Chapter 27
The Amazing Pen ✍️.......
BAHAGON TUNANI
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
027
Da sauri Sahura ta zube a ƙasa jikinta na rawa ta riƙe ƙafar Madam Ngozi. Nan take ta fashe da matsanancin kuka mai nuni da tsantsar firgici da tsoro ta ce
''Madam! Sorry Madam! Wallahi tallahi me no sake dukan yaran miji! Wallahi me kullum zan ba su food well well! Madam sorry me no sakewa!" Duk ta rikice ta fita hayyacinta a ɗan ƙanƙanin lokaci. Hankaɗeta da ƙarfi Madam Ngozi ta yi har tana bigewa da centre table. Take ta saki wata razananniyar ƙara tana riƙe goshinta,ihunta ya saka Maryam farkawa da kuka.
''Bata nono!" Madam Ngozi ta umurta tana zare mata idanu. Duk da azababben ciwon da kanta ya fara yi saboda bigewan da ta yi haka ta ɗauki Maryam ta fara shayar da ita,wani irin tsoron Madam Ngozi ya mamaye gangar jiki da ruhinta. Tabbas ba mutum bace. A bazata ta ji muryarta
''Ina miijinki?"
''Madam bai dawo gida ba" ta bata amsa a matuƙar sanyaye kamar ba ita ta gama ɗaga murya ɗazun ba.
''Wannan ne tambayar da na miki! Ina mijinki!" Ta faɗa da tsawace. A ruɗe Sahura ta ce
''Madam church! Mosque Madam!"
Banbaraƙwai Madam Ngozi ta ji maganar. Ƙara tamke fuska ta yi ta ce
''O'oooooh! Mijinki na zuwa church kenan?"
Sai a sannan Sahura ta ankara da katoɓarar da ta yi. Da sauri ta ce
''Sorry Madam. Yana masallaci! Jumma'a masallaci mosque"
Juyowa Madam Ngozi ta yi kansu Juliana ta ce
''Two of you should kindly go and call him now''
''Yes Ma!" Suka furta a tare suna sara mata da ƙamewa. Duban Yasir ta yi sannan ta sassauta muryarta ta ce
''Yasir ka kai su wurin Dad ɗinka a Mosque ku dawo yanzun nan"
Jinjina mata kai ya yi sannan suka tafi tare. Bayan fitarsu Madam Ngozi ta dubi Sahura da gumi ya gama wanke jikinta ta ce
''Ban taɓa ganin muguwar mata irinki ba! More than ciwo biyu a jikin yarinya ƙarama kuma duk ke ce source of it! Ki ci abinci da yaranki ki hanasu! Ki dinga ma yarinya ƙarama wanka da ruwan sanyi. Kasheta kike so ki yi? You wan kill herrrr?"
Da sauri ta girgiza kai tana share hawayen da suka kasa daina zuba tamkar idaniyar ruwa. A tsawace Madam Ngozi ta ce
''Baki da baki ne! Kina nodding!"
''A'a ina da shi Ranki shi daɗe kamar bishiyar dabino. Kin gani" ta yi maganar tana wage mata baki a ruɗe kamar ƙaramar yarinyar ta aka ce mata Haaa!. Sosai tsoranta ya yi nasarar dabaibaye lungu da saƙon zuciyarta,ga kwarjininta da ya cika idanunta. Tun da take,za ta iya cewa bata taɓa ganin mace mai girma kamar Madam Ngozi ba,ga tsawo,ga ƙiba,ga manyan idanunta masu ban tsoro da suka cikata. Kai za ta iya cewa ko namiji albarka, don girmanta ya wuce gaban kwatance. Sahura ta sha faɗa,don tsaf Madam Ngozi ta zageta ta kuma mata mumanan kashedi a kan su Yasir har su Juliana suka dawo. Da sallama Dauda Imamu ya shigo falon zuciyarsa a jagule da taraddudin me ke faruwa a gidan da har sojoji suka zo kiransa,don bai samu damar tambayar Yasir ba saboda sojojin. A sanyaye ya ƙaraso cikin falon. Sahura na ganinsa ta yi saurin ajiye Maryam tana matsowa kusa da shi, sake fashewa ta yi kuka ta ce
''Baban Hamid ka taimake ni. Haka kurum ban santa ba ta shigo ɗakina ba tare da na bata izini ba ta mareni, tana mini ƙazafin ina muzguna ma su Yasir! Kai shaida ne Baban Hamid nafi ƙaunar su Yasir sama da 'ya'yan cikina kuma...''
''Shut that your dirty mouth! Maƙaryaciya!" Madam Ngozi ta faɗa a hasale,da sauri Sahura ta rufe bakinta da hannu tana haɗiye sauran maganar. A fusace Madam Ngozi ta juyo wurin Dauda Imamu ta ce
''Kai ne mijin Sahura!''
