ƘADDARARMU CE TA ZO A HAKA

KADDARAMU CE....3

by @nusybee143

🫰 ƘADDARAR MU CE....👌
(Ta zo a haka)




✍️ Nusy bee 
❤️ *Young talented writers association YOTA*❤️ 


Page 3


My TikTok account 👇


***



My Instagram account 👇

***


My arewa pen link 👇


https://arewapen.com/u/nusybee143


*TALLA!TALLA!!TALLA!!*

*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.


*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL,****, 
***

ASOKORO,ABUJA, NIGERIA 


Matashiya ce kyakkyawa,a kallo ɗaya mutum zai tabbatar wa kanshi ita ɗin ruwa biyu ce(halfcast)sanye take da Black luxury abaya,ta yane kanta da mayafin rigar, fuskarta sanye da wani baƙin spec da ya haska farar fuskarta,a hankali ta gama daidaita parking motarta ƙirar land cruiser,sai da ta ɓata kusan mintuna biyar tana kalle kallen compound ɗin gidan nasu a yatsine sannan ta buɗe murfin motar ta fito,riƙe da wayarta ƙirar iphone 15 pro max tana daddannawa 

"Barka da dawowa ranki ya daɗe!"ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ya furta yana rissinawa gami da washe baki don neman shiga 

Fuska a yatsine ta kalle shi,a maimakon ta amsa masa sai ta ce"wanene wanda yake da alhakin share compound ɗin nan?"

Har yana ƙara rissinawa ya ce"Shu'aibu ne ranki ya daɗe"

"Shu'aibu!then me ya hana shi share compound ɗin yau?ko ya gaji da aikin shi ne?ko don kwana biyu an ga bana nan shiyasa kowa yake abinda ya ga dama?ga flowers can ba'a rage su ba,ga compound ba'a share ba, I can see motar Ammina ma ƙura ta yi yawa babu wanki,what you guys do you mean by all this?"

Ƙara ƙasa da kanshi ya yi yana mai nadamar yi mata magana da niyyar neman shiga, saboda kowa ya san yadda take son a girmamata,amma sai ya ce cikin kwantar da murya 

"A yi haƙuri ranki ya daɗe, in sha Allahu zan yi musu magana kuma zasu gyara"

"Better for you!hour ɗaya na bayar kar na zo na samu wani abu kamar datti a compound ɗin nan, otherwise mutum yayi ta aikinshi,ka tabbatar ka sanar da waɗanda abin ya shafa"ya sake rissinawa ya ce"an gama ranki ya daɗe"bata sake magana ba ta wuce shi ta nufi cikin gidan tana ƙoƙarin aika kira da wayarta

Kai tsaye ta kutsa kai rantsatstsen parlourn gidan ba tare da tayi wani abu wai sallama ba, Mimi da ke zaune akan ɗaya daga cikin luxury sofa dake parlourn ta taso da gudu ta rungume ta tana faɗin 

"Welcome welcome aunty MALIKA! I miss you so much"sai yanzu ta yi ɗan murmushi tana zare spec ɗin da ta rufe ƙwayar idanunta,ƙwayar idanun ta bayyana

Blue eyes ne da ita exactly kamar na turawan kasar Estonia ko Finland,tana murmushi ta shafa kan yarinyar tana faɗin"Mimi I miss you too,Ina Ammi?"yarinyar ta yi ɗan murmushi ta ce"Ammi ta je gidan momy Zarah,suna tattaunawa akan wasu kaya da za su fitar, aunty Malika dama the house is so boring,su aunty basa nan, Ammi ma haka,kenan kuma ba kya nan "wani murmushi Malika tayi ganin yadda Mimi take ta shagwaɓewa,itama dai da gaske ta yi kewar yarinyar,cikin kulawa ta sake rungumeta ta na faɗin"let me get my shower first,just give me thirty minutes,uhm?"murmushi Mimi ta yi ta ɗan matsa baya tana faɗin "I'm waiting for you lovely aunty"Malika ta shafi kanta tana murmushi sannan ta wuce sashenta 

Wani luxury apartment ta nufa,tun daga staircase ɗin har har zuwa tiles,fitilun sashen duka abin kallo ne, ballantana kuma tsadaddun sofa da suka mamaye parlourn,babu wata hayaniya sosai a parlourn,amma an narka masa kuɗi sosai

