BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

Chapter 25

by @narrnarhhbukar00

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

025

''Kin kai karshe ko da sauran magana!'' Momy ta faɗa fuskarta a matuƙar ɗaure kamar bata san wata aba dariya ba.

''Hajiya na kai ƙarshe! Sannan saboda in kareku daga sharrin Jalil ne ya sa na yi tattaki tun daga unguwarmu na zo wurinki. Daga nono ya tsotsa sata don mahaifiyar...''

A hasale Momy ta daka mata tsawa tare da faɗin

''Tashi ki bar mini gida makira!"

''Maman Muhsin! kar ki yi saurin yanke hukunci ta hanyar korana,soyayyar gaskiya nake muku,bana son Jalil ya cutar da ku ne. Na fi kowa sanin halinsa da shegiyar uwarsa da ya gado'' Cewar Sahura tana miƙewa a lokaci guda. Miƙewa ita ma momy ta yi tana mata kallon ƙasa da sama,domin mijinta ya sanar mata komai a kanta,sannan ta ji izayar da take ma Jalil da 'yan'uwansa daga bakinsa.

''Look Madam! Kindly leave my room! An faɗa miki ban san komai a kanki ba ne! Ban da lokacin ɓatawa da irinki wacce ta gama kwashe albarkarta a gaban ma'aiki,kina azabtar da yara saboda son zuciyarki da rashin imani. Ke ga annamimiya kin zo da ƙarairayinki saboda kin ɗauki kowa irinki! Tun wuri ki kama gabanki idan ba so kike na haɗaki da sojoji ba. Sannan Jalil yanzu ya fara zama a gidan nan,ko abin da ya fi sata yake yi mu a shirye muke mu zauna da shi duk kalar halinsa,balle ma ƙarya kike, saboda ɗanki ya dawo nan kike faɗi haka. Ni Karima! zan maye gurbin mahaifiyarsa kamar yadda abban Muhsin zai cike gurbin mahaifinsa. Sannan ki sani sauran 'yan'uwansa ma muna nan zuwa kansu,don ba za mu bar miki su ki ci gaba cutar da su ba. Mijin da kika shanye ki ƙarata can da shi! Amma ki sani asiri da mallaka ba su taɓa dawamma. Komin daran daɗewa zai warware kuma ke da yaranki ne a ƙasa in shaa Allah. Sannan idan na sake ganin ƙafarki a gidana sai na saka an kulleki a guard room na kwana biyu. Get out of my house! Stupid woman!" Ta furta a tsawace tana nuna mata hanyar waje. Sahura ta tsorata sosai da kalaman Momy,babu abin da ya fi ɗaga mata hankali irin na kullewan da ta ce za a mata,cike da rawar jiki ta yi hanyar waje,har ta kai ƙofa sai ta dawo da sauri ta sunkuci plate ɗin kayan maƙulashen ta yi waje da gudu.

''Mayya! Sai dai ki mutu! Daman kwaɗayi ya kawoki. Useless human. Mtsssssss!" Ta ja tsaki sannan ta je ta rufe ƙofar ta koma kicin.

Sahura na fita ta ajiye plate ɗin a ƙasa ta goya Maryam sannan ta saka plate ɗin cikin hijabi ta ci gaba da tafiya,a cewarta tun da abin da ta je nema bata samu ba gwara ta ɗauki kayan maƙulashen yaranta su dangwali arziƙi. Ranta a matuƙar jagule ta koma flat ɗinsu...✍️

^^^^^^^^^^^^^^^

Hayin Bijini Mada jihar Zamfara Nijeriya

Jamila alla-alla take yamma ta yi su tafi gidan Kawu Rabi'u, yadda ta tayar da hankalinta ya wuce gaban kwatance,ba komai ya hautsina tunaninta ba illa wahalar da su Yasir suke sha hannun Sahura. Ji take kamar ta runtse ido ta buɗe ta ganta a gaban Sahura. Wata zazzafar ƙiyayyarta ta sake tabbatuwa a cikin zuciyarta. Da yake Maman Ruƙayya ke da girki,sai hakan ya faranta ranta. Bayan sallar Asr suka nufi gidan Kawu Rabi'u. A ƙafa suka taka har unguwar. A cikin zauren gidansa suka sameshi tare da babban ɗansa. Cike da girmamawa suka gaishe shi.

