BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

Chapter 29

by @narrnarhhbukar00

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

029

A hankali ta goya Maryam sannan ta fara tafiya kamar wacce ƙwai ya fashe mata a ciki. Ta shanyo kwanar flat ɗinsu kenan ta haɗu da maman 'yar gayu ita da yaranta,alamun daga unguwa suka dawo,duba da yadda suka cancaɗi ado suna walwali. Maman 'yar gayu na haɗa ido da Sahura zuciyarta ta halba, kamar an sauya mata kamanni. Fuskarta ta yi ɗan jaja,idanunta sun ƙara girma kuma sun sirka kamar ta yi dambe an naushesu tsabar yadda suka kumburo. Suna haɗuwa Mama 'yar gayu ta ce

''Maman Hamid! Me ya sameki haka? Faɗa kika yi ne aka tumurmushe fuskarki? Kin ga kuwa yadda kika sauya kuwa?"

Murmushin gefan baki Sahura ta yi tana share hawayen da suka gangaro mata ta ce

''Ko ɗaya maman 'yar gayu. Hankalina yanzu yana kansu Nu'aymah na san har yanzu ba su ci abinci ba. Idan na natsu za mu yi magana''

''Muje gidan naki yanzu sai 'yar gayu ta tayaki girkin,hankalina ba zai kwanta ba idan ban ji abin da ke damunki ba"

''To'' kawai ta ce sannan suka ci gaba da tafiya.

A dakalin gidan Sahura ta iske su Hamid sun yi jugum-jugum kamar marayu, ko uniform ɗinsu ba su cire ba, Nu'aymah na kwance a saman cinyar Aunty Saudah tana kuka. Lokaci guda tausayin yaranta suka sake mamaye zuciyarta,ko ba a faɗa mata ba ta san ba su abinci ba. Wasu hawaye masu ɗumi ta share zuciyarta ta tuƙuƙi. Su Halima na ganin mamarsu suka kira sunanta da iya ƙarfinsu,da gudu suka yo kanta tare da faɗawa jikinta suna sakin wani sabon kukan. Cak! Ta ɗauki Nu'aymah da ke ambaton ta bata abinci cikinta zai gudu,yunwa take ji. (Allah sarkin daɗi wai in ji ɓarawon takanɗa! Haba Nu'aymar Sahuralliya me aka yi da maza 😂 just yunwar wuni guda kina faɗin cikinki zai gudu. Allah ya ba su Yasir haƙuri da Gyatumarki ta dinga azabtar da su da yunwa😭.  Wallahi akwai kishiyoyin da suke da irin halin Sahura a wannan duniyar. Allah ka tsarkake zukatanmu. Ka ba mu ikon aikata alkhairi ka kuma tsare mu daga aikata sharri duk ƙanƙantarsa)

Idanun maman 'yar gayu sun cika da ruwan hawaye ganin yadda su Hamid suke kuka ita ma Sahuran na zubar hawaye,duk da bata ma san taƙameman abin da ke faruwa ba,ƙarasawa cikin flat ɗin suka yi. Sahura na shiga cikin falon ta zauna saman kujerar jagwab kamar kayan wanki duk da goyon da ke bayanta,ita ma karan kanta yunwarce ke ƙwaƙular hanjin cikinta, bata taɓa kaiwa yamma bata ci abincin rana ba,ko lokacin watan ramadan idan ta ji azumin na wujijjigarta bayi take shiga ta kulle ta ci ta ƙoshi sannan ta fito. Maman 'yar gayu da kanta ta shiga kicin ta ɗora girki,ganin akwai jajjagyen kayan miya ga kuma taliya a gefe har guda biyu sai kawai ta ɗora jollof ɗin taliya na manja. Bata fito a kicin ɗin ba sai da ta kammala girkin tsaf. Tire guda ta zuba ma su Hamid ta cika shi sosai,ta zuba ma Sahura a plate. Kiran Hamid ta yi ya shigo ya ɗauka sai ta fitar ma Sahura da nata. Koda ta fito ta iske su Hamid har sun fara kai hannu cikin tiren duk da turirin da abincin ke yi. Hannu na rawa Sahura ta amsa abincin tana kwanshe goyon Maryam,Maman 'yar gayu ta amsheta sannan Sahura ta ja zip ɗin rigarta ƙasa don abincin ya shiga ciikinta da kyau. Haka ta fara cin abincin hannu baka hannu ƙwarya duk da ƙonewan da hannunta yake yi. Sosai tausayinsu ya kewaye lungu da saƙon zuciyar maman 'yar gayu,ta matsu ta ji me ke faruwa da babbar aminiyarta. Tsaf suka cinye tafiya suka suɗe tiren kamar an wanke ka ce masu kamun yunwa ne. (😂 Wa ya faɗa muku Borno gabas take,yunwa ai ba sa'ar ubansu  ba ce😂 ko ya kuka ce my Esteem fans. Wallah ina jinku Kamar jinin da ke wayo a jikina my Esteem fans. I love you lodi lodi muahhhh😘😘😘🥰🥰🥰)