A yatsine take bin ko'ina da kallo don tabbatar da an gyara ko'ina?ganin babu wata matsala,ko'ina a share yake, asalima ƙamshin insence sticks masu asalin tsada da ƙamshi ne yake tashi,ta yatsina fuska tana cire mayafin kanta,dogon jan gashinta ya bayyana,ya sauka har gadon bayanta,ta miƙe kai tsaye izuwa tangamemen bedroom ɗinta 

Ashe parlournta ba komai bane akan bedroom,hatta da gadonta ƙirar jado steel style gold bed an lulluɓe shi da wani tsadadden zanin gado,hatta da best side lamp ɗinta abar kallo ce,ba'a maganar closet ɗinta da shoe rack ɗinta da ke gefe,shi kanshi rack ɗin abin kallo ne

Kan gado ta zubar da wayarta da mayafinta,kai tsaye ta faɗa toilet,ta samu aƙalla mintuna talatin kafin ta fito,sanye da bathrobe kanta naɗe da madaidacin towel 

A cikin ƴan mintuna ta yi drying kanta ta shirya cikin wasu riga da wando masu tsada,ta ɗaure dogon gashinta da wani ɗan ƙaramin ribbon ta sake shi baya ta sauko izuwa parlourn Ammi inda Mimi ke zaune har yanzu tana karatu

A stairs ɗin ƙarshe ta yi tsaye tana kallon waɗanda suka shigo fuskarta babu yabo babu fallasa,ƴan mata ne su biyu,sun yi kyau sosai cikin English wears da suka yi musu matuƙar kyau,kusan a tare suka furta

"Maleeka!You are welcome!!!"

Ɗan yatsina fuska ta yi tana shafa brown girarta kafin tayi magana kamar an tilasta ta

"You are welcome too"daga haka ta ƙarasa sauka daga kan stairs ɗin ta nufi dinning area inda aka shirya mata abincinta ba tare da ta sake kallonsu ba

Kallon juna suka yi,ɗaya daga cikinsu ta nufi inda Maleeka take ta zauna tana cigaba da danna wayarta,ta fara serving ɗinta tana faɗin "kin san ba iya serving kanki kika yi ba,amma kamar wata yarinya sai jin zauna kina wani nuƙu-nuƙu"ko kallonta Maleeka bata yi ba ta cigaba da abinda take yi, budurwar bata damu ba ta cigaba da serving ɗinta 

Tana gamawa ta turawa Maleeka plate ɗin,ciki-ciki ta ce"thanks!"ta fara cin abincinta,budurwar ma ta ja plate ta yi serving kanta tana ɗan murmushi ta ce"babu yadda ban yi mu shiga restores ba amma uwar taurin kan nan ta ƙi yarda,gashi na dawo a yunwace sosai"ita dai Maleeka ko kallonta bata sake yi ba

Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu, ba'a jin ƙarar komai sai na plates da cokula,kafin Maleeka ta yi breaking silence ɗin ta ce 

"Maleeka when are we leaving this annoying country ne?"Maleeka ta ɗaga kai fuska a ɗan ɗaure ta kalle ta,a hankali tace"for where?"

"Like US haka,ko Cuba,ko dai Canada,ko Luxemburg ko......"da sauri ta gintse bakinta tana kallon Maleeka da take aika mata da wani mugun kallo,a nutse kuma cikin isa ta ce"tell me the truth LATEEFA!are you here to talk about someone?"

Da sauri Lateefa ta girgiza kai tana faɗin"not at all,ni ba haka nake nufi ba, I'm sorry if I offended you in anyway "Maleeka bata kula ta ba ta cigaba da cin abincinta a nutse,itama Lateefa cigaba da cin abincinta ta yi tana satar kallonta 

Ƴan seconds Lateefa ta kasa jurewa ta kalli Maleeka ta ce"but I don't understand the reason da za ki ce bakya son zancen......"