''Eh'' ya furta a hankali domin jikinta ya gama mutuwa. I.D card Madam Ngozi ta ciro a aljihunta ta nuna masa tare da faɗin
''Sunana Ngozi Obi. Ni Wing commander ce. An ba ni umarnin tafiya da matarka saboda samunta da child abuse''
Tamkar an soki zuciyarshi da mashi,haka kalaman Madam Ngozi suka daki ƙofofin kunnuwansa har suka antaya ma'adanar sirrinsa. Lallai akwai cakwakiya a gabansa,yaransa ne take muzguna maa amma ai ita matarsa ce kuma uwar 'ya'yansa. Idan ya bari aka tafi da ita gaurd room mutuncinsa zai zube a barikin. Duban Madam Ngozi ya yi
''Madam sorry! Babu abin da take ma yaran! Ƙarya ake mata! Tana shayarwa sannan tana da yara har biyar. Madam idan kuka tafi da ita wa zai kula da yaran da jaririyar"
''Yawwa Baban Hamid faɗa mata gaskiya,sharri ake mini. Ina kula da yaran kishiyata tsakani da Allah'' ta faɗa tana jin sanyi a ranta,ko ba komai za ta kuɓuta.
Wani irin mugun kallo Madam Ngozi ta wurga ma Dauda Imamu da Sahuran a tare tana sakin tsaki.
''Kai Malam! Ko me zaka faɗa sai na tafi da ita ta yi wuni guda a can. Har kana da bakin faɗar babu abin da take ma yaran! Ni witness ce domin da hannuna na ɗauki small girl ɗin zuwa asibiti. Kar ka kawo wani stupid excuses saboda ba zan ɗauka ba. Commanding officer ya ba ni dama,and dole sai ta je gaurd room na wuni ɗaya. Saboda breast feeding ne ya sa punishment ɗinta ya ragu. Ba shawararka muke nema ba. She must serve punishment for her stupid act on innocent child. Juliana come with her to the guard room''
Tana gama faɗin haka ta kama hannun Yasir suka fita,ta yarda da maganar maman Jawaheer da ta ce asiri ta masa,ta ya matarka tana muzguna ma yara cikinka kake kareta,alhalin har 'yarka aka kwantar a gadon asibiti silar muguntarta. Da sauri Dauda Imamu ya biyo bayanta har waje yana roƙon ta,sai dai tamkar da dutse yake. Bata saurareshi ba sai ma ƙara sauri take saboda yau take son zuwa Abuja amma sai ta biya asibiti ta ga jikin Hamida tukunna. Rantsatstsiyar motarta ta hau suka bar wurin. A kan idanunsa aka saka Sahura a mota Maryam na goye . Da yake ba da Khaki suka zo gidan ba,shi ya sa babu wanda ya yi tunanin an zo kamata ne. Ita kanta Sahura da aka fito da ita bata yi iface-iface ba saboda bata son mutuncinta ya zube a barikin,yadda ake gaisheta maza da matan sojoji da kunya su ga an kamata. Janyo hijabin ta yi ya rufe fuskarta har ta shiga motan. Zuciyarta fal tsoro da firgici. Tana jin labarin gaurd room a bakunan mutane yau wai ita ce za ta shigeshi silar yaran kishiya,amma kuwa kishiya bata mata rana ba. Shaye hawayenta ta yi tana gyara zamanta a cikin motar. Duk wanda ya ga Sahura a lokacin zai tabbatar da a tsorace take,idanunta sun yi ja sun kumbura,abinka da farar mace fuskarta ta koma kamar ƙosai saboda jan da ta yi.
Ko minti biyar bai cika da wucewarsu Sahura motar mahaifin Muhsin ta tsaya a kusa da Dauda Imamu. Kafin Officer Kabir ya gama fitowa daga motar Dauda Imamu ya yi saurin zuwa inda yake a ruɗe.
''Officer ka taimake ni! An tafi kulle matata!"
''Matarka Imam! Subhanallahi! Garin ya ya! Yaushe aka kulleta?"
''Yanzu suka wuce da ita guard room,saboda muguntar da take ma yaran uwar gidana, duk da yarana ne amma ita ɗin matata ce kuma uwar yarana har biyar,ga shi tana shayarwa. Wallahi ina tsoron mutuncina kar ya zube a idon mutanen barikin nan.''
