ABUNDA KE 'BOYE...

sunday bonus

by @surayyahms

SUNDAY BONUS!

zainab Arifah tana rike da veil din abayan ayaanah gabaki daya hankali tareda imaninta duka sukayikan yoloyolon doguwar sumanta da tsabar yauqinsa ya gama warwarewa dakansa yana kuncuwa baya itakanta ayaanahn ma bata farga ba. wani irin abu zainab arifah taji ya kara riqe mata saman kirjinta, maiqarfi da kuma karsashi, nan take tabi ta kankance idanunta akan yarinyar gashi it almost feels like kusan kowa mind insa baya wajensu duk anata dariya akan surutun da hajiya mairo takekan xubawa..

yunkurin miƙewa tsaye zainab arifah din tay da tunanin hala ma gashin ayaanan is not even real, it must be attachment or smtin. tana mikewar kuwa tay wani walakantaccen flinging da veil din lokacin ibaad ya shigo kenan wurgin yasauka akan fuskansa yabi ya riƙe da hannunshi da sauri tun kafin veil din ya isa kasa

yana daga ido yaga ayaanah acan kurkusa da su sultana bata lura kanta a bude har zata zauna yayi sauri yasaka hannu yadan jawota kurkusa dashi yadda ya jawotan ahnkli kuma cikin kulawa yasa sai tadan ji bugun zuciya me karfi musnn ma dataga veil din abayanta ahannunsa, wani irin kallon kwayar idonsa takeyi ta kasa cewa komi, nan kowa ya dawo da idonsa ta wajensu anata kallonsu, atake ibaad ya hade rai ya dauke wuta tamkr da baisan ana kallonsun ba ya warware veil din abayan ya kara rufe mata akanta gently snn ya turata gefensu sultana kadan baice mata komi ya dauke kansa ya karaso ciki kai tsaye, wani durus zainab Arifah ta dinga kallonsa da shauqin mamaki a idanunta

sede ganin yadda ya haɗa ransa yabasar ya karaso cikin mutane kmr baiy komi ba yasaka kowama ya shashentar aka cigaba da saurarar surutun hjy mairo dake bada kowa takaici da  dariya.

da wani irin sanyin kunya ayaanah ta koma can wajen su kulthum tazauna daf dasu tanata kokowa da suman nata tare da kkrin cusashi can ciki, har sultana tafara tayata sunayi tare, ahnkli kulthum ta dubesu tace"wait, zanje na dauko miki hula kawai" tana fadin hakan tamiƙe tafita wajr da sauri taje sashensu takawo ma ayaanahn inner under cap dakyar ta karba kirjinta na dan bugawa sabida tasan ibaad ya hanata karban abun wani bada son ranta ba tasaka hular akanta tareda cusa gashin ciki.

idanun zainab ya koma kan ibaad da gabaki daya ta lura yana kallon ayanaa, ba shiri tafarajin kamar tana neman rasa nitsuwarta,cos who the hell is this girl? kuma mesa ma ibaad yafara kulata harma yamaida nata veil akanta batare da ya mata masifa ba while she knw baya wasa da kowa,..ryt frm the looks datake mashi zakasan she expected him to be a little bit overactive on the girl koma ace he left the veil to fall on the ground in yaso ita yarinyar ta tsuguna ta dauka dakanta, da taga hakan bai faru ba duk sai kuma taji haushin abun ya kamata..

after a while of endless labarin kauyen tudu da funny banters manyan matayen gidan suka  gayyace kowa kan wata dgwar 45inches luxurious dinning table, yau kusan babu wanda baya wajen face mujaheed da bai iso nijeriya ba tukuna.

cikin sakin sabon hira da nishadi aka faraciye ciye sede abubuwan kwadayi da Ammi karama tafarayi shi aka fara lashewa ana santi, hira a table din sai ya kara yawa, farin ciki kamar xai kashe hjy mairo mai tuwo dataga kowa fuskrsa da farinciki ayayinda ran ammi babba ya baci ya kuma cika yay fam da haushi, duk su uncle moh da maheer suka dawo da hiran zalla akan abinci, musmn da hajy hajara cikin watsa magana direct irin tasu na tsoffi tace ita sam rice dinsu ammi babban bai gama jin maggi ba dan haka chops da masan kawai zataci, hatta zainab arifah dambun naman da samosa da salad nd eggs kawai taci bata taba musu coloured smoky rice dinsu ba, ko ajikin anty safeera as long as lefi baishafate ba sai hira kawai akeyi da ita ammi karama kuma dama tanada kunya kuma batason tay wani magana akan girki da zaisaka bappa zaidu ya saki layi akan abincinta, sai tau sanyi bata fiye magana ba takama kanta tay shiru saidai tay dariya ko murmushi me sanyi

duk wajen ammi babba ne kadai ranta yake ci da wuta, duk wahalar nan iyakan masa da su kajinne kadai suka samu karbuwa duk wani abu bayan haka da suka dafa gabaki daya yan qauyen ne kawai sukafi ci sosai.