"Lateefa!get out of my side!!leave this place please!!!"a razane Lateefa take kallon Maleeka da mamakin haukan da takeyi mata, Maleeka ta miƙe tsaye jikinta yana tsuma,ta nunawa Lateefa hanya ta ce"leave this place, don't let me repeat myself!!!"babu musu Lateefa ta miƙe jikinta na rawa ta wuce ɗakin ɗaya matashiyar da already ta daɗe da shigewa ma, Maleeka ta raka ta da dogon tsaki kafin ta cigaba da cin abincinta a nutse tana danna wayarta 


SABUWAR GANDU, KANO STATE, NIGERIA 




Kwanan Major Ahmad biyu a gida ya koma bakin aikinshi, ya ji matuƙar daɗin ganin yaran nashi basu chanja mata ba,itama Ammi da ta fusata yanzu ta sauko tun zuwan Alhaji Nasir 

Yau kwana biyu da tafiyar Abba, Aneesa tana kwance akan gadonta tana chatting da ƙawayenta na makaranta game da WAEC ɗin da ta tunkaro su nan da ɗan lokaci,shirye shirye suke yi ka'in da na'in don ganin sun rubuta jarrabawarsu ba tare da wata matsala ba

Wayar Ammi da ke gefenta ce ta fara ƙara,ta ɗauki wayar ta fice daga ɗakin don kai wa Ammi da ke kitchen tana girki 

Miƙawa Ammi wayar ta yi ta zauna tana ƙoƙarin cigaba da haɗa miyar da Ammin takeyi,Ammi kuma ta ɗaga wayar tana sallama cikin sanyin muryarta

Daga ɗaya ɓangaren aka amsa cikin karsashi"waalaykis Salam maman Aneesa mun wuni lafiya?ya yaran kuma?

Ammi ta ɗan ja numfashi ta ce"lafiya ƙalau,yaran alhamdulillahi kowa lafiya,sai dai ban gane mai magana ba"

Matar ya ɗan ja numfashi,sannan ta ce "baki sanni ba ma maman Aneesa,ni matar abokin mijinki ne,na kira ki ne kawai don batun abokiyar zamanki"gaban Ammi ya buga,amma ta dake ta ce"wani abun ya faru kuma?"

"A'a babu abinda ya garu,kawai dai zan baki shawara ne da kula da abokiyar zamanki,ko na ce kiyi hankali da ita,don babu alamun mutuniyar kirki ce "

A hankali Ammi ta koma ta zauna akan kujerar da ta tashi, Aneesa dai tana jin su bata saka musu baki ba,matar ta cigaba da faɗin 

"Mutuniyar kawai ce,na ji an ce gidansu maneman malamai ne,sannan idan suka shiga gida sai sun raba mutum da matarshi,ko dai su fitar da ita daga gidan ko su mayar da ita hoto,don haka ya kamata ki zage dantse,abin babu daɗi ke da gidanki wata ta mallake miki gida"banda inna lillahi wa inna ilayhi rajiun babu abinda Ammi take maimaitawa a ranta,da ƙyar ta iya faɗin"ta Allah ba tata ba,in sha Allahu lafiya ƙalau zamu rabu da mijina "

"To Allah ya sa,don an ce idan suka auri mutum akwai su da saka mutum yayi ta musu hidima,amma iyalinshi babu abinda suke gani sai wahala,idan ma ba'a raba su ba

Cikin karayar zuciya Ammi ta ce"gaskiya ne,sai dai....."bata samu zarafin ƙarasawa ba ta ji Aneesa ta karɓe wayar,cikin azama ta kashe kiran ta saka wayar a Flight mode fuskarta a haɗe 

Cikin faɗa Ammi ta ce"ba Ni wayata!wanne kalar wulaƙanci ne zai sa ina waya za ki amshe min waya?ko sai salon raini ne kika samo kika zo za ki gwada min?"

Ran Aneesa a ɓace ta ce"Ammi kema wani lokacin duk da ke wallahi,ya mutum zai kira ki ya yi ta tsara miki magana akan abbanmu amma ki tsaya kina saurarenshi?har tana gaya miki wai ki nemi taimakon malamai amma kika cigaba da biye mata?Ammi kar wata da baki sani ba ta yi nasara akan ki da iymaninki,ƙila ma haɗa baki suka yi ta zo tana yi Miki Wannan maganar kina saurarenta,don....."