''Amaryata wannan kyau haka! Duk ni kaɗai aka ma kwalliyar. To zo na ga kwalliyar da kyau'' Kawu Rabi'u ya yi maganar yana duban HAFIZA da ke murmushi tana sunkuyar da kanta. A hankali ta tako zuwan inda yake idanunta a ƙasa,ita wai ta ji kunya. Murmushi su Jamila suka yi sai zauran ya ɗauki shiru daga bisani Mairi ta katse shirun da cews

''Kawu daman wata 'yar matsala ce ta sake tasowa tsakanina da mijina,shi ne na ce bari na zo na sanar maka ko za a ma tufkar hanci''

''Matsala! Subhanallah! Me ke faruwa ni da na sanki da haƙuri,ko dai maganar yaran ne?"

Natsuwa ta yi sosai sannan ta fara ba shi labari tiryan-tiryan abin da ya faru,tun daga farko har zuwa yau. Bata ɓoye komai ba,asirin da Sahura ta yi mata wanda lokacin baya bata sanar masa ba ta faɗa masa tare da dramar da suka kwashe a Bariki. Sosai hankalinsa ya tashi,sai ambaton ''Subhanallah'' yake tana ba shi labarin har ta kai ƙarshe. Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce

''Ikon Allah! Yanzu Maryam kina nufin kishiyarki ce ta hana Dauda ya baki yaranki?"

''Eh Kawu. Duk abin da ta ce shi yake yi"

''Amma lamarin bai yi daɗi ba. A gaskiya ba za a bar mata yara ta ci gaba da azabtar da su kamar marasa gata ba. Gaskiya sai an haɗa da roƙon Allah. Domin ƙarara asiri ne ke jan linzamin Dauda. Babu yadda za a yi a ce kina a matsayin matarshi ki je har inda yake,ya muzantaki ya kuma hanaki yaranki. Wannan ai hauka ne, Ubangiji zai yi maganinta.''

''In shaa Allah. Ai Ubangiji ba ya bacci. Za ta kwashi kashinta a hannu da yardar Allah '' cewar babban ɗansa. Mairi da Jamila bakinsu bai bar furta ''Ameen'' ba cike da yaƙinin Allah shi ke komai.

''Zuwa jibi zan tura Mamman barikin, na so na je da kaina,amma akwai tafiyar gaggawa da zan yi gobe tare da wasu daga cikin malamai zuwa Kano. Za mu yi sati ɗaya a can. Don haka za ki kwatanta ma Mamman gidan a barikin ya je ya ji''

''Mu gode sosai Kawu. Allah ya ƙara girma da imani" cewar Mairi tana jin wani sanyi a ranta.

''Ki ci gaba da haƙuri Maryam, duk da na san idan haƙuri halitta ne to tabbas kin cancanci a kiraki da mai haƙuri. In shaa Allah za ki ga ci gaba a rayuwarki da ta yaranki. Allah ya yi muku albarka''

''Ameen Kawu'' cewar Jamila ita ma hankalinta ya ɗan kwanta. Naira hamsin Kawu Rabi'u ya ciro ya miƙa mata amma ta ƙi amsa. Ya yi juyin duniya ta amsa sai dai ta ce ''Kaka ka bar kuɗin ka ci goro'' Sai da Jamila ta saka baki sannan ta amsa cike da ladabi tana faɗin

''Na gode! Allah ya ƙaro buɗi''

''Ameen Amaryata'' cewar Kawu Rabi'u. Sosai ya ji ta burgeshi da kuma mamakin hankalinta da natsuwarta ba kamar sauran jikokinsa ba,waɗanda kai tsaye suke roƙonsa kuɗi. Ya san natsuwar HAFIZA ta samo asali ne daga mahaifiyarta,domin tun tana ƙarama take da natsuwa. Cikin gidan suka ƙarasa tare da gaida 'yan gidan daga bisani suka yi sallama da Kawu bayan Mairi ta yi ma Mamman kwatancen flat ɗin Dauda Imamu da sunan da ake kiransa a barikin. Daga nan suka koma gida, Mairi ta bar komawa Gusau sai bayan Mamman ya dawo...✍️