Bayan sun kammala ci suka shiga gasar gyatsa,idan wannan ya saki gyatsa sai ɗayan ya saki,zuwa lokacin an fito daga sallar magrib. Har yanzu Dauda Imamu bai shigo gidan ba,ita Sahura har ta manta da batun Dauda Imamu,da yaranta take. Bayan Sahura ta natsu yaran sun sauya kayansu saai suka zauna kallo,ɗan matsowa ta yi kusa da maman 'yar gayu. Tamkar mai faɗin rahoto a gidan redio, tiryan-tiryan ta shiga labarta mata abin da ya faru,,komai ta sanar mata. Tana kai ƙarshen maganar ta rushe da kuka tana faɗin

''Maman 'yar gayu yau na gama ganin tozarci a idon duniya. Ni Sahurar gwaggwan bugaje za a kai gaurd room da garƙame tamkar wacce ta saci tagullar sarki. Duka a kan yaran tsinanniyar kishiyarta! Kalli shatin hannun basamudiyar sojan a kuncina'' ta yi maganar tana jujjuya ma maman 'yar gayu kumatunta,sai a sannan maman 'yar gayu ta ga tambarin yatsun hagu da dama sun yi ja abinka da farar mace. Tsoron,tashin hankali da mamaki suka cika zuciyar maman 'yar gayu. Lallai Sahura yau ta yi gamo da gamonta. Wata nauyayyar ajiyar zuciya mai ƙarfi maman 'yar gayu ta sauke jin lamarin ya girmi tsohonta.

''To yanzu ke wani mataki kika ɗauka. Za ki mayar da yaran ko za ki zuba musu ido ne tun da dai yanzu an yi miki karan tsaye a kansu?"

Share hawayenta ta yi zuciyarta na tabbatar mata hukuncin da ta yanke shi ne daidai.

''Haba dai! Ai wallahi sun zo kenan babu komawa! Ai maman 'yar gayu abin da baki sani ba idan na mayar da su shikenan Mairi ta yi galaba a kaina,ga mari ga tsinke jaka duk a lokaci guda sannan na mayar da su sai ka ce BADAKKARIYA! Zaman su a nan shi ne babban makamina da zan ci gaba da yin nasara a kanta. Na san yanzu haka tana cikin baƙin cikin rashinsu,balle lalacewar da ta ga sun yi,na san zuciyarta na cunkushe da tsantsar damuwa. A Da na so ki ba ni shawara amma yanzu kan na samar wa kaina mafita''

Jinjina kai maman 'yar gayu ta yi,a fili ta nuna farincikinta da matakin da ta ɗauka,a baɗini kuwa bata ji daɗin haka ba, mene ne amfanin barinsu a gidanta tun da bata da iko a kansu, gwara ta mayar da su hannun uwarsu sai ta ci gaba da juya mijin. Gyara zaman mayafinta ta yi sannan ta ce

''Tun da dai yanzu baki da iko a kansu,idan ki bi tawa shawarar ki mayar da hankali a kan yaranki sosai,duk da na sanki gwanace wurin kula da yara,musamman matan don yaranki za su yi kyau da matan manya wallahi''

Wani sanyi Sahura ta ji a ranta wanda rabon da ta ji irinsa tun safe,juyawa ta yi ta kalli 'yan matanta zuciyarta na tabbatar mata da sun fi dacewa da masu ƙumbar susa musamman Nu'aymarta. Juyowa ta yi fuskarta kwance da maɗaukakin murmushi ta ce

''Tabbas kin kawo shawara mai tsada,kuma in shaa maka Allahu zan mayar da hankali sosai a kansu. Kin san Allah yanzu yaran Mairi ba su raina,koda sun dawo gidan nan babu ruwana da su, hankalina zan mayar gurin 'yan matana na ci gaba da tsumasu da kayan mata"

''Da kyau animiya! ni ma dai idan kin tashi aika saƙon kayan matan,ki mini magana zan bayar da nawa kuɗin a haɗo da ni don na fara tsumasu,kayan mata su ne a gaba a inganta gidan aure''