ana gamawa hajiya ta umarce maheer akan ya dauko mota shida uncle moh sukai bakin ta masaukinsu inyaso inta huta nan da sati biyu haka duk zasu koma bakin aikinsu na gidan abinci.

haka baqin nan maza uku da mata biyu suka dinga ma su bappa zaidu addua da kuma godiya dan bakaramin murna sukayi da hajiya ta kawo su binni snn ta basu matsuguni ba, ta musu gata iyaka alherin da zasu saka mata dashi shine kawai sumata aiki tsakani da Allah a shagonta dan tana caskar kudinta. hakanan aka tarkata hilimin rice dayawa da aka ki ci tareda da sauran tarkacen namomin a kuloli aka bisu dashi, har waje duk aka rakosu ruthy ne kawai aka kyaleta da hajy hajara sabida tay karama wa xaman kanta agidan. tun a tudu da haj mairo ta naimi ta musuluntar da ruthy sarki da wani pastorn garin sukace sam sam, shine akayi yarjejiniya cewa inhar zasu sallama mata amanar ruthy saidan indan ruthyn ne dakanta ta furta cewa tana son tacanxa addini tayi musulunci bayan tamallaki hanklin kanta bawai asata ciki na dole ba. haka kuwa suka hakura musu, dan sunsan muddin suka barta a hannun magajiyan can karuwanci kawai za'a turata da danyen shekaru.

hajiya hajara tace ita xata wuce da ita gidanta su zauna daga can zatana zuwa aikin akan sai inta girman takai irin 16-17yrs snn subata nata dakin a gidan wokers din itama.

acikin wata luxurious sienna bus maheer ya kwashe bakin dukansu da kayansu da kuma tarkacen abinci, da su drinks shiyana tuki uncle moh yana gefensa, sai bakin abaya,..kai tsaye aka wuce dasu can workers estate saida kowa ya zabi dakinsa kafin suka kamo hanyar dawowa gida..

daga gidan kuwa tsayuwar Ibaad da bappa zaid a waje yasa zainab arifah ta tarkata gifts inta data kawo masa taje can sashen anty safeerah dashi tabi ta zauna a falonsu ta kunna wayarta sunata video call da kawayenta..

safiya kawai tasaka gadi akan tana duba mata ibaad yana shigowa gidan maza tazo ta gaya mata akan lokaci..


sulthana da kulthum duk suka wuce sashen ammi karama tare da ruthy da ayaanah, Ruth is slightly dark skinned bakar fata ce amma ba dulum ba, sosai ta gane ayaanah tun lokcin da suka hadu ashgon hajy mairo ranar da inayah zata rasu itace ma taimaketa sukaje police station har ta kira mata hajya mairo, tunda suka zauna take ma ayaanah jajen rasuwar addanta tare da bata labarin duk abunda yafaru a school dinsu na tudu bayan ta dawo birni, tace mata a duka malaman su sunyi jajen mutuwar inayah sosai, kuma son so ace da anbar ayaanahn ta cigaba da karatu da su amadadin addanta inayah musmn ma da akaxo da tarkarda na full schorlashp din da inayan tazo ta samu daga wajen sabon LGA chairman bayan rasuwarta

..ayaanah dai batace komi ba tanata hawaye sosai duk tama rasa abunda zatace ma ruthy
..duka su sultana da kulthum suka taru sunata rarrashinta suna bata hakuri. dakema ruthyn tana da saurin sabo da surutu babu shiri tafara bawa su sultana irin labarin unbeatbl reputation din da su ayaanah da addanta suka setting na karatu a kauyen su na tudu akan karatun boko da islama which was very impressive to hear dan sukansu basuyi tsammanin cewa mutumin kauye kamar su ayaanah da addanta jajirtaccu bane a boko da islamiya sosai har haka ba.