^^^^^^^^^^^^^^

Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya

A ɓangaren Jalil bayan fitarsu daga barikin kai tsaye Officer Kabir ya wuce da su central market inda ake masa ɗinki, sai da ya fara zuwa shagon yaduddukan maza da shaddodi,ya saye kalolin yadudduka har shida da shadda biyu tare da uniform ɗin islamiyya da na boko,sai ya kuma sayen yadi kala biyu wanda za a ɗinka ma Jalil da Muhsin tare,daga bisani ya wuce plazar. Shago ne da mayan mutane masu kuɗi da 'yan ƙwalisa suke kawo ɗinkunansu da na yaransu. Babban shago ne da ke ɗauke da kekunan ɗinki kusan guda shida,na wuta da taka-taka. Su biyu aka gwada daga nan ya ɗaukesu zuwa shagon ƙananun kaya. Kala ɗaiɗai har kala biyar ya siya sannan suka dawo gida. Cike da farinciki Momy ta tarbesu. Raihana na saman cinyar Officer Kabir Momy tana ba shi labarin zuwan Sahura da yadda suka kwashe. 'yar dariya ya yi sannan ya ce

''Ta yi ɓatan hanya,don bukatarta ba ta karɓu ba. Ina tunanin yadda zan yi rescue ɗin 'yan'uwan Jalil, i know they're suffering too. Amma wannan matar ba za ta gama da duniya lafiya ba''

''Never wallahi kuwa! Abbansu Muhsin baƙinciki da hassada ne ke damunta,ka san wani rainin hankali kuwa? ''

Girgiza mata kai ya yi,sai ta ce

''Saboda ta mayar da kowa irinta,wai Jalil yana da ciwon sata kuma wai gado ya yi daga wurin mahaifiyarsa. Just imagine this rubbish! Wai ita kuma soyayyar gaskiya take mana,mene ne da mene ne har da cewa idan rikon muke so,sai ta kawo yaronta, Jalil sya koma can saboda riƙon mahaukaci sai sarki,sarkin ba ma sai da guntuwar dorina''

Take Officer Kabir ya kwashe da dariya,momy da yaran suka tana shi,sosai yake dariya har da ƙwalla, cikin dariyar ya ce

''Hhhh an ya matar nan bata samu taɓin hankali ba kuwa! hhhh wai riƙon mahaukaci sai sarki. She mean Jalil ne mahaukacin ita ce sarkin'' a nan ma ya sake kwashewa da dariya. Murmushi a fuskar momy ta ce

''As you hear,wallahi tun da ta tafi nake analysing maganarta, the most funny part of her,bayan na ce ta fitar mini daga ɗaki,har fa ta kai ƙofa,sai kuma ta dawo da sauri ta ɗauki plate ɗin da na zubo mata snacks a ciki ta ruga da gudu waje. That woman's brain needs deep check up wallahi''

''Exactly. I think zuwa gobe sai na kawo mahaifin Jalil nan ya ga wuri, tun da yau za mu je shan ice cream''

''Allah ya kai mu goben lafiya''

''Ameen ya Rahman.''

Cike da annashuwa momy da officer Kabir suke hira ,yayin da Raihana da su Jalil suna hirar makaranta. Officer Kabir ɗan asalin jihar Kaduna ne a ƙaramar hukumar Giwa,mahaifinsa soja ne amma ya rasu a yaƙin Biafra a shekarar 1967. Officer Kabir ya taso da son zama babban soja kamar mahaifinsa duk da mahaifiyarsa bata so duba da ta hanya soja mahaifinsa ya rasu,amma haka ya kafe a kan burinsa har Ubangiji ya tallafa masa,ya samu makarantar sojoji ta NDA a ɓangaren sojan sama,ya fito a matsayin officer, yanzu haka ana shirye-shiryen kara musu matsayi. Bayan passing out ɗinsa ne ya haɗu da Karima,mahaifinta tsohon soja ne,ta kammala nursing school sai suka yi aure. Yaransu biyu ne.Muhsin da Raihana daga su momy bata sake wata haihuwa ba...✍️

