Sahura bayan ta koma gida ta ɗaura girkin rana. Dubu biyun da ta samu hannun oga Sabo ta ɓoyesu tana ƙudirtar sai ta sake tambayan wasu sojojin da matansu basa barikin,idan sun aminci shikenan ta samu hanyar tatsar aljihunsu idan an yi musu albashi. Ɗan waken fulawa ta yi,sai ta soya mangyaɗa,yajin tafarnuwa da ta daka ta fito da shi. Ta raba ɗan waken sannan kowa ya zo ya ɗauka. Suna tsaka da ci Sahura ta dubi yaranta cike da shauƙi ta ce
''An jima nan babanku zai kawo yaran kishiyata gidan nan su dinga yi mana aiki''
''Yeeeeh! Har da HAFIZA da baba yake yawan kira sunanta ko? Don wallahi na tsani yarinyar. Kullum baba bai da magana sai HAFIZA na da kaza,ai HAFIZA ta iya kaza. Don ma kwana biyu yanzu na ga ya rabu da kiran sunanta'' cewar Aunty Saudah.
''Ni ma haka! Na tsaneta wallahi" cewar Amina. Hamid da Halima su ma suka tafi a kan sun tsani HAFIZA. Nu'aymah bakinta bai da lokacin magana sai na ci. Sosai Sahura ta yi farinciki da furucinsu.
''Da alamu dai wannan HAFIZAR za ta yaba wa aya zaƙinta a wurinku?"
''Kullum zan dinga mata duka idan baba baya nan'' cewar Aunty Saudah.
''Ke kaɗai! Ni ma zan kwaɗa mata mari. Kalli yadda zan yi" cewar Halima ta cire hannunta daga kwanon ɗan waken sannan ta miƙe tare da nuna musu yadda za ta ɗauke HAFIZA da mari. Nan da nan suka tuntsire da dariya har da Nu'aymah. Yadda Halima ta daddage tana cijewa kamar a zahirin za ta kai mata marin. Cike da annashuwa suke cin abinci suna hirar yadda za su muzgunaa ba HAFIZA. Abin sa ba su sani ba ba tare da ita za a zo ba. (Hmmmm! Na gasgata barewa ba za ta yi guɗu ɗanta ya yi rarrafe ba. Sun tsotsa mugun nono. Allah sarki HAFIZAR mu Allah ya riga da ya tuɓutar da ke daga sharrinsu)
Bayan Isha'i
Zaune suke sun shagala da kallon wani Film ɗin india da Hamid ya amso casette ɗin daga wurin abokinsa. Sunan film ɗin MARD Aminta Baccha mai kare da doki. Suna tsaka da kallo suka tsinkayi sallamar Dauda Imamu,yana gaba su Yasir na biye da shi,sun yi matuƙar gajiya kasancewar wannan ce tafiyarsu ta farko mai tsayi musamman Hamida. Dukkaninsu suka juyo suna dubansu har suka ƙaraso cikin falon. Kallon ƙasƙanci Sahura ta bi su Yasir tana tsuke fuska irin kar su kawo mata wargi. Har gabanta Dauda Imamu ya je ya tsaya kansa a ƙa ce
''Ga su nan na kawo miki"
Murmusawa Sahura ta yi tana gyara zama
''Ka fita ko babu soso da sabulu,ka je akwai sauran abinci a kicin ka ci''
'''Yaran fa" ya tambaya a ɗan tsorace. Wawan tsaki ta ja sannan ta ce
''Da yunwa za su kwana yau. Ko kana da abin faɗa ne?" Ta yi maganar tana zare masa ido. Da sauri ya girgiza mata,ya juyo zuwa kicin.
''Kamar Mairi yara huɗu ta haifa. Ina HAFIZA a cikinsu'' ta furta a tsawace. Take tsaro da firgici bya ɗarsu a zukatan Yasir da Hamida, yayin da Jalil ko gezau,hasalima kafeta ya yi da manyan idanunta irin na Mahaifiyarsa. Cikin rawar murya Yasir ya ce
''Ba da ita aka zo ba!"