itade sultana ta jima da lura da yadda ayaanah take saukin gane kowani irin turanci in anmata duk dama bata taɓa amsawa ba amma tajima da lura kmr tanajin turanci sosai. su hudunsu suka zauna a shashen ammi karama tun ana jimamin kukan mutuwar inaayah har aka dawo hirar sabon shagon abinci, tun anan ruthy tafara ma ayaanah tayi akan itama ta dage kawai tana zuwa restaurant in hajiya mairo dansu na koyan abinci kala kala atare tunda wannan restaurant din na birni ne, kuma na yan gayu, snn za'a kawo smart profesionl chefs da food servers zasuzo suna musu marketing kuma suna dafa abincin zamani da zaa na sayarwa wa masu kudi sosaiz duk wani shirye shiryen upgrade da ake shirinyi ma restaurant din duk ruthy ta gaggaya musu komi na yan gayu za'ayi, can hardai abun yafara bawa ayaanah sha'awa saidai batace mata eh ko aa ba sabida tana tsoro batasan ko ibaad zaizo ya bari tana zuwa ba.


daga dayan bangaren kuwa wani sabuwar hira akan bude tsakanin hajiya mairo da surukanantan tare da hajiya hajara acikinsu tanakan basu labarin halin data shiga da yan kidnapping acan tudu kusan kowa yana mata jaje saidai na ciki na ciki.. domin kuwa sauran matan duk basu wani jin dadin yadda hajiya mairo takeyima fatima kallo kmr yar cikinta na asali ba a amtsayin surkuwa ba,wanda kusan duk tafi maida hankli kanta acikin hirar

...gajiya da jin hirar kauyen ammi babba tay maza maza ta miƙe tayi excusing dinsu taje can can waje tafara bada workers dinsu sabbin oda akan su fara shirya kayan da zasu bukata na abincin dare dan harda baƙin suma za'a kai musu nasu da wuri tunda yau sukazo.

bada son ranta ba tafito amma sai taji hakan ya fi mata, gara tay aikinta na babban mace acikin surukunayen gidan data zauna tanaji ko tana kallo ana fifita fatima agaban idanunta.

anty safeera kam sam taki ta tashi acikinsu saima kara sakewa datayi ana hiran da ita,  dan dama ita batason kayan takura musmn ma ana aikin gida kuma duk tsiya itama so take taga ta samu wnn karbuwa sosai awajen hjy mairo kodama wata rana zata samu matsayi irinna ammi karama agidan itama. duk  bata da shkru sosai amma sosai tafi ammi babban nisan tunani da wayo, mostly takanji qishi da hassada akan ammi karama amma ko kadan bata nunawa bare zafafawa, she still respect her nd she look up to her secretly dan ganin itama takoyi hali me kyau na kama zuciyar yan gidan gaba daya shiyasa ta zamo neutral bata gaba a fili da kowa.


ibaad da bappa zaidu basu shigo ciki ba har su maheer da uncle moh suka dawo akay sallahn azhr atare.

bayan sun idar ne maheer ya fita zaikoma cikin gida sede ganin safiya dayayi tanata leke leken ibaad kamr jelɓe yasa ya kirata tana zuwa ya masifeta akan taje tay sallan snn ta kira masa kulthum yanxun nan

da sauri ta koma ciki aikuwa tana zuwa sashen datagansu su hudu sunata hira wani irin tsaki taja ta hade rai tawuce dakinta dan taje tay alwala, haka tay sallah batace musu uffan ba suma basu ce mata ba nan suma suka tashi sukai alwala a extra room sukay sallahnsu sun idar kenan safiyan tazo tace ma kulthum cewa yaa maheer yana kiranta awaje..

tun kafin kulthum ta amsata tafita waje da sauri ta kara lekawa can kuwa ta hango ibaad yana fitowa daga masallaci da waya a hannunsa kamr zaije ta bakin gate, da wani irin gudu ta dawo gidan taje sashen anty safeera har tana haqi tana isa tace "anty zainab arifah ganan yaa ibaad yana waje kiyi sauri kije naga kamar waje zai fita.."Katse wayar zainab arifah tay tace "safiya kiyi sauri kije kice masa ya tsaya gani nan zuwa abayan ki..wani kifi kifi da ido safiyan tay tajuya tana takawa ahankli dan tasan har abada bazata iya xuwa tace ma ibaad ya tsaya ba dan tasan jininsu baiwani gama haduwa ba tukuna zai iya falla mata mari yace mata magulmaciya..

ahnkli ta dinga tafiya har zainab arifah ta gama shafe shafenta ta dauko gifts bags din tafito ta wuceta ta fita can waje, tana lekawa kuwa idonta ya sauka caraf akan maheer acan gefe yana zaune akan chair kulthum tana nanike ata gefensa ta dan tsuguna kusa daf dashi sunata magana ahankali kmr saurayi da budurwa.