^^^^^^^^^^

A ɓangarensu Hamida,sosai take kuka saboda azababben ciwon da cikinta ke yi,malamar ajin ta saka aka kira Yasir ta ce ya wuce da ita gida a kaita asibiti don ta bata magani amma ciwon cikin bai lafa ba,ga shi Dauda Imamu bai zo islamiyyar yamma ba. Haka Suka fito daga islamiyyar suna tafiya,Hamida kuka take kamar ranta zai fita Yasir na bata haƙuri,kana ganinsa kasan yana ɗauke da matssanancin damuwa. Sun yi nisa a tafiyar sai Hamida ta zauna a ƙasa tana riƙe cikinta,girgiza kai take saboda yadda yake murɗa mata,can kuma ta fara tari mai ƙarfi da zurfi, Yasir na bubbuga bayanta cike da tashin hankali yana mata sannu. A gefe guda Madam Ngozi ta fito daga haɗaɗɗiyar motarta ta jingina tana jiran a kawo mata saƙo. Ilahirin Wurin ta bi da kallo,sanyi yamma na ratsata,ta juya gefan dama kenan idanunta suka yi tozali da Hamida a kwance kamar matacciya Yasir na jijjigata yana kuka,take ta ƙwalla ƙara tana ambaton ''Jesus Christ!" Da gudu ta nufo inda suke. Kuka Yasir yake yana jijjiga Hamida,sunanta yake kira yana faɗin  ''Hamida! Ki tashi zan nemo miki abincin! Ki tashi Hamida! Ammu na sonki! Kar ki tafi ki bar...'' bai kai ƙarshen maganar ba ya ga an sunkuci Hamida,ɗagowan da zai yi ya haɗa ido da ƙaƙƙarfar mace mai ƙirar maza. Kafin ya yi magana Madam Ngozi ta ce

''Follow me. Ba mu da lokacin ɓatawa'' ta yi gaba a rikice. Da sauri Yasir ya bi bayanta da gudu. Kai tsaye ta buɗe murfin baya ta saka Hamida,Yasir ya zauna kusa da ita yana riƙo hannunta da kiran sunanta a ɗimauce. Da sauri Madam Ngozi ta dawo mazaunin driver tare da kunna motar ta figeta ta gudu. Kai tsaye ta wuce da ita asibiti,bayan ta yi parking ta ɗaukota gudu-gudu sauri-sauri Yasir na biye da ita suka shiga asibitin. Da gudu nurses suka zo karɓarta amma taƙi ba su.

''Call doctor! The condition is critical!"  Ta furta a tsawace.

Wata daga cikin nurses ɗin ta amsa tare da juyawa kiran likita,da yake yawancin 'yan asibitin sun san Madam Ngozi da matsayinta da na mijinta a barikin ma bakiɗaya. Tare da ita aka shiga da Hamida emergency room. Da ƙyar nurses suka bata haƙuri a kan ta zauna a reception,jikinta sai kakkarwa yake har likita ya shiga emergency room bata motsa daga wurin ba. Ba za ta manta lokacin da ta rasa babbar yarinyarta ba,wacce bata fi Hamida ba,a gabanta ta rasu,tun daga lokacin take tsoron mutuwa musamman ta yara. Babu zato kuka ya suɓuce mata,da sauri ta rufe bakinta tare da ciro hanky daga aljihun wandonta ta goge hawayen. Hannun Yasir ta kama suka nufi reception, duk sojan da suka haɗu sai ya sara mata tare da ƙamewa sannan sai wuce,sun zo daidai ƙofar shiga ciki suka yi kaciɓis da maman Jawaheer ta zo gaida wata yarinyar maƙociyarta da aka kwantar a children ward. Mamaki sosai ya lulluɓe maman Jawaheer.

''Yasir me ya kawoka asibiti?"

''Sister na shi ne ta suma"  Madam Ngozi ta bata amsa da yake tana jin hausa.

