BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

Chapter 28

by @narrnarhhbukar00

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

028

Amsa ta yi sannan ya koma mazauninsa. 'yan rubuce-rubuce ta yi sai ta ɗago ta ce

''Sharaɗin farko shi ne: Babu ke babu hana yaran kishiyarki abinci tun da ba yoir Papa ne ya kawo ba!"

Jinjina mata kai Sahura ta yi kamar wata ƙadangaruwa. Hararta Madam Ngozi ta yi tana faɗin

"You don't have mouth ne kina nodding!"

''Ina da shi ranki shi daɗe. In shaa maka Allah su Yasir abinci har sai sun tureshi,ba zan sake wasa da cikinsu ba'' ta yi maganar cike da muryar tabbatarwa.

Tsaki Madam Ngozi ta yi sai ta ce

''Eh! Mayar da ni wawuya like you mana! You think say your sweet mouth ɗinki zai saka ni yarda! So buɗe kunnenki da kyau. Yanzu haka na saka sojoji sun sassaka na'ura a ko'ina a cikin flat ɗinku, idan kika hanasu abinci ko kika dukesu za mu gani a nan''

Babu shiri Sahura ta ware manyan idanunta a fuskar Madam Ngozi,don tamkar ta karanci zuciyarta ne,ta dai faɗa ne amma sam bata tunanin za ta iya ciyar da yaran kishiyarta kamar 'ya'yanta, haka kurum su fi nata ƙiba da kyawun kallo. Ganin yadda Sahura ta ware idanunta a ɗan tsorace ya tabbatar ma Madam Ngozi ƙarya take,kawai ta dai faɗa ne. Ɗan Murmusawa Madam Ngozi ta yi sannan ta ce

''Kina tantama ne ko?"

''A'a ranki shi daɗe wace ni ''

Taɓe baki Madam Ngozi ta yi sai ta ce

''Bari na karanto miki sharuɗɗan complete sai ki amsa lokaci ɗaya don i have alot to do now. Sharaɗi na biyu: ko da wasa kar ki sake amfani da ruwan sanyi wurin yi musu wanka,sannan dole yaran su dinga kwana a wuri mai ɗumi because likita ya ce yarinyar tana da pneumonia don haka ita da brother ɗinta must sleep in a warm place,sannan karki manta idan ma baki cika waɗannan sharuɗɗan ba ko shekara hamsin za a yi as far as kina cikin gidan za mu gani kuma za mu hukuntaki. Sai sharaɗi na gaba: babu ke babu saka su aikin da yafi ƙarfinsu,sannan ban da faɗa balle kuma dukansu,idan muka sameki da ɗaya daga cikin waɗannan za ki fuskanci serious punishment,domin har da duka za mu miki idan ta kama. Sai the last but not the least: buɗe kunnenki da kyau saboda wannan yana daga cikin manyan sharuɗɗan, dole ki yarda momy Jawaheer ta dinga zuwa flat ɗinku a duk lokacin da hakan ya samu don kula ta yaran, because ba za mu bar miki yara kina threatening ɗinsu badly ba. Don haka dole ki yarda momy Jawaheer ta dinga shigo gidanki at her own comvinient time,and yaran su ma za su dinga zuwa gidanta direct babu shamaki. Kin yarda!"

Jar uba! In ji kanawa. Yau ake yinta wai ita Sahurar gwaggwan bugaje ake ginyawa Waɗannan muggan sharuɗɗan da ko a mafarki bata tunanin iya aiwatar da su balle a zahiri. Sharaɗin da ya fi ɗaga mata hankali shi ne zuwan maman Jawaheer gidanta. Matar da ta sakata cikin jerin maƙiyanta a bariki shi ne ake son ta barta zuwa gidanta don kula da yaran kishiyarta. Kutumar dumadu,za ta iya amincewa da duka sharuɗɗan amma ban da na zuwa maman Jawaheer gidanta,domin ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa. Kamar Madam Ngozi ta fahimci tunanin da take yi,a ɗan tsawace ta fara magana ganin bata da niyyar amsa mata.