''Kam bala'i wato ni Dauda zai raina ma hankali. Dauda!'' ta kira sunansa da karfi,kafin ta sauke numfashi ya iso wajen da sauri yana faɗin
''Gani ranki sh daɗe''
''Ina HAFIZA ''
Take ƙirjinsa ya buga,shi kwata-kwata ya manta da wata HAFIZA,hasalima idanunsa a rufe suke a lokacin da yake gidan,burinsa kawai ya ga ya kawo yaran zuciyarsa ta samu natsuwa.
''Da kai nake!" Ta furta da hasale kamar za ta ari murya.
''Ki mini afuwa! Wallahi ban ganta ba lokacin da naje kuma ban yi tunanin tambayar Mairi ba. Ki yi haƙuri'' ya furta a sanyaye kamar marayan da babu uwa ba uba. Ɗan tausayinsa ta ji sai kawai ta ce ya tafi,babu jira ya juya zuwa kicin,duka yaran hankalinsu ya bar TVn ya dawo kansu. Juyar da hankalinta ta yi kan su Yasir. Tana musu kallon ƙasa da sama. Ta lura a duk cikinsu na tsakiyan ne bai nuna tsoranta ba,fuskarsa a murtuke take yana kallon ƙasa.
''Ya sunanka'' ta tambaya tana kallon Jalil. Banza ya yi da ita kamar ba da shi take maganar ba. A ƙufule ta sake tambayarsa
''Dan kutumar ubanka ya sunanka?"
Sai da ya ɗan ja wasu sakanni sannan ya buɗi baki kamar an yi masa dole ya furta ''Jalil'' daga haka ya tsuke bakinsa ya sake tamke fuska. 'Jalil' ta maimaita a ranta,ko dai shi ne wanda Gwaggwon Bugaje ta ce a cikin yaran akwai wanda ba zai mallaƙu ba,duba da yadda ya bata amsa a dake yana kallon ƙwaryar idonta ba tare da tsoro ba,kenan shi ne. Cije laɓɓanta ta yi na ƙasa da matuƙar ƙarfi karfi ta miƙe bayan ta ajiye Maryam a saman kujerar. Tana zuwa wurinsu ta ɗauke Jalil da lafiyayyan mari hagu da dama,ji kake Tasss! Tasss! Waro ido su Aunty Saudah suka yi ganin yau mamansu na mari,tun tasowarsu bata taɓa musu faɗa balle duka ba,amma yau gashi ta yi mari. Da sauri Jalil ya riƙe kumatunsa biyu,saboda marin ya shigesa sosai,sai dai a zahiri bai nuna ya ji zafi ba amma zuciyarsa cike take da tsanar Sahura duk da ƙarancin shekarunsa. Marin da Sahura ta yi ya yi daidai da fitowan Dauda Imamu daga kicin hannunsa riƙe da tire. Sosai hakan ya sosa ransa amma yana tsoron bayyana ɓacin ransa cibi ya zama ƙari. Haka ya danne ya ƙaraso falon ya zauna ya saka abincin gaba amma ya kasa ci,sai ambaton Allah yake a cikin zuciyarshi tare da neman ya kawo masa ɗauki. A hasale Sahura ta cacumo wuyan Jalil tana jijjiga shi tana faɗin
''Dan tsuliyar mamanka har ka yi girman da zan tambayi sunanka ka basar da ni! Ko uwarka Mairi bata isa ba balle kai ɗan karan kaɗa miya! Shige tsinanne! Ɗan gidan Abun kwari! '' tana gama faɗin haka ta tura shi ƙasa,ji kake Tim! A ƙasa,duk da haka bai yi ihu ba sai ruwan hawaye da idanunsa ke ambaliya. Juyowa kansu Yasir ta yi zuwa lokacin sun gama kiɗimewa da tsoranta,Hamida ƙiris ya rage ta saki fitsari tsabar tsoronta.