"Ba ni wayata ko na mare ki Aneesa!ina ruwanki da maganata da har kike saka min baki?dalla fita ki bani waje"babu musu Aneesa ta miƙa mata wayar ta fice daga kitchen ɗin ranta a ɗan ɓace,tana jin Ammin tata tana cigaba da faɗa amma bata ce komai ba ta koma ɗakinta ta cigaba da kwanciya zuciyarta a ɓace



QUEBEC CITY, MONTREAL,CANADA



Ƙaton luxury room ne wanda ya ƙunshi abubuwan more rayuwa dabam dabam,kama daga kan gadon zuwa cupboard da sauran kayan more rayuwa ja ɗan adam,ɗakin ya yi shiru tamkar babu wata halitta mai rai a cikin ɗakin

Sai dai akan ƙaton luxury bed da ke ɗakin wani matashi ne a kwance ya lulluɓa da duvet yana ta shan baccinshi,ɗakin ya yi asalin shiru baka jin ƙarar komai sai na AC 

Daidai lokacin da tsadadden agogon ɗakin yake buga ƙarfe takwas da mintuna sha biyar daidai na safe wayarshi ƙirar latest Samsung ta ɗauki tsuwwa,a hankali ya buɗe idanunshi waɗanda ba su da maraba da na Maleeka,sai dai a fuska ba sa kama,ta fishi hasken fata,sannan kuma kamannin fuskarsu ba ɗaya bane,sai dai shima kyakkyawa ne sosai

A hankali ya zauna a kan gadon yana jan tsaki,yana kallon wayar ta katse,sannan ya koma ya kwanta 

Yana kwanciya wayar ta sake ɗaukan tsuwwa,ɗan gajeren tsaki ya sake ja sannan ya janyo wayar a fusace ya ɗaga, ba tare da ya damu da kallon mai kiran ba ya fara sura masifa 

"Hello Rachel!how many times do you want me to warn you about calling me in this early morning?are you out of your sense? or do I have something to do with your fucking call?"

Daga can ɓangaren Rachel kamar zata yi kuka take faɗin"I'm sorry love! I know I can't do without you,you are everything to me,I can't sleep last night just because you are angry with me, please baby!"

Tsaki mai ƙarfi ya ja,a gadarance ya ce"then, don't call me again until I call you back,for now I'm doing something important,I bet for now you know I'm more than important to you,I can live without you,and you can't do without me,so respect yourself!"bai jira amsarta ba ya kashe wayarshi ya yi jifa da ita ya miƙe tsaye yana miƙa 

Giant guy ne sosai,fari ne amma ba tas ba,shima Blue eyes ne dashi,amma gashinshi baƙi ne wanda ya sha gyara sosai,daga shi sai shotneaker da singlet,kai tsaye ya nufi tangamemen banɗakin nashi da ke cikin ɗakin

Ya kai a ƙalla mintuna talatin kafin ya fito sanye da bathrobe,a nutse ya ƙarasa gaban dressing mirror ya fara gyara ƙawatacciyar sumarshi,yana cikin shafa mai wayarshi ta yi ƙara

Tsaki ya ja da ƙarfi,ya janyo wayar,ganin mai kiran bai yi tunani biyu ba ya yi rejecting ya jefar da wayar sannan ya cigaba da shirinshi a nutse ba tare da ya sake bi ta kan wayar da ta ɗauki sabon ring ba

Tsaf ya shirya cikin riga hoodie baby blue riga da wando,sai p-cap da ya ɗorawa kanshi,ya sanya wani baƙin Boot,ya saka baƙin glasses,ya ɗauki key da wayar shi ya fito daga cikin gidan

Yana shirin fita aka ɗage gate ɗin,cikin takaici yake kallon motar da take danno kai cikin gidan, lokaci guda ya sake ɗaure fuska tamau yana bin motar da mugun kallo,har zuwa lokacin da mai motar ya gama daidaita parking ya fito ya nufo India yake yana ɗan murmushin ganin yadda yake haɗe rai 

"Ya dai babban likita!duk wannan fushin ganin nawa ne?"ya faɗa yana murmushi,har double dimple ɗinshi suna bayyana a kumatunshi 

"Saif what do you want please?why kake son shiga rayuwata ne? You know that I hate disturbing ko?"

"Then so?"Saif ya faɗa yana masa kallon raini,"idan ma wata macen ka kawo kake shakkar na gani that's your own cup of tea,da har nake kiranka kake ƙin ɗaga min kira, ASHRAF!do whatever you want,but I must be by your side "yana gama magana ya tsallake Ashraf da ya bishi da kallon takaici ya shige gidan,ya yi amfani da key ɗin hannunshi, Ashraf kam bai samu zarafin magana ba,ya buɗe tsadaddiyar motarshi ya shige ya tayar ya bar gidan


#Nusy_bee