A fili officer Kabir ya tausaya wa Dauda Imamu amma a baɗini farinciki ne fal ransa,gwamma da aka tafi da ita,ko ba komai za ta koyi darasi. Nan gaba ba za ta yi gigin kallon banza ga yaran ba balle kuma ta yi musu mugunta. Ɗan gyara tsayuwa ya yi yana duban Dauda Imamu da ya gama rikicewa ya ce
''Kwantar da hankalinka Imam,babu abin da za su ma matarka balle ma tana shayarwa. A dokar soja ba a wulaƙanta mace balle mai goyo. Kawai dai za su ja mata kunne ne a kan yaran saboda ta kiyaye nan gaba. ''
''Amma Officer Kabir yanzu har sai yamma za su sako mini mata ga yara har huɗu a gida. Da wanne zan ji,da yaran ko da masallacin da islamiyyar. Ga shi Hamida na asibiti an kwantar da ita jiya''
''Subhanallah ƙanwar Jalil ce? Me ke damunta''
''Hmmm, in ji mai ciwon haƙori. Kawai dai a yi sha'ani. Wai an ce saboda matata ce aka kwantar da Hamida asibiti, amma ni yanzu babban damuwa shi ne ka taimakeni matata ta fito don girman Allah '' ya yi maganar yana roƙonsa da hannu biyu. Ajiyar zuciya officer Kabir ya sauke,a gaskiya ba ya tunanin zai iya taimaka masa don fito da muguwar matarsa. Bai ƙi ta shekara a can ba. Gwara ɗiyar zai iya yin ruwa ya yi tsaki a kan ta samu lafiya ban da shaiɗaniyar matarsa. Ɗan dubansa ya yi sannan ya ce
''Yanzu hau muje na ga jikin yarinyar idan ya so daga baya sai muje can gaurd room ɗin. Allah ya sa su yarda. Daman na zo n kai ka gidana ne ga ka iyalina''
''To to mu je Officer'' ya faɗa yana yin gaba kamar shi zai tuƙa motar tsabar yadda yake a rikice. Murmushi officer Kabir ya yi yana girgiza kai sannan ya biyo bayansa. Kai tsaye ya wuce asibiti. Children ward suka nufa ɗakin da aka kwantatr da Hamida. Sun tarar da Madam Ngozi a ciki. Officer Kabir na haɗa ido da ita ya yi saurin ƙamewa tare da sara mata. Ogarsa ce a wurin aiki,mijinta ma uban gidansa ne kuma yana kyautata masa sosai. Da ɗan murmushi a fuskarta ta ce
''Kabir how family? So you know this man and his family?"
Jinjina mata kai ya yi yana faɗa mata inda ya san su ,har silar dawowan Jalil hannunta. Ganin Madam Ngozi a wurin sai Dauda Imamu ya shiga roƙonta kamar zai yi kuka. Ko kallon inda yake bata yi ba balle ta tausaya masa,ita haushi ma yake bata,yadda ya bi ya rikice a kan shaiɗaniyar matarsa. Maman Jawaheer na zaune tana kallon ikon Allah,bata san an tafi da Sahura gaurd room ba sai yanzu da Dauda Imamu yake faɗa,domin Madam Ngozi bata sanar mata ba. Ta dai tambayi ya jikin Hamidan sannan ta tambayi matsayin mijinta a wurin aiki,don tana son saka sunanshi a cikin waɗanda za a ƙarama matsayi nan da wata biyu masu zuwa. Sannan Madam Ngozi ta tambayi ko za ta dinga saka ido a kan su Yasir tunda mahaifiyarsu bata nan kuma ta ga yadda kishiyar uwarsu take cutar da su,sai kuwa ta yi sara a kan gaɓa domin ɗari bisa ɗari maman Jawaheer ta yarda sannan ta sanar mata ai ta yi ma mahaifiyarsu alƙawarin kula da su,kuma ta san mijinta zai yarda shi ma domin yana da tausayi sosai,saboda haka za ta ɗaukesu kamar yaranta. Sosai Madam Ngozi ta yi farinciki da kuma alƙawarin taimaka mata da duk abin da take buƙata. Har ga Allah Yasir da Hamid sun shiga ran madam Ngozi sosai ta yadda misaltawa ɓata lokaci ne.