''Duk abin da kike faɗa a ranki koma mene ne i don't care. Dole ki yarda da sharuɗɗan complete idan ba haka ba. Na rantse da Yesu almasihu sai kin kwana goma a gaurd ɗin nan,ba zan damu da kina breastfeeding ba,ko kuma kina da yara sannan a ɗaki mai duhu da mosquitoes za mu ajiyeki mu amshe yarinyar. Idan kina ganin it's a lie kar ki yarda da sharuɗɗan ki gani ko ba zan yi abin da na ce ba!"

Tun da Madam Ngozi ta fara zayyano danƙara-danƙarar uƙubar da za ta mata idan taƙi amcewa jikinta ya yi mugun sanyi. Ta yarda sojar nan da gaske take za ta aikata abin da ta faɗa. Dole ta sallama idan tana son lulluɓa wa kanta kwanciyar hankali da natsuwar zuci. Gumin da ya tsattsago a dandamalin goshinta ta share,cikin murya mai tsanani sanyi da tsantsar karaya ta ce

''Na amince da duka sharuɗɗan ranki shi daɗe. In shaa maka Allahu ba za ki sameni da karya ɗaya daga cikinsu ba''

Murmushi mai ƙayatarwa Madam Ngozi ta yi sannan ta ce

''Good job! Ai ba just a baki za ki faɗa ba,dole ki saka hannu don tabbatar da abin da kika ce,domin idan kika kuskura kika yi gigin breaking just a single rule za ki sha mamakina,sannan zan dinga zuwa gidanki a bazata and karki manta duk abin da kike yi a gidan muna gani a cikin na'urarmu a nan, idan ma ƙarya ne za mu sani kuma za ki sha mamakinmu. Don haka ga pen ki saka hannu '' ta yi maganar tana miƙa mata biron tare da juyo da littafin zuwa gabanta. Hannunta na rawa ta amsa biron,sai dai ta kasa riƙe biron da kyau balle ta iya saka hannu. Ba islamiyya ta yi ba balle a kai ga boko. Babu abin da ta iya indai a kan harkar karatu ne. Madam Ngozi bata ce komai ba tana kallon ikon Allah,maganganu fal cikinta,kenan Sahura bata yi boko ba.

''Iletarate woman! Riƙe pen ɗin da kyau ki rubuta ko rubbish ne''

Jinjina mata kai Sahura ta yi tana riƙe biron da ƙarfi ta ɗan yi rubutu wanda ita kaɗai ta san shirmen da ta rubuta. (My Esteem fans ko kuna son na faɗa muku abin da Sahura ta rubuta 😂)

Amsar takardar ta yi sannan ta sake kiran Sergeant Mathew ya zo ya ɗauki littafin saita miƙe.

''Ina ƙara faɗa miki Sahura! Idan kika kuskura kika karya sharaɗi ɗaya i swear to Almighty God sai kin zauna a gaurd room na kwana goma sannan babu mai cetonki a duk barikin nan. Idan kina ganin ƙarya ne Please try to break one and see my true color. Muguwa!" Tana gama faɗin haka ta wuce wurin da ake sojojin suke kai mutane akurki,'yan maganganu suka yi sannan ta bar ɓangaren baki ɗaya.

Bayan tafiyan Madam Ngozi wasu mata biyu suka zo tafiya da ita. Kai tsaye suka kaita wani akurkin ɗaki sai dai babu datti a ciki suka sakata sannan suka kulle ɗakin. Abu goma da ashirin suka haɗe mata kai,a hankali tabi ɗan kurkukun ɗakin da kallo,wasu zafafan hawaye suka shiga rige-rigen sauka daga gurbin idanunta. Mutsu-mutsu Maryam ta fara yi a baya alamun farkawa take son yi. A hankali ta sauketa ta fara shayar da ita nono. Wani abu mai kauri da ɗaci ya tokare mata maƙoshi,zuciyarta na tafarfasa kamar talgen tuwo. Ta nuna kanta tana zubar hawaye

