KADDARARMU CE....1
by @nusybee143
🫰KADDARAR MU CE....👌
(tazo a haka)
*Paid book*
❤️*young talented writers association YOTA*❤️
✍️ Alƙalamin Nusaiba Ibrahim Rimi (Nusy bee)
Marubuciyar:
Matar khalees
Barrister Hibba
Siraɗin uƙuba
*TALLA!TALLA!!TALLA!!
*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.
*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL,****,
***
To kamar yadda kuka sani Nusy bee bata kawo muku labaran banza, littafan Nusy bee saƙonni ne masu tsuma zuciya da tsayawa a rai,to a wannan karon ma gata ta dawo a sabuwar tafiya mai taken KADDARAR MU CE,ku biyo ni don jin yaya ƙaddarar take juyawa da waɗanda ke cikin ta,shin sun haye SIRAƊIN UƘUBAr rayuwa ko ya afka dasu?yaya fafutukarsu ta kasance a yayin neman MAFITA?
Kamar yadda kuka gani a rubuce,kuma kuka sani a aikace,idan aka ce ƘADDARA abu mara kyau ya fi zuwa zuciyoyinmu tare da fargaba, labarin ƘADDARAR MU CE ta zo a haka ba labarin soyayya bane, labari ne mai cike da sarƙaƙiya, al'ajabi,da ban mamaki,shin ƙaddarar wanene ta fi zuwa a wahale?kuma ta wanene ta fi zuwa a hagunce? tsakanin ASHRAF, ANEESA, A'ISHA (AMMI)HAMDA(MUM)da kuma MALEEKA
Shin suna haye SIRAƊIN UƘUBAr rayuwar da ya same su?ko ana samun akasi?
Shin sun karɓi ƘADDARAR SU a haka ko sun yi gaggawa sun yi raki?ki biyo ni don samun wadannan amsoshin
Gargaɗi 👇
Littafin KADDARAR MU CE ƙirƙirarren labari ne,mallakin Nusy bee,ban yarda a juya min ko a chanja min littafi na ta kowacce fuska ba sai da izini na🙅
Haka zalika ban yarda a karanta min littafi na a YouTube channel ba sai da izinina,bin doka da tsari a rayuwa yana kawo zaman lafiya da mutuntawa 🤗
SADAUKARWA:
Na sadaukar da littafi na ga mutane na da suke bibiya ta a kowanne lokaci,princess phadimatu, Aisha Aliyu humaira,maryaama's collection da sauran su da bazan iya lissafa su ba🥰 Allah ya bar zumunci Amin summa Ameen
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 1
SHIMFIƊA
Tabbas idan ance ƘADDARA ga duk musulmi,ya san da wani abu ne da ke shigowa rayuwar bawa mai kyau ko marar kyau a lokacin da baiyi tsammani ba,ya kan zo wa bawa da sauƙi ko a yanayi mai wahala,akan samu waɗanda zasu yi nasara,su haye ta,amma akan samu waɗanda take ruftawa dasu daga baya kuma su riski ranar DANA SANI!wadda bahaushe ya kan ce ƙeya ce
TSOKACI...
A hankali ta lumshe idanun ta hawaye Masu zafi suka zubo akan farar fuskar ta, zuciyar ta ji take yi kamar ana hura mata wuta tsabar yadda take ruruwa tana tafasa,kukan ta yana ratsa mata zuciya,bata so ta karaya ballantana ta karyawa ƴar tata zuciya gaba ɗaya, cikin wani irin gunjin kuka taji tana faɗin
"Don girman Allah mamana ki taimake ni!ki ceci rayuwa ta don girman Allah!kar ki bari Abba ya aura min wanda bana so,Ammi ki ba shi haƙuri, zan yi masa biyayya amma kar ya aura min ɗan giya Please Ummi!ko a addini Manzon Allah ya ce ku zaɓa mana nagartattun maza,kowa kuka zaɓa min zan zauna dashi amma ku taimaka min Ammi, ba zan iya auren ɗan giya ba wallahi,manemin mata ne, kuɗin da yake da shi sun siya masa mygayen dabi'u da yawa Ammi,don Allah Ammina!"ta ƙarashe tana girgiza Ammi cikin tashin hankali na fitar hayyaci
A hankali Ammi ta lumshe idanunta, hawayen da suke zuba suka sake samun masauki akan kyakkyawar fuskar tata,tana shirin magana muryar shi mai kama da sautin aradu ta katse ta
"Dole ki aure shi ki zauna dashi ko shine ɗan magajiya!umarni na ne kuma dole ki bi,saɓa hakan yana nufin ficewarki daga cikin ƴaƴana,don har yanzu ban yi lalacewar da ɗan da na haifa zai bijire min kuma na bi ra'ayinshi ba!
Ban taɓa nadamar nuna miki soyayya,na fifita ki a cikin yarana ba sai yanzu,butulu!