Officer Kabir ya saka baki a kan a ɗan sassauta mata hukunci, madadin a kulleta har yamma,a rage zuwa ƙarfe uku na rana haka,sai duk kashedin da ya dace a mata a kan yaran sai a mata. Madam Ngozi ta yi na'am da shawararsa sai dai Dauda Imamu bai so hakan ba,kawai a fito da matarsa ba wai a rage hukuncin ba. Rai bai so ba haka ya haƙura domin da babu gwara babu daɗi. A nan Madam Ngozi ta natsu ta sanar ma Dauda Imamu maganarsu su Yasir da kuma amincewarsa a kan zuwan maman Jawaheer gidansa ko kuma yaran su dinga zuwa gidanta a duk lokacin da hakan ta taso don kula da su. Da farko ya so ƙin amincewa tsoron Sahura kar ta kawo cikas,sai dai Madam Ngozi ta fahimtar da shi amfanin hakan tunda mahaifiyarsu bata nan. Officer Kabir ma ya saka baki don shawarar Madam Ngozi tana kan layi,shi ya sake fahimtar da shi daga baya Dauda Imamu ya aminta da hakan. Sun ɗan jima suna tattaunawa har Hamida ta farka maman Jawaheer ta bata abinci sannan suka miƙe. Maman Jawaheer ta dubi Dauda Imamu ta ce
''Malam idan da hali za ka iya tsayawa da Hamida na je gida girka abinci saboda yau nake saka ran dawowar yarana daga Kano''
Ɗan jimmm! Dauda Imamu ya yi kowa na kallon suna son jin amsarsa. Buɗar bakin Officer Kabir ya ce
''Idan babu damuwa bari naje gidan yanzu na ɗauko matata ta zauna da ita sai ki tafi ''
''Yawwa hakan ya yi officer Kabir ina godiya sosai'' cewar Dauda Imamu. Murmushi Officer Kabir ya yi don ya fahimci hankalin Dauda Imamu kacokar yana ga matarsa. Kuɗi mai yawa madam Ngozi ta ajiye ma maman Jawaheer ta rubuta bayanan mijinta sannan ta yi musu sallama har ta tafi sai ta dawo ta amsa lambar ɗakin maman Jawaheer sai ta wuce. Kai tsaye Officer Kabir ya wuce gida ɗauko momy. Madam Ngozi ta wuce bangaren masu laifi,Dauda Imamu ya so bin ta amma ta ƙi haka ya hakura ya koma masallaci. madam Ngozi na isa ta yi parking sannan ta fito zuwa ciki. A zaune ta samu Sahura ta kafa uban tagumi tamkar wacce aka yi mata mutuwa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta faɗa,fuskarta ta yi fayau kamar mara lafiya. Suna haɗa ido ƙirjin Sahura ya yi mugun mugawa har tana razana kamar ta ga mala'ikan mutuwa. Da sauri Juliana da sauran waɗanda suke tare suka tajo wurinta suka sara mata tare da ƙamewa. A daƙile ta ce su taho da ita, tana faɗin haka ta ƙarasa ciki inda ake rubuta sunan masu laifi a file. Taso ƙeyar Sahura suka yi har ɗakin. Wani daga cikin sojojin wurin ya tambayi ya sunanta. Cikin kuka ta ce
''Sahura Kabiru''
Ya rubuta sunan sannan ya tambayi wasu bayanan,duk ta sanar mata ya rubuta. Juyowa mutumin ya yi wurin Madam Ngozi,cike da girmamawa ya ce
''Ma is your turn''
''Ok'' ta faɗa tana tashi daga kujeran zuwa inda Sahura ke zaune tebiri a tsakiya. Ko kusa Sahura bata yi gigin haɗa ido da Madam Ngozi ba. Kusancinsu ya ƙara sabbaba bugun zuciyarta hauhawa. Bayan madam Ngozi ta zauna ta ce
''ke ɗago ki kalle ni don't waste my precious time i have alot to do''
A hankali Sahura ta ɗago da fuskarta sai dai idanunsa basu kallon Madam Ngozi. Murmushi mugunta Madam Ngozi ta yi sannan ta ce
''Za ki zauna a gaurd room na tsawon awa biyar zuwa shida instead of complete day for the sake of your husband and children. Sannan akwai sharuɗɗa da za mu saka miki a kan yaran,za ki saka hannu because idan kika yi gigin karya sharaɗi ɗaya za ki zauna a gaurd room na tsawon kwana biyu a kuma wurin da yafi ƙazanta za mu ajiyeki''
Babu shiri Sahura ta ware manyan idanunta tare da saukesu a kan Madam Ngozi. Hankalinta idan ya kai duba ya tashi,shikenan burinta na muzguna ma yaran Mairi ya tashi a banza. Suna so su ce bata da iko a kan su Yasir. Buga tebirin Madam Ngozi ta yi da ƙarfi sai amon sautin ya farauto Sahura daga kogin tunanin da ta yi nutso a ciki. Tsawa ta daka ma Sahura tana faɗin
''Are you stupid! Ina magana kin shiga tunani. Sergeant Mathew'' ta kira. Wanda ta kiran sunansa ya amsa yana ƙarasowa wurinta.
''Bring me the oath book''
''Ok Ma'' ya faɗa yana sara mata tare da ƙamewa. Babu jimawa ya zo da ƙaton littafi da biro. Amsa ta yi sannan ya koma mazauninsa. 'yan rubuce-rubuce ta yi sannan ta ɗago ta ce....✍️
Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️
***