BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

Chapter 22

by @narrnarhhbukar00

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

022

Da asuba lokacin garin ya ƙara sanyi da iska,a lokacin Sahura ta miƙe tare da zuwa ɗakin Hamid hannunta riƙe da bokiti cike da ruwan da ta ajiye da daddare kafin da kwanta saboda da su. Tana zuwa shimfiɗarsu Jalil ta ɗaga bokitin ta juye kusan rabin ruwan a cikinsu,take suka farka a razane suna ƙwalla ihu. Da sauri Sahura ta daka musu tsawa tana faɗin

''Ku rufe mini baki kar ku tayar mini da yara suna bacci 'yan iska! Maza ku tashi ku biyoni''

Da Sauri suka miƙe suna rawar sanyi,kai tsaye ɗakin su Aunty Saudah ta shiga, sauran ruwan da ya rage ta juye a jikin Hamida. A gigice ta farka tana sakin ƙara wanda hakan ya saka Nu'aymah farkawa da kuka tana kiran mamanta. Tsaki Sahura ta ja tana dungure kan Hamida

''Ta so ki biyoni kema.'' tana faɗin haka ta juyo. Da sauri Hamida ta miƙe tare da biyota tana ƙanƙame jikinta saboda sanyi. Mayafi Sahura ta saka sannan ta shiga kicin ta ɗauko bokita uku ta miƙa musu suka fito gidan. Lokacin garin ya yi haske sosai,mutane sun fara kai-kawo a barikin musamman masu fita zuwa aiki. Tana gaba suna biye da ita,jikinsu ta rawa saboda sanyi har zuwa fanfon da suke ɗiban ruwa idan fanfon gidan ya samu matsala. A wannan karon babu matsalar da fanfon ya samu tsabar mugunta ne da rashin imani ya sakata hakan. Dubansu ta yi tana sakin murmushin mugun sannan ta ce

''Idan kuna son cin abinci to ku mayar da hankali ku cika mazubar ruwana,idan kuma kuka yi wasa to a cikinku.'' tana gama faɗin haka ta juya tana dariyar ƙeta ta koma gidan ta yi kwanciyarta. Tana barin wurin Hamida ta saki kuka

''Yaa Yasir sanyi nake ji. Sannan ina jin yunwa"

''Ki yi haƙuri Hamida. Ni ma da Jalil duka sanyi muke ji da yunwa. Kin ga ta ce idan ba mu ɗiba ruwan ba,ba za ta ba mu abinci ba. Ki zauna a nan mu sai mu dinga ɗiban ruwa''

''Sanyi nake ji'' ta yi maganar tana takurewa wuri ɗaya.

''Idan za mu dawo san zo miki da wata riga a cikin jakarmu'' cewar Jalil. Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta samu wuri a saman dakali ta zauna,sai faman hamma take tana kallon mutanen da ke kai-kawo a wurin...✍️

^^^^^^^^^^^^^^^^

Hajin Bijini Mada, jihar Zamfara Nijeriya

A ɓangaren Mairi da daddare bayan mijin Jamila ya dawo suka tafi gidan kawunsu. A zaure suka sameshi ya kunna wutar kara yana jin ɗumi. Da sallama a bisa laɓɓansu suka ƙarasa inda yake zaunan. Bayan sun gaisa ya ɗauki HAFIZA a saman cinyarsa sannan Jamila ta natsu tare da sanar masa abin da ke faruwa da Mairi kamar yadda ta sanar mata. Sosai abin ya yi matuƙar tayar da hankalinsa. Jiinjina kansa ya yi yana faɗin

''Wannan aikin asiri ne babu shakka! Mallaka ce ke ɗawainiya da Dauda! Kamar yadda Jamila kika ce a bari bayan hutu ni na gamsu da hakan. Mu tsaya mu ga gudun ruwan su. Idan bai dawo da su ba,ke Mairi sai ki je Kadunan ki ɗaukosu kamar yadda Jamila ta ce. Amma idan yaƙi to dole na saka baki,don ba za a bar mata yara ta lalata rayuwarsu ba. ''