''Wai ni yau Sahurar gwaggwan bugaje aka saka cikin gaurd room silar yaran kishiyata! Ni Sahura! Kai ina! Wallahi da sake! Yanzu duk tarin uƙubar da na tanadar ma yaran kishiya sun tashi a banza!'' ta faɗa a fili tana share hawayen da suka kasa daina sauka daga kwarmin idanunta.  Wata zuciyarta ta ce mata ta mayar da yaran kawai ta huta da bala'in Madam Ngozi,domin ba barin za ta yi domin ta tabbata duk abin da ta faɗa babu makawa za ta aikata,amma kuma wani ɓangaren na zuciyarta na raya mata gurɓatacciya kuɗuba a kan idan ta sake yaran Mairi suka koma wurin uwarsu shikenan Mairi ta yi gwaggwaɓar nasara a kanta. Ita kuma ba haka take so ba,a kullum bata da wani tunani sai na ganin ta baƙanta ranta,ta cusa mata baƙincikin da har ta mutu tabon na nan a ranta,hakan kuma ba zai tabbatu ba sai idan yaran suna hannunta,duk da an shata mata babban layi a kansu amma suna hannunta kuma tabbas tana da yaƙinin Mairi tana nan cikin ƙunci da baƙin ciki mai girma na rashinsu ga Dauda Imamu da take juyawa tamkar waina a tanda. Dole ta nemi shawarar maman 'yar gayu ta ji ta bakinta. Lokaci guda kuma ta saki kuka mai sauti tuno da sanwar da ta ɗaura a risho,ta san da wuya hankalin Dauda Imamu ya je wurin kicin ɗin. Yanzu haka yaranta za su dawo da yunwa su samu bata gidan? Ya Nu'aymah za ta kasance idan bata ci abinci ba? Wa zai kular mata da yara kafin ta dawo? Yanzu haka za su wuni basu ci abinci ba har sai lokacin da aka fito da ita. Hannu ɗayan da bata riƙe Maryam ba ta ɗaura a kai tana kwarma uban ihu tare da kururuwa tamkar wacce aka aiko ma saƙon mutuwar Gwaggwon Bugaje. Sosai take kukan kamar ranta zai fita tana faɗin

''Wayyo ni Sahura na mutu na lalace! Shikenan yau yarana za su wuni da yunwa! Gwaggo! Gwaggo ki taimake niiiiii! Yiiiiiiii! ''

Ihunta ya farkar da Maryam da ta koma bacci,take ta saki matsanancin kuka saboda firgitar da ta yi. Sahura na jijjigata tana kukan,ba komai ya ɗaga mata hankali ba sai yaranta,bata tunanin Dauda Imamu zai dawo gidan ya duba ko sun dawo balle ya yi tunanin nemo musu abinci ko kuma gyara sanwar da ta ɗaura a saman risho. Haka ta ci gaba da kuka tamkar ƙaramar yarinyar goye...✍️

^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

A ɓangaren mahaifin Muhsin yana komawa gida ya ɗauko Momy suka taho asibitin,har da sauran break fast da suka rage ta taho da shi asibitin. A gurguje suka gaisa da maman Jawaheer sannan ta musu sallama ta bar asibitin domin hankalinta ya koma gida kar su Jawaheer su dawo bata nan Mahaifin Muhsin ya wuce cikin gari aka bar momy da Yasir da ke shan pepper soup cikin natsuwa wanda momy ta kawo, lokaci bayan lokaci tana jansa da hira,tun yana takurewa har ya saki jikinsa da ita. Dauda Imamu na komawa masallaci tafiyar gaggawa ta taso mishi zuwa barikin da ke cikin Jaji wurin limamin masallacin juma'arsu.Kasancewar shi ne babba sai haƙƙin zuwa barikin ya rataya a wuyanshi. Da tunanin Sahura da Hamida da kuma su Aunty Saudah idan suka dawo daga makaranta babu abinci ya tsallake zuwa Jaji,ko samun damar zuwa flat ɗinsu bai yi ba.