Waro ido Maman Jawaheer ta yi waje, kafin ta sake magana Madam Ngozi ta jafo mata tambayar ya yake azalzar zuciyarta

''Where is their parent? How can i contact them?"

''Actually these kids are with thier stepmom in this barrack. She is threatening them badly. It was yesterday thier mom came to take them back,but the stepmom warn the husband not to give the kids. It's seems like she charm the husband. The way she is commanding him looks abnormal.'' cewar Maman Jawaheer.

Sake baki Madam Ngozi ta yi tana kallon maman Jawaheer har ta kai ƙarshe. Tasan me ake kira da kishiyar uwa musamman muguwa,domin bata manta uƙubar da ta sha hannun stepmom ɗinta ba,da yake tun tana ƙarama mahaifiyarta ta rasu,mahaifinta ya sake aure,ya auro musu jalli joga,babu kalar azabar da bata sha ita da ƙaninta a hannunta ba,har daga ƙarshe suka gudu zuwa dangin mamansu. Zama suka yi a kujerun da aka tanadar a reception ɗin. Duban maman Jawaheer Madam Ngozi ta yi sannan ta ce

''Ennnn! So that's how the stepmom is!. Thunder go fire her!. I will surely teacher her lesson no matter who her husband is in this barrack. No wonder this little child looks unhealthy. Shegiya!'' ta yi maganar tana kallon Yasir cike da tausayi.

''Hhmmmm! The woman is too wicked. Let me  greet my neighbor before the doctor is out'' maman Jawaheer ta yi maganar tana nufar children ward. Tambayar Yasir Madam Ngozi ta yi ko yana jin yunwa,da sauri ya jinjina mata kai. Wata nanny a asibitin ta aika ta siyo mishi abinci. Sun ɗan jima a zaune,nurses ba su zo kiransu ba, hankalin Madam Ngozi ya sake tashi jin shirunsu ya yi yawa. Zuwan nanny ya yi daidai da zuwan maman Jawaheer. Jiki na rawa Yasir ya fara cin abincin gwanin ban tausayi. Duk yawan abincin tsaf ya cinye ya sha ruwa. Tausayin Yasir ya gama mamaye zuciyar Madam Ngozi, a ranta tana alwashin maganin kishiyar uwarsa. Ko mintuna biyar Yasir bai yi da kammala cin abincin ba wata nurse ta zo kiran Madam Ngozi. Tare da Maman Jawaheer suke je ofishin likitan. Mazaunin marasa lafiya suka zauna,Yasir ya tsaya a gefen Madam Ngozi. Rubuce-rubuce likitan ya yi a file ɗin Hamida sannan ya ɗago ya dubesu fuskarsa kamar ya sha kunun kanwa.

''Ke ce uwar yarinyar? '' ya yi tambayar yana duban maman Jawaheer. Da sauri ta girgiza kai tana faɗin

''Ba ni ba ce mahaifiyarta,sai dai za ka iya sanar mana duk ɗaya ne''

''Exactly Sir. Just tell us what's wrong with the baby,so that i can know how deal with the stepmom'' cewar Madam Ngozi. Cike da rashin fahimta likitan ya ce

'''Madam i didn't get you. What are you trying to say?"

Kafin Madam Ngozi ta ba shi amsa maman Jawaheer ta ce

''Likita yaran suna hannun kishiyar uwarsu ne, kuma tana azabtar da su,shi ya sa muka ce ka sanar mana me ke damunta,daga nan sai mu san matakin da za mu ɗauka a kan kishiyar''

''Ok.'' ya faɗa

''Dr just speak in hausa I'm hearing too" cewar Madam Ngozi tana murmushi.

Ɗan murmusawa Likitan ya yi sannan ya ce

''A gaskiya yarinyar tana cikin haɗari mai girma,domin tun fara aikina na likitanci kuma ɓangaren yara ban taɓa cin karo da irin case ɗinta ba''

Take jikin Madam Ngozi da maman Jawaheer ya yi sanyi. Bayan likitan ya ɗan numfasa sannan ya ɗora da cewa...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***