''Maganarki dutse, idan Dauda Imamu ya tashi zuwa Sakkwato zan yi miki magana,Gwaggota sai ta haɗo mana kayan''

''To shikenan bari na wuce gida kar dare ya yi mana,Allah ya kiyaye na gaba'' Ta yi maganar tana miƙewa, yaranta da ke kallo suka miƙe ,ta yi ma Sahura sallama sannan suka wuce. Da ƙyar Sahura ta iya miƙewa ta je kicin ta jona ruwan wanka a heater,sai ta dawo falon. Hirar da suka yi ta maman 'yar gayu ta shiga dawo mata,tabbas yanzu ne ya dace ta mayar da hankalinta a kan yaranta musamman 'yan mata,don tana da yaƙinin masu kuɗi za su aura idan sun girma. Lokaci guda ta sakarwa kanta kasaitaccen murmushi. Har ta fara hasaso yadda masu manyan motoci za su jeru a ƙofar flat ɗinsu sun zo hira wurin yaranta. Kamar wasa ta tsunduma kogin tunanin 'yan matan,babu irin hasashen sa bata yi ba. Ta ce Nu'aymah za ta auri yaron sarki,Aunty Saudah ta auri ɗan shugaban ƙasa,Amina ta auri yaron shugaban sojojin Nijeriya. Halima da auro babban likitan ƙasa da ƙasa sai autarta ta auro yaron babban ɗan kasuwa mai kamfanoni bila adadin a cikin gida da wajen Nijeriya. Hamid kuma ya zama major genaral. Kai idan wannan tunanin ya tabbata ta gama hannun riga da talauci. Murmushi ne kwance a fuskarta tana tunanin,can ta miƙe zuwa kicin ta juye ruwan wanka ta nufi bayi,bayan ta yi wanka ta amshi Maryam daga hannun Amina ta yi mata wanka ta shiryata sannan ta fito ta zauna tare da yaran. Sai a sannan tunanin Dauda Imamu ya faɗo ranka,ko yana ina har yanzu bai dawo gidan ba oho.

Sai kusan goman dare Dauda Imamu ya dawo gidan a matuƙar gajiye,ga mamakinsa sai ya tarar da yaran duka suna falon suna kallo idan ka cire Nu'aymah. Kallo ɗaya ya yi musu ya kawar da kansa,idan da da ne ta nuni sun firgita ko kuma su ruga daƙinsu da gudu saboda sun san ya hana kai goma ana kallo,tun da suka yi masa sannu da zuwa suka ci gaba da kallonsu ba tare da shakkar komai ba. Abu mai ɗaci ya tsaya masa a maƙoshi,bai tsaya a falon ba ya wuce uwar ɗaka inda ya samu har Sahura na minsharin bacci. Komawa falon ya yi ya kulle ƙofa sannan ya dawo ya kwanta,daman tumbinsa a cike yake ga kuma gajiyar da ta nannaɗe gaɓɓan jikinsa. Cikin ƙanƙanin lokaci bacci mai daɗi ya yi awon gaba da shi...✍️

^^^^^^^^^^^^^^

Hayin bijini Mada jihar Zamfara Nijeriya

A ɓangaren Mairi da 'yar uwarta hankalinsu ba a kwance yake ba,sun yi matuƙar ƙosawa gobe ta yi Mamman ya je Bariki ya ji halin da su Jalil suke ciki. Suna raya daren da nafilfili, sun yarda da Allah shi ke yin komai sannan shi yake da iko a kan kowa,duk raka'ah ɗaya suna daɗewa a sujjada,Mairi wani lokaci. har kuka take tana addu'ar Allah ya kare mata yaranta daga sharrin kishiyarta. HAFIZA kuwa ta sake zama miskila ta ƙarshe,kaɗaicin 'yan'uwanta ya saka ta zama shiru a koyaushe,halayyarta takan tsoratar da Mairi da Jamila,sai ta wuni bata ce uffan ba,tana nan tana zane-zanenta wanda ta mayar da shi kamar ibada,bata kula yaran gidan kwata-kwata, koyaushe za ka sameta da littafi kuma tana tilawar Al'qur'ani mai girma. Wannan kenan...✍️

