Chapter: 9
by @pinkylady
"Stalker?"
Beelah ta fada ta na zooming hoton amman ta kasa ganin fuskar yarinyar saboda an rufe fuskar tata. Screenshot tayi ta tura hoton a wata number ta whatsapp ko minti biyar ba a yi ba aka maido mata reply da "Skye royale"
"Aunty Bee an gama"
Amira da ke fitowa daga kitchen ta fada. Hannunta dauke da jug din kunun aya mai dan karen sanyi da ta yi kafin ta gama girkin da take masu. A duk cikin kannen Naseer da ma 'yanuwansa Amira ce kawai suke shiri da ita, don Amira sam bata da kuiya kuma tana sonta sosai tun ma kafin auren su da yawa mutane bai masu dadi ba. Wannan dalilin ne ya sa Amira tsab zata zo ta kwana yadda ta so kuma taga murmushin Beela din, ban da ita babu mai ganin shi.
"Okay bari in dan watsa ruwa minti biyu, ki rabo Noor daga wasan cen haka nan "
Kai ta gyada mata sa'ilin da ta ke aje jug din kafin ta fita harabar gidan in da Noor ke wasa da motar yara.
Beelah ta riga su zuwa dining din don daman ba karamar yunwa take ji ba, da safe cake kawai ta ci da black coffee. Ko da ta zauna ma waya ta cigaba da latsawa har Amira ta zo. Abincin ta zuba ma Beelah ta mika mata gabanta sannan ta zuba masu ita da Noor. Ta riga ta saba da Halin Beelah ba wani labari ake da ita ba don haka ta maida hankali ga abincin ta kawai.
"Amirah wannan sanyin kike sha ko? Duk fadan da yai miki ranar nan? Baki tausayin kanki ne?"
Aje cup din kunun ayar tayi tana marairaice fuska.
"Yau ne kawai fa, na dade ban sha ko ruwan sanyi ba"
Dan tabe baki Beelah ta yi tace
"Ni dai ba ruwa na to"
Saboda ta san in ciwon Amiran ya tashi baya mata da kyau, sai ta yi wata asibiti ma.
"An rage masa abinci?"
Da mamaki Amiran ta kalle ta, tun da ta gane wa ta ke nufi. Kafin ta ce
"Aunty kin manta baya cin sakwara?"
Dan bata fuska tayi, ita sam ta ma manta wallahi.
"Duka doyan kika yi da shi?"
"Eh"
Ta bata amsa, don ita bama ta san wai yau zai dawo ba. Ta dai san baya gari.
"Bari sai in dafa mashi white rice kafin in tafi"
"Thank you Amira"
Ta fadi tana sakin ajiyar zuciya. Don dai a halin yanzu bata ma hango shiga kitchen ba wallahi. Ta sani sarai abin da take yi bata kyautawa, to amman ya za tayi? Wata kalar kuiyar da sam ba halinta bane a da, a yanzu ta zama jinin jikinta.
*Inna dawo tiya biyu na kirba yau....*
Ta rufe idon ta tana cije leben bakinta na kasa. Ba ta son kalar tunanikan nan suna harbo mata cikin kai. Ta riga ta wuce wajan...
***
"Don girman Allah Farha ki bar ni in runtsa bacci na ke ji.."
"Yaa Layla ba zaki gane bane. Kalar wadan nan matan ba wai da alheri suke bin mutum ba..."
"Ina ruwan ki to? Ko ya fada maki bai san yadda zai yi bane? Wannan sababin da kike min tun jiya amfanin me zai yi maki ne wai?"
"Na ji, yi baccin ki ni dai. Babu abin da zaki fahimta a nan"
Layla ta juya bayanta, takaici na kara kashe ta. Wato ita ce stalker din? Har yaushe ma aka samu minafikin da yai mata hoto da ya ja sai faman tsige mata albarka Fj fans suke, a ciki har da Farha. Abin takaicin ma yau sam bata samu ganin shi ba, sai ji tayi m baya hotel din duk yinin yau bare ta samu damar maida mashi abinsa.
Dakyar bacci barawo yayi awon gaba da ita.
*****
FJ...
Ya zare headphone da ke sargafe a wuyansa ya na huro iskar bakinsa. Bacci ne fal! A cikin idonsa. Kusan kwana uku kenan baya samun baccin kirki saboda waƙar da ya ke haɗawa wadda zai yi a Golden hour club. A duk sadda za suyi akwai competition da ake shiryawa kowa sai yayi participating according to his profession. Don haka shi da sauran mawaka biyu da ke zuwa kowa waƙa ya ke shiryawa sai a zabi wanda ya ci. Tun bayan da ya rubuta wakar bai samu damar gyarawa da yin rehearsal ba sai a kwana biyun nan da ya rage masa.
Khalid ya ƙwankwasa kofar ya leƙo tare da daga masa hannu.
"Za mu iya tafiya?"
Kai kawai ya gyaɗa masa ya aje paper rubutacciyar wakar, suka fita.