''Kai na san sunanka Yasir! Ke kuma fa!"
Kafin da rufe baki Hamida ta furta sunanta da iya ƙarfinta ''Hamidaaaaa''
Murmushi Sahura ta yi
''Uhmm! Yanzu na ji batu. Ke Hamida kenan! Ya yi yanzu ku biyoni na kai ku inda za ku kwanta,sai zuwa gobe za ku ci abinci don ban girka da ku ba'' ta yi maganar tana tafiya. Da sauri Yasir da Hamida suka bi bayanta. Jalil kuwa ko ɗaga kai ba yi ya kallesu ba. Ɗakinsu su Aunty Saudah ta kai Hamida,zuwa yanzu gabo biyu ne amma sai ta shimfiɗa mata wani yagalgallan zani a ƙasa ta ce da kwanta. Babu musu ta kwanta duk da yunwar da take ƙwaƙular cikinta. Yasir kuwa ta kai shi ɗakin Hamid ta shimfiɗa masa zani ya kwanta sannan ta dawo falon. Inda ta bar Jalil a nan ta iske shi. Mugun kallo ta watsa mishi sannan ta zauna tana ɗaukar Maryam.
''Kaɗan na maka in dai zan yi magana ka basar da ni! Wanda ya fi haka ma zan yi maka! Ɗan tsinanniya kawai! Mtsss!"
''Mama ashe kin iya mari. Shi ne baki taɓa marinmu ba?" Cewar Amina tana matsowa kusa da Sahura. Murmushi Sahura ta yi tana shafa kumatun Amina taa ce
''Ta ya zan mari kyakkyawar fuskarki mai matuƙar tsada! Mari ko duka ai sai 'ya'yan ya ku bayi!"
''Kenan mama Jalil 'ya'yan ya ku bayi ne ko?" Aunty Saudah ta tambaya. Ƙasaitaccen murmushi irin na manyan mata Sahura ta yi sannan ta ce
''Faɗi ki ƙara Aunty Saudah! Ɗan ya ku bayi ne shi!"
Take yaran suka tuntsire da dariya suna duban Jalil. Sosai Jalil ya ji zafin kiran Ɗan ya ku bayin da ta kira tare da dariyar da suka masa. Wasu hawayen da suka gangaro ya share. Dauda Imamu na gefe yana jinsu amma bai da bakin magana,a ƙasan ransa ya ji zafin kalmar da ta jefi Jalil da shi amma bai da karfin iko yanzu. Nan da nan yaran suka shiga tsokanarsa suna kiransa da Ɗan ya ku bayi suna dariya. Hakan ya ƙara rine zuciyar Jalil,kukan da yake riƙewa tun lokacin da ta mareshi ya cuɓuce masa. Sosai yake kukan su ku Aunty Saudah na masa dariya. Tsam! Ya miƙe zuwa ɗakin da ya ga Yasir ya shiga ba tare da ya bi ta kansu ba.
Koda ya shiga ɗakin ya iske Yasir zaune ya kife kansa a gwiwa yana kuka,kusa da shi ya matso suka ci gaba da kukan kamar marayu gwanin ban tausayi.
''Ba...baba ba ya sonmu yanzu! Ya Kawomu wurin wannan muguwar matar! Allah zai saka manaaa!" Jalil ya faɗa cikin kuka yana shassheƙa. Kuka sosai suke kamar ransu zai fita. Daga ƙarshe suka lallashi junansu,suka kwanta suna makyarkyatar sanyi. A ɓangaren Hamida ma kukan ta ci sannan ta kwanta a ƙasan. Da asuba lokacin garin ya ƙara sanyi da iska,a lokacin Sahura ta miƙe tare da zuwa ɗakin Hamid hannunta riƙe da bokiti cike da ruwan da ta ajiye da daddare kafin da kwanta saboda da su. Tana zuwa shimfiɗarsu Jalil ta ɗaga bokitin...✍️
Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️
***