To kema lokaci yayi da dole kiyi min biyayya, idan ba haka ba sai dai ki sauya uba!!"a tsananin razane ta ɗago tana kallon mahaifin nata,a hankali ta furta "Abba!"
Cikin fushi yace "Eh!na san kinji abinda nace!na gama magana!!"yana kai wa nan ya juya ya fice daga ɗakin ranshi yana wani irin ɓaci
✨✨🌟✨✨
SABUWAR GANDU,KANO STATE, NIGERIA
Sauri-sauri take ƙoƙarin kammala shirya wa,duk da lokacin gaba ɗaya bai wuce shida na safiya ba,amma kuma dole ta yi sauri saboda tafiyar da ke gaban su ta ɗalibai ta ƙaro ilmi(excursion),sanye take da farar riga shirt da straight skirt dark blue,ɗan baby hijab ɗin ta fari yayi matuƙar yi mata kyau,ta ƙarasa sanya farar socks ɗin ta ƙal,da baƙin takalmi ,ta ɗauki ƴar madaidaiciyar side bag ɗin ta mai ɗauke da wayar ta da sauran abubuwan buƙatar ta,ta ƙarasa ta shiga kitchen ta ɗauko lunch box ɗin ta da ta shirya abincin da zata tafi da shi,ta ƙarasa ƙofar ɗakin mahaifiyar ta tana faɗin
To Ammi!mu dai zamu tafi,na san suna can suna jira na, a yi mana addu'a,sai mun dawo"maman ta ɗan ɗago kaɗan daga azkar da take yi ta ce"to Allah ya kiyaye,ya bada Sa'a "
Ta amsa da"Ameen "gami da juya wa zuwa in da ƙannen ta da za su raka ta Al'amin da Haidar ke tsaye suna jiran ta,da hannu ta yi musu alama,suka rufa mata baya
Basu yi doguwar tafiya ba ma suka haɗu da Amina, Amina ƙawar ta ce,ajin su ɗaya,don haka su Al'amin suka juya suka koma gida,ita kuma suka jera da Amina suna tafiya cikin farin ciki
Amina ta kalle ta da murmushi a fuskar ta ta ce"ANEESA da fa zan bi ta gidan ku mu tafi tare,sai na yi tunanin ko kin wuce ne,don na san ki da sabga Sharp sharp,ba kya ɓata lokaci "
Ƴar dariya Aneesa ta yi ta ce"wannan karon kam na so na makara,don sanyin nan da ake fama ya so ya hana ni sakewa,kin san bana shiri da sanyi,sai da na samu na yi wanka da ruwa mai zafi na ji daidai, sannan na yi girkin abinda zan ci"ta ƙarashe ta na ɗan murmushi,don murmushi ɗabi'ar Aneesa ce,duk da cewa itama idan miskilanci ya motsa mata ko magana sai ta ga damar yi ballantana fara'a
Amina ta ce"gaskiya kam!ni kam Mamie ta yi min komai ita da masu aikin ta,da na tashi Sallah kawai na yi,na yi brush,na yi wanka sannan na shirya na biyo hanya"
Murmushi Aneesa ta ƙara yi ta ce"ni kam inaaaa!da kai na na yi komai,kin san Ammi na bata son masu aiki babu ma a gidan mu"Amina ta ce"ai kina ƙoƙari sosai Aneesa,ni fa bana iya aiki ko da rabin aikin da kike yi"Aneesa ta ware oily eyes ɗin ta ta kalle ta tace"bai kama ki bane,da ya kama ki da za ki iya Meena"
"Ai Allah ya san ba zan iya ba ma shi yasa bai kama ni ba"Meena ta bata amsa, Aneesa ta yi dariya sosai,ta ce"ki bari ki yi aure tukunna,kafin ki faɗi haka"Meena ta yi dariya ta ce"kema kin san babu yadda za'a yi na iya auren wanda ba zai ɗaukar min mai aiki ba,for God sake bana son wahala"haka suka ci gaba da suna taka wa har suka isa bakin katafaren gate ɗin tsadaddiyar private school ɗin ta su
San da suka isa sun tarar ana tantance waɗanda suka biya don tafiya,don haka suma suka shiga sahu
A dogayen motocin makarantar zasu yi tafiyar, Aneesa ta samu waje a can baya jikin window kamar yadda take so,ta Ciro wayar ta ta soma daddannawa
Ƴan seconds kaɗan da kara wayar a kunnen ta ta soma magana cikin raha da farin ciki
"To Abba na na kai na abin alfahari na!gamu mun gama shirya wa tsaf, motar mu zata ɗaga zuwa yankari game reserve "
Ƴar dariya ta yi,da alamu wanda ta ke wayar da ita ne ya yi abinda ya bata dariya ta ce"ameen Abba,amma ai dai duk runtsi ina son gari na,farin cikin zuwa sabon waje ne kawai ba wani abu ba"ta ɗan yi shiru alamar saurare sannan ta sake faɗaɗa murmushin ta har ƴar wushiryar da ke tsakanin jerarrun haƙoran Tata fito fes sannan ta furta