''To Kawu na gode!" Mairi ta furta a sanyaye. Sun ɗan taɓa hira daga bisani suka koma gidan Jamila. A daren Mairi bata rintsa ma. Damuwa sosai ya cika zuciyarta da tunanin a wani hali yaranta suke ciki. Kasancewar mijin Jamila ba a ɗakinta yake ba sai ta samu damar keɓewa. Jamila bata yi ƙasa a gwiwa ba ta shiga yi mata nasiha da ƙara jaddada mata ta dogara ga Allah,shi zai zama gatanta da yaranta. Sannan ta jira ta gani babu inda asirin zai je zai warware da ikon Allah. Sun jima suna tattaunawa daga bisani suka kwanta. HAFIZA ta jima da bacci bayan ta yi muraji'ar karatun da Ammu Jamila ta koya mata. Wurin ƙarfe uku na dare Mairi ta farka tare da tayar da Jamila suka ɗauro alwala,tare da kabbarta sallah. Raka'ah shida suka yi tare da kullewa da Salatul Wutr. Bayan sun sallame Mairi ta ɗaga hannunta sama,hawaye na bin kuncinta ɗaya bayan ɗaya. Ta karanta ayatul kursiyy da amanar Rasulu tare da salatin Annabin Rahma Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama. Cikin rawar murya ta fara wa Ubangiji kirari.

Allah! Kai ne Allah! Kai ne ka halicci sama da ƙasa!  Kai ka haliccemu! Kai ka halicci fiyayyan halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama! Kai ya saukar masa da Al'qur'ani mai tsarki ta hanyar Mala'ikanka Jibrilu Alaihissalam! Ina tawassali ta sunayenka kyawawa waɗanda ka ambace su a cikin al'qur'ani mai tsarki! Ya Allah ka tsare yarana daga sharrin abokiyar zamana! Allah ban taɓa nufarta da sharri daidai da ƙwayar zarra ba! Allah ka dubi zuciyata ka kare yana daga sharrinta da sharrin duk wani abu mai cutarwaaaa!

Kuka sosai ta shiga rerawa wanda hakan ya sakata tsaida roƙon,sosai ta ci kuka,daga bisani ta ja majina ta ci gaba da addu'ar

Allahumma ya Hannani! Ya Mannanu! Ya badi'usa- samawati wal ardi! Ya zul jalali wal ikram! Ya hayyu ya Qayyum! Allah ka kawo ma yarana ɗauki! Allah ka dawo da hankalin mijina gareni! Allah ka karkato da hankalin mijina gareni sannan ka karesa daga sharrinta! Allah ya albarkaci rayuwar yarana! Ka tsayar da su a kan bin tafarkin annabinka! Ka haskaka yau ɗinsu da goben su! Allah ka jiƙan iyayenmu! Ya yafe mana ba don halinmu ba! Allah na tuba ka yafe mini!

Sosai ta ɓata tsayin daren tana addu'a,gefe guda Jamila na amsawa da ''Ameen'' har ta kammala suka koma kwanciya. Washegari da safe ta dawo Gusau tare da HAFIZA. Bayan ta dawo matan unguwa suka shiga yi mata Allah ya kyauta wasu kuma don zo bugun ruwan cikinta ne. Amma sai ta dake ta nuna komai ba komai ba ne. Duk hanyar da suka bi don sanin abin da ke faruwa ta toshe hanyar. Haka suka kowanne ya wuce gidansa gwiwa a saɓule...✍️

^^^^^^^^^^^^^^^

Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya

A ɓangaren su Jalil haka suka yi ta jidar ruwan suna kai wa gidan suna dawowa. Wata ma'aikaciya ta zo wucewa ta yi tozali da su Yasir suna kai ruwa gidan ta tsayar da su tare da tambayar wa ya sakasu ɗiban ruwa da sassafe haka. Jalil ya ce matar gidan kasancewar ba su san sunanta ba. Da yake matar ta ɗan san Sahura,sukan gaisa idan suka haɗu a hanya  sai ta bi bayansu zuwa gidan. Lokacin Sahura na waje ta tsaya tana kula da yadda suke zuba ruwan. Da farko ta so kwanciyar amma saii wata zuciyar ta ce gwara ta tsaya su kammala cika mata robobin ruwa karsu mata ba daidai ba.