tsabar son taji gulma da sauri tay ta wajensu ta kasa kunne har sanda taji kamar they are actually talking about yadda zai taimaketa tay catching up da wuri a tajweed na qur'anic competition na islamiyarta da aka sata kwanan nan tukunna ta kara sauri tay gaba.

samu tay ibaad ya jingunu da jikin motarsu yanata latsa wayarsa da alamar chating yakeyi, tana isowa caraf tazo zata leka cikin wayar batare da ya daga ba ya mata wani irin mugun kallon da saida kirjinta ya tsaya cak taja tatsaya tana kallonsa, kallo daya yamata ya kuma dauke kansa ya mayar kan wayan, budan baki tay zata masa magana cikin datsar numfashin ta yace ke wai baki sallama ne?? ta dan turo bako tace "my bad, asallam alaikum
..saida yaja mata aji snn cikin hade rai ya amsata ciki ciki

..cikin sauke ajiyan zuciya ta rage murya tace"can i talk to u for a min? idonsa nakan wayan yace "ure already talking, so? cikin wata yangatacen rolling eyes tace "i bot u some gift ne sabida ranar naga kamar ranka ya baci da wanda na siya ma sister dinka, naga kuma kamr kyauta ma kayi dasu ko? kmr bazai amsa ba can kasar wuyarsa yace is dat all?shiru tay sounding abit off tace "no. inaso ne ka karba, ..ibaad, pls accept this one cos i am sure zaka so shi. batare da ya kalla komi takeso ya karban ba yace 'thanks" batace komi ta mika masa dakyar ya karba kai tsaye ya aje akan motar baiko kalla meye ne ba..

cikin hadiyat zuciya tace daddy yace he will talk to u abt you home schooling me na karatun islamiya...has he? yace 'nop" ahnkli tace..okay, i just want to know if ure okay with it bana son na takura maka, dama daddyna ne yace kaiine kawai zaka iya koyamin addini agida and kawaye na sunce..tun bata karasa kalaman ba wayarsa ya fara kara kai tsaye ya dauka yakai kunnensa yay sallama anitse

mujaheed ne ya kirasa yanakan rokansa akan yazo ya daukesa a airport sun riga sun sauka..yana amsashi da toh ya katse wayar yamata kallo daya yace "are u done cos i am heading out now".ranta baiso ba ahnkli tace ohh to where can i come with yoi? kmr bazai amsa ba yace "airpot, nd no thanks...cikin kyabe baki dan yangace tace its okay, toh zan jira kawai sai inka dawo zamu karasa srn maganan...baice komi ba yana bude motar ta matsa gefe tanata kallonsa har ya zauna zai kulle kenan snn tay sauri ta dau gift bag din ta saka masa akan seat din gaba snn ta kama hanya ta wuce cikin gida...

baiko kalle inda tay ba ya dauki wayarsa yanata so yakira maheer dan suje tare saidai ganinsa da kulthum dayay acan gefe suna magana sai ya fasa, ya kunna motar ya tafi shidayansa abunsa..

sai har da yay nisa a hanyar aiport snn yay ma maheer din text akan idan yagama ya samesa acan minjibir along gezawa road cikin PortoGolf Resort bayan asr prayer.
maheer bai ma ga text dinba sai har daya gama hirarsa da kulthum aka fito daga sallan asr snn ya gani. zai karbi key din babansa kenan yaji bappa zaidu suna hira uncle moh

he is obessed nd still on ayaanahs matter, casually yake gaya ma bappa zaidu cewa ai ayaanah tamkr iri ce, da irinta kuma ake gyaran zuria shiyasa bai kamata su aurar da ita wana waje ba. shide bappa zaidu bai cewa komi ba dake kele kelen duniya ba'a agabansa yake ba.

shikansa yasan ayaanaah is exceptionally beautiful amma baida raa'ayin dole a tursasa wani yaro ko yarinya agidan ace dole yay auren dangi ko hadin gida sai kwata kwata bai dau maganan uncle moh din da muhimmanci ba.

dama kuma yasan halin kaninsa, shi dan boko ne wayewan ta masa yawa akansa, rayuwar turawan nan na yin abu anyhow yasaka agaba.. he is more obsessd with materials things, kai ko anty safeeran ma ya aurota ne sabida big girl slay queen life inta, da kuma arxikin gidansu, da farin fata da kyanta me yawan daukar idanu. uncle moh har ya gama zubansa akan ayaanah bappa zaidu bai basa wani kakkawaran amsa ba, har maheer yazo ya amshi key ya bi bayan ibaad.