"Ameen Abba!amma ni kam aure ba yanzu ba,ka manta sai na gama degree da service na fara masters zaka aurar da ni?kuma fa ni na fi son zama kusa da ku"ta ƙara yin shiru kafin ta ce"to Abba,idan mu ka isa zan kira ka,yanzu zamu ta shi"suka ajiye wayar tana ta murmushi, idanun ta na kan su Meena da wata ƙawar su zee Sardauna da ke zaune a gaba gaban motar
Ba'a fi ƙarin mintuna biyu ba motar su ta tashi zuwa Bauchin Yakubu,addu'o'i a bakin Aneesa Kamar yadda ya zame mata sabo
Awanni ƙalilan ya ɗauke su zuwa Bauchi saboda nagartar motocin su,zuwa yankari game reserve itace tafiya ta ƙarshe da Aneesa zata yi a matsayin ta na ɗalibar secondary, kasancewar suna daf da fara rubuta SSCE ne,sai dai ita ce tafiya mafi soyuwa a gare ta,kuma ɗaya daga cikin tafiye-tafiyen da suka nishaɗantar da ita sosai
Ba su dawo gida ba sai daf da maghriba,ta cire uniform ɗin ta ta ɗaura towel ta shiga wanka,ta ɗauro alwala,ta na fitowa ana kiran sallah,don haka ta na shiga ɗaki hijabin ta har ƙasa ta sanya ta tayar da Sallah,sannan ta yi Sallah,ta yi azkar ɗin ta ta miƙe
A gurguje ta shirya cikin wata rigar sanyi fara da dogon wando baƙi,ta sanya hula baƙa akan ta,wannan ita ce shigar da ta fi ƙauna a rayuwar ta,tana matuƙar son riga da wando, musamman kalar fari da baƙi,gashi sam bata da ƙyuwar wanki,don sam bata iya maimaita kaya,ko sun yi datti ko ba su yi ba, saboda yawan faɗan ammin ta na tara kayan wanki sai ta daina bayar da kayan a wanke mata,sai dai ta wanke da kan ta,tun tana shan wahalar wankin har ta saba
Gashi ammin ta ta tsani shigar riga da wandon da ta zame mata jiki,ta yi faɗan har ta gaji, Aneesa ta saba baza ta iya dainawa ba
Kai tsaye ɗakin Ammi ta nufa bayan ta fito daga ɗakin ta,ta yi sallama tana ɗaga labulen ɗakin,Ammi ta ɗago da kan ta tana amsawa, Aneesa ta shiga tana faɗin "kai! gaskiya yau na gaji,rabon da na yi doguwar tafiya irin haka ai ba zan iya tunawa ba"
Ammi da ke kallon ta ta watsa mata harara,a maimakon ta bata amsa sai ta fara ƙorafi
"Wai ke Aneesa wannan shigar banzar ba zaki daina yi min a gida na ba ko?da alamu ina ga sai na kwashe kayan na ƙona,idan kika rasa na sakawa ina ga sai kin fi mayar da kai kina shigar mutunci"
Murmushi Aneesa ta yi tana faɗin "I'm sorry Ammi na ,na ga ma da alamu yau ko kewa ta bakiyi ba,ko tayin abinci ma fa baki yi min ba"tayi maganar da raha sosai,kamar ba faɗa mama take yi mata ba
Mama tayi mata banza ta cigaba da ninkin kayan da take yi,ba ɗabi'ar Aneesa bace yawan magana a inda aka share ta,bugu da ƙari Aneesa tafi shaƙuwa da mahaifinta akan mahaifiyar ta kasancewar ta ƴar su ta fari
Aneesa da iyayen ta major Ahmad da sister A'isha suna zaune cikin rufin asirin Allah, Aneesa ce ƴar su ta farko,sai Al'amin da ke biye mata,sai Muhsin,sai Sauban sai kuma auta Hafeez
Duk da kasancewar Aneesa ita kaɗai ce mace a cikin ƴan uwan nata hakan bai hana ta jan ƙannen nata a jiki ba,tana matuƙar ƙaunar su sosai,sune abokan hirar ta,kuma aminan ta a koda yaushe
A yanzu shekarun ta na haihuwa sha bakwai ne, Al'amin yana da sha huɗu,sai Muhsin sha biyu, Sauban tara,sai auta Hafeez mai shekaru biyar
Ahmad soja ne mai muƙamin Major, A'isha kuma midwife ce,itama ta na nata aikin a asibitin Muhammad Abdullahi Wase,su ɗin ba wasu masu wadata bane,suna rayuwar su dai cikin farin ciki da rufin asiri,kafin wata ƘADDARA ta afko rayuwar su
Wacce iriyar ƙaddara ce? menene SABABI na wannan ƙaddarar?ku biyo NUSY BEE a cikin littafin KADDARAR MU CE don jin yadda take kasancewa
#Nusy_bee