*
Ya na shiga dakin ya zube wayoyinsa bisa kujera kai tsaye ya shiga wanka, sai bayan ya fito ne cikinsa ya fara kukan yunwa don rabon shi da abinci tun na safe. Haka kawai ya ji yana son taste din miyar sakwaran da ya ci kwana biyu don haka ya kira yayi requesting sakwaran kawai. An shaida masa zai jima don haka ya kwanta kawai ya rufe ido yana tunanin sadda Mommy na raye, duk dare zai tadda abinci na jiran shi. Yayi murmushi yana jin kewarta sosai a ran shi. Kulawarta, soyayyarta da yadda take bin bayanshi akan a duk sadda tasu ta hada shi da Abba. Wani dare da ya ke daya daga cikin dararen da ba zai manta ba ya bijiro masa
Misalin ƙarfe goma da rabi na dare ya shigo gidan jikinsa cure yana rawan sanyi kasancewar sanyin da ake yi sosai. Sadaf-sadaf ya zo shi ga dakinsa, yaji muryar Daddy a kausashe.
"Koma in da ka fito...ba zaka kwanar min gida ba Fahad tun da ni dai ban isa da kai ba a rayuwarka."
Ya juyo yana kallon sa cike sa roƙo, amman yadda fuskar Daddy ke murtuke hannunsa na nuni da kofar fita dole ta sa ya juyo da nufin ficewa kawai.
"Fahad"
Muryar Muryar Mommy ta sa ya saki ajiyar zuciya. Kafin ya juyo kuma ya ji muryar Mami ma
"Ah Fahad sai yanzun muke ganinka?"
Kafin ya ba daya daga cikinsu amsa Daddy ya sake daka masa wata tsawar
"Ka fita na ce!!"
Da sauri Mummy ta isa in da ya ke tana kamo hannunsa sannan ta juya ta kalla Daddy
"Haba Daddyn su hakan bai kamata ba, ta ya zaka fidda yaro cikin sanyin nan.."
Ya katse ta
"Bai san da sanyin ba ya shigo yanzu? Na tabbata yana can yana bin yan iskan mawakan nan a gari da na yi masa katangar karfe da su.."
"A dai yi hakuri, tun da dai ba shaye-shaye ya ke yi ba.."
Wani kallo da Mommy ta yi mata ya saka Mami yin shiru. Aikuwa kamar guguwa haka Abban ya iso gabansu ya fizgo shi ya na shinshina kayan jikinsa. Sai da Mommy ta ga abin ba mai karewa bane kawai ta janye shi suka bar wajan, shi kuma Abba cikin bacin rai ya wuce daki, Mami da kwananta ne ranan ta bi bayansa.
Karar kwankwasa kofar da aka yi ya saka shi bude idonsa har sun sauya kala ya bada damar shigowa. Yadda wacce ta kawo abincin ke kiciniyar zuba masa ya sa ya fahimci ba yarinyar da ke kawo masa kwana biyu ba ce don tun da take kawowa bata taba attempting zuba masa ba, akwai dai nacin dawowa zai shaida hakan.
Da ya ke yunwar yake ji sai ya tashi zaune kawai yana jiran ta gama zubawa. Tun daga kamshin miyar ya gane ba kalar waccen bace. Kamshi kam akwai sosai kamar ko yaushe don babu abincin da zai ce baya dadi aduk abincin da ya ke ci. 'what?' Ya saba da girkin yarinyar ko me? Ya girgiz kai yana nanatawa kansa abincin duk daya ne. Ya sauko ya fara ci bayan ta fita. Sai dai duk yadda ya so sharewa ko bayaso akwai bambanci. Ba wannan ne karo na farko da ya taba cin sakwaransu ba, yakan ci akai kai duk da yafi son ta mommy gaskiya, amman tun daga ranar da ta kawo masa sakwara ya ji ta yi masa sak yadda yake so, ydda suke cin ta da Mommy. Don sau biyu ya na complain da ya lura da matsalar da masu girkin ke shiga ne sai ya daina cewa a bashi sakwaran kawai gaba daya, sai a ranar da ya ji lallai yana son cin favorite dinsu. A miyar ma zai shaida nasu yana duhu sosai ba kamar nata da yake kallo kamar na Mommy. Bai ci sosai ba ya tashi. Bayan ta da wo ɗauke kayan ya ce
"Uhm..wane sakwara ne aka kawo min kwana biyu da suka wuce?"
Ta danyi jim, kafin ta ce
"Da rana ta ke aiki."
Kai kawai ya gyada ya shige washroom. Sara ta juya ranta na tafasa ta fita. Ita tun farko Laylan nan ba birgewa ta ke ba, gashi ta na zuwa aka bata special duty, shiyasa ma ta samu dakyar itam aka bata shi ma wata ce bata lafiya yanzun da ta samu sauki shi ne ta dawo yin night duty. Duk da shi night optional ne in baka so sai ake sa maka morning da evening kawai, amman duk sadda za kayi nigh ana kara yawan kudin mutum.
***
Beelah
Ta gama duk wasu shirye-shiryenta na yadda zata zabtare wani yankin mutunci na Fahad a idon duniya, wanda kuma take jin kamar ta jawo ranar da za su yi GHC. Burinta ta ga, fuskar Fahad a lokacin da ya rasa mafita, a lokacin da yake kallon igiyar tauraruwarsa da ke haskawa tana lilo tare da barazanar tsinkewa. Ta yi wata dariyar jin dadi. Kafin ta dauki wayarta ta yiwa Farha SMS akan in da zasu hadu wannan karon. Ita ce tudun dafawarta a yanzun, ita ce fuskar da zata ara tayi amfani da ita wajan wargaza duk wani farincikin rayuwar
sa. soyayyarta da Farha kewa Fahad zata yi mata rana, da ita za ta yi amfani ta cima duk wata manufarta!
🦋🦋🦋