Lokacin dawowa makaranta ya yi,su Hamid cike da farinciki suka saho gida,sai dai ga mamakinsu suka tarar da gidan babu kowa. Nu'aymah kuma sai jera hamma take tana shafa ɗan cikinta. Hankalinsu su Hamid ya ƙara tashi domin tun da suke da mahaifyarsu a duk inda take idan lokacin dawowarsu ya yi za ta dawo ta ɗora musu girki. Kicin Aunty Saudah ta nufa sai dai bata iske abinci ba,hasalima tukunyar da take saman rishon take ƙauri alamun abin ciki ya ƙone. Da sauri ta ɗauki tsumma ta sauke tukunyar tare da kashe rishon. Dawowa falon ta yi tana yin kicin-kicin da fuska. Hamid da ke lallashin Nu'aymah ya ce

''Mama ta bar abinci kuwa?"

Girgiza masa kai ta yi, nan da nan fuskarsa ta sauya.

''Aunty Saudah ke da su Amina kuje gidan ƙawayen mama ku ga ko tana nan. Ni zan je masallaci na amshi kuɗi hannun baba mu saye wani abu mu ci. Babu musu suka fita shi ma haka aka bar Halima da Nu'aymah a gida. Sosai Nu'aymah take kukan ita ina mamarta ta bata abinci yunwa take ji. Hamida ya je masallaci bai ga Dauda Imamu ba sai ya wuce islamiyya,a nan ba mai ganshi ba sai ya dawo flat ɗin. Su Aunty sun gama gantalinsu gidajen ƙawayen Sahura ba su ganta ba. Maman 'yar gayu ma ɗakinta a kulle yake alamun bata nan. Haka suka dawo gidan a galabaice. Hankalinsu ya tashi,kuka suka shiga rerawa kowanne da kalar sautin muryarsa suna kiran baba da mama. Nu'aymah ta fi kowannensu galabaita,a ɗan ƙaramin tunaninsu iyayensu su gudu sun bar su. Babu wanda a cikin ya yi tunanin zuwa kicin ɗin ko akwai garin kwaki su sha,abinka da 'ya'yan gata komai yi musu ake,ba su san wata aba wai wahala ba.

Kai tsaye mahaifin Muhsin ya wuce makaranta ya ɗauko su Jalil bayan ya dawo daga cikin gari ya wuce da su asibiti. Sai da ya tsaya restaurant ya saye musu abinci aka saka a robobi masu murfi,ya haɗa da drinks sannan ya nufo barikin. A asibitin suka ci abincin har da shi, Hamida ma tashi abincin sosai,domin zuwa yanzu ta ji sauƙi,ƙurajen sun fara mucews, tarin da take yawan yi ta daina sakamakon kyakkyawar kulawan da take samu wurin ma'aikatan asibitin da maman Jawaheer. Suna ci suna hira har maman Jawaheer ta dawo tare da yaranta biyu mace da namiji,sai ƙanwarta budurwa da suka zo tare domin bata kammala girki ba suka iso. Tamkar Family ɗaya haka suka shiga hira, yayin da mahaifin Muhsin ya fita. Bayan fitarsa wata nurse ta zo duba Hamida,ganin ta samu sauƙi sosai sai nurse ɗin ta ce zuwa gobe za su sallameta. Wannan kenan...✍️

^^^^^^^^^^^^^^^

Ƙarfe 5:40pm na yamma

A daidai wannan lokacin aka fito da Sahura daga akurkin ɗakin, domin da gangan sojojin suka ƙara mata lokaci don ta sake ladabtuwa. Ko ba a faɗa ba Sahura ta ladabtu kuma ta shiga taitayinta, idanunta sun ƙara manya saboda kukan da ta sha. Kafin ta tafi sai da suka sake jaddada mata sharuɗɗan sannan ta wuce. A hankali ta goya Maryam sannan ta fara tafiya kamar wacce ƙwai ya fashe mata a ciki. Ta shanyo kwanar flat ɗinsu kenan ta haɗu da...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***