A zuciyata

Chapter 4

by @aishatu98

“The star fell. Not because it was weak  but because the sky was never its home.”


Safna ta kasa runtsawa. Tunda ta kalla video ɗin da ya katse kafin Fahad ya faɗi abinda ke ransa, zuciyarta ta zama kamar ƙoƙon wuta. Abinda Fahad ke so ya faɗa… ya shafi Khalil. Amma me?


Ta kunna laptop ɗinta fiye da sau 20 a cikin daren, tana kokarin dawo da ragowar clip ɗin. Amma duk a banza. Video ɗin yayi cut kai tsaye kamar wani ya yanke shi da gangan.


Yanzu, sai kawai ta zauna  ta lumshe ido. Kuma tunani ya fara kai ta baya.





💭 FLASHBACK – 

The Day Fahad Disappeared



Wata rana kafin auren ta da Khalil, Fahad ya ce zai zo ya gana da mahaifinta.

Sai kwatsam ya ɓace. Ba waya, ba saƙo. Mahaifinta ya hana ta Amma yau… Safna na jin kamar akwai wani abu da aka ɓoye.





🛬 THE ARRIVAL OF SALMA



Da yammacin Asabar, Safna ta tsaya a babban falon gidan, ta haura kafet ɗin Turkish da kafar tsirara. Sai ta jiyo car horn a waje  Salma ta iso.


Salma ta shigo da kaya, ta rungume Safna“Na rasa lafiya,” Safna ta ce da murmushin ɓoye damuwa.


Suka zauna suna cin suya da kunun zaki a garden. Sai Salma ta faraon Zara Aliyu.”


Zuciyar ta ta tsaya 

safna ta kalleta.

🌪️ THE DEEPER WOUND



Da dare, bayan Salma ta kwanta, Safna ta koma dakin Khalil  ta fara leƙen drawer ɗinsa. Ba komai mai haɗari  sai wata ƙaramar red box.Ta buɗe ta.Ring ne a ciki. Amma ba zoben aurensu ba.Wannan baƙi ne, with a silver stone  engraved da sunan: Z.A.

zuciyar ta faɗi. Zara Aliyu?


Sai wani ƙaramin sticky note ya faɗo daga ciki. An rubuta:


“– For what you did, I’ll never forgive you. – F.”


Fahad?


Fahad ya rubuta wannan?


Khalil yana ajiye zobe da saƙon ƙiyayya da Fahad ya bar masa?


Kamar iska, ƙoƙon sirrin da ta daɗe da kokarin mantawa da shi, ya fashe. Tauraronta… ya faɗi.

Amma Safna ta san yanzu, ba zata zauna shiru ba.