Su Jalil suna gaba tana biye da su har suka karaso inda take. Sallama ta mata,Sahura ta amsa cike ta fara'ah

''Matar malam don Allah ki yi haƙuri zan shiga hurumin da ba nawa ba.''

Ɗan ɓata fuska Sahura ta don ta gane inda zancenta ya dosa.

''Ina ji'' ta furta a ɗaure. Matar bata damu da yanayin Sahura ba ta ce

''Matar malam bai da ce ki tura yaran nan da sassafe zuwa ɗibe ruwa ba. Why not ki bari like 10 haka, lokacin rana ta ɗan fito sosai. Wannan sanyin safen da kike gani ba ƙaramin illa garesa ba musanman ga yara ƙananu.''

Taɓe baki Sahura ta yi sannan ta ce

''To likita gogon turai! Na gode da shawararki! Amma ki sani shawararki bata da wurin zama a wannan ƙwaƙwalwar tawa'' ta yi maganar tana nuna tsakiyar kanta. Sai ta ci gaba da cewa

''Yara kuma yanzu suka fara ɗibo mini ruwa! To miye amfaninsu idan ba su ɗibo ruwan ba! Haka kurum zan dinga ciyar da tsinannu ba zan moresu ba.''

Sake baki matar ta yi tana kallon Sahura. Bayan ta gama ɓaɓatunta sannan ta ce

''Hala waɗannan yaran ba naki ba ne''

''Yaran kishiyata ne''

''Eh lallai matar malam! Dole ki azabtar da su saboda ba yaranki ba ne! Su 'ya'yan naki shafaffu da mai suna kwance suna bacci amma kin fito da 'yan yara kina azabtar da su! Wallahi kin yi asara! Sannan waɗannan yaran da kike azabtarwa sai Allah ya ɗaukakasu sama da naki! Wallahi kin ban mamaki''

Tafi Sahura ta yi tana riƙe haɓa sannan ta ce

''Bakinki sai dai ya sari ɗanyen kashi domin wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa''

''A haka Ubangiji zai kashe raƙumar sannan wutsiyar da kike tunanin ba za ta taɓa kasa ta zama abincin tsutsotsi. Wallahi matar malam ki ji tsoron Allah! Kar ki ga kina azabtar da yaran kishiyarki ki yi tunaanin kin ci ɓagas! Domin Ubangiji ba ya yafe haƙƙin wani a kan wani! Wallahi kin gama asara ta duniya da lahira! Mtsssssss!" Matar ta ja tsaki sannan ta bar Sahura da sakin baki. Sosai zantukanta suka mata ɗaci a maƙoshi. Komawa kicin ta yi zuciye ta ɗora sanwar safe. Bayan sun kammala ɗiban ruwan suka dawo tare da Hamida gidan. Abin karin ma kaɗan ta saka musu,ta ɗauki alwashin sai ta gasa musu aya a hannu,tun da har suka iya faɗa wa wannan matar abin da take musu.