yana zuwa resot din kuwa ya samesa tare da mujaheed suna zaune har sunyi odern burger da lemonade da alaman basu jima da dawowa daga airpot ba, da dan murmushi ya miƙa ma mujaheed din hannu suka gaisa snn ya tambaye ibaad akan meyasa basu wuce gida MJ din ya huta acan ba, shikuma dama delibratry yay convincing mujaheed harda bashi kyautar gift bag da zainab arifahn ta basa ko budewa yaga meye aciki baiyi ba dan kawai su zo nan  suhuta sabida ko kadan baison ya koma gidan ya sake gamuwa da zainab arifah cos she is seriously annoying him

da sukaga kamr baza su wani ganema bayanin sa ba shine kawai maheer ya jonasu suka xauna anan suka fara hiran games din da mujaheed yaje south africa sukayi MJ yanata nuna musu hotuna da videos awayansa can da suka gaji suka shiga sashen da akwai pools da snooker games acikin resort din, anan suka balain bata lokacinsu har saida aka kisa kiran magrib ya tabbata by now zainab arifah ta wuce gida snn yafara matsa musu akan su dawo gida.

suna isowa kuwa aka kira sallahn, dede lokcin su hajiya mairo da anty safeera da ammi karama sun rako hajiya hajara da ruthy waje kenn har ansako musu abincin daren a cooler suma sun wuce gida kenan..

agaban masallacin suka parkr mota sukay alwala su ukun suka shiga ciki basu fito ba har saida akay sallan ishai, kowa cikin iyayen yaji dadin ganin mujaheed duk dama ya gaji sosai basu wani jima dashi ba dukansu suka shiga ciki, mai gadine yakai ma MJ bags dinsa har dakinsa sukuma suka zauna ashashen hajya mairo akafara wani sabon surutun dataga mujaheed dake duk tafi daukarsa me hankli da tausayin acikin mazajen gidan.

ammi babba ita tay komi na abincin  dare amma kuma tafi kowa fushi da daure fuska wai an bar mata aiki ita daya. gara ma anty safeera ta kulata tana bata haquri ammi karama kam batace uffan ba haka takoma sashenta tay ma su ayaanah hadadden tea dayaji milo da madara suka sha kafin 9.30pm suka barta suka wuce dakin kulthum wai anan yauma zasuyi bacci.

wani farin leda me kauri ta dauko ta bawa sultana akan ta kai ma babanta acan awaje da sauri taje can wajen ta samesa suna waya da ammin karaman takai masa ledan ya karba da sauri tabi su ayaanah sashen anty safeerah

wanka ammi karama tay ta kimtsa ko inanta sashenta yay fess arnd 10pm tana kwanciya akan gadonta taga tex dinsa na sallama da kuma godiya da dambun naman data bashi
..yace mata sai gobe zaizo gidan ya duba maman sa da yamma..

murmushi tay batama sa reply ba dan tasan duk tsiya yana tare da matarsa a motar nan

nan ta jawo reading glasses dinta ta saka ta cigaba da karanta addua awani littafi har bacci ya dauketa. tunda su maheer suka gama hirar kaka da jikoki da hajiya suka koma gida mujaheed shima yabar sashen, dakinsa kawai ya wuce direct basuwani dogon surutu da mum dinsan ba sabida ya gaji sosai.

wajajen 11 uncle moh ya fito daga wanka ko shafa mai baiyi ajikin sa ba ya zauna da towel abakin gado suna hira da wani amininsa alhaj ameer wanda bai jima da aure ba amma mata biyu ya aura a lkci daya gasu kyakyawawa yana bala'in jin kansa musmn yadda yake flaunting wealth maza suna hura mai kai ana yabon life style insa da matayensa slay queens da ya auro duka a rana daya...

da uban zumudi a voice nashi yake bawa alhaj ameer din labarin irin mayen kyan ayaanah dan dama can ya rasa da uban waye xaiy wannan hiran a daukesa serious,

aikuwa yana fara gaya wa abokin nasa atake ya fara bashi goyon baya 100% harda kirga masa shekaru acewar sa by the time he is in his mid 40s ayaanah ta gama secndry schl  ta isa aure..wani washe baki uncle moh yake yi yana balain jin dadin maganganun da alhaj ameer din yake masa suna cikin hirar yaji anyi knocking tunda ya shako qamshin wata kasaitacceiyar humra yasan safeerah ne da sauri sauri ya rage murya yace ma Alhaj ameer yabar maganan kawai sai sun hadu zasu tattauna.
#SURAYYAHMS
***