^^^^^^^^^^^^^^^^

Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya

Cikin dare Sahura ta ji amon muryar Dauda Imamu a falo yana karatun Alqur'ani. Tsaki ta ja mai tsayi tana sake ƙudundunewa cikin bargo,ita ta rasa wannan jarabar,mutum kullum cikin karatun Alqur'ani ko gajiya ba ya yi. Da safe da ta tashi bata iskeshi ba,sai ta yi ma yaran wanka ta ɗora abin kari gudu-gudu sauri-sauri ta kammala saboda kar su yi latti. Bayan sun ci ta ba su kuɗin break suka wuce makaranta. Miƙewa ta yi ta gyara gidan sannan ta koma bacci ita da Maryam. Yau da wuri Dauda Imamu ya dawo gidan. Ganin bata falon sai farinciki ya cika ransa. Kai tsaye ya nufi kicin ya ɗauko abin karinsa ya karya,ya ɗora ruwan wanka a risho ya yi zafi ya juye sannan ya wuce bayi wanka. Duk bidirin da yake a gidan Sahura bata san yana yi ba,domin bacci sosai take sharɓa ita da 'yarta,gajiyar zaman akurkin ɗakin bai gama sakinta ba. Bayan ya sanya kaya ya fito. Zuwa lokacin ƙarfe 12:12am na rana har ta yi. Ya fito kenan ya haɗu da mahaifin Muhsin ya fito daga motarsa zai nufo flat ɗinsu. Cike da mutuntuwa suka gaisa.

''Daman na zo mu je da kai wurin iyalina,don zuwa gobe nake son zuwa Abuja amsar takardar transfer. Wannan karon jihata ta Kaduna suka ajiyeni'' ya faɗa cike da murna.

''Alhamdulillah haka ake so. Allah ya ci gaba da tsare mana ku. Da na so zuwa ganin jikin Hamida ne''

''To muje tare daga can ba sai mu wuce gidan nawa ba''

''Eh hakan kuwa ya yi. To muje''

Har Dauda Imamu zai shiga mota kenan ya ga an sauke Mamman a mota. Cak! Ya tsaya daga shiga motar. Mahaifin Muhsin ya fito yana kallon inda Dauda Imamu ya mayar tamkar TV. Bayan an sauke Mamman ya ƙaraso inda motar mahaifin Muhsin take da yalwataccen murmushi shimfiɗe a fuskarsa. Hannu ya miƙa suka da Mahaifin Muhsin sai ya juyo ya gaisa da Dauda Imamu wanda mamaki ya ƙawata fuskarsa.

''Na san ka yi mamakin ganina ko Dauda''

Ɗan murmushi Dauda Imamu ya yi sannan ya ce

''Sosai kuwa Mamman! Rayuwa ta yi tsada,na jima sosai idanuna ba su yi tozali da kai ba. Ya iyalin,ya ka baro su''

''Duka suna nan lafiya Alhamdulillah.''

''Officer Kabir ga yayan uwar gidana ku gaisa'' cewar Dauda Imamu yana nuna Mamman. Sake gaisawa suka yi sannan Mamman ya ce

''Daman Malam ne ya aiko ni wurinka a kan batun yaran Mairi. Yana so na zo na gani da idanuna. Shin da gaske ne ka muzanta iyalinka a gaban mutane ko dai Mairin ta faɗa ne dai saboda tana son ka bata yaranta?''

Ɗif! Dauda Imamu ya yi saboda an kai gaɓar da bakinsa ba zai iya furta komai ba. Bayan faruwar al'amarin ya yi nadamar abin da ya aikata mata yafi cikin kwando,ya rasa mai ya shiga kansa a lokacin. Har yanzu bai daina nadamar hakan ba. Gyara tsayuwa Dauda Imamu ya yi sannan ya ce

''Toh yanzu dai Mammann abin da ya faru ya riga da ya faru. Batun yara suna cikin ƙoshin lafiya,Hamida ce dai take kwance asibiti,kuma jikinta ya yi sauƙi sosai don da wuya yau ba su sallameta ba.''

Mamman bai ji daɗin amsar da Dauda Imamu ya ba shi ba,domin ba tambayar da ya yi masa ba kenan,amma sai ya share ko don mutumin da suke tare.

''Subhanallah! Allah ya bata lafiya da ɗaukakin musulmai. Daman na zo tafiya da yaran ne a gaskiya,tun da dai uwarsu na raye ban ga amfanin zamansu a barikin nan ba. Matarka tana wahalar da su da bauta don haka ba zamu lamunci hakan ba. Malam ya so zuwa da kansa amma tafiyar gaggawa ta same shi,shi ya sa ya aiko ni don na yi wa tufkar hanci. Yau zan koma da su Zamfara in shaa Allah! Domin ban zo da shirin kwana ba. ''

''Malam zan iya saka baki a maganarku'' Mahaifin Muhsin ya tambaya yana duban Mamman.

''Bismillah! Za ka iya'' cewar Mamman yana ɗan sakin fuska. Ɗan gyara tsayuwarsa ya yi sannan ya ce...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️

***