Haka su Jalil suka ci gaba da azabtuwa a hannun Sahura,duk wani aikin gida su ne, aike su ne harta da rainon Maryam ya dawo hannunsu. Lokaci guda suka rame sakamakon rashin wadataccen abinci da wurin kwanciya. Ƙurajen sanyi sun fesoma ma Hamida a duk ilahirin jikinta masu ɗan karen ƙaiƙayi,idan ta fara susa kamar za ta zauce. Tana kuka tana susa,Yasir da Jalil suna tayata gwanin ban tausayi. Su Aunty Saudah idan tana susar har kiran ƙawayensu suke su zo su gani. Zuwa yanzu 'ya'yan ya ku bayi yaran barikin suke kiransu. Musamman abokan Hamid da Aunty Saudah. Dauda Imamu yana matuƙar damuwa da halin da yaransa suke ciki amma bai da bakin magana. Musamman yadda ƙurajen Hamida suka koma suna fitar da ruwa. Hakan bai damu Sahura ba,zuwa yanzu wani irin tari Hamida tare saboda duk a cikinsu tafi illatuwa,idan tana tari kamar lumfashinta zai ɗauke. Amma ko a kwalar rigan Sahura,yaranta ko ciwon kai suke za ta kai su asibti a duba su. Kullum cikin tsangwama da kyararsu take,ba su zama a falon idan tana nan da yaranta,abinci sai yaranta sun ci sun rage take ba su. Kullum da rana tana aika Yasir kai ma oga Sabo abinci,wani lokacin Jalil.Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har lokacin dawowa makarantar boko da islamiyya ya yi. Daman su Yasir sun jima da sallamawa hadda. Ita da kanta ta ɗinko musu kayan makarantar boko da islamiyya. Yasir a Jss2 dinsa aka saka shi bayan sun yi mishi gwaji ya ci,Jalil a primary five,sai Hamida a primary two ajinsu Amina...✍️

^^^^^^^^^^^^^^^

Tudun Wada premier road Gusau jihar Zamfara Nijeriya

A ɓangaren Mairi haka ta rarrafa har aka cinye hutun tana tunanin yaranta, HAFIZA kullum bata da magana sai ina yayyenta suke, musamman idan ta kai ta hadda,sai ta turbuƙe ta ce ita da yayyenta za ta hadda,da ƙyar take lallashin ta yadda ta kaita makaranta,wani lokacin har hawaye Mairi take tana tausayin HAFIZA da ita kanta. Zuwa yanzu HAFIZA na da izu uku a hadda,Mairi ta mayar da hankalinta sosai a kan HAFIZA. Da yake HAFIZA tana da son karatu sai Mairi bata sha wahala a kanta ba. Har sabon uniform da ɗinka ba. Duk wainar da ake toyawa Sadiƙu bai sani ba, kasancewar yanzu da kanta take zuwa amsar cefanan,daga bisani ya ci gaba da aiko mata kasancewar akwai yaro a shagon. Bata sanar masa dalilin rashin zuwansu Yasir ba haka shi ma bai tambaya ba. Ana gobe za ta zo Kaduna ta je Mada wurin Jamila,sun tattaunawa sosai nan Jamila ta bata wasu shawarwari a kan yadda za ta amso su Jalil. Sai kusan yamma ta dawo Gusau ta bar HAFIZA wurin Jamila saboda kar wurin dawowa yaran su yi mata yawa. Tana dawowa ta fara shirin tafiya duk da a goben take fatan dawowa. Washegari da safe ta yi wanka ta shirya,jakar kuɗinta ta dauka sannan ta zuri mayafi ta kulle gidan. Kai tsaye ta hau mashin a unguwsr ya kaita tasha daga can ta hau mota. Ta yi amfani da labarin da Dauda Imamu yake bata a kan yadda yake hawan mota daga Gusau zuwa Kaduna,da kuma yadda yake zuwa daga tasha zuwa barikin har yanayin gidan da suke ciki ya kwatanta mata sunan da ake kiransa. Sun jima suna tafiya a hanya. Motar da ta hau tana a matsala,tafiya kaɗan sai a tsaya a ɗauki lokaci wurin gyara sannan su ci gaba da lafiya. Sai kusan 5:40pm na yamma motarsu ta shiga garejin Kawo,da ta yi tambaya wani ya rakata inda ta bus ta sauka da Airforce base. A bakin gate din aka mata wasu tambayoyi sannan suka barta ta shiga. Daga nan ta samu lift bayan ta sanar masa inda za ta je ta hau gado. Cikin sa'a ya ajiyeta a daidai gidan Dauda Imamu. Ta yi masa godiya sannan ya ci gaba da tafiya. Ta kusa isa kofar flat din Sahura ta buɗe. Lokaci guda idanunsu ya sarƙafe...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***