KADDARARMU CE....2
by @nusybee143
🫰ƘADDARAR MU CE....👌
(ta zo a haka)
❤️*Young talented writers association YOTA*❤️
*Paid book*
✍️Nusy bee
Page 2
*TALLA!TALLA!!TALLA!!
*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.
*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL,****,
***
** **
Ammi ce a tsaye a ɗakin ta ta na yunƙurin kiran Abba(major Ahmad)bayan fitar Aneesa daga ɗakin,sai dai baya ɗagawa,abin ya ba ta mamaki,ta koma bakin gado ta zauna ta na tunanin abinda zai hana Abba ɗaga waya,don sam ignoring kira na ɗabi'ar shi bace
Ƙwalawa Aneesa kira ta yi,wadda take tsakar gida ta na ɗan gudanar da aikace-aikacen da ba za'a rasa ba,babu ɓata lokaci Aneesa ta shigo ɗakin ta na faɗin "ga ni Ammi"
Kallon Aneesa ta yi,cikin sanyin murya tace "Aneesa kunyi waya da abban ku kuwa?"
Shiru Aneesa ta yi da farko,kafin ta ce"akwai wata matsalar ne?"zuciyar ta kamar ta fito saboda fargabar amsar da za ta fito daga bakin Ammin
Ammi ta zauna a gefen gado, cikin sanyin murya ta ce"na kira shi sau wajen uku bai ɗaga ba"Aneesa ta sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya jin ba abinda take tunani bane,a sanyaye ta ce"wataƙila ko yana da wani uzurin ne, maybe idan ya gani zai kira ki"Ammi bata sake magana ba,itama ta juya ta yi hanzarin ficewa zuwa ɗakin ta
A gefen gadon ta ta zauna tana kallon wayar ta da ke sanye a chajin socket ɗin da ke gefen gadon ta,a sanyaye ta janyo wayar,ta ciro wayar daga chaji tayi dialing number ɗin Abba
Bugu biyu aka ɗaga,amma maimakon Muryar Abba sai ta ji muryar wata mace,ta na faɗin
"Hello! wane ne?"
Bata yi mamaki ba,amma ran ta ya ɓaci,ta yi shiru ta na tunanin amsar da za ta bawa wannan baiwar Allah da ta ɗaga mata waya
Ji ta yi an ja tsaki an kashe wayar,ta bi wayar da kallo ran ta a ɓace,a wani ɓangare na zuciyar ta fargaba take ji na yadda Ammi za ta ji idan wannan ɓoyayyen abu ya fito fili
DODAN BARRACK,IKOYI, LAGOS STATE, NIGERIA
A hankali ta sake ɗaga wayar ta na kallon number ɗin da aka yi saving da suna na musamman 'luvly daughter', wani abu ya tsaya mata a maƙoshi,take idanun ta suka sauya kala,cikin ɓacin rai ta furta"mu je zuwa,sai na raba ki da mutumin da kike gadara dashi,sai na yi maganin girman kan ki yarinya!"
Da sauri ta mayar da wayar jikin chaji ta koma ta kwanta kamar ba ita ba har da lumshe idanu ta na jin sanda Ahmad ya shigo ɗakin da sallama,amma sai ta yi kamar bacci take yi
Kai tsaye inda wayar shi take ya nufa,bayan ƴan seconds ta ji yana faɗin "MAIMUNA me ya haɗa ki da waya ta?"
Banza ta yi masa,ya sake cewa "na gaya miki bana son ki rinƙa taɓa min waya ta,ko so kike ki haɗa ni da iyalina ne?"
Buɗe idanu ta yi tana yi masa wani kallon rainin wayo ta ce"iyalin ka?iyalin ka ko?su iyali manya!wato ma gaya min kake yi iyalin ka ce ko?ita kaɗai ce ma iyalin naka,mu kuma bola ko?
Ahmad ya lumshe idanu ya buɗe ya ce "baki fahmice ni ba maimuna
Ya kamata ki san cewa har zuwa yanzu mata ta bata san na aure ki ba,so nake na koma idan ya so sai na gaya mata a tsanake,don bana son damuwa"Maimuna ta taɓe baki tana ɗauke kai ta ce"Allah ya kyauta!Ni da na san ba namijin gaske zan aura ba ai da ban fara kawo kai na ba,ace wai namiji ya na tsoron matar shi"
Ahmad ya ɗan ji zafin maganar,amma sai ya shanye,don babu yadda ya iya da ita,ya ce" ba tsoron ta nake ji ba,zaman lafiya nake buƙata a cikin ahali na ne"Maimuna bata sake magana ba,sai janyo hularta da ta yi ta rufe ɗan gajeren gashin ta,ta miƙe ta fice daga ɗakin
Bayan isha'i ta na zaune a ɗakin ta,lokacin Ahmad baya nan bai kai ga shigowa gidan ba,wayarta ce a hannun ta ta na daddannawa,kafin ta kara a kunnenta,ƴan seconds ƙalilan aka yi magana daga can
"Allah ya ja da ran uwar ɗaki na!"
Yatsina fuska ta yi,cikin isa ta ce"Farida kina son yi min wasa da aiki ko?"
Murmushi mai sauti fareeda ta yi tace"haba uwar ɗaki na!kema kin san kin fi ƙarfin na yi Miki wasa da aiki,yanzu haka ma shirin da nake yi na kammala tsaf,gobe war haka na ɗauki hanyar kwara,in sha Allahu nan da kwana uku komai ya gama hawa kan network "
Maimuna ta ɗan ja fasali cikin izza ta ce"na ji wannan,ya batun number ɗin da na ba ki don ki kira?ina buƙatar result da wuri"
Fareeda ta ce"ina jiran sai na dawo daga kwara ne,amma ke ya kika ce?"
Maimuna ta ja tsaki ta ce"ce miki nayi dama ki jira sai kin dawo daga kwara?Kinga idan baza kiyi ba ki gaya min,sai ki dawo min da kuɗina in nemi wata"
Fareeda ta ja tsaki ciki ciki ta ce"Allah ya huci zuciyar uwar ɗaki na,zan kira in sha Allahu "Maimuna ta ja tsaki ta kashe wayar
SABUWAR GANDU, KANO STATE, NIGERIA
Shigowar ta kenan gida,a hankali take tafiya,ƙirjinta ya buga jin kamar muryar Ammi tana magana cikin kuka,kanta ya juya,da sauri ta nufi ɗakin har tana cin tuntuɓe jin abinda Ammi take cewa
"Yanzu abinda Abban Aneesa zai yi min kenan?ni ya barni a nan ya je can yana bin matan banza?wanne irin wulaƙanci ne zan kira shi a waya ya bawa mace ta ɗaga tana ƙoƙarin gaya min magana?innalillahi wa inna ilayhi rajiun!"
Da gudu Aneesa ta faɗa dakin Ammi, jikinta na rawa tana shiga ta zube a gaban Ammi da ke ta kuka cikin tashin hankali tana sambatu,a gigice ta ce"Ammi Abba fa aure yayi!"
Ɗif kukan Ammi ya ɗauke,tuni ta fara ganin ganin Aneesa bibbiyu,a hankali ta fizgo kalmar inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!"
Cikin kuka Aneesa ta ce"don Allah Ammi ki yi haƙuri ki bi komai a sannu,ban san me yasa Abba bai gaya miki ba,amma Abba yayi aure kusan watanni uku baya"
Ammi ta fashe da kuka sosai ta ce"amma wane laifi nayi wa abbanku da zai yi min irin wannan hukuncin?meyasa zai yi min haka? Allah shine shaidata duk yadda ya so haka nake zuwar masa,kuma ban taɓa yunƙurin hana shi ƙarin aure ba,yanzu da Abinda zai saka min kenan?shikenan!!"
Aneesa ta rungume mahaifiyarta cikin kuka tana faɗin"don Allah Ammi kiyi haƙuri,komai yayi farko zai yi ƙarshe,ki daina kukan kan,kar hankalin su Al'amin ya dawo kanmu don Allah,kiyi ta maimaita hasbunallahu wa ni'imal wakeel Ammi "cikin dakiya da zubar hawaye Ammi take maimaita hasbunallahu wa ni'imal wakeel, Aneesa ta kwanta a jikin kafaɗarta itama tana zubar da nata hawayen
Washegari wajen ƙarfe sha biyu na rana Abba (Ahmad)ya diro gidan kamar an jefo shi,babu kowa a gidan sai Ammi,dukka yaran suna makaranta,har Aneesa, Ammi ta ɗaga kai ta kalle shi,ta yi saurin ɗauke kai hawaye masu zafi suna zubo mata
Da sauri Abba ya ƙaraso gabanta ya rissina yana faɗin"don Allah A'isha ki yi haƙuri ki saurare ni,wallahi ba da niyya na yi hakan ba,don Allah ki saurari abinda zan faɗa, Please maman Aneesa!"
"Me za ka gaya min Ahmad?me zan kira abinda ka yi min?wannan shine sakamakon irin zaman da muka yi da kai shekaru kusan ashirin tare?kana ganin ka kyauta min kenan?"
"Na san ban kyauta miki ba A'isha,amma ya kamata ki saurare ni Please, wallahi ba da niyya na yi auren ba, Allah ne ya kawo shi ban yi tsammani ba,don Allah ki yi haƙuri mu fahimci juna don Allah "
A'isha ta ɗan yatsina fuska tana goge ragowar hawayen idanunta ta ɗauke kai ta ce"ko ma me zaka gaya min ka barshi don bashi da amfani,aure ne ka riga ka yi, Allah ya sanya alkhairi,ya rage naka ka ji tsoron Allah ka kamanta adalci,ya rage naka ka cigaba da zalunci da ƙumbiya ƙumbiya, ni dai na kai ka kara wajen Allah muddin ka zalunce ni "tana gama faɗin hakan ta miƙe a zafafe ta nufi ɗakinta ta shige ta rufo ƙofar
Yin duniya Major Ahmad yayi A'isha ta buɗe ƙofar taƙi,ko magana bata yi ba ma,ta yi masa banza,ganin bazata buɗe ba ya tilasta masa ciro wayar shi ya daddanna ya aika kira
Maganar mintuna biyar yayi cikin damuwa,sannan ya kashe wayar,ya samu waje a parlourn ya zauna yana tunanin mafita
Da kamar one hour wayarshi ta yi ƙara,a sanyaye ya ɗaga,ƴan mintuna yayi magana sannan ya miƙe ya nufi bakin gate
Tare suka shigo da Alhaji Nasir, Alhaji Nasir yayan A'isha ne uwa ɗaya uba ɗaya
A parlour suka zauna, Alhaji Nasir ya ƙwala kiran A'isha,ta buɗe kofar ta fito ba tare da ta amsa ba
Suka daga kai suna kallonta,sai goge hawayen idanunta take yi da gefen hijabinta,ta samu gefen kujera ta zauna kanta a ƙasa,cikin sanyin murya tace
"Sannu da zuwa yaya!"ta faɗa kanta a ƙasa tana goge hawayenta da gefen hijabinta
"Yawwa sannu A'isha,na same ku lafiya?"ya faɗa yana kallonta cikin tausayawa
Ta ɗago ba tare da ta kalle shi ba ta ce"lafiya ƙalau alhamdulillahi"
Gyara zamanshi yayi ya ce"to madalla!
A'isha komai na duniya ɗan haƙuri ne,a hankali ake bin shi sai a ci ribar rayuwa,duk abinda haƙuri bai baka ba rashin shi ma na zai baka ba, Allah ya nufa sai mai gidanki ya ƙara aure ko da saninki ko babu saninki,daga gare ki abinda ake so shine kiyi haƙuri,ki karɓa sannan ki godewa Allah,idan muka bi komai a sannu komai zai wuce ya zamo tarihi,watan watarana ma ko tunawa ba zamu samu zarafin yi ba"
A'isha ta sauke ajiyar zuciya kanta a ƙasa ta ce"yaya Ni bana jayayya da hukuncin Allah,ko ya kara aure ko bai ƙara ba na san duka na Allah ne,amma yaya ya zai shigo da wulaƙanci cikin lamarin?last week sai da whole week ɗin ya wuce ko sau ɗaya bai kira ni ya ji lafiyarmu ni da yara ba,idan na kira shi kuma bana samunshi,jiya kuma na kira shi ya bata ta ɗaga min waya don ya gwada mata bani da daraja a wajenshi,tun kusan wata guda baya tunda ya turo kuɗin monthly shopping ko sisi bata sake shiga tsakani na dashi ba,bayan bayan nan Muhsin yayi jinya amma babu yadda banyi ba ƙarshe dole na kai shi asibiti da kaina
School fees ɗin yara kuwa ina ga na Aneesa kaɗai ya biya,amma ragowar duka Ni na biya da kaina,da na kira shi nayi masa complain sai ya hau ni da faɗa
Yaya dama haka ƙarin auren yake?daga faruwa sai wulaƙanci da rashin adalci ya fara shiga ciki?"
Ba iyaka Major Ahmad ba hatta Alhaji Nasir jikinshi yayi sanyi,a hankali ya girgiza kai,cikin sanyin murya ya ce"hakane,amma ina mai ba ki haƙuri tare da tunatar dake,ƙarin auren Sunnah ne,don haka babu laifi idan yayi, ki godewa Allah ma kina da sana'a,ya barki kina fita aikin ki,akwai matan da babu aikin,babu sana'ar sannan kuma suna zaune a gidajen mazajensu suna fuskantar abinda yafi naki,kuma ƙalau suke zaune,ba wai fata nayi miki ba,ina son don Allah ki yi haƙuri "sannan ya waiga ga Ahmad,cikin taushin murya ya ce
"Officer! Allah ya ƙara maka zaman lafiya da matanka,ka kasance mai adalci a tsakaninsu,kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya faɗa,ba zamu so mu ganka cikin waɗanda Allah ya tsinewa ba,ba zamu so mu ganka cikin waɗanda zasu tashi da shanyayyen ɓarin jiki ba,don haka ka ji tsoron Allah ka daidaita da matarka,a yawancin lokuta zaman lafiya yana fatawa ne daga mu maza,idan muka gaza komai zai iya faruwa
Cike da gamsuwa Ahmad ya jinjina kai, Alhaji Nasir ya ƙara yi musu nasiha sosai,kafin yayi musu sallama, Major ya raka shi har bakin gate yayi masa godiya ya hau motarshi ya tafi
Gida ya dawo ya cigaba da bawa A'isha haƙuri, murmushi kawai tayi,ta kalle shi ta ce"Allah ya sanya alkhairi,ni ban damu da aurenka ba,amma ya kamata kayi abinda zaka haɗu da Allah lafiya,kai musulmi ne Abban Aneesa"
Murmushi ya yi,ya bayar da zancen da faɗin "ba ki damu da aure na ba?da gaske kike kuwa?Ni dai na san matar nan tawa tana so na,kuma idan da so akwai kishi,anya kuwa zan yarda?"A'isha ta jefa masa hararar wasa ta ɗauke kai,yayi murmushi ya ƙarasa kusa da ita,yayi kissing goshinta batare da ta ankara ba,ta miƙe sa sauri zata bar wajen,ya janyo ta ta faɗo jikinshi,dukkan su suna dariya cike da so da kulawar juna kamar ba sune suka ajiye su Aneesa ba
(WASA FARIN GIRKI!)
Bahaushe yace WASA FARIN GIRKI!ko nace WUYAR AIKI BA'A FARA BA!!wannan littafin na KADDARAR MU CE ya zo da wasu cukurkuɗaɗɗun al'amura,ya zo da wani irin rikitaccen salo,ku kasance tare da ni NUSY BEE don samun dukkan amsoshinku 🤗
